daya saura har yara sun kusa tasowa daga makaranta, kuma kun yi baki ina jin mahaifiyar Sajida ce da kakarta. Sau biyu babar Sajida na lekowa kicin tana tambayata ba ka tashi ba ne. To kar su ga ko nice ba na so ku gaisa, gara ka je ka gaishe su kai ma ka ci abinci.”Bakura ya murje ido ya ce “Ki je zan yi wanka yanzu zan fito.”
Tana fita ya mike ya shiga bandaki ya yi wanka, gami da dauro alwalar Azahar. Tunda rana ta yi zafi ba shi da niyyar fita sai da yamma, amma jin surukansa sun zo sai ya saka manyan kaya. Rigar shadda ce koriya tazarce da wando ya dauko hula ya dora, sannan ya fito. A nutse ya wuce falo, don cin abincin safe. Samira ya iske a zaune a falon tana ganinsa ta tambaya.
“Ka je kun gaisa da bakin?”
Ya ce “So na ke in ci abinci yunwa nake ji, ko so kike inje gaban surukai yunwa ta buge ni in kwanta?”
•Samria ta kwashe da dariya ta ce,” Allah ya
kiyaye ma, ci abincin tukunna sai ka je ku gaisa. Ba na so dai su Kara lekowa su tambaya.”
Bayan sun gama cin abinci, domin ita ma ruwan shayi kawai ta kurba tun safe kasancewar idan ba da Bakura ba, bata iya in abincin kirki.Bakura ya mike ya ce da Samira To zo ki raka ni in gaishe su.”
Samira ta fada cike da mamaki, “Wai nice zan yi
maka zaman auren ne Abban Yagana? Ka ji mutum, nasan sanda ka je ka yi durkushe-dur kushe da gaishe-gaishen dangi har aka ba ka ‘ya, babu inda zan ji, ka je kai kadai kun fi kusa.”
Bakura ya tafi fuskarsa cike da murmushi, ya kwankwasa kofar dakin Sajida cikin ladabi ya murda ya bude. A falo ya iske su, su duka ukun suna zaune a kasa akan kafet.
Sajida na ganinsa ta tsuke fuska ta kawar da kai gefe kamar ta ga makiyinta har sai da Umma Furera ta lura da haka ta shiga tunanin ashe daman har yanzu da matsala a zamansu? Ashe Sajida ba ta saduda an zauna da ita lafiya ba?’
Ya yi sallama ya zo a nutse ya durkusa a gabansu yana mai sunkuyar da kai kasa, don zama da girmamawa. Ya gaishe su suka amsa dukkansu a kunyace.Umma Furera ta ce da shi, ‘Wannan kakar Sajida ce ta zo jiya daga Gashuwa, don ba ta samu tazobiki ba, sunanta Iya. Azumi.”
Bakura ya ce “Ai jiya Malam ya fadamin, Allah sarki iya yaya hanya?”
Daidai lokacin ne Bakura ya dago ido ya dubi lya.
Azumi. Ta ce,Angona lafiya kalau.”
Ita ma tana dubansa, amma wannan karon duban ” da suke yi wa juna ya tashi daga surukai ya koma.na duban keke-da-Keke mai dauke da alamar tambaya.
Duba ne irin na ban mamaki da tsantsar gigita mai hade da tashin hankali tamkar su kurma ihu haka yana yin kowannensu ya canja. Karkarwa Bakura yake yana nuna iya Azumi ita ko hannu ta dora a ka tana hawaye.
“Lafiya, me ya faru?” Haka Umma Furera da
Sajida suke tambayarsu.
. Babu wanda ya iya ba su amsa a cikinsu.
=* Bakura ya yi karfin hali ya ce “‘Innono.”.
Ta amsa masa “Na’am, Bakura kai ne?”
Sai su duka suka fashe da kuka mai tafe da zazzafan hawaye. Babu kalmar da take fitowa daga bakin Innono sai “La’ilaha illallahu Muhammadul Rasulullahi sallallahu alaihi wasalam, Bakura kana raye ashe?”
Wannan dogayen salatai ne yasa Samira shigowa cikin dakin, don ta ganewa idanuwanta abun da ke faruwa. Ta iske Bakura tsaye ya kifa kai da bango yana wani kuka mai tsanani, har idanuwansa sunyi jawur. Ta rike shi a gigice tana tambayarsa lafiya.
Haka Sajida da mahaifiyarta suka shiga wannan rudanin suka rike Iya Azumi suna tambayarta “‘lafiya”.
Ta ce, “Labarin yana da tsawo, yana da ban mamaki.”
Da jin haka sai Umma Furera ta dauko waya ta danno lambar maigidanta tana sharbar kuka. Ta ce
“Malam, ka taho gidan Sajida yanzun nan akwai magana.”A gigice ya. ke tambayarta.
Lafiya, guduwa ta yi?”Umma Furera ta ce “Ko daya babu abin da ya faru, illa Iya Azumi ce da Bakura suka shaida juna suna ta koke-koke. Na san lallai akwai wani boyayyen al’amari sun san juna. Ka san kuwa dole yau a fayyace wa Saida komai.”
Malam ya fada cikin sauri “To gani nan zuwa.”
Hankalin Sajida ya tashi matuka da jin bayanan
Ummarta sai ta dora hannu a ka ta rusa kuka.
Ta ce, “Umma, ba dai tsintata ku ka yi ba, ba ke ce ki ka haife ni ba?”
Umma Furera ta girgiza kai ta ce, “Ni na haife ki
Sajida ba tsintarki na yi ba.”
Sajida ta koma gaban Iya Azumi ta durkusa.
Ta ce “Iya ki fada min gaskiya me ya faru da ni?”
Iya Azumi ta runtse ido hawaye ya surnano sai ta nuna Bakura. Ta ce “Bakura ne ya fi kowa sanin ko ke wace ce, amma ‘ni ban sani ba.”
Sajida ta mike da gudu ta nufi inda Bakura ke tsaye ta durkusa a gabansa cikin kuka.
, Ta ce “Bakura ni wace ce? Me yake faruwa ne?” Bakura ya matse hawaye yasa hannu ya tashi
Sajida tsaye.Ya ce, “Je ki ki zauna bari Malam ya zo, bari su Zahra su dawo daga makaranta, sannan in zo in bayar da ‘tarihin rayuwata. Zan sanar da ke ko ke wace ce, amma kada ki damu kanki kina da uwa, kina da uba ba yar tsuntuwa ba ce.”
• Sajida ta sulale ta zauna zuciyarta na dukan uku-uku, kwakwalwarta ta kasa shiryo mata abun da zai riya kasancewa. Fatana ta dai kar ace ba Furera da Malam ba ne suka haife ta ba, kada dai ace Bakura ne Babanta Mahaifi. Haka Samira ta shiga wannan hali na mamaki da tambayoyi iri-iri. Umma Furera ma kukan take da alama ta san komai.
Bakura ya fice Samira ta bi shi da sauri zuwa kofar fita.
Ta ce da shi “Ina za ka je ne?”
Ya tsaya cak ya ce da ita “Masallaci zan je yanzu zan dawo.”Samira ta tambaya Me yake faruwa ne Malam?”
Ya ce “Yau zan ba ku tarihin rayuwata kacokan.
Yau zan bayyana muku ko ni wanene, kuma daga ina na fito, mene ne asalina? Yau za ki ji ko wacece Zuhuriyya kuma ya ya take a wajena. Yau za ki tabbatar da maganata da na ce Sajida ta yi kama da Zuhuriyya. Yau za ki tabbatar da dalilina da na dage na auri Sajida dan ada ban yarda na fada muku komai ba.Samira ta tsaya tana kallon Bakura jikinta a sanyaye. Ta fada cikin cikin siririyar murya mai tafe da rashin kuzari,A dawo lafiya.”
Ya fice da sauri zuwa masallaci. Fitar Bakura ba
Hmmm