CANJIN RAYUWA CHAPTER 11 BY HALIMA A K/MASHI ,shi, ai ba ki rama ba, sannan kin shirya me za ki ce ma Hajiya? Kar ki manta dai da ta gargade ki sosai sannan aka turo mi ki shi. A fili ta ce, to me zan mishi in huce? Ta kalli wayarta, yawwa bari in kira Mina Dakingari. Bakin gadonta ta shiga, bedroom ta zauna, Mina ta daga tare da fadin Khadija Masari ya? Mimi ta ce, lafiya Dakingari, kin san mene ne? (ta ci gaba) Mom dita ce in fada miki ta dage sai wani malami ya koya min karatun islamiyya. Mina ta ce, mene ne laifi? Mimi ta ce, dan rainin wayo ne, kinga yanda ya ke son nuna min iyaka ta? Nan ta kwashe komai ta fada mata, Mina ta ce, kin san me za ki yi masa? Mimi ta ce, a'a, Mina ta ce, in Dad din ki ya dawo ki sa a kira shi, sai ki ce kina son a ware lokacin karatun ku minti talatin ko awa daya, yanda dai ki ka zaba, king ba zai taba tashi daga gurin karatun ba sai lokaci ya cika, Mimi ta ce, yawwa kin kawo shawara, kin ga sai in yi masa duk cin mutumcin da na so na tsawon lokacin, kuma dolen shi ya tsaya ya saurare ni, Mina ta ce, in kin ga zai wuce gona da iri, ki mari fuskarsa, suka sa dariya ta ce, kin san ba na son taba jikin talakawa, amma zan tsirta mishi yawu, Mina ta ce, haka ya yi. Ya ya Khalil dinki? Oshshh! kin tabo rabin rayuwata, yana lafiya, ya ya Faisal dinki? Mina ta ce, sun gama hutunsu ya koma jiya, ta ci gaba da cewa, ina mamakin irin son da kike yi wa Khalil dinki, kamar ba kitsane shi ba, Mimi ta ce, kin san me Mina? can dama ina son Khalil tun lokacin da na soma ganin shi, na ja aji na ne kawai. Mina ta ce, don Allah da gaske? Mimi ta ce, Allah kuwa, Mina ta ce, kin iya jan aji kuwa, to,shikenan in kunyi waya ki ce, ina gaida shi, Mimi ta ce, zai ji. Bayan sun yi sallama ta shiga nazarin mau'du'in wulakancin da ya kamata ta dinga yi wa wannan malami. Tara daidai lokacin cin abincin su na dare kenan, ta sauko da 'yar jar doguwar rigarta da kadan ta wuce gwiwarta, kamar kullum ta yi ado da gashin kanta, kowa ya hau kan teburin. Tuni yara sun soma ci ma, sai da ta isa kusa da mahaifinta ta gaida shi, sannan ta dawo gurin zamanta ta kalli Momi Nafisa, Mommy kin dawo? Ta ce, ai ban dade ba Mimi, Alhajin ya ce, ina ki ka je? Ta ce, gidan Hajiya Adama na je, in duba masu takalma, ta dawo daga Ingila. Mimi ta ce, kin samo mana? Ta ce, duk kina da shigen su, ke kuma na san ba ki son duk wani abin ki ya zama gama gari. Amma ta ce, wasu kayan na zuwa. Mimi ta ce, Mommy ki bar shi ma kawai, takalma sun min yawa, akwai wadanda har yau ban sa su ba. Na'ima ta ce, ‚Sis ina wadanda ki ka ce za ki ba ni? Mimi ta ce, ki tuna min da safe. Allal ya sa su yi miki. ke da katon kafar nan na ki, duka suka sa dariya. Alhaji ya, ce. Mimi, ke komai na ki. daidai aka yi maki, kuma mai kyau, kalmatta soki zuciyar momy. Nafisa tace, duk dai dan adam tara yake bai cika goma ba, yaçe, me ki ke nufi? Ta maida abin wasa. Alhaji na gani ne koyaushe sai ka wasa mamarka. cikin. dariya tayi maganar, shima cikin dariya ya ce, kin ga laifina kenan. Ya kalli Mimi, uwata ci abinci mana, ta zuba farfesun kaza ta soma ci tana yi, tana •chating, bayan sun gama ne, Alhajin ke ce ma Mimi zai yi bako ranar lahadi, ina so ayi masa tarba ta musamman, nan zamu yi diner da shi, inda zai zo da iyalansa, sai nafi yin murna. Mommy Nafisa ta ce wane ne? Ya ce, Alhaji Akilu Bala, ministan man fetur, Mimi ta kalli mahaifinta, Dad, ka samu ganawa da shi kenan, ya ce, uwata ai yanzu mun zama abokai tamkar tare muka taso. Shi ya sa na gayyace shi don ya ga iyalaina, Mimi ta ce, Dad Insha Allahu za mu tarbe su. Kiran Hajiya Sauda ya katse shi, ya daga bayan sun gaisa ta ce, ya binciki Mimi ko ta yi karatun, ya ce, ki daina damun kanki Sauda, za ta yi, sannan suka ci gaba da maganarsu, jin haka ne, bayan ya gama wayar ya mike daga kujerar ya nufi dakin shi, Mimi ta cé, amma Dad dama ina son mu yi magana a kan malamin nan. Ina son a tsaida lokacin da zan dauka, don koya min karatu, ya ce, kamar ya ya? Ta ce, Dad yau karatun minti hudu ya yi min, ya ce, Ok na gane, da safe zan neme shi mu yi magana. Ta ce, Ok Dad ni ma zan fito da wuri don a yi komai a gaba na, •ya ce, to bari in shiga ciki, ta ce tam, Dad ni ma zan koma sama ne sai da safe ya' ce, Ismail yana tsaye bakin kofar falon, tunda ya danna ba'a bude ba, kusan minti biyu, ya sake dannawa sai lokacin aka bude, daga ganinta 'yar aiki ce, kuma ba musulma ba ce, ta ce kaine Malam? Ya ce eh, nine, tace, ka shigo, a nan cikin falon ya same su dukkan su, ya kalli Alhaji cikin girmamawa ya gaida shi, sannan ya gaida Mommy Nafisa, ya ce gani Alhaji, Malam Hamisu ya ce, kana nema na. Alhaji ya nuna masa kujera za ka iya zama a kan kujera, Mimi ta kalle shi da gefen ido, a'a Dad kar ka ba shi damar zama a kan kujera, ya kalle ta, saboda me? Ta ce, Dad bai kai matsayin ba, shi mabukaci ne a gurin mu, ta kalle shi, zauna a kan kafet, ya danne zuciyarsa, babu damuwa in maganar ba mai tsawo bace zan iya tsayawa Alhaji, Alhajin ya ce, kar ka damu zauna a kan kafet din, abin ya bawa Ismail mamaki, amma sai ya zauna saboda Alhajin ne ya bukaci hakan. A ransa ya ce, lallai dama an ce karshen zamani baiwa za ta haifì uwar gijiyarta. Muryar Alhajin ta katse shi, malam wanene ma sunanka? Ya ce Ismail, Alhaji ya amshe da cewa, yawwa Ismail, Mimi ce ta bukaci ka sa lokacin da za ku dinga yin karatu, da kuma tsawon lokacin da za ku dauka gurin yin karatun. Ismail ya ce, hakan yana da kyau, wane lokaci ne ta tsaida? Alhajin ya kalle ta, uwata wane lokacin ki ka fi so ya koyar da ke? Ta dan yatsina baki, sannan ta kalli damfareren agogonsu a jikin bango kirar Dubai, ta ce, kamar sha daya sai * ya dinga zuwa don kada ya ce sai an aika a kira shi, ni bana son jira, na fi son a jira ni. Ismail ya yi dan murmushi a ransa ya" ce, son kai, amma a fili sai ya ce, to mu tashi nawa? Ta kalle'shi sama da kasa, tsawon awa daya za mu yi gurin karatun. Ismail yä kalli Alhaii, ba damuwa kullum zan zauna Karfe shadaya mu tasha sha biya kenan. Ba laliai hakan ba'ta katse shi, za ka iya zuwa misalin sha daya ya zama ban sauko ba, kai dai in ka zo shadaya daga lokacin da na sauko, daga saman na zo gurin karatu shine za'a dauki awa daya, Ismail ya yi murmushin takaici, babu laifi matsawar lokacin sallar azahar ba zai shigo ba, Alhaji ya ce, sai batun albashi, Hajiya ta ce min ka ce duk abinda aka ba ka, Ismail ya ce haka ne. Alhaji yace, a'a zai fi kyau ka fada, Ismail ya ce, Alhaji me karantarwa ladan shi yana gurin Allah, abinda za'a ba mu kyautatawa ce. Alhaji ya ce, to da kana samun dubu Hamsin a wata? Ismail ya ce; a'a gaskiya ba su kai ba, ya ce, to zan dinga ba ka dari. Da sauri Ismail ya kalle shi, sai Mimi ta fashe da dariya kudin sayan kayan kwalliya na kenan fa, ta kalli Na'ima, dubi yanda ya rude, ashe ni ma zan iya biyan shi da kaina, Alhaji ya ce, ka iya tafiya, sai lokacin ya yi. Ismail ya ce to, tare da mikewa, ransa bace ya fita, lallai yarinyar nan 'yar wulakanci ce, anya kuwa zai jure?. Alhaji ya kalli Mimi, uwata ki daina irin wannan a gaban mutum. Ta kalle shi, Dad wallahi duk duniya ba wanda na tsana kamar shi, Na'ima ta ce, shine to zai dinga yi miki karatu? Ta ce, eh, amma na tsane shi, tace to mu fa karatun mu yaushe ne Sis? Mimi ta ce, ku kan sai Karshen sati. Alhajin ya mike cikin murmushi bari na fita, Mommy Nafisa wadda kallo ya daukar mata hankali, ta mike don yi masa rakiya, ya shafi kumatun Mimi ki yi min addu'a uwata, ta ce, sai ka dawo Dad Allah ya ba ka sa'a, Na'ima ta ce, sai ka dawo Dad, ya ce, yawwa Na'ima. Mommy Nafisa ta zauna a kan kujerar madubi tana kallon Na'ima wadda ta fada kan gado tayi ruf da ciki, ta ce, Na' ima taso kiji, ki taso mana Na'imata, ta dago fuskarta da jurwayen hawaye, ta ce, Mommy Dad ba ya so na, komai Sis Mimi, ni kam na gaji. Nafisa ta ce, amma me nike fada miki kullum? Bake kadai ba ce yake yi ma haka, ku duka ne, amma na yi miki alkawarin sai ya so ki fiye da Mimi. Naema ta soma kuka, na gaji da jin haka mommy, sai yaushe ne haka za ta faru? Mommy Nafisa ta tashi ta koma bakin gado ta zauna, sannan ta janyo Na'ima zuwa jikinta, kar ki damu, mu bi a hankali da sannu za ki zama 'yar gaban goshi. Akwai shirin da na jima ina shiryawa, Na'ima ta kalle ta da gaske? Mommy Nafisa ta ce, kar ki yi shakka. Ta share hawayanta, shikenan zan so in yi kamar abinda take yi, ko kuma fiye, suka sa dariya. Shadaya daidai Ismail ya shiga cikin falon, bayan me aikin ta zo ta bude, Na'ima ce kadai a falo tana kallon fim din India, ya ce, ki fada mata na zo, ta yi mishi kallon banza, ba ta ce, in kazo ka jira ta ba ne? ga falon da ku ka zauna can a jiya, za ka iya jiranta a ciki. Ya nufi falon ransa bace, anya rayuwar gidan nan za ta yiwun masa? Mintinsa goma shabiyu, sannan ya soma da jin Kamshin turaren ta, gabansa ya fadi, ta ja Kofar wadda ta kasance ta gilashi, kallo daya ta yi masa yana sanye da jallabiyya fara sal, ya yi kyau matuka, ta tabe baki, sannan ta zauna shima ya kalle ta kamar koyaushe shigarta babu tsari, ya kauda kai, sannan yace, ta ina za mu fara? Ta daga wayarta ta sa a kunne, hello Dear ka tashi lafiya? Ta dai yi jim, ok zamu yi waya anjima, yanzun ina tare da talakan nan ne, sai kuma ta sa dariya, Khalil kenan sai anjima din. Ta kalli Ismail me ka ke fada? ya ce, ta ina zamu fara? Yanda ya kafa mata ido hadi da hade ranshi, sai ta ji ya yi mata kwarjini, ba za ta iya kallon shi ba, ya yinda za ta yi masa rashin mutunci, ta kauda idanunta gefe, ko ta ina ka fara mana, ka tsare ni da idanunka, ya yi dan murmushin takaici, ya ce, to za mu fara daga huruful hija'iyya, Alifun kenan. Ta dube shi da sauri tun ina yar nursery na yi wannan, yanzun kam University nike, don haka sai ka koya min karatun da ya yi daidai da ajina, Ismail ya ce, zan so in ba ki shawara, duk me neman ilimi ko ba na addini ba zai fi kyau ya zama me biyayya da saukar da kai, girman kai ba ya kai mutum ga gaci. Ta daga mishi hannu, ba'a dauke ka don ka ba ni shawara ba, an kawo ka ne kurum ka koya min karatu. Ya ce, to bari mu fara daga fatiha sai mu shiga Bakara zuwa kasa ko? Ta tabe baki, ina jin ka, ya ce, zan karanta miki kamar sau uku, sai ke ma ki yi. Hmmmm