NUFIN ALLAH CHAPTER 9 BY AYSHA DAN SABO HAUSA NOVEL

📱 *NUFIN ALLAH…!* 🤲🏻
*_Arewabooks@ayshadansabo_*

*Paid book:500 08167768704*

*Chapter 9*

_Free page_

Duk yadda Najma taso su tattauna maganar da Hakimi ya yi na zuwansu kaduna Inna Mairo taƙi bata dama. Shigewarta ɗaki tayi sabida yadda take jin kanta na wani sarawa da matsanancin ciwo, ga idanunta da sukai masifan yi mata nauyi tamkar an ɗaura musu bulo. Najma tayi zugum zaune a falon tana jin hankalinta na sake tashi.Dukkanin jikinta na yin tsananin sanyi,domin ta tsani ganin Innarta a cikin hali na damuwa. Taja ƙafa ta nufi ɗakinta hawayen da take riƙewa na ɓalle mata, ta jima zaune a bakin katifarta tana rasa irin tunanin da ya kamata ta faro ma.Sake fitowa tayi ta nufi ɗakin Inna don ganin a wani hali take.A kwance ta sameta hawaye na bin fuskarta, hakan ya sanya Najma ƙarisawa da sauri bakin katifar tana faɗin, “Inna don Allah karki sanya damuwa a ranki!” Inna ta sake rintse idanunta, kafin tayi magana cikin rawar murya ta ce, “Najma bani ruwa da maganin da aka kawo in sha.” Najma ta fice a guje ta ɗakko ruwa da maganin ta bai wa Inna.Ta zauna kusa da ita tana faman sharan hawaye kamar yadda Innar keyi. Sai da ta ga bacci ya fara ɗaukar Inna Mairo sannan ta miƙe ta nufi ɗakinta.Nan ma ta jima bacci bai ɗauketa ba sabida damuwar da ke cinkushe a zuciyarta. A ɓangaren Inna Mairo kuwa ba bacci ne ya kwasheta ba, tayi wa Najma lamfa ne don ta je ta kwanta.Amma ba don wai da gaske baccin ne ya kwasheta ba. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, kwana tayi cikin tunani da damuwa mai yawa. Sai bayan ta samu da ƙyar ta sallaci asuba sannan bacci ya sace ta, hakan yasa bata farka ba sai wajen goman safe. Ta tadda har Najma ta gama tuyan ƙosai ta gyara ɗaki.Tausayin Najmar ya kama zuciyarta don tabbas tana wahala matuƙa da irin bautar da take yi, shiyasa dole damuwa ba zai bar zuciyarta. Bayan tayo wanka ta sanya kaya sai Najma ta gabatar mata da koko da ƙosai ta karya, ta sha magungunanta bayan ta gama karyawan ta kishingiɗa daga tsakar ɗakin. Misalin sha biyu na rana sai ga sallamar su Hanne da Luban gidan Hakimi. Najma ta taryesu cikin farin ciki, suka isa ɗakin Inna Mairo hannun Lubah ɗauke da kular wainar shinkafa, ita kuma Hanne nata hannun riƙe da kular miya. Suka gaida Inna Mairo tare da yi mata sannu da jiki, ta amsa cikin fara’a tana tambayarsu mutan gidan suka ce lafiya lau. Suka aje kular waina da haɗaɗɗiyar miyan taushe da Inna Karima ta yisa, suna mai sanar da ita cewa gashinan in ji Innarsu. Inna Mairo tayi godia suka nufi ɗakin Najma don sakewa suyi hiransu irin ta ƴan mata, waɗanda suka shaƙu da ƙaunar juna tun daga yarinta har grima. Inna Mairo ta buɗe kular wainar tana yaba kyawun da suyan ya yi ,don ya yi fari tar dashi abin sha’awa. Ganin yawan wainar zai ishe su har dare ma suyi taci, sai Inna ta sanar da Najma cewa kar a ɗaura komi da rana don wainar zai ishesu watakila ma har ya yi musu yawan da sai dai suba almajirai sadaka idan ya ragu.Kusan yini su Lubah suka yi a gidan Inna Mairo, hakan sai ya kawo raha da annashuwa hatta a zuciyar Inna Mairo. Wacce ta tashi cikin ƙarin damuwa da tunanin yadda zata bi Hakimi su fuskanci Gwaggon kaduna, alhali rabonta da garin kaduna da Gwaggon shekaru kusan bakwai kenan.Zuwansu Lubah da Hanne suna hira da raha a cikin ɗakinta,sai ya sanyaya zuciyarta sabida wasu daga cikin hirarrakinsu dake sanyata cikin nishaɗi. Sai can bayan la’asar suka bar gidan bayan Najma ta wanke kular waina da miyar da suka kawo don su wucewa Inna dashi. Ta dawo daga yi musu rakiya tana ji zuciyarta na sake cika da ƙaunarsu,domin sune farin cikinta kuma ƴan uwan da take wa kallon tamkar jini ɗaya suke da juna.

Kamar wasa sati ya zago ya rage saura kwana ɗaya su Inna su wuce kaduna tare da Hakimi kamar yadda ya faɗi. Da dare misalin ƙarfe tara Hakimi ya aiko Auwalu ya sake jaddadawa Inna Mairo su shirya da wuri, domin yana so su isa da wuri sabida ba kwana zasu yi ba. Inna Mairo ta aika Auwalu ya sanar da Hakimi cewa zasu shirya da wuri idan Allah ya yarda, sannan ya faɗi masa ta gode da dukkanin ƙoƙarinsa. Bayan tafiyar Auwalu Inna Mairo ta dubi Najma da ta zuba mata ido don son jin ta bakinta, ta ɗan taɓe baki kaɗan tana faɗin, “Najma to kinji dai saƙon Hakimi, idan Allah ya kaimu sai ki shirya da wuri. Ƙosan ma ayi kwano guda ne kawai yadda zai ƙare da wuri, sabida kar mu makara shirin akan lokaci.” Najma ta jinjina kai cike da gamsuwa da kalaman Inna, ta buɗe baki cikin sanyin muryarta ta ce, “To shikenan Inna, Allah ya kaimu goben lafiya.” Inna ta amsa da cewa, “Ameen ya Allah!” Daga haka suka dinga tattauna matsalar Gwaggon,Inna na sanar da Najma irin fargabar da ke damun zuciyarta.

Washegarin ranar misalin tara da rabi na safe Najma ta tashi daga gindin murhu. Wanka ta faɗa a gaggauce bayan ta kammala gyaran wajen da tsakar gidan ma baki ɗaya.Lokacin da ta fito ta samu Inna zaune a falo tana shan koko da ƙosai, ta wuceta zuwa ɗakinta don shiryawa bayan tayi mata sannu. Cikin wata straight gown na wata atamfa mai kyau Najma ta shirya, atamfar na ɗaya daga cikin waɗanda ake aikowa Inna Mairo dasu duk sallah. Kalar a tamfar mint green ce da akaiwa adon ƙananun zane da red and black.Sosai kalar ya haska black skin ɗin Najma ya yi mata mugun kyau. Ɗinkin ya zauna a jikinta domin telan da ya ɗinka kayan yana da ƙwarewa sosai, kuma shi yake musu ɗinkin sallah tare dasu Lubah sai Hakimi ya biya kuɗin ɗinkin. Ta ɗauki ƙaramin madubi ta kalli kyakykyawar fuskarta a ciki, wanda ya yi fresh dashi babu ɗigon finfus ko makamancinsa akan fatar fuskar. Kamar ta share karta shafa komi akan fuskar,sai wata zuciyar ta bata shawarar shafa powder. Ta shafa kaɗan tare da zizara baƙin kwalli a fararen idanunta,cute lips ɗinta ta gogawa lip balm mai arha daidai ƙarfinsu. Ta sanya wasu ɗan kunni masu faɗi a kunninta, waɗanda suka ƙawata kyawun fuskarta da shigar jikinta. Turaren Safeer oud mai ƙaramin kuɗi ta fesawa jikinta,tana aje kwalbar turaren daidai da ƙwalla mata kira da Inna tayi. Hakan ya sanya ta fito da sauri falon tana amsa kiran da Innar ke kwaɗa mata. Inna Mairo da ke daga tsaye yafe da mayafi, ta sauke manyan idanunta akan Najma tana yaba irin kyawun da tayi. Cikin murya mai cike da nuna kula ta dubi Najmar ta ce, “Najma me kike yi ne haka har gashi Hakimi sun iso shi da Auwalu suna mota a waje, maza ki ɗakko mayafi mu wuce kar a cigaba da ɓata masa lokaci.” Najma ta buɗe baki cike da mamakin isowar su Baba Hakimin ta ce, “To Inna bari nayi sauri, ai dama na kammala shirin.” Daga haka ta juya zuwa ɗakinta don ɗakko gyalenta mai kyau irin masu arhannan daidai ƙarfin talaka.Ta yafashi tana zura takalminta flat mai tudun ƙasa kaɗan, ta fito daga ɗakin zuciyarta na cika da ɗokin tafiyar. Ita ce ta kulle gidan ta fice ta samu su Inna a cikin mota, ta buɗe back seat inda Inna ke Zaune ta shige tana mai gaida Baba Hakimi dake kame a gaban motar. Ya amsa da tsananin kulawa yana yi mata ba a da cewa sai da ta ja musu aji kafin ta fito. Najma tayi dariyar maganarsa tana duban ɓangaren driver seat ,ta gaida Yaya Auwalu kamar yadda suke kiran babban ɗan Hakimin. Ya amsa shi ma da kulawa yana mai kallon fuskar Najma ta jikin madubi, tayi masa kyau matuƙa da gaske hakan ya sanya yaji zuciyarsa na sake dilmiya a ƙaunarta da yaketa binnewa tsayin shekaru biyu zuwa uku. Ya san cewa Najma matar manyance kuma baya cikin irin choice ɗinta, domin bai tsaya ya yi zurfin ilimi irin wanda take da burin samun mijin aurenta dashi ba. Sannan shi bai taɓa sha’awar ya bar garin giwa ba, bare a sanya rai idan ya shiga birni zai yi wayewar da zai sake zurfafa iliminsa. Hakan yasa yake ta danne soyayyarta yana gayawa zuciyarsa cewa basu dace da juna ba shi da Najma, domin ita kallo ɗaya za a mata a ɗauka cewa wata wayayyace da ta samu ilimi mai zurfi.Sabida yadda suke da wayewar kai ita da ƙanninsa su Hanne.Sannan daidai gwagwardo suna shiga mai kyau koda ace na robobin atamfa ne, zaka gansu masu kyau a jikinsu, sam basu yadda da mugun shiga don suna zama a ƙauye ba. Tunda sun sama ilimin boko mai kyau,kuma da wayayyu sukai cuɗanya ba ƴan ƙauye ba a makarantar kwanar da sukai.Shiyasa kansu a buɗe yake sosai, hatta turanci sun jisa daidai gwagwardo, sai dai kawai ace basu yi zurfi sosai wajen iya speeking ba sosai.

Ya tashi motar bayan Hakimi ya bashi umurni. Suka kama hanyar baro garin giwa zuciyar Inna Mairo cike da zullumi,sabida bata san irin tarban da zasu tarar daga Gwaggo ba. Musamman daya kasance a bazata zata gansu bata san da zuwansu ba, sannan zata ganta tare da baƙin da bata taɓa tunani ba. Da wannan zullumi da fargaban a zuciyar Inna Mairo, Auwala ke ta falala gudu dasu a mota har suka baro garin giwa baki ɗaya suka ɗauki hanya.Najma tayi shiru a motar tana faman saƙe-saƙe a zuciyarta, ita ma zuciyarta na cika da tarin fargaba da tsoran irin tarban da zasu samu daga wajen Gwaggon kaduna.

Lokacin da suka shigo garin kaduna daga Najma har su Inna Mairo, sake baki suka yi suna kallon yadda garin ya sauya.Ko’ina ya sauyawa Inna Mairo sabida irin cigaba da gagarumin sauye-sauyen da garin ya samu,a sakamakon samun nagartaccen shugaban da ya gyara birane da ƙauyakun jihar.Inna Mairo ce ta dinga yiwa Auwalu kwatance har suka isa unguwar Rimi GRA,bayan sun sha matuƙar wahala sabida gaba ɗaya garin kaduna ya sauya mata cikin shekaru bakwai da tayi bata tako ƙafafunta ciki ba. Da ƙyar ta iya gane street ɗinsu Yaya Kabeeru,suka isa ga tangameman gidan nasa da ke a farko-farkon shiga street ɗin. Daga bakin wani ƙaton black gate motarsu Hakimi ya faka, Auwalu ya danna horn har sau biyu amma shiru kake ji babu alamun za a buɗe gate ɗin. Hakan ya sanya ya kashe motar sukai zugum a ciki suna jiran ganin abinda zai faru.Zuwa kamar sakan biyar aka buɗe ƙaramar ƙofar dake manne da jikin gate ɗin shiga gidan, wani baƙin buzu ya danno kansa waje yana mai sauke idanunsa akan motar Hakimi samfurin 406. Ya tako zuwa wajen motar ya yi tsaye, cikin hausarsa da bata fita sosai yake tambayarsu wajen wa suka zo? Hakimi ya waiwaya yana duban Inna Mairo, hakan ya sanya ta gane abinda yake nufi.Ta buɗe baki ta ce da buzun, “Ka sanar cewa Mairo ce daga garin giwa tare da Hakimin garin.” buzun ya juya ya koma daga ciki tare da rufo ƙofar gam. Inna Mairo ta sauke wani numfashi zuciyarta na cigaba da dakan lugude, yayinda ita ma Najma tayi tsumu a cikin motar tana taya Inna Mairo shiga zullumi. Mintuna biyar suka wuce shiru, sai daga bisani suka ga an wangale ƙaton gate ɗin gidan buzun na musu alamu da hannu akan su shiga da motar ciki. Hakan da Auwalu ya gani ya sanya shi tada motar tare da danna hancin motar zuwa cikin wawakeken harabar compound ɗin gidan. Tun shigar motar cikin compound ɗin, daga Najma har Hakimi da Auwalu sake baki suka yi suna ba idanunsu abinci,domin gini ne da ya gama tsaruwa matuƙa da gaske.Kallon ko’ina suke cike da birgewa yayinda Hakimi da Najma tunaninsu ya tafi iri ɗaya, wajen mamakin yadda mai kuɗi kamar wannan, amma ya iya barin ƴar uwarsa a ƙauye cikin wahala da ƙuncin rayuwa. Auwalu ya isa ga parking space ɗin gidan mai ɗauke da manyan motoci har huɗu ya faka tasu motarsu daga waje-waje. Duka suka fito kusan a tare, suna sake baza ido suna kallon kyawu da tsarun gidan Alhaji Kabeer Dukku. Adamu driver da tutir yana gidan sabida jiran aike ko fita da Gwaggo unguwa, shi ne ya hango cewa Inna Mairo ce da ɗiyarta suka iso garin. Ya taho cikin hanzarinsa yana musu barka da isowa cike da tsantsar farin cikin ganin Inna Mairo a garin.Shi ya yi musu jagora zuwa sashin Gwaggon kaduna da ke tsakiyar manyan apartment guda uku dake cikin gidan. Hakimi da Auwalu dai na tsaye jingine a jikin motarsu,zasu jira har a basu masauki ko izinin shiga daga ciki tukunna. Najma da Inna Mairo suka dinga bin bayan Adamu har zuwa sashin Gwaggo, wanda Inna Mairo ta dinga ganin tamkar an sake sauya komi ne na gidan sabida yadda gidan ke samun gyara duk ƙarshen shekara sai anyi masa wasu sauye-sauyen dake sake ƙawata shi. Cikin wata iriyar murya wacce zullumi da rashin karsashi suka sake kassara amonsa, su Inna Mairo suka rafsa sallama daga baƙin ƙofar shiga main parlor ɗin Gwaggo.Daga ciki muryar wata ta amsa musu sallamar tare da basu izinin shiga, hakan ya sanya suka kutsa kai cikin falon bakin Inna Mairo ɗauke da addu’ar samun nasara akan Gwaggo tare da fatan kada Allah ya bata ikon wulaƙantasu ko Hakimi.Najma dai zare idanu kawai take yi mamaki da wani irin abu mai girma na sake mamaye zuciyarta, ta kasa gasgata cewa ɗan uwan Inna ne keda wannan aljannar duniyar amma ya iya wofintar da rayuwar Innarta. Suka samu waje cikin kujerar 2 seater mai asalin kyau da nauyin kuɗi suka zauna, Inna Mairo ta gaida matar da suka samu a zaune cikin falon. Matar ta amsa da fara’a tana musu lale da zuwa tare da sanar dasu yanzu Gwaggon zata fito. Bata gama rufe baki ba sai ga Gwaggon ta fito daga cikin wani cooridor. Idanunta ta sauke akan Inna Mairo kamar yadda Inna Mairo ita ma ta sauke idanunta akan Gwaggon kaduna,tana mai yi mata cikakken kallo.Cikin nutsuwa Hajiya Gwaggo ke takowa zuwa cikin falon dukkanin jikinta na yin wani irin sanyi da ganin yadda Mairo duk ta lalace. Har ta ƙariso cikin falon ta kasa ɗauke idanunta akan Inna Mairo da ƴarta Najma, wacce Gwaggo ke hango tsananin kamanninta da Mairon. Sannan baƙin beauty face ɗinta ya tuna mata da Malam Mahmuda, mutumin da ko kaɗan bata taɓa jin ƙaunarsa a zuciyarta ba har ya koma ga mahaliccinsa. Yau ga ɗiyarsa da babu inda ta baro baƙin fatarsa a gabanta,tana kuma jin wani irin mutuwar jiki na kassara zuciyarta.Sabida wani irin kamanni na jini ta hango kwance akan fuskar Najma,wacce tayi mata kama da jikarta Nasreen……✍🏻

*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *Evidence of payment to this number:08167768704*

🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA’AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*

*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻

 

#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰

You cannot copy content of this page