Arewa writers

NIHLATULKHAIR CHAPTER 2 HAUSA NOVEL

NIHLATULKHAIR.CHAPTER 2 BY UmmuAffan HAUSA NOVEL

_Dole ne, cin kasuwa da maƙiyi._

A wahalce na farka tamkar kwaɗon da ya faɗa ruwan zafi. Agwogwo na ɗaga kai na duba daidai ƙarfe huɗu na dare 4:00am. Tafiya ma kasawa nayi saboda tsabar ƙugin da cikina ke mini, sai fararrafawa nayi har na fita kofar ɗakin baccina.
Na daɗe gurin zaune riƙe da ciki tamkar wacce ke cikin matsanancin ciwo, duk da makamanciyar hakan ne, a hankali na samu na miƙe ina dafa bango na ƙara sa kitchen. Gas na kunna tare da ɗaura ruwan lipton na jefa citta da kanun fari, na zauna daɓas a gasa ina nunfarfashi, minti biyar na miƙe na juye ruwan a kofi tare da zuba suger da madara na kafa baki, biredin da na gani na jawo tare da fara kai masa haƙora. Ina da ulcer wacce nasan ko awa biyar cikakkiya nayi ban ci abinci ba sai ta tasar mini kamar mai asma. Amma nayi wannan saken, dumuwa ce silar komi. Wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro daga kwarmin idona.
Bayan na kammala jiki a sanyaye na koma ɗaki, toilet na shiga tare da kama ruwa na fito, Yaya Md har lokacin yana sharar baccin shi.
Tun daga sannan bacci ko gigin kama ni bai kuma ba ina zaune aka fara kiraye-kirayen kiran farko, na tashi na ɗauro alwala na fara nafila har zuwa lokacin da a ka kira sallar asubahi, daidai lokacin Yaya ya farko, kallo ɗaya ya mini ya wuce toilet, yana fitowa kuwa ya doshi hanyar fita domin zuwa masallaci. Ana tada sallah na miƙe nabi jam’i kasancewar ba mu da nisa da masallaci tamkar a cikin gidan idan ana sallah.
Wajajen shidda da rabi Yaya ya shugo, wanka ya shiga yana fitowa ya fara kiciniyar shiryawa.
“Me zan dafa maka Yaya?”
“Duk abin da ya miki!”
“Zaka jira na kammala?”
“Ina sauri!”
Numfashi na fesar kafin na ce”Don Allah Yaya zaka sauke ni a gida?”
Bai ɗago ya kalleni ba har lokacin.
“Me zaki yi a gida?”
Nan take yanayi na ya sauya, wani sabon tashin hankalin ya bayyana a maɗaukar gani na.
“Tun bayan bikinmu sau ɗaya naje gaishe su, ina son ganin mahaifiyata Yaya.”
Sai lokacin ya dube ni, tausayina yaji? Sabon imani ne ya ziyarce shi? Allahu a alamu! Sai ji nayi ya ce”Ki shirya na sauke ki.”
A fili na saki ajiyar zuciya ya yin da fuskata ta wadatu da annuri, da tsantsar farin cikin da naga ya gagara daina kallona. Mamaki yake ko wani tunanin oho. Nikam toilet na faɗa nayi wanka sam na manta da wani batu nayin girki domin neman yunwar nayi na rasa.
Shiryawa nayi cikin atamfa ɗinki zani da riga na yane kaina da ɗaurin zamani, na ɗauki mayafi da yayi daidai da atamfar tare da zura takalmi mara tudu. Ƙaramar jakata na rataya nayi saurin fitowa domin tuni ya riga ni zuwa parlourn.
Amal zaune hannunta da waya, ina fitowa ta miƙe.
“Sai ina naga anci kwalliya?”
Ta tambaye ni fuskarta ba annuri bakinta taɓe.
Cikin farin cikin na na kasa ɓoyewa na ce, “Yaya zai sauke ni gida ne.”
Ban jira amsarta ba na fita da saurin gudun kar na ɓata mishi lokaci ya cenza shawara akan fitar tawa. Har ya hau babul ɗin shi da sauri na ƙarasa. Baya na hau muka fice daga cikin gidan, tunda muka fara tafiya ba wanda ya cewa wani ko ta tafasa, ganin ba hanyar ya nufa ba gabana ya faɗi sosai sai bin hanyar da kallo nake. Don bana tunanin a ‘yan uwanmu akwai wanda na taɓa sani a unguwar, shuru nayi kamar ruwa ya cini har muka isa wani makeken gida(Babban gida), sosai gate ɗin ya tsufa yana da faɗi da tsayi, a ƙofar gidan muka tsaya, tun kafin ya mini magana na sauka. Mamaki ya cikani ganin ya gungura mashin ɗin zuwa cikin gidan, ni dai ina biye da shi tamkar raƙumi da akala. Sai da muka shiga naga yanayin gidan part-part ne, da alama gidan haya ne ko family house. Part na biyu naga ya nufa na tokare haka kawai naji gabana na faɗuwa, bayan ya faka mashin ɗin a ƙofar part ɗin ya juyo ya dube ni.
“Ba zaki shugo ba ne ko me?”
Gabana na dukan tara-tara nabi bayan sa. Ina mamakin me ya shagayi gidajen matan aure, ko wata tamu ce ta dawo gidan? Na tambayi zuciyata domin ni dai nasan ba halin Yaya ba ne shige-shige. Muna shiga ƙirjina ya yi wani daram ganin Aunty Farrah zaune a parlourn ita da yaranta biyu. Maamah da Najma, yaran suna ganina kuwa suka doka tsallen murna,
“Oyoyo Aunty Nihlah!!”
Na buɗe hannuwana cikin tsantsar farin cikin ganinsu, sai dai tsawar da mahaifiyarsu ta doka musu ne yasa su yin suranda sai muka yi wani dako-dako.
“Firɗinku wallahu, wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa! Sau nawa nake ja muku kunne akan wannan baƙar ƙadarar baƙar fura sannan farar ƙafar?”
Tuni hawaye suka tsanke fuskata yayin da jikin yaran ya yi sanyi duk da ƙananun shekarunsu.
Duba ta kai mini “Mtsuwww!!!” Taja dogon tsakin da yayi sanadiyyar gangarowar hawayena.
“Tur da shugowa cikin rayuwarmu da kika rusa mana farin cikin shekaru takwas! A cikin wata huɗu zuwa biyar kika rusa duk wani fundishon da tanaji na rayuwarmu. Shin muguwar farar ƙafar uwarki da ke bibiyar rayuwarki zata sa na yarda ki raɓar mini ‘ya’ya ki shafa musu kashin awaki ne?”
“Ya isa Farrah!”
Yaya Md ya daka mata tsawa, yayin da ƙarar kukana ta tsananta……

*Ina mai baƙin cikin sanar da ku nayi typing mai ɗan tsayi na NIHLATULKHAIR amma na rasa shi. Sanadiyyar alƙawarin da na muku ya sa ba shiri na ɗaura wannan typing nawa. Ina fatan zaku mini uzuri domin maganar gaskiya sabon typing nake ku tayani jimami. Nasan yadda na tsara wancen ba lallai ne komi ya dawo kaina ba, amma zanyi ƙoƙari domin ganin na gina labarina kamar yadda na faro na farkon. Matsala ɗaya ce ba zai kai tsayi kamar yadda na fara waccen ba, domin wancen readmore 4 duk nayi, yanzu kuwa duk yadda ya samu haka zaku ganshi, na gode da soyayyar da kuka nunawa labarin Nihlah tun daga ɗanɗano.*

_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 July 20 in sha Allah._

1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE