DIYAR DR ABDALLAH

DIYAR DR ABDALLAH CHAPTER 2 HAUSA NOVEL

Haka Ruma Sa’u ta zauna sai ciye ciye da lashe lashe takeyi, Rahina batada karanci. Ta tabbata abinci bai tsinke mata ba.

WiFi din gidan aka kunna mata tayi ta bi layi layi a

Instagram, tareda amsa comments din da ake mata. Har yanzu dai Qwaro baibi ta kanta ba.

Cikin takama Mahfooz ya fito daga bayi, wanka yayi kana ya dauro alwala. Yadda yake abinsa zaka san lallai yana bala’in ji da kansa. Ash Jallabiya dinsa ya saka saiya wuce Masjid, bayan ya dawo sai yaje durowa dinsa ya dauko kayan kwallon sa. Miskili ne na bugun jarida.

Gashi ya shahara sosai wajen buga ball, za’a iya ce masa

Messi din Najeriya. Yaje Dubai sau biyu wani academy amma basu dauke shiba sannan har Under 17 ya buga ma Naija. Yanzu dai yana buga ma Kaduna United ne katin ya sake samun wani waje a Turai. Sannan kuma shi civil Engr ne, yana aiki a wani campany Julius Berger.

Shima ya shahara a Instagram tunda an san shi duk kasar,

Uwa uba gashi dan masu hannu da shuni ne. Baya rasa hotuna gefen motoci masu alfarma, sannan ya goge, ya iya saka sutura.

Yanada kyau kuma ya cancanci a soshi. Idan yana magana dole zuciyar ka zai dan sosu. Akwai hikima ga bala’in kwarjini. Yan mata kullum binsa suke yi suna crushing. Yana kula wanda yake kulawa ayi soyayyar shan miya. Tun farko zai fada maki cewa bai tashi aure ba. Sau da dama matan suna tunanin karya yakeyi. Idan suka gwada mashi madarar soyayya zai canza ra’ayi. Amma akasin haka suke samu,

daga masu sine mashi suna ya cuce su, bai aure suba amma sun bashi benefits din masu aure.

Da Mahfooz ya gama saka kayansa, saiya dauki takalmin sa ya wuce filin ball. Bai kunna datan sa ba balle ya shiga

•Instagram. Kwana biyu baya jin dadin jikinsa. Suna match da yan Eyimba United sai wani ya buge masa gwiwa, toh ya samu karamin injury.

“Rahina me zaka yi ne?” Ruma ta tambayeta yayin da taga ta kwashe takardu ta nufe gefen data kebe ma kanta a matsayin library.

” Wallahi ina da Impromptu test ne,” ta amsa.

“Inace kin gama, banaga hoton kinyi bautar kasa a

Instagram ba???”

“Eh, PGD nake yi,”

“Masters?” ta fada cikin sauri.

“Eh toh, bai kai Masters ba. Post Graduate Diploma ne”

Girgiza kai Ruma Sa’u tayi. Amma sam bata gane abinda Rahina tace ba. Ita a sanin ta. Kana gama degree sai masters daga nan ka zama professor. Abin yayi mata sabo wai wani abu PGD.

Rahina tana karatu ita tana chatting, anan tayi updating duka apps dinta. IPhone X ne ta siya a hannun wani friend dinta na One Love group. Clean wayace babu inda ya fashe.

Bature yace, “an ideal mind is a devil’s workshop” kuma hakikanin gaskiya ne saboda tana cikin zaman banzan ta sai dabara ya fado mata.

Bulala, nace ba… Ina admission letter dinki na degree zan duba abu ne, ” Rahina bata kawo komai cikin ranta ba saita mike ta dauko files dinta. Anan ta ciro admission letter dinta na Kaduna State University.

Cikin murna Ruma Sa’u ta karba ta soma dubawa. Data faka idon Lala tana karatu saita dauki hoton admission din.

Bayan minti biyar saita mike tsaye tace zata tafi amma gobe idan Lala ta fito daga test dinta tayi kokarin kiranta sai su hadu.

Ta soma tafiya zata tafi, dayake mirror din yana gefen kofa, sai Ruma Sa’u ta dauki wani turare mai dan karin tsada ta saka Jakarta tareda fadin, “Ina so,” bata damu da ko an bata ba. Ita dai ta dauka.

Miyau mai zafi Lala ta hadiye saboda taji haushin abin.

Turaren yana cikin masu tsadar wajen sannan kadan tayi amfani dashi. Tana lura da Ruma Sa’u dazu datake wasan turaruka. Domin harta mirror selfie tayi das Video tana fadin nanne dakinta.

Kai tsaye café Ruma Sa’u ta wuce. Anan ta nuna masu

hoton tareda fadin abinda take so ayi mata. Scanning da

editing takeso ayi mata. A cire sunan Rahina a saka nata.

Tsab ta mance ita shekarar ta biyu da farawa. An juya date

din samun addmision amma abinka da wanda bata sani ba,

balle idan Fa’iza tana bama su Inna Labari Ruma ba sauraro

takeyi ba.

Batama san da wani abu wai shi Matriculation number na.

Suma yan café din basuyi mata magana ba. Sun lura baho

ce irin yan matan nan marasa abin yi. Anan suka karba

dubu biyu wajen ta sannan suka tausaya ma wanda zata

damfara da admission letter din.

Ranta fari tas Fa’iza zata kiyaye ta daga yau. Zata cigaba da

cin karenta babu babbaka. Balle kuma yanzu ta samu kawa

mai kashin arziki. Duniya yana kai mata yadda take so.

A filin kwallon Mahfooz ya soma ganin dishi dishi, baya iya

passing kwallo da kyau. Kafin ka sani sai ya taka Kafar

opponet dinsa. Aikam bai yi wata wata ba ya kwada mashi

mari. Suma yan team dinsu Mahfooz suka rama mashi.

Anan fada ya kacame.

Nan maza suka yi ta bama hammata iska. Shi kam Mahfooz

tunda ya sha mari yayi gefe yana jinyar kansa. Ashe wanda

ya mare shi ya dade yana jin haushin sa. Anan ya sake cin

kwalarsa yayi ta kilarsa. Duka yakeyi kamar an aika ya

kashe shi. Coach dinsu da kyar ya kwace shi. Duk an fasa

mashi baki jini sai kwarara yake yi kamar famfo.

Garin banza Mahfooz zai mashi duka. Amma wannan karan

abin yazo da rashin lafiya. Nan aka wuce dashi ‘Abdallah Specialist Hospital’ dake

Alkali Road tunda ansan shi dan masu dashi ne kuma ko nawa ne kudin asibiti za’a biya mashi.

Naseera tana dakin Babanta, babu wani emergency a asibiti sai ta dawo wajen mahaifinta domin tayi mashi jinya.

Mahaifinta yanada cutar Aplastic Anemia kuma yanzu haka yana bukatar bone marrow transplant.

Tabbas tasan ita match ne da Babanta, da farko bata maso tayi gwaji ba amma sai tayi. Anan ne tasha madarar mamaki. Watau bone marrow dinta bai yi matching da nashi ba.

Anan ta soma gwaji kala kala bila adadin. Amma duka haka abin yake. Harta was asibiti ta tura samples amma aka ce mata ga gaskiyar zance.

Sanda take karama ance mata genotype dinta AS ne saboda ranar da aka haifeta ka’ida ne ayi ma yaro gwaji kafin subar asibiti, amma dataje medical school ta sake ma kanta test inda ya fito a AA. Abin ya bata mamaki amma tasan cewa shima karfen nasara bashi da tabbas.

Yanzu ta kasa saisaita tunaninta waje daya, da farko tasha kila anyi adopting dinta ne. Amma kuma da kanta taje durowan da ake ajiye takardu, haka ta rinka bi har shekarar da aka haifeta. Taga cewa tabbas Umma Hajia Binti ta haifeta. Kuma Nurse on duty na Ranar Jamila Magaji.

“dan Baba bashi bane ubanta toh waye?”ta tambayi kanta tambayar da babu wanda zai bata amsar, “Shi kenan yanzu ba ita bace diyar Dr Abdallah.” ta sake ayyanawa.

Wani yar taji a jikinta ta soma tausayin kanta. Duka wani alfahari datake yi akan asalinta ya rushe. Ko ina bata kunyar fadin Sunanta Naseera Abdallah Kwarbai. Yanzu tasan she doesn’t deserve that name.

Haushin Ummanta ya dirar mata. Da mutuwa da haihuwa ai duk na Allah ne. Mamaki takeyi yadda tayi sabon Allah domin ta sameta. Taci amanar aurenta da Babanta sannan kuma ta cuce ta. Gashi yanzu Babanta ya riga ya saka rai da cewa Naseera zata bada bone marrow dinta. Ta ina yanzu zata soma gaya mashi ita ba yarsa bace. Ita shegiya ce wanda aka haifa ta mugun hanya. Ta ina zata ce masa Ummanta ta cuce su. Tabbas Dr Abdallah zai iya hadiye zuciya ya mutu.

Sau da dama idan Ummanta tana bata labarin irin wahalar data sha kafin aka haife ta tausayi take bata. Amma ba tayi tsammanin akan haihuwa zata zubar da mutuncin taba.

“Yaushe za’a yi surgery din? ” Dr Abdallah ya tambaye

Naseera wanda ke kan sallaya tana tunani bayan ta idar ta sallah.

Murmushin karya ta kwakulo, “Jiya machine din test baya aiki, sannan yau kuma Dr Chinedu bai zo ba, wai yanada family emergency. In sha Allah gobe za’a yi test din. Cikin satin nan zaka warke.”

Tasan karya takeyi, amma wannan yafi mashi sauki akan abinda yake faruwa.

Beeper dinta ya soma ruri, anan ta mike tsaye. Labcoat dinta ta saka saita masa murmushi ta fice. Murmushi sukayi ma juna ba tareda sun ayyana wani abun a fili ba.

Naseera itace abin alfaharin Dr Abdallah. Duk da tana mace bai taba damuwa ba. Shi dama addu’a yakeyi akan ya samu dan da zai jikan sa. Fata yakeyi ya samu tsawon kwana saboda yaga aurenta.

Emergency ward ta nufa, anan taga masu kwallo sun kawo mutane kusan shida duk da ciwo a jikinsu. Da ita da sauran likitoci da taimakon was nurses suka soma basu first aid.

Uku daga cikin su za’a kwantar dasu, sauran ukun kuma bandage ne ake nade masu jiki inda ke zubar da jini.

Bayan an kwantar da sauran uku, sai wani daga bisanin wanda ba’a kwantar ba ya dawo yace shima yana so ya kwanta domin ya samu sauki sosai.

Shi a lokacin ya lura da ita, gabansa yayi mugun faduwa.

Tanada yanayin fuskan da bazai taba mancewa ba. Fuskan daya jawo mashi tashin hankali da rudani. Fuskan da yafi tsana a duniya. Abin yayi mugun basa mamaki, saidai kuma dama ya taba jin ance kowa yanada lookalike dinsa a duniya. Nan take tsanar ta ya dirar masa a birnin zuciya.

“Ciwon da kake dashi bamai tsanani bane, kawai kaje gida ka huta zai fi barnar kudin asibiti,” ta fadan masa cikin kulawa.

“Ban san sanabe, babu ruwan ki ban tambayeki ba” ya

amsa a hasalce. Saida ta daga ido taga ko waye zai mata rashin mutunci amma duk stitches a fuskan sa. Da kafada ta amsa mashi saita kira Nurse domin su bashi daki.

Washe gari…

Ruwa aka kwana ana yi, garin yayi duhu ga sanyi da yake tashi. Nurse dinda take duty tazo wucewa sai taga wutan dakin Mahfooz a kunne, duba karin ruwan tayi taga yana shiga saita kashe mashi wuta ta fice.

“Daki ne ciki da tarkace, komai na cikinsa soho ne. Sannan ga yanan gizo da was manyan manyan qwari. Ga bakin duhun dayake wajen, banda warn Kura da tsoffin kaya baka jin komai’

A firgice Mahfooz ya tashi yana salati, saiya ruga yaje ya kunna wutar. Zaman dirshan yayi a bakin kofar yana dafe kansa.

“Same dream… Harda girma na,” ya fada yana hawaye. A duniya baya san duhu. Yasa yanzu a kalla shekara goma sha biyar kenan kullum da wutan lantarki yake kwana. Idan babu wuta kuma saiya kunna lantern ko candle har a dawo da wutar ko asuba tayi.

Anan ya karasa zaman sa kafin asuba yayi inda ya tashi yayi sallah saiya koma gadonsa.

Zulumi fal ran Naseera, abin duniya yayi mata cinkoso. Yau ne dodon bango zai fito. Ance dama ranar wanka ba’a boye cibi. Idan da sabo yaci ace ta saba da yadda zuciyar ta ke mata bugu. Amma sam kullum daci take ji sabo a ranta.

Fargaba kala kala, sai wani tunanin ya fado mata idan

yanzu Baba ya kore ta tareda Ummanta akan wannan abin fah. Saboda tana gani a fina finai da kuma Littatafai. Saidai kuma Dr Abdallah mutum ne mai dattako da mutunci.

Akwai shi da sanin ya kamata cikin al’amarin sa.

Sanye take cikin doguwar riga pink, ita ma’abociyar kwalliya ce saboda ta iya har na zuwa biki. Saidai tun sanda wannan abu ya faru fuskanta payau yake bai hadu da hoda ba. An saba mata lakabi da Dr yar gayu saboda kokarin yanda ta iya murza hoda da jambaki. Gashi hancinta yayita sheki na bronzer.

A hanyar kitchen ta hadu da Ummanta, a dikilce ta gaidata.

Ita kuma Umma ta amsata fuska duk annuri. Hada kofin shayi tayi tasa ma kanta a flask saita fice. Ga dankalin turawa da sausage Umma tana soyawa amma saboda abinda takeji a ranta yasa ta daina cin girkin ta.

Koda ta isa asibiti dakin Babanta ta fara zuwa, a zaune ta gansa DR yana mashi bayanin al’amuran asibitin.

Rinsinawa tayi har kasa ta gaida shi saita samu gefe ta zauna. Tana cikin waige waige saita lura harya sha kofin shayi. Shine ya umurce su akan bai san su rinka kwana, an hada shi da nurses da zasu rinka lura dashi.

Bayan likitar ya fita sai tayi mugun ajiyar zuciya, kallon ta yayi sai yace, “Dr Lafiya dai koh?”

Murmushi tayi mashi, dama idan kana san ganin murmushin ta toh sai tana tareda iyayen ta. Yanzu kuma ta ware Umma saida Babanta.

“Idan wanda ka yarda dashi duk duniya yaci amanar ka ya zakayi?” ido ta bishi dashi domin taga yadda yanayin fuskan sa zaiyi.

“Abu daya na sani Nasira, kowa makiyin kane. Kuma kowa masoyinka ne. Idan kika rike wannan toh babu abinda zai baki mamaki. Kuma duk nauyin laifin da mutum zai maka, yana da kyau ka zamana mai uzuri. Kila akwai wani dalilin daya sa ya aikata hakan wanda kai baka sani ba,” saiya dauko kofin ruwa ya kurba. Anan yayi ajiyar zuciya saiya cigaba.

“Yasa idan abu ya faru ya kamata mutum yayi hak’uri yayi dogon nazari. Na san hakuri ba karamin abu bane. Yanada wuva saboda zucivar ka zai ta tafasa sannan ga shedan da zai rinka kawo maka wasiwasi. Amma idan ka dake kabi diddigi al’amarin zakiga ashe ba wani abin tashin hankali bane.”

Da kai ta amsa mashi saita soma duba BP dinsa, shi kam binta yake da idanu. Akwai damuwa karara fuskanta. Amma tunda bata kasa dashi ba bai kwasa ba. Bayan ta gama saita fita tayi rounds.

Ta dade wajen Babanta har an kusan gamawa. Daki daya ya rage na yan kwallon da aka zo dasu jiya. Bata kawo komai cikin ranta ba suka shiga tareda sauran residents. Anan aka

gama duba shi.

Sun tafi sai Supervisor dinsu ya mika mata wani magani taje ta bama Mahfooz Abubakar Gwaiba. Bata san waye ba ta shiga dakin farko amma aka ce mata dayan dakin ne.

Shi kuma tun jiya da brothers dinsa suka zo diba shi tareda kai masa kaya da wayansa bai kunna ba sai yanzu. Anan yaga notification kaca kaca. Baibi takai ba sai ya shiga

•Instagram Explore. Hoton Ruma Sa’u ya gani yana yawo.

Shafunan su Arewa da sauran su sunata reposting dinta.

Bata burge shi ko kadan, ya lura tanada hayaniya. Kullum tana biki kokuma wajen cin abinci. Bai taba ganinta a gida ba sai wannan karan. Gata a gaban madubi cikin daki na alfarma. Tayi kyau babu haufi anan ya shagala yana kallon ta. Burin sa yanzu ta zama yar hannun sa. Zaiyi liking kenan sai yaji ana taba kofa.

Sallama Naseera tayi tareda tura kofa, saita karasa inda yake domin ta bashi maganin. Bai dago ba balle ya kalle ta.

Magana ya soma yi cikin izza da takama domin ya nuna shi din dan wani ne.

“Waye jiya ya shigo dakina ina barci ya kashe min wuta?”

Ya bala’in bata haushi, ta lura bai da mutunci. Sannan idan yanada abinda zaiyi yazo yayi mata tunda asibitin mahaifinta ne.

” Nice na kashe danake rounds, menene?”

Gyara zaman sa yayi saiya kalle ta. “Hmmm, zany maganin ki.” kawai ya furta saiya kwanta.

“Gashi wannan zaka sha sau biyu a rana, da safe guda….

bata karasa ba ya daga mata hannu alamar tayi mashi shiru.

“Dalla malama go and call your supervisors…. Kina tunanin zan yarda da abinda intern or whatever tace ne? ” sai yaja karamin tsaki tareda kwanciya yana kallon sama.

An riga an masu ethics a medical school, ba’a fada da patient. Yau da sana’ar conductor takeyi da sai taci kwalar sa taga wanda ya daura uwarsa aure.

Fita tayi ta koma bakin aikinta, sam baya gaban ta. Idan irin wannan patients din marasa da’a zata rinka cin karo dasu yafi mata sau dubu akan abinda yake wakana a rayuwar ta.

Ranar ya tafi mata sumul ba wani tashin hankali kuma. Ta lura Mahfooz baida mutunci saita kiyaye shi. Sannan ta dauki alwashin yau zata gayama Babanta komai bayan sallar isha. Bawa baya wuce kaddarar sa. Duk abinda zai faru tasan bazata kunyata ba.

Yamma yayi wajen karfe shida, ta hada kayanta kenan zata koma gida tayi wanka sannan ta dauko ma Babanta abincin dinner.

•Har zata fita sai DR Abdallah yace ta biya Kawo ta kaima

Nurse Jamila Insulin a diabetes dinta. Nurse Jamila tana cikin manyan kuma wanda suka fara aiki a asibitin. Kuma ranar da aka haifa Naseera Nurse on duty bata zoba itace ce ta taimaka tunda DR baya kasar lokacin. Yasa yanzu kamar yar uwa take wajen Naseera.

Ta soma tafiya saita tuna Anty Jamila Mijin ta yay masu gini last week suka koma sabon gidan. Suna jinyar Dr Abdallah basu samu damar sun ie sun gani ba.

“Wani anguwa ne?” ta tambaye shi

“Kawo baida wuyan ganewa, ga address din nayi maki copying, ki bama masu gadi kawai sai a ajiye mata”

Napep tayi chata tunda bata san wajen ba, kafin ayi mata kwace ana ganinta mace kuma dole tayi ta tambayoyi. Balle zata dawo asibiti anjima sai lokacin ta tafi da motar.

Mai napep din yaga kalar manya, bai san wajen ba amma ya dauke ta. Da suka kai Kawo anan suka soma tambaya.

Hadari ya doso sannan ga dare. Mutane duk sun kare a wani layi da suka shiga. Anan suka ga wasu samari su uku kofar wani daki. Mai napep yace ta sauka ta karasa dakalin da suke zaune. Shi baya so ya sauka wani yay gaba da napep din.

Ta sauka ta soma gaida su saita lura da irin kalar mutanen.

Yan sara suka ne, ga zungureren wuka hannun daya,

sannan duka wiwi suke busa. Mai nape shima yana ankara ya burga ya gudu baibi ta kanta ba.

Anan wannan mazan suka soma murmushi tareda damfaro

kanta. Ita kam baya ta Soma ja tana addu’a cikin ranta.

Miyan bakinta a bushe yake amma tayi kokarin ta soma masu magana.

“Dan Allah kuyi hakuri ban nufe ku da sharri ba. Tambaya nake so nayi amma kuyi hakuri kubar ni na wuce”

Dariyar Keta suka soma yi, “Yar shila karki damu yanzu zamu fige ki mu wuce.” daya daga cikin su yace saiya nufeta gadan gadan ya fizgo mata hannu ya janyo ta jikinsa. Anan ya soma lashe mata kumatu yana dariya.

Suma sauran dariya suka soma, banda kaurin Wiwi da warin hammata batajin kowane irin wari jikinsa. Idanta ya fito tana basu hakuri. Sunata mata dariya.

“Shegiya tana fah so, jibe ko kuka batayi sai hun banza.

Wanna kana ganinta kaga jarabbaba…. Yasa saina kwasa rabona” sai suka sake fashewa da dariya.

Wani ne yazo wucewa saiya gansu, “Kai meye haka kuke yi?” ya fada a hasalce.

“Haba Qwaro karka saka mana baki, yar hannun mu ce fah, kuma nanfa ba filin ball bane. Nan fah area dinda muka fi kwarewa ne. Kabar mu muyi abin mu dan Allah.” ya fada yana lankwasa baki.

Bata san waye ba, kuma koma waye Qwaro yafi su imani.

Anan ta kalle shi da kyau. Tunda take bata taba tunanin cewa ganinsa zai taba mata dadi ba sai yauzu. Asalima bata

fatan su sake haduwa. Cikin hanzari ta soma magana.

” Mahfooz dan Allah zo ka taimaka min.” idanta a kade yake. Kana ganinta kasan akwai razana karara. Shiru yayi bai ce komi ba. Dama Chemist zashi ayi mashi allura tunda ya sallama kansa a Abdallah Specialist.

Duk kawo an san shi, ana masa lakabi da suna Qwaro a filin kwallo. Saboda akwai kwari masu tirjiya har wanda suke sati biyu raye ba tareda kansu a jikinsu ba.

“Dan Allah Mahfooz kace ka sanni,” ta Cigaba da rokon sa.

Jikinta sai bari yake. Gumi kawai takeyi. Ga wani mugun daci datake ji cikin ranta. Zuciyar ta kamar zai fashe, ta kasa saisaita tunani waje daya. Wanda ke rike da ita ya sake lashe mata kumatu. Anan tsigan jikinta ya kuma tashi. Daya daga cikin yan daban ya bude dakin su dama kofar waje ne sun soma janta.

Qwaro bai hana suba yana kallon yanda take tiriewa tana dambe dasu. Tabbas idan yayi masu magana yasan zasu daina. Ana ganin mutuncinsa. Amma yayi shiru. Anan Naseera ta samu ta yanka ma daya daga cikin su cizo wanda yake kokarin rufe mata baki. Aikam nan ya yanka mata mari. Layin shiru daga su sai Qwaro.

Haka ya tsaya yana kallo, haushi take bashi. Yay mugun tsananta. Yasan koda sun illanta ta bazai saka ya daina mugun mafarki ba. Bazai dawo mashi da farin cikin sa ba.

Bama ita tayi mashi laifin ba, yana gain sanda aka yi mashi tana rarrafe. Amma still, ubanwa yace tayi kama da makiyan sa.

“Mahfooz dan Allah ka taimaka min,” tayi ta nanatawa

jikinta sai rawa yake. Dumi taji a fuskanta. A karo na farko hawaye yana sauko mata a idanu na tsawon lokaci. Kadan kadan ya fara sai kuma a guje kamar famfo. Nan ta rinka rero kuka mai ban tausayi. Duk rashin imanin ka saika tausaya mata. Yi takeyi tana shesheka. Amma Mahfooz ko gizau, tsananta ya cigaba.

“Nifa ban santa ba,” ya fada saiya fice.

“Babu ruwana, da banbi hanyar ba dama zasu yi abin su. I did not rape her, yayita nanata ma kansa yayinda yake tafiya.

Anan suka samu suka sake toshe mata baki tareda karasa

ingiza ta cikin dakin. Duka su ukun suka yi mata fade sai suka wurgata waje kan titi. Gashi sun kwace mata waya da kudinta.

Tana cikin ruwan take tafiya gashi da bala’in karfi. Bata ko ganin gabanta banda kuka babu abinda takeyi. Anan ta fantsama titi. Wani mota yazo da gudu bai yi tsammanin wani zai shiga ba saboda yanda ake kwarara ruwa. Nan ya kadeta tayi gefe.

Anan mai motan yayi salati ya fito a guje ya duba ta. Sake salati yayi dayaga wacece.

“Naseera me kike yi a waie cikin daren nan?”

A hankali ta soma bude idanta, sai taga wanda yake rike da ita ya rungume. Murmushin takaici tayi. Numfashinta yana kokarin daukewa saboda ta galabaita. Da kyar ta iya magana,” Uncle Sadiq, sun min… sun min fade…. Kuma bai hanasu ba… bai hanasu ba…. Ni ban mashi komai ba.

Banma taba gain saba amma ya kafa min karar tsana.”anan ta sake fashewa da kuka mai taba rai.

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE