DA MA NI CE BY JAMILA UMAR TANKO

DA MA NI CE BOOK 2 CHAPTER 4

DA MA NI CE BOOK 2 CHAPTER 4 BY JAMILA UMAR TANKO

Nasrin ta ce “Allah sarki. Wacce irin matsala kuma?Ya ci gaba da cewa, “Bayan mun tare an yi farin ciki na amarci kamar na watanni biyu kafin halayar gaskiya suka fara bayyana.Matsala ta farko da muka fara samun damuwa itace yawan zargina, ba damar in je aiki sai ta kira ta ce ta ji muryar Mace a kusa da ni haka idan na dawo gida ta dinga binciken wayata da taga sako ko kiran da bata gamsu ba ta yi masifa, ban isa in fita unguwa ba sai tace zance na je amma duk na dauke shi a matsayin so kuma halinsu na mata.

Abu dai ya yi ta gaba-gaba na tantance

Rayyana ta raina ni bata ganin darajata balle ta

‘yan uwana talakawa idan suka zo, haka abin ya gangaro kan abokaina, taita zagin abokina akan idonsa ma ba komai ba ne. Bata dafa min abnci sai dai in fita in saya tamkar banyi aure ba amma ana ta bani shawara ana bani hakuri an ce idan ta haibu zata bari.

Bayan shekara da yin aurenmu Allah Ya bata haihuwar da namiji, sai na ga rashin mutunci kamar ana Kara mata, ta kai ta kawo

babu abokina da yake iya zuwa gidana saboda tsoron rashin mutuncinta. A ‘yan uwana kuwa kanwata ceFatima kadai ta taba zuwa gidana tayi min kwanaki amma bata ji da dadi ba, suka rabu baram-baram ta koma garin da take aure.

Kullum na kira surukata zan gaishe ta sai ta balbale ni da fada ta ce ta gaji da halayyata ina wahalar da “yarta, ba taga amfanin auren nan ba dan bani da hakuri. Ba sa ganin laifin *yarsu ko kadan kullum karana take kaiwa tana batamin suna

Na yi takaici da da-na-sa-ni ban yi auren nan ba saboda ko daya bata taba nuna min halayenta na gaskiya a waje ba, da duk son da no ke yi mata da ban Allah cikim ikonsa wata rana wata matsalarsu ta hado ta da Mamarta da yayyanta suka zo suka same ta a falo suka yi mata tatas, sai a lokacin mahaifiyarta ta yabe ni cewar ba dan uwa uwa bace da bazata yarda da halin yartaba, dan albasa ba ta yi halin ruwa ba.

Yayanta uwa daya, uba daya yace, “da ace matar da zan aura mai irin halinki ce ko na yini daya ba zan iya zama da itaba saboda

rashin jin maganarki da rashin mutuncinki. Jalo ya yi hakuri da ya iya shekaru da ke.”

Ina jin haka sai na dafe kai nace «innalillahi wa’inna ilaihi raju’un. Allah Ka canja min halin kunci da nake ciki na zama da matar nan.

Muka ci gaba da rayuwa a haka watarana na sami wata harka ni da abokaina, ta Karamar kwangila na fita tunda safe ban dawo gida ba sai karfe tara na dare, na shigo na same ta ta cika ta base gaba daya ita a rayuwarta mummunan zato take yi min a tunaninta wajen

‘yan mata nake zuwa saboda taga na fita da abokina Yahya shi kuma baiyi aure ba kuma tana ganinsa da ‘yan mata a jami a. Ita da take da auren ma ina ganinta da maza’ yan ajinsu kuma tana karbar Note dinsu ta zo gida da su amma ni bana zarginta. Na yi mata sallama ta ki ta amsa budar bakinta ke da wuya sai ta yi min addua wai ‘Allah ya sa in yi hatsari motata ta yi kwarankwatsa da ni.’ Kalmar ‘Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un.’ Na ambata na shige daki na barta.

Haka na ci gaba da zama da ita cikin rashin ‘yanci da fargaba, ina ta takatsantsan dan kada in bata mata rai a ce nayi laifi. Idan tana fushi da ni sai ta huce akan dana guda daya wanda na ke matukar ji da shi, dan ta fahimci raina yana matukar baci idan ta bata masa, sai take hucewa akansa.

Watarana tana fushi da ni sai kuwa ta tunkude shi ya fadi akan tiles da ya zo da tsautsayi sai ya karye, muka sha faman zaman asibiti na kashe kudi sosai amma ta fadawa iyayenta wai fadowa ya yi daga kan gado.

Haka har rana irin ta yau ban fadawa kowa cewar ita ta karya shi ba.

Nasrin ta yi tagumi babu abirda take sai girgiza kai tana salati a bayyane saboda tashin hankalin da take zuka a cikin kunnenta.

Ya ci gaba da Magana cikin marainiyar murya “Babu wacce ban tuna ba daga cikin jerin

‘yan matan da suka so ni a garinmu

Yelleman da na Lagos, na yi da na sanin barin

‘yan kauye masu tarbiyya na fadowa ‘yar birni. Amma daga baya na saddakar da cewa Allah ne bai so ba amma na tabbata har yanzu

da yawansu suna can suna sona duk da sun yi aure kasancewarwasu dangina ne mu kan hadu a wata hidimar suna mutunta ni sosai.

Nasrin ta ce “Kwarai kuwa komai sai

Allah Ya yarda za ayi.”

Jalo ya gyada kai ya ce, “Tabbas haka ne. Wata rana Rayyana ta tsare ni ta ce Babanta yace baya so ta dinga yin tuki da kanta saboda tana da ciwon ido dan haka duk abinda nake yi na bari na dinga zuwa ina kaita unguwa. Na amsa masa da to. Haka kuma aka yi ko me nake yi sai na bari na zo na kaita unguwa wata unguwar ma kirkiro ta take yi da gangan dan ta wahalar da ni, ban damu ba saboda bana son tashin hankali ko kadan.Nasrin ta bude baki dan mamaki tace

“abin har ya kai haka? Sun zamar da kai direba ma kenan?”Jalo ya gyada kai ya ce, “Direba ma ai yana da ‘yanci bawansu na zama. Rayanna bata zaman lafiya da makwabta ko kadan duk sun bata, gashi ni kuma da son mutane karfi da you ta sa nake ja da baya da jama’a. Gashi ko dayaushe tana yi min gaba sai muyi sati bata yimin Magana.

Gaba daya bana jin dadin

ravuwata bana samun walwala a kowanne bangare, babu: in da zan shiga in ji senyi a raina.

Hawaye ya cikawa Jalo ido haka ma

Nasrin sukayi shiru na dan lokaci kowanne yana takaici.Nasrin ta rike baki zuciyarta cike da bacin rai ta ce “subhanalla! Wannan bata da ilimin addini amma ko tana da ilimin ma bata amfani da shi.”

Jalo ya yi murmushi yace, “ke kenan da kika san za’a mutu za’ a koma ga Ubangiji ai ita ko salla ma sai ta ga dama.”Nasrin ta dafe keya ta ce, “wayyo Allah mata mun shiga uku. Ya ci gaba da cewa, “bata dade da yaye Hisham ba ta Kara samun cikin na biyu. A lokacin na sami tallafi daga gwamnati (schoolership)

па tafi London karatu a

Universit of Bedford na yi PHD shekaru uku.

Ina zuwa Najeriya akai-akai in gansu suma idan suka yi hutu suna zuwa wajena acan London dan a lokacin ta gama karatunta har ta fara aiki.

Babu abinda ke tsakaninmu a can

London din ma sai fada saboda Allah Ya yi mata mummunan zargi, duk in da na shiga ta dinga kira na a waya ta ji ko ina tare da wata, idan kuma ban amsa wayarta ba sai ta yi ta turo sakonni na zagi tana kira na mazinaci. Alhali Ubangijina shine shaidata ban taba yin zina ba tunda nake a rayuwata.”

Nasrin ta ji kwalla ta cika mata ido ta ce

“Allah sarki.”Ya sharce kwalla ya ci gaba da cewa

“Idan na zo Najeriya daga London bacin rai ne,

Idan nece su zo da fada za’a rabu, idan basu zo ba a waya zagi ne, idan na ki amsa wayarta ta yi ta turo sakonni munana.

Da na ga bacin ranta ya na Kokarin ya taba karatuna na share to na daina kula damuwarta na ci gaba da karatuna dan in fito da sakamako mai kyau. Amma duk da haka sai ta je ta huce akan mahaifiyata da kannena duk da ma Mahaifiyata tana boye min amma wasu daga cikin kannena suna kira su fada min a

boye. Idan raina ya yi dubu sai ya baci sai na kira Mahaifiyarta na shaida mata, mahaifiyata. Tun daga nan na yi alkawarin na daina fada musu komai kawai dai zan yi addu’a Allah Ya zaba mana abinda ya fi alkhairi amma bana son yin saki saboda darajar yarana.

Ina can naji an ce an bawa mahaifinta

Minister dan haka sun kaura sun koma Abuja.

Ba izinina Rayyana ta rufe gida ta kwashi yara ta canja aiki ta canjawa yara makaranta ba tare da ta fadawa Mahaifiyata ba ta bi iyayenta, sai da kannene suka je giden suka ganshi a datse, kwana da kwanaki da na kira na tambaye ta take fadamin hukuncin data yanke.

Na rabu da suna ci gaba da karatuna har

Allah Yasa na kammela na fito da sakamako mai kyau na zama cikakken Dakta. Na so in yi zamana acan in fara aiki dan Jami’ar sun so su rike ni

ina kishin kasata Naieriya yadda gwamnati ta biya min ya kamata su more mi, ina so in zauna kusa da Mohaifiyata da ‘yan uwana dan in taimake su suna cikin wahala. Haka zan so ina kusa da yarana in kula da tarbiyyarsu dan ban yarda da tarbiyyar

Rayyana ba daga ita har iyayenta.

Nasrin ta langwadar da kai dan tausayi ta ce, Allah sarki.”

Ya ci gaba da cewa “Na kunso kudina da yawa na zo na biya kudin gidana da nake haya-daman sunyi min magana idan ina so in saya, duk da gida na da tsada a Lagos sun yi min ragi

‘sosai kuma duk da haka ban gama biyunsu ba amma na biya su fiye da rabi. Munyi da su zan dinga biyansu a hankali har in gama. Gidan wata hajia ce mai kirki wacce take sona da alkhairi, mijinta ya rasu ya barta da dukiya mai yawa.

Na je Abuja na zaune da waliyinta da

Waliyina aka yi Magana sosai akan yadda zaman auren zai kasance, na shaida musu a tambayi Rayyana in har ta gaji da auren ta bani yarana in sauwake mata, ni ban fadi abubuwan

da take yi min ba amma mahaifinta ya zakalkale yana ta zano sharri wanda ban san an yi ba. Gaba daya wajen suka ga laifina bana so inyi masa musu ko in Karyata shi sai da yagama fadar nasa sannan na kalli Rayyana nace ta rantse idan haka aka yi, da yake bata tsoron Allah ta rantse dan haka na bar ta da Allah.

Na gyara zama na fara karanto abubuwan da suke yi min daga nan kawunan waliyanmu ya kulle suka rasa mai gaskiya a cikinmu kin san manya sai suka ce abar zancen kuma a cire maganar rabuwa a sulhunta. Ni dai ina kan bakana ko ta biyo ni Lagos mu zauna

•ko ta bani yarana a tafi do su, Ta rantse ita da Mahaifiyarta ba za’ a ba ni yara ba sai dai nima in dawo Abuja a ba ni wani aikn mai kyau. A lokacin ne na fada musu bazan iya yin aiki a karkashinsu ba yanzu nafi son in koma Lagos in ci gaba da koyarwata.

Nan dai suka nuna basa son saki kuma aka amince zata dawo Lagos nan da watanni uku idan yara suka yi jarabawar canja aji. Aka bani hakuri na amince na dawo Lagos na zauna

Hmmmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE