
CANJIN RAYUWA CHAPTER 4 BY HALIMA A K/MASH
turare ya ce, ban sani ba ko zamu gama tattaunawa da wuri ko ba zamu gama ba, amma ko ya ya ne dai daga can zan wuce Malumfashi. In duba su Binta da yara sannan in kewayo gona ta, na jima ban leka ta ba. Sannan inda lokaci zan shiga Masari can ma na jima ban je ba. Kin ga sai na kwana kenan, gobe zan dawo in dauki uwata mu koma inda muka fi wayo. Hajiya, Sauda ta ce, Allah ya tsare sai ka dawo din, amma batun tafiya da Mimi ne nake tunani a kai. Ya kalle ta, kamar ya ya? Ta ce, sai ka dawo dai Allah ya tsare, ya dan tabe baki amin.
Suna fitowa Falo yara suka nufo suna yi masu sannu da fitowa tare da gaishe shi, ya amsa da daidai, sannan ya kalli Usaina, Mimi fa? Ta ce, tana kwance Dady,: ya: ce, shikenan za mu yi waya. Hajiya ta raka shi har mota, wannan ba sabon abu bane, haka ta saba tun suna da kuruciya.
Falon ya kacame, yaran suna ta karin kumallo, sai hayaniyarsu da Karar kofuna.
Mimi ta fito sanye cikin riga da wando masu dan kauri na barci. Sauri take yi, tare da fatan Allah Ya sa Dad dinta bai fita ba, don ba za ta taba bari ya fita ya bar ta ba. Ta iso gurin Hajiya, fuskar ta babu annuri ta ce, ina kwana Hajiya? ba tare da ta dube ta ba ta ce, lafiya lau. Mimi ta yi tsaye shiru, tana son yin magana amma tana tsoro.
Hajiya ta dago ta dube ta, ga kayan shayi can a kan dining, na san ba kya shan kunu, ta ce, tam! Ehemm! Da ma zan gaida Dady ne, yana ciki ne? Hajiya ta ce, a’a ya tafi Malumfashi sai gobe zai dawo. Mimi ta zaro idanu ya ya Dady zai min haka ya tafi ya bar ni, ta kalli Hajiya wanda ta soma watsa mata harara ta ce, Hajiya don Allah ina waya ta? Hajiya ta ce, sai za ku tafi sannan zan ba ki, don ni ba za ki yi mani wannan chatin din naki ba a nan, sannan ki karya ki je ki yi wanka, in malamin su Hussai ya zo za ki bi su, ki je daukar karatu a gurinsa. Ina sa ran ma Alhaji ba zai tafi da ke ba, nan zai bar ki sai kin san Addininki sannan za ki tafi, ko da za ki cinye hutun ki a nan. Cikin sauri Mimi ta koma daki cikin kuka sai da ta yi me isarta sannan ta shiga wanka, a fili kuwa fadi take, Allah ba zan zauna ba, shi ya sa na tsani zuwa Katsinan nan.
Dolenta ta saka atamfa,riga da siket, a cikin durowarta ta ciro don tana da kaya a nan gida, duk lokacin da aka yi wa su Usaina sai an yi mata. Ta shirya tsaf ta koma kan gado ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi. Amma ko ta halin kaka ba za ta zauna cikin irin wannan takurar ba. Can ta hango wayar Hasana kan durowar ta. Cikin sauri ta tashi ta dauko, layin Dad ta kira wanda ta san in ta kira zai dauka da sauri, cikin kuka ta soma Magana, bayan ya daga dad ka ga Hajiya ta dauke min waya ta, kuma wai ba zan tafi ba, ni-dai Dad wallahi ba zan zauna ba. Ya ce, yi shiru uwata kar ki damu ba zan barki ba ni ma, yanzu me kike so? Ta ce, Phone di na, ya ce, shikenan zan ce ta ba ki, kin ci abinci? Ta ce, a’a, ya ce, to ki je ki ci zan sa ta ba ki wayarki kin ji?.
Ta na zaune a kan Dining ta hada shayi tana sha da cokali cikin hankali don ita sam ba ta da hanzari, tana kallon lokacin da Hussaina ta kawo ma Hajiya waya ta ce, Dady ya kira, ta daga. Ta na jin lokacin da Hajiyar take cewa, tsaya ka ji Alhaji, sai kuma tayi shiru, da alama ya katse ta ne, ya hana ta Magana, don ta ga Hajiya ta yi shiru, amma ranta a bace yake. Sai kuma ta ce to Alhaji na ji zan ba ta, amma ba na son chatin din nan da ta ke yi. Mimi ta yi murna, a ranta ta ce Dady na kenan, ta nufi daki da murna.
Alhaji ya ce, kar ki damu Sauda,
‘yarki mai kamun kai ce. Ita da kowa ya shaida ko saurayi ba ta da shi. Shi yasa nike dubawa don in samo mata miji wanda zai kimanta min ita, ya ba ta kulawa fiye da wanda take samu a guri na.
Hajiya ta ce,
umm! Allah ya taimaka, ai ni da na zaci ma ba za ka iya auradda ita ba (cikin gatse ta yi maganar). Ya ce, kash kin ji ki da wata magana kuma Sauda, in ban aurar da ita ba ai kuma na cuce ta. Ina ma ki ka ga an tada , haka? Ke dai ki yi mana addu’a, ta ce, Allah ya taimaka, kun gama ganawar ne? Ya ce, eh, yanzu haka muna hanyar Malumfashi sai na dawo ta ce, Allah ya tsare, ka dawo lafiya, ya ce, Amin, ga dai uwata nan amana na ba ki, katse wayar ya yi ba tare da ya jira jin amsa daga bakinta ba.
Ga zaton Mimi tana aje wayar Alhaji za ta zo ta ba ta tata, amma sai ta ji shiru. Ta sake fitowa falo nufin ta kila Hajiya ta ganta ta tuna, idan ta manta ne, amma sai ta ga Hajiya ta ci gaba da lamuranta. Yaran duk suka yi wanka suka fito, Husna da Hasina suka shiga falo da gudu suna cewa, ga malam nan ya zo. Ga mamakin Mimi sai ta ga duk yaran sun rude, wasu sun dauko Alkur’anin su suna karantawa da sauran littafai da yake masu. A ranta ta ce niko bari in ga wanene malamin, kai har na ji na tsane shi tun kafin in ganshi. A zaton ta nan zai shigo sai ta ga Abdullahi da Umar da Aminu da Sadik sun soma fitowa bayan dawowansu sai Zainab da Hasana da Hussaina suka fita.