CANJIN RAYUWA CHAPTER 7 BY HALIMA A K/MASHI wannan wulakancin, don Allah ka yi zuciya ka bar mata yarinyar ta. Isma'il ya ce, hmm ka san na sha yunkurin yin haka, amma sai in samu kaina cikin tashin hankali, ban san lokacin da na soma son ta ba. Ka yi hakuri Mahamud ban ki batunka ba, abin ya wuce duk yanda ka ke tunani. Kai dai ka gode ma Allah, tun da ba ka da matsala da iyayen Rabia. Mahamud ya ce, ko da ina da matsala da su ba zan dauki haka ba, sai in bar su da 'yarsu. Kaima ina mamakin duk zuciyar da ka ke da ita, ya dafa Mahamud kar ka ji komai, ka sa ni cikin addu'arka. Mahamud ya ce, ka binciki asalinsu? Isma'il ya ce, Yaya Amina ce ta binciko, ranar take gayamin wai Ubansu bakano ne. dan wani kauye wai shi Kurje keya. Ita kuma Uwar 'yar Ruma ce, can wajen Safana. Ya auro ta lokacin yana da abin hannunsa. 'Ya'yansu shida maza uku mata uku, mazan ne manya matan kuwa Zainab ce babba, tunda arzikinsa ya karye sai buga- buga sai ta raina shi, 'ya'yan ma suka raina shi, sai abinda ta ce. Sannan ta dauki dogon buri ta dora ma Zainab, don kuwa ta ga yarinyar tana da kyau, ita sam ba za ta ba talaka ba. Sannan yaran babu tarbiya babu karatu sai talla. Mazan kuwa daga kwandasto sai kwasan bola, sai karamin su mai sayar da rake. Ka ji bayanin da Yaya Amina ta yi min. Mahamud ya ce, tabdijan kuma ka ji ka gani? Isma'il ya ce, to yaya zan yi? Ba ni da zabin da ya wuce Aurenta. Buri na shine in ta zama tawa zan tsaya mata ta yi karatu duka biyun. Mahamud ya ce, Allah ya taimake ka.Bayan sallar Isha sukayi sallama da Mahamud kan cewa sai gobe in sun hadu, kafin Ismail din ya tafi gida, gidan Yaya Amina ya nufa, a tsakar gida ya same su ita da yara suna cin abinci. Nan yaran suka shiga yi masa sannu da zuwa. Ya ciro naira dari ya ba Sadam babban, je ka sayo maku Biskit, ya ruga da gudu yana murna, Yaya Amina ta ce, ba ka gajiya ne? ya ce, haba dai. Sannan ta ce, Aisha dauko ma kawunku tabarma. Bayan sun gaisa sai yake sanar da ita batun tafiyarsa Abuja. Ta ce, gaskiya na yi murna, Allah ya sa alheri ne ya kira ka Abujan. Isma'il ya ce, amin, Yaya ina son in na dawo in tura gidan su Zainab, Yaya ta ce, Umm! Kai dai kana son wannan Zainab din, ya yi dan murmushi, ku taya ni da addu'a Allah ya sa haka shine mafi alheri. Ta ce, umm to amin, sun jima suna hira sannan suka yi bankwana ya tafi. Yana shiga gida ya kunna wayarsa ya shiga soron su ya ciro makullin dakin ya bude. Ya dubi makunnin wutar ya kunna haske ya wadace dakin ya shiga. Ya dauki buta ya fita zuwa cikin gida don zagawa ban daki. A tsakiyar gidan matan yayyin sa ne da 'ya'yansu suke ta hira, ya yi sallama suka amsa ya yi masu sannunku ya wuce. Don shi dama tsakaninsu bai wuce haka ba, sai' da ya fito bandakin sannan ya nufi dakin inna, ya yi sallama tana ta gyangyadi. Sallamar shi ce ta tashe ta, ya shiga ya gaida ta, ta amsa tare da cewa kananan? Ya ce, eh na shigo da safe ki na bandaki. Ta ce, haka dai ka ce, inda ni na haife ka ai don ina bandaki ka jira ni. Ya yi dan murmushi, zuwa yanzun ya saba da halin inna. Ya daina jin haushin maganganun da take fada masa marasa dadi. Dama zan sanar da ke ne gobe in Allah ya kaimu zan tafi Abuja. Ta ce, Habuja? Kai ko me za ka yi a Habuja? Ya ce, koyarwa na samu a wani gida zan dinga koyar da yaran gidan. Ta tashi tsaye, can kuma ka kutsa, lallai ba shakka, ya mike, ya jima da sanin inna zai yi wuya ta yi masa addu'ar Allah ya sa alheri. Ya fito ya sa takalmi tare da daukar butarsa. Tun kafin ya bar tsakar gidan yana jinta tana cewa kunji mutan gidan nan, Samaila ya samu koyarwa a Habuja, ya fadawa mazajenku? Fatu ce ta soma magana, lallai ba shakka, ya fadawa ,mazajenmu su a su wa? Ke ma don kar a ce dai bai fada ba ne, Kala bai ce ba ya wuce dakinsa. Da safe sai da ya shirya tsaf, sannan ya yi wa yayyansa maza sallama, su kam sun yi masa Allah ya sa a dace. Gidan su Mahamud ya nufa. Ya yi sallama da malam Aminu mahaifin Mahamud sannan suka nufi gidan Hajiya Sauda. Mahamud ya goya shi a mashin, kuma sun yi shawara a kan Mahamud zai ci gaba da koyar da su Hussaina. A waya ya kira Hajiya ya fadi mata ya iso, ta sa ya shigo, kar ya damu ai shima tamkar shi dan gida ne. Suka shigo falon baki nan ta same su, ya gabatar mata da Mahamud, bayan sun gaisa ta kuma Kara rokonsa a kan ya tsaya mata sosai a kan Mimi, sannan duk lokacin da ta yi yunkuri ko barazanar koran shi, to ya kira ta. Ta ce na san aiki ne na ba ka mai wahala, amma kamar jihadi ne, ya ce, na yi miki alkawarin zan tsaya a kanta kamar kanwa ta, zan jure saboda Allah da kuma halaccin da ki kai mun. Ya'u direba ne zai kai shi, sai da motar ta tashi sannan Mahamud ya buga mashin cikin kewa. Suna tafe suna labari shi da Ya'u cewa ya yi, gaskiya ina yi maka jaje a kan wannan aiki, gara inyi aikin kwasar kashi don na tsani wulakanci. Isma'il ya ce, hmm ni fa gani na ke kamar wata Kaddara ta sa zan je koyar da yarinyar nan. Wata zuciya kuma tana fada mini Allah zai taimake ka. Sannan ina tunawa ni namiji ne, sai inga to wai me ye ne abin tsoro. Ya'u ya ce, ba za ka gane ba, ai Ubanta za ta sa ya tozarta ka. Ga zagin wulakanci, Ismail ya ce, Allah ta zage ni sai na mare ta. Ya'u don dariya sai da motar tayi kamar za ta sullude masa. Ya ce, gaskiya kar ka yi wannan kuskuren, Ismail ya ce, iyakar dai a kore ni ba zan wulakanta kaina ba, suna tafe har suka zo Zariya. Isma'il ya ce nanne Kaduna? Ya,u ya ce, eh amma ba garin Kaduna ba ce Zaria ce, nan dama ba ka tada zuwa ba? Isma'il ya ce gaskiya ban taba zuwa ba. Kai ni ina zaton Sokoto kawai muka taba zuwa yin gasar karatu lokacin ina SS1. Ya'u ya ce gaskiya. ni ban zata ba, in na kalle ka sai ka ce ka taba fita kasashen duniya. Ismail ya ce, ni kifin rijiya ne ban san ko ina ba. In mun zo Kaduna ka nuna min ina jin labarin garin ina son zuwa. Ya'u ya ce, shikenan zan nuna maka, tun daga nan yake nuna masa garuruwa har suka isa Kaduna. Ya ce, bari in bi da kai ta cikin garin maimakon by pass tunda kana son ganin garin. Shikenan Isma'il sai kalle-kalle ya ke yi. Ya ce, garin ya birge ni. Amma duk a zato na ya fi haka, yadda sunan Kaduna ya cika ko ina. Ya'u ya ce, zaman garin yana da dadi saboda ba su shiga harkan abinda bai shafe suba. Isma'il ya ce, wani ya taba ba ni labarin garin 'yan karya ne ko? Ya'u ya ce eh, to ni ma dai haka na ji ana cewa, to muna da 'yan'uwa suna zuwa Katsina gurin innarmu, mu ma mukan zo, ba wasu masu karfi ba ne, amma komai za su yi sai inga suna son yin wanda yafi karfinsu, ni ma sai na amince 'yan karya ne. Amma daga baya lokacin ina yin tuki a nan Kaduna a wata unguwa wai ita unguwar Rimi sai na gano ba wai karyacce da su ba, yin hakan a jinin 'yan Kaduna ne yake. Ka gane Malam Isma'il? Su mutane ne masu son yin komai me kyau, kuma ba su da kyashin sayan duk abinda ransu ke so, ko da kudinsu kenan. Idan za a aje maka dan Kaduna mai dubu dari biyar, da dan wani gari mai milyan biyar, za ka ce dan Kadunan ne mai milyan biyar, wancan mai dubu dari biyar. Ismail ya ce na gane, in ko haka ne sun burgeni, saboda ni ma irin ra'ayi na kenan, arziki na. Allah ne, in na samu zanyi abinda nake so da halas dina. Haka suka yi ta labarin 'yan Kaduna har suka kai Abuja garin manya: Shi kam a ranshi 'yan Kaduna sun yi mashi, yana son mutane masu test, wadanda ba komaine ya yi masu ba. Tafkeken gida ne na gani na fada, tunda suka doshi gidan Ismail ke mamaki sai ka ce fadar Shugaban kasa, duk yadda yake kisima gidan a ranshi ya wuce nan, tun kafin su shiga ma kenan. Su na shiga sai ya ga ma kamar wata sabuwar duniya ce, wannan mutumin wane irin kudi ya mallaka? Isma'il ke tambayar kanshi. Dama tun kafin su Kara so ya kira Hajiya ya fada mata cewa sun iso unguwar, ita kuma ta kira Momi Nafisa ta sanar da ita. Ismail ya na jingine jikin mota, wani matashi ya iso wurinsa ya ce, wai wanene Malam Isma'il? Ya ce, nine. Ya ce, to zo mu je, ya kalli Ya'u direba zo mu je, ya ce, a'a, ni dama aiki na shine na kawo ka, kuma na. kawo ka, yanzu zan juya. Ismail ya ba shi hannu suka yi sallama. Bayan gidan suka nufa inda suka nufa gefen yara, suka je ya bude wani daki, an ce ka shiga nan. Ismail ya kalle shi, ba mu gaisa ba? Ya mika masa hannu suka gaisa. Ya ce, suna na Isma'il, kai fa? Ya ce, Hamisu, kuma ni ne direban yaran gidan nan. Ga daki na nan kusa da na ka, mu biyu ne a cikin dakin, ni da me share-share, game da kula da fulawoyi. Isma'il ya ce, Allah ya sa mu amfani juna, Hamisu ya ce, amin. Ismail ya shiga yana kallon dakin tamkar ba dakin masu aiki ba, Hamisu ya ce, ai Kurar dakin ba ta yi yawa ba, don kanin Momi bai yi sati da tafiya ba, da cikin dakin yake. Isma'il ya ce, Kurar ba tada yawa ma kenan, amma duk da haka bari in dan kakkabe. Ya shiga ciki sosai, Hamisu ya ce, in za ka yi sallah ga bandaki nan. Isma'il ya ce, tunda muka taso, duk inda sallah ta same mu, sai mu tsaya mu yi ta. Hamisu ya ce, shikenan ba ka da wani nauyi a kanka. Isma'il ya gyara daki mai dauke da katifa katuwa, sai durowar ajiye kaya, sai kuma dan teburi a gefan katifar. Hamisu ya ce, bari in sa a sanar da Momi cewa ka iso, kuma na ba ka masauki, yanzu saura abinci. Kusan minti talatin da fitar Hamisu,, sai ga wani kuma dauke da Plate a rufe da cokali da kuma ruwa. Suka gaisa, sannan ya ce, ga abincin ka. Shi ma nan haka Ismail din ya sake gabatar masa da kansa, suna na Isma'il kai fa?. Ya ce, suna na Jabiru, kuma ni ne mai dafa abincin rana da dare, Isma'il ya ba shi hannu suka gaisa. Bayan fitan sa ne ya bude Plate din abincin, dafadukan shinkafa ne, ta ji kifi da alayyahu, ya ci ya Hmmm