
“Oho! Ibrahim sai yanzu na fahimce ka, wato kana so ka raba zumuncinmu a kan Fati, ka manta yadda muke da mahaifin Sulaiman ko?
Don ya rasu shi ne za ka manta shi, ‘yarka ce a gabanka”.
“Yaya ni duk ba haka nake nufi ba ina…
“Bana son dogon magana, an fasa auren da Sulaiman kuma ba za ta auri Faruk ba, tunda nima ina da ‘yar na bawa Sulaiman Zubaida, kai kuma ka dauki tsiyarka ku bar min gida. Butulu kawai!”Yaya don
Allah ka yi hakuri, dama shawara ce in ba ta yi ba ai shi kenan”.
“Bana son dogon zance, ka dau ‘yarka ku bar min gida”.Ba rokon da Alh. Ibrahim bai masa ba amma ya ki. Kwalawa Fatin kira ya yi, a firgice ta fit don Abban bai tada mata irin wannan kiran ba.
“Abba gani”
“Ga mahaifinki ki bishi ku tafi kar na kuma ganin ki a gidana”. “Abba ban da mahaifin da ya wuce ka,
bani da wani gidan da ya finan”
Daka mata tsawa ya yi, “Nace ki fita”.
Ta dinga ihu tana kiran Umma. Da sauri
Umma ta fito.
“Alhaji meke faruwa? Ba inda za ta?’
Alhajin ya harare ta, “In har kika sa baki a
maganar nan bakin auren ki”
Maganar la girgiza su duka, ba musu Fatin ta fita don tasan Umma ba zata fasa janta ba,
haka nan ba za ta so auren Umma ya Kare a
kanta ba.Batun cin abinci babu shi a familyn gidan
su Fati, tashin hankali da bai misaltuwa Fati da
Faruk din suka kuma shiga.