DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Posted by

DANGI DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

 

 

“NIHLA! lokacin tafiyar ki makaranta fa yayi, kitashi haka kada ki makara”

Cikin jin dadin baccin tayi juyi tabawa wadda take yimata magana baya,hakan yabawa dogon gashin kanta Wanda duk ya cukurkude damar rufe mata fuska, cikin magagin bacci tace “Diddi Allah ni baccin bai isheniba”

Dan qaramin tsaki taja, tasa hannu tadauketa cancak, bata ajiyeta ako’inaba sai afilin Dan qaramin tsakar gidansu na qasa Wanda yake ashare tas
Tsugunnawa tayi daidai Tsawon yarinyar tace “dan ubanki bude idonki, idan kika makara dukanki zasuyi ”

Jin maganar duka yasa ta wartsake lokaci daya, ganin tatashi sarai yasa mahaifiyarta rabuwa da ita, takoma cikin dakin tad’auko mata d’an qaramin brush dinta, tabata, sannan tadauki baho tafara hada Ruwan Mai d’an d’umi.
Ruwan wankan data hada tad’auko takawoshi gaban yarinyar, sannan tadauko kwandon wanka Wanda yake d’aukeda soson wanka Mai laushi, da alama na yarinyar ne, ta tsugunna a gabanta “wai bazaki hanzarta kigama wanke bakin ba?”

Cikin sauri yarinyar ta wanke bakinta, ta ajiye brush din akan wata yaluwar jarka ta OKEY wadda take cikeda ruwa, bakin ma bai wani fita sosai ba, haka tahaqura tace “Diddi nagama, afara wankan”

Hannunta tasa ta tattare gashin kan yarinyar, Wanda yakeda tsawo sosai, cikar batada yawa, ta d’aureshi waje d’aya, sannan tafara yimata wankan

Idanunta a runtse tace” Diddi baza’a wanke kanba? ”

“Nihla idan aka wanke wannan kan naki shi kad’ai ma zaisa ki makara kafin ya bushe, kibari idan za’a miki wanka da yamma saiki siyo omo awanke miki”

Tace “to Diddi”

Tsaf tagama yiwa yarinyar wankan anan filin tsakar gidan nasu sannan tasata tayi alwala , kasancewar akwai rairayi kad’an agidan hakan yasa qasar wajan ta shanye Ruwan, lokaci d’aya farar fatar yarinyar tasake futowa, wani zanin atamfa taja akan igiyar tsakar gidan nasu, tarufa a jikinta sannan tashige d’akinsu da gudu.

Itama bayan yarinyar tabi zuwa d’aki, ta goge mata jikinta, sannan tashafa mata Mai Vaseline na Habiba, tasa ta tafara sallah, dukda yarinya ce qarama, tayi kokari wajan yin sallar saide gyara ‘yan kad’an

Hijabin datayi sallar dashi tacire, tad’auki mataji tabawa mamanta tace”Diddi gashi ”

Batare da tace komai ba ta karbi matajin, tafara tajewa yarinyar gashin kanta, me mugun tsawo sosai, tad’aure matashi da ribom sannan tatufke mata sauran, zanin atamfar data goge mata jikinta dashi tad’auka ta goge mata fuskarta, saboda maiqo, sannan tasaka mata d’an qaramin hijabinta fari me hula, kasancewar hijabin d’an qarami ne hakan yabawa jelar gashinta damar futowa ta qasan hijabin, takalmin ta tasaka silifas, sannan tace “Diddi natafi”

“to Muje wajan babanki kikarbi kud’in karyawa”

Wani d’aki suka shiga Wanda yake kusada Wanda suka shirya, tana tsaye abakin kofar d’akin ta doka sallama, radion dayakeji yarage sautinta, sannan ya amsa mata, ko ina kwana Babu tace masa “Baba kudin karyawa”

Murmushi yayi, yadauki nera goma acikin aljihun rigarsa yabata, takarba tafuto, ta kalli Diddi dake tsaye abarandar gidan nasu tace “Diddi natafi”

“to Nihla saikin dawo, banda wasa ahanya kinji ko”

“to Diddi, idan anyi tara nataho gida ko?”

“Haba Nihla, mezakiyi idan kinzo?ba ana baku abinci a makaranta ba? Kiyi zamanki sai antashi, nisan ai yayi yawa”

Cikin shagwaba tace “to Diddi idan basu bamu bafa?”

“tome amfanin nera goman da aka baki? Saiki siya wani abun kici”

Tace “to natafi”

Itama tace “to Allah yakiyaye, banda wasa de kinji ko”

Tace “to” tareda ficewa daga gidan
Ita kuma Diddi tad’auki albasa yan madaidaita guda uku tafara Yankawa, amma abin mamakin shine hancinta yana gab da albasar datake Yankawa tana shaqar yajin albasar Kamar batajin zafi

Kamar kullum tana futowa daga gida adede lokacin shima megadin gidansu ya wangale musu get, kallo d’aya tayiwa motar qirar Mercedes Benz tadauke kanta, ta gabanta motar tazo tawuce, tana d’ago kanta taganshi shi kad’ai a bayan motar ana jansa, shima uniform ne ajikinsa amma ba irin nataba, da alama na private school ne nasa, cikin sauri yajuyo ta glass din bayan motar yafara d’aga mata hannu yanayi mata bye-bye,sarai taganshi, amma taqi yimasa bye-bye din, sai murmushi datayi masa har dimple d’inta suka futo gaba d’aya biyun

Juyawa yayi yadena Kallanta, yabude school bag dinsa yayi rubutu ya cukwikwiye yasaukar da glass din gefensa, ya wulla mata takardar, sannan Yarufe glass din yana daria, baisake Kallanta ba

Itama tana kallan motarsu, har sukai mata nisa, takardar dataga ya wullo mata tad’auka, ahankali ta bude takardar “You’re my friend”
Shine abinda tagani ajiki, bata fahimci komai ba, Dan haka tayagata ta watsar awajan 😃
Taci gaba da tafiya tana ball da duk abinda tagani agabanta

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

“Abubakar”

“na’am Hajiya”

Wata takarda tabashi doguwa alinke, sannan tasake kallansa tace “riqe wannan takardar”

Karba yayi yariqe fuskarsa cikeda mamaki, bai iya boye mamakinsa ba yadubeta yana qoqarin bude takardar “Hajiya wannan takardar mecece?”

Cikin sauri tace masa “karka kuskura kabud’e wannan takardar Abubakar, abinda yake cikin ta Sirri ne tsakanin nida mahaifinka da mahaifiyar ka wato abokiyar zamana”

Kallanta yasakeyi sosai”to Hajiya meza’ai da’ita? ”

” yauwa Tun farko abinda yakamata ka tambayeni kenan, Abubakar wannan takardar wasiyya ce da mahaifinka yabari ahannun mahaifiyarka Tun kafin yabar duniya, ita kuma tad’auka tabani kafin itama Allah yayi mata rasuwa, ni kaina inaji ajikina ba lalle naqara shekara d’ayaba nan gaba, shiyasa nima na damqa maka wannan wasiyyar ahannunka amatsayin ka na babba acikin MAZAWAJE FAMILY,”

” haba hajiya, meyasa zaki dinga yimin irin wannan maganar? Ke kad’ai ce kika rage mana, sannan ke kad’ai muke gani muji dadi, kinasa jikina yanayin sanyi sosai ”

” Kayya, Abubakar kenan, shekara tamanin da biyu ba nan bace Abubakar, gara inyi abinda yakamata Tun kafin lokaci ya quremin, mutuwa bata sallama ”

Shiru yayi, kansa a sunkuye, maganar hajiya tasa jikinsa yayi mugun sanyi, bata taba nuna masa banbanci da ‘ya’yanta ba duk da ba’itace ta haifeshi ba, kishiyar mahaifiyarsa ce, idan itama tatafi tabarsu yaya zasuyi? 🤔
lokaci d’aya Idanunsa yakad’a yayi jajir, yadago yadubeta “Hajiya yanzu yaya zanyi da wannan takardar?”

Hannunta ta miqa masa tace “bani takardar Abubakar”

Takardar yasaka mata cikin hannun ta, yana Kallanta ta bude wata qaramar akwati agefenta tasaka takardar aciki, sannan tasaka key tarufe akwatin, tamaida Kallanta gareshi tace “Wannan takardar zataci gaba da zama acikin wannan akwatin har Tsawon shekara goma”

Cikin sauri yad’ago kansa yadubeta “Hajiya shekara gomafa ba wata goma bane, mu kanmu bamuda tabbacin zamu iya kaiwa wannan shekarun dakika ambata”

“Abubakar kenan, kullum addu’armu itace Allah yaraya mana ku, nasan zaka iya amatsayin ka na babba Mai fada aji acikin yan’uwansa shiyasa nabaka wannan takardar, kuma har gobe ina fatan gaba d’ayanku kukai wannan lokacin”

Cikin sanyin jiki yace “to Hajiya Allah yasa”

Tace “Amin Abubakar, Allah yayi maka albarka, mukullin dazai bude muku wannan akwatin zaku iya samunsa awajan Alhaji mamuda, Wato aminin mahaifin ku idan shima lokaci bai cikaba, sannan abu na qarshe dazanyima kashedi akansa shine daga rana irinta yau kada asake taro kowanne irine acikin MAZAWAJE FAMILY, idan anyi haihuwa asakawa yaron suna kawai, maganar taro na biki shima daga kan masu shekaru irinna FAROUQ zuwa qasa kada abari kowa yayi, idan so Samu nema kubarsu su girma kowa ya mallaki hankalin kansa tukunna kafin ku aurar dasu”

Wannan karon kam gumi ne yajiqe masa fuska, wannan wanne irin sharad’i ne? 🤔
Kallanta yayi” Amma hajiya… ”

Cikin sauri ta d’aga masa hannu” dakata Abubakar, wannan umarni nane, banaso kace komai akan haka, Yaya maganar takardar filaye na yara?”

Daqyar yace” Hajiya angama yankawa kowa nasa, dukkan yaran maza kowa angama sama masa nasa filin, takardun ma sunzama ready”

“to idan kowa acikinsu ya tasa, kad’auka da kanka kabawa kowa nasa, Wanda ya wulakanta nasa shiya jiyo, idan mutum yanason zama acikin gida na family shikkenan, idan baya buqata saiya gina filinsa”

Cikin ladabi yace “to hajiya, insha Allah zanyi kokari inga nacika umarninki, nizan wuce gida su Rahma suna jirana itada yara zasu tafi jigawa suyi kwana biyu”

“meyasa kai ba zakaje ba Abubakar?”

Shiru yayi, bai tanka mataba, Dan haka tayi Murmushinsu na tsofaffi tace “Ayi hakuri haka Abubakar, abinda yafaru yariga yafaru, Aisha qanwar ka ce dakuka futo ciki d’aya, bayan ‘ya’yana bakada Wanda yafita duk duniya,kaida Aisha duka DANGI ‘DAYA kuka futo,sannan ba ita kad’aice Mai irin wannan laifin ba, kamanta da abinda yafaru abaya kajiko?”

Yace “to hajiya insha Allah, mungode sosai da sosai da irin ruqon dakika mana, Allah yaqara girma”

Cikin rashin damuwa tace”Amin Abubakar, Allah yayi maka albarka, ya albarkaci mazawaje family ”

Yace” Amin hajiya”daga nan yatashi yafita

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda yadawo gida yarasa meyake masa dadi, idan yatunada maganar dasukai shida hajiya duk sai yaji wani iri, wannan ba qaramar magana bace, amatsayin sa na babba acikin family dole abin zai dame shi, to yanzu ita hajiya data d’ora masa wannan nauyin tana da tabbacin zata rigashi mutuwa ne? Idan kuma shi yarigata mutuwa fa? Wannan ba maganar ‘boye-‘boye bace, dole zai kira yan’uwansa gaba dayansu yafad’a musu komai, saisu sake tattaunawa akan batun, duk Wanda Allah yayi masa Tsawon rai acikinsu haryakai lokacin da hajiya ta ambata, saiya zartar da hukuncin, bazai iyu yabarshi aransa shi kad’aiba, zai hada meeting akan hakan dole

“Alhaji tunanin mekake haka tun d’azu nashigo inata sallama bakajini ba?”

Ajiyar zuciya yasauke yakai dubansa zuwa ga matar da tashigo cikin d’akin nasa, kallo d’aya zaka mata ka hango hutu da jin dadi atare da ita, yace”Rahma banji shigowar ki bane, ina yaran suke? Kun gama shiryawa ne?”

Shiru tayi masa tanemi waje ta zauna a gefensa sannan takama hannayensa tace”Alhaji meyake faruwa? Yanayin ka ya sauya bayan qalau kafita, kafadamin meyake damunka?”

Kallanta yayi “wallahi Rahma hajiya ce tadauramin wani Babban nauyi akaina,tabani wasiyya ne, sannan maganganun nata duk sun sanyaya min jiki, tanamin magana Kamar bazata qara kwana d’aya aduniya ba”

Cikin mamaki tace “wasiyya kuma?”

Yace “qwarai kuwa” nan take ya labarta mata abinda yafaru tsakaninsa da hajiya

Ajiyar zuciya tasaki tace “Alhaji, tunda kaga tanemeka kunyi wannan maganar da’ita haqiqa ta yarda dakai ne,tunda duk cikin yaranta bata nemi d’aya daga cikin su ba saikai, kayi kokari kaga kacika umarnin datama, amma gaskiya kasamesu kuyi maganar shi ne yafi, dukda nasan ma wasiyyar bazata wuce maganar hadin kanku ba ”

” nima abinda nake tunani kenan Rahma, saide kuma idan hakanne me yakawo maganar taro da za’ace bandashi? ”

” ka kwantar da hankalin ka Alhaji, insha Allah Babu abinda zai biyo baya sai alkhaairi ”

” to Allah yasa, kwana nawa zakuyi idan kunje? ”

” Kamar dai yanda mukai maganar dakai Alhaji, kwana biyu zamuyi insha Allah ”

” to saikun dawo, Allah yakiyaye hanya, ki kulamin da yarana ”

Murmushi tayi” Alhaji kenan, kanaji da wannan samarin naka, ni kuwa suna sakani ciwon kai, shikkenan za’a kula dasu ”

Yace” to asauka lafiya ”

Tashi tayi zatabar d’akin, harta fara tafiya Tajuyo tace masa”Alhaji banji kace na gaida Aisha ba ”

” fad’ar gaisuwa ta a gareta ai batada amfani Rahma, tunda nina shirya muku tafiyar ai yakamata kisan cewa inaso ki ganomin ita ne”

Murmushi tayi tareda girgiza kanta, cikin ranta tace “Alhaji kenan” 🤣
Amma afili sai tace masa “to shikkenan zanfad’a mata yayanta yana gaishe ta kuma yana cikin kewarta akoda yaushe”

“kudin hannun ku zai isheku ko?”
shine abinda ya tambayeta a memakon yabata amsa akan maganar datayi masa, sai itama ta basar, tace “zasu isa, mungode,”

Tafuto daga d’akin batare data sake cemasa uffan ba, kai tsaye compound ta nufa, driver na ganinta yataho Dasauri ya karbi handbag d’inta, sannan yabude mata gaban motar ta shiga

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tunda tataho daga makaranta take kalle-kalle tana waige ko yauma zataganshi and’aukoshi daga makaranta Kamar kullum, saide ko alamun tayar motarsu bata ganiba, afili tace “inajin yauma yarigani dawowa , ko meyasa baya jirana?”

Takardar daya wullo mata d’azu dasafe tatuna tasaki dariya tasake cewa “kome ya rubuta oho masa, DANA SANI na nunawa Diddi”

Tana tafe tana waige har Allah yakawota gida, Tun daga bakin kofar gidan ta d’aga murya tace “Diddi nadawo ” sannan ta qarasa shigowa cikin gidan, turus tayi ta tsaya waje d’aya ganin baqin fuska agidan nasu, maza ne harsu hud’u reras, guda uku suna tsaye suna buga ball atsakaninsu, gaba d’aya wandone ajikinsu three quater, sai guda d’ayan dayake zaune kusa Diddinta ko d’ago kansa baiyiba bare ya kalleta

d’aya daga cikin masu buga ball d’inne ya kalleta dakyau yace “fine girl”

‘Dago kai Diddi tayi ta kalleta tace “Alhamdulillah kinga ‘yar halak, Nihla zonan,”

Kallan uniform d’in jikinta tayi sosai, tasan fad’an Diddi baya wuce anbata kayan makaranta, Dan haka tace “Diddi ki kalli kayana Allah yau ban batasu ba”

Diddi ta kalli matar datake kusata ita wadda taketa zubawa Nihla murmushi tace”Anty Rahma kinji ‘yartaki harta fad’i d’aya daga cikin halin ta ko? ”

Matar da aka kira da Anty Rahma tayi daria tace” Nihla zonan, ina kika tsaya baki dawo gidaba har biyu tawuce?”

Qarasowa cikin rumfar tasu tayi, jin Diddi takirata da anty Rahma yasa itama tace ” Anty ina wuni ”

damuwa ce ta baiyana a fuskar matar, Dan haka tace” Nihla Anty kuma? Momy zakice kinji ko? ”

d’aga mata kai tayi, ta zauna awajan tareda cire d’an qaramin hijabinta, doguwar sumar kanta ta baiyana, Diddi tasake Kallanta tace” A’ina kika tsaya? Kintsaya kad’ar tsamiya ko? ”

Tace” a a Diddi, qara nakai wata yarinya wajan malamin mu, kullum saita dinga tsokanata tana cemin ‘yarme fad’in gira “🤣
Daria sukasa gaba dayansu harda yaran dasuke tsaye suna buga ball, amma shi Wanda yake zaune agefen Diddi ko murmushi baiyi ba bare dariya

Diddi tace” to Allah ya kyauta, aisaikiyi haquri, wataran zata daina tsokanar ki”

Mazan dasuke ball ne suka fara musu atsakaninsu, momy tace, “Farouq, Usman, Aliyu, kudena mana, banasan shirme ”

Ta kalli diddi tace “shiyasa fa banasan tafiya da maza wallahi”

Daria Diddi tayi tace “toya zakiyi tunda mazan Allah yabaki?”

Dena buga ball din sukayi, suka dawo cikin rumfar, suka zauna Nihla tabisu da kallo, dukansu farare ne Kamar ita, Wanda ke kusa da Diddi ne kadai wankan tarwad’a, bekaisu haske ba

Momy ta dubesu tace “Usman ga qanwar ku Nihla,”

Cikin wasa Farouq yace “taso nakoya miki ball my sister”
Daria kawai Nihla tayi batace masa komai ba

Momy ta kalli na gefen Diddi tace “ABBA, bakaga Nihla bane?qanwarka cefa, yarinyar Diddinka”

Sai a lokacin yakai Kallansa gareta, sau daya yakalli fuskarta, duk a tunanin su ita yake kallo, amma azahiri ba fuskar tata yake kallo ba, hankalinsa yana kan dogon gashinta, ahankali Kamar me koyon magana yace “na gan ta”

Dan Baqin ciki Momy ko kulashi batayi ba, ta dubi Diddi tace “nikam Aisha anan wajan ku Babu malamai ne masu addu’ah, irin masu roqon Allah d’innan?”

Cikin mamaki Diddi tace “malamai kuma anty Rahma? Me zakiyi awajan malamai?”

Momy tace “zuwa zanyi nayi musu bayani su temaka su tayani da Addu’ah akan Abba,😂 inma rubutu ne suyi masa saiya dinga sha, Aisha idan Abba Yazauna awaje bazakiji maganarsa ba, idan ma zaiyi magana saide kiji yanayi daqyar Kamar anyi masa dole kokuma wani d’an sarki, bayan Babu Inda muka had’a dangi da sarauta, idan kinga Abba yazage yana miki surutu da Fara’ah to yaga jirgin sama ne, shi ala dole yanaso yazama matuqin jirgin sama”

DOWNLOAD COMPLETE BELOW 

DANGI ‘DAYA CMPLT by Amnah El Yaqoub -1

You cannot copy content of this page