DIYAR DR ABDALLAH CHAPTER 1 HAUSA NOVEL

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taba samun kansa cikin wannan yanayin ba. Yanayin da zai zama useless baida amfani. Sai yanzu ya lura da dalilin dayasa ya kasa barci. Ba komai bane illa wanna sabon shafin dake bakunta sa.

A hankali yake mamayansa, ya shammace shi cikin dare. Yanzu gashi yazo yayi kane kane yana kokarin gina muhalli cikin rayuwarsa. Tabbas zuciya batada kashi, kuma ba’a kwabanta. Amma idan tace zatayi mashi abinda yake tsammani bata kyauta mashi ba.

Tayi mugun cutan sa. Ya kamata tayi tunani saboda abinda take so yafi karfin ta. Runtse ido yay ransa yana mashi daci. Shi dama dukansa akayi da itace zai fi jin dadi akan radadin dayake ji cikin ransa. Akwai abubuwa da ke faruwa da bawa wanda baida ikon hanawa. Kamar yadda zuciyar sa take raya masa ga abinda takeso yanzu, idan kuma bata samu ba tabbas zatayi masa tijara.

Toh tijara na yaushe kuma, fafur ta hanashi barci.

Murmushi yayi na takaici, “akwai kura,” yace a fili.

“Mutuwa hutu ce a gareni,” ta ayyana a ranta yayin da zufa

ya karyo mata a wuya, bayan ta da sauran ilahirin jikinta.

A farad daya labarinka zai juya, daga fari zuwa baki. Tabbas

ta saba jin yadda rayuwar mutane ke canza wa amma bata

taba cin karo dashi ba sai yau.

“Daga ina zan daura?” ta sake ayyanawa, sai dai kuma babu

wanda zai bata amsar tambayar ta.

So da dama zaka kwanta cikin walwala amma ka tashi

komai ya tarwatse maka. Duka abinda kake tunanin shine

gaskiya sai kaga akasin haka. Wanda ka yarda dasu sai su

kasance sune masu cutar dakai. Rayuwar da kake zama da

makashin ka amma ta sigar mutunci. Tabbas a yanzu ta

yarda da maganar da bahaushe yace, “mugu bai da kama.” 7

Ance rashin sani yafi dare duhu, amma da wani sanin gwara

zama cikin tandun kwalli. Saboda yanzu rayuwarta ya canza fasali.

Hadiye miyau tayi mai mugun zafi, idan kana kusa da ita

zaka iya jin karar sa. Sannan ga wani matsanancin ciwon

kai da ke addabar ta, tashin hankali tareda rudani data

shiga kwanakin nan shine sila.

Fuskan ta a tamke yake babu annuri ko kadan, girar sama

da kasa a harde. Goshin ta kuma yayi layi layi. Idanta kuma

ba kalar daka saba gani bane, ruwan toka ne kwayar

sannan kuma yana sheki. Budurwa ce ajin farko mai

kimanin shekaru ashirin da hudu a duniya.

Tanada bala’in juriya da dakewa, duk abinka da ita, bazaka

ga wani gazawa a al-amuranta ba. Ko yaya matsala yake

damun ta bazaka gansa a fuskanta ba. Hawaye kam idan tace tunda take bata taba kuka ba bazaka musa ba. Shi kansa ma murmushi za’a iya dirga sau nawa takeyi a rana.

Hakan bawai yana nufin da chan ta shiga wani rudani bane, a’a ita haka halittan ta yake. Akwai juriya da dakewa.

Matse karamin towel dinda ke hannun ta tayi, sai ta sake shafa mashi a saman goshi. Bata iya hada ido dashi saboda dacin dake ji cikin ranta. Yana bala’in bata tausayi. Ita bata kuka, a yau tayi kishi da wanda suke iya kuka tareda nuna damuwan su karara. Tabbas kuka rahama ne a tareda dan adam. Kukan zuciya wanda yafi na bayyane ciwo shi takeyi.

Shi kam murmushi yakeyi tareda binta da addu’a cikin ransa.

Dattijo ne mai kimanin shekaru sittin da biyu, fuskan shi akwai furfura wajen girar sa da kuma gemun sa. Hannun sa yake kokarin motsi dashi inda ta mika nata tareda magana cikin sauri.

“Baba! Ina ke maka ciwo?”

Murmushi yayi sai yace, “Ba inda ke min ciwo Naseera, ki daina damuwa.”

Daci kawai zuciyar ta ke mata, ga gudun dayake yi kamar jirgi. Tabbas BP dinta ya hau a yanda take jin kanta. Ita kadai tasan abinda ke mata ciwo. Saboda Zuciyar ta yana mata barazanar fashewa, ga kuma tausayin mahaifinta daya lulubeta kamar bargo. Hakika an zalunce shi.

“Ki tashi ki tafi ya isa haka kafin supervisors su fara neman ki. Kada ace zaki nuna preferential treatment saboda ni Babanki ne.”

“I want to be here.,” ta fada a sanyaye tareda Kara saka towel cikin ruwa ta sake matsewa. Wanna karan wajen wuyan sa tabi tana gogewa. “Baba, bana so na rasa…”

Bata karasa magana ba sai kofa ya bude, “Assalamu Alaikum,” aka ce yayin da wata dattijuwa ta shiga. Hannun ta cike yake da coolers.

Amsa sallamar Naseera tayi a dikilce saita mike tsaye tareda gyara mazaunin rigarta, “Baba to bari na tafi zan dawo anjima…” shima bata kalle matar ba tayi maganar.

Baza’a ce mugun kallo ta watsa ma matan ba amma

Kaninsa ne.

“Allah ya maki albarka,” saiya kalle matar data shigo, “Binti kice yarki ta daina damuwa. Zan warke in sha Allah.”

Haila Binti ta kalle Naseera fuskanta cike da annuri, “Yar Siri Siri, Naseeran Babanta naga tana jin gari, ciwon nan yasa ta sai kumbure kumbure takeyi, ita a dole Daddy’s girl.” Hajia Binti ta fada fuskanta babu damuwa.

A dikilce Naseera ta murmusa saita dauki jakarta tareda wani envelope ta fita bata sake cewa komai ba. Tana rufe kofar a bayan ta saida a tsaya ta gyara kallabin ta saboda duk ya sukurkuce. Ajiyar zuciya ta sake yi saita tafi office dinta, Resident Doctor ce amma kasancewa asibitin

Babanta ne Dr Abdallah dole saida aka bata nata office din.

Zama tayi akan kujerar ta, saita dauko takardar tana sake kallo. Ta kasa gasgata abinda yake bayyanawa. Ba karo na farko ba kenan tana sake tura sample lab, zai Kai kusan sau 6 amma duka haka results din ne.

Tafasa kwakwalwarta ya cigaba da yi, anan ta soma ganin dishi dishi, duk ilahirin jikinta yayi mugun sanyi. Bakin ta daci yakeyi kamar taci danyen shuwaka.

Buga kofa aka yi tareda shiga, “Dr, ana neman ki a male ward yanzu,” wata Nurse ta fada a ladabce. Da kai Naseera ta amsa, saita kalle Beeper dinta, anan ta lura an dade ana mata magana batama lura ba. Envelope din hannun ta takai cikin safe din office dinta ta kulle. Saita saka lab coat dinta tareda fita.

Hajia Binti ta lura da mugayen kallon da Naseera ke binta dashi kwana biyu. Amma duk abin ka bazaka ji cikin

Naseera ba, kamar kwalta take saidai ka wuce amma ba’a bambaranta. Zurfin cikin ta ya bala’in baci. A duniya kuma Hajia Binti ba abinda take so kamar Naseera. Kasancewar sun shekaru bila adadin bayan aure kafin suka sameta.

Gatan duniya sun nuna mata, yasa yadda ta canza mata kwana biyun nan ya bala’in daga mata hankali.

Saidai abinda ta sani shine duk abinda ruwan zafi ya data,

idan aka yi hakuri ruwan sanyi zai dafa shi.

****

“Kas Kas Kas” din taunar cingam ke tashi tareda wakar

Hamisu Breaker tana bi, baiti baiti babu wanda bata sani ba kamar ita ta rubuta wakar. Tanayi tana fesa kwalliya. Idan wani ya gani zaiyi tunanin biki zata. Amma kwalliya kawai takeyi na nishadi saboda zata gidan kawarta anjima domin ta samu tayi hoto wanda zata watsa Instagram. Yau Laraba kuma rana ne na hashtag din WCW watau Woman Crush

Wednesday.

Madubala wanda aka fi sani da saurauniyar kyau ta cige ta satin daya gabata, hotuna tayi masu kyau, gashi samari sunata yabon ta. Tabbas tasan was sun bita private domin su bata kudi. Kuma abin ba karamin bata mata rai yayi ba.

Dama itace abokiyar hamaiyarta a duniya. Basu taba haduwa ba, kuma ba garin su daya ba, asali ma basa following juna amma suna kishin juna sosai.

Kofa aka tura yayin da aka shiga, a wulakance ta kalle wanda ta shigo, ba kowa bane illa kanwarta Fa’iza.

“Ruma jiva naie ajin ku amma ance babu wata mai irin sunan, babu irin kwatancen da banyi ba harta hoton ki babu wanda ya gane ki. Kadan kuma sun gane fuskan daga

Instagram ne,” ta fada fuskanta babu yabo babu fallasa.

Ninke kayan saman gadon ta soma yi ba tareda ta kalle

Ruma Sa’u ba. Ita kam gabanta ne ya soma fadi amma ta kware a bariki.

“Meaning?” Ruma tace a dikilce tareda watsa mata harara da dara daran idanta.

“Eh yana nufin ko karya kike baki samu admission ba, ko an kore ki, ko kuma ba’a department din kike ba.”

“Toh FBI, da wannan lokacin da kika bata wajen bin diddigi da kin bincika meyasa kike da masifan muni daya fi miki…

Matsalata da talaka bakin ciki da hassada. Ina ruwan ki da rayuwa ta??? ” sannan saita ja dogon tsaki.

Murmushi Fa’iza tayi, idan da sabo tsab ta saba. Da kuma zagi yana aibu daya yi mata wani abu. Amma bazai yiwu yanda iyayen su ke kokarin gain sun basu rayuwa mai inganci ba a rinka zalinta su.

“Kuma idan kin ga dama ki hada min annamimanci wajen su Inna, wallahi saina makure maki wuya, ki koma kina zare ido kamar akuyar data lashe gishiri.” Ruma ta sake cewa.

Tas Fa’iza ta gama Nike kayan saita dauki khaki dinta na nysc ta fita tabbas Ruma zata aikata. Yau sunada CDS-community development service. Ruma Sa’u kuwa ko a jikinta, bayan ta gama kwalliya saita saka hijab dinta sannan ta dauki wani katon jaka ta fice.

A tsakar gida ta riske mahaifiyarta tanata fama da itace, laifin ta ne ruwa ya dake shi saboda ance ta rufe da leda ita kuma ta mance.

“Inna ni zan tafi makaranta, munada tutorials sai mangariba zan dawo.”

Murmushi Inna tayi tareda ta fitowa daga inda aka kebe a matsayin kitchen. Idanta sai ruwa yakeyi saboda hayaki. Da haban zaninta ta goge kana tayi magana, “Ba zaki karya ba, koda koko ne kisha mana?”

“Inna kenan! Zaki da mai na biyo birni.” ta fada tana murmushi.

“Shikenan Ruma Allah ya bada sa’a, dan Allah a maida hankali.”

“Amin” tace sai ta nufa zaure.

Bata sha wuyan samun napep ba, anan ta dauka suka wuce GRA. Gidan wata tsohuwar aminiyar ta Rahina zata je. Koda yake bafa kawarta bace, cin zalin yarinyar takeyi sanda suke kanana. ‘Ruma Annoba’ ake mata lakani dashi, saboda ta buwayi yaran mutane.

Kullum Inna sai taje ban hakuri makota, Ruma Allah yayi mata jin haushin mutanen da acewarta basuda kyau. Idan bakada kyau kullum saita takale ka da fada tayi maka

dukan tashi kasha gishiri. Ajin su daya lokacin a islamiya da Rahina, kuma ta wahala matuka sai daga bisani babanta ya fito takarar chairman kuma yaci. Anan ya siya gida a GRA suka koma. Yanzu shekaru uku kenan basu hadu da Rahina ba. Saidai kwanan nan ta ganta a Instagram ta bala’in gogewa.

Ruma Sa’u tayi mugun mamaki saboda Rahina kamar an hakota a rami take. A sanin data mata duk kyan kaya baya mata kyau, a tsuke take kamar bulala. Shiyasa Ruma ta laka mata suna Rahina Bulala, wanda sunar ya bita lungu lungu daga baya kuma sai aka koma ce mata Lala tunda wancan yayi tsawon fadi.

Lala ta wuce tunanin mai karatu yanzu saboda ko turanci da hanci take fadin was kalamai, ga wani kamala da natsuwa wanda arziki ke sanyawa. Uwa uba har umara taje da dubai duka tayi hotuna a chan tayi posting.

Ruma da kanta tayi mata friend request a Instagram sannan ta karbi number dinta. Yanzu zata je tayi mata yini, ita da biyu zata saboda ta samu ta watsa hotuna gidan yan gayu.

Tunanin abinda da Faiza tace ya fado mata. Anan taja dogon tsaki tareda tsine ma Faiza da la’anta ta. Ruma tayi jamb sau 4 duk bata samu abin kirki ba, daga baya idan an bata kudin jamb jambaki da Hoda take siya, ranar jarabawar ta fita gantalin ta saita dawo tace, “Inna an kuma, nifa bada boko zanyi arziki ba”

Faiza kanwarta ce, amma yanzu haka tana bautar kasa a banki. Ganin yadda ake takura ma Ruma Sa’u akan inda zata sai tayi karya tace ta samu admission. Yanzu haka a karyar ta har anyi shekaru 2 tana aji biyu a jami’a.

Kowa yayi mata murna sanda admission din ya fito harta yayanta shine ya biya mata kudin makaranta. Duka kudin ta kwasa ta siya ankon kawaye da kayan kwalliya. Kullum ta buga hijabi tace taje lectures ko tutorials amma tana kan titi tana gantali kala kala da bin kawaye musamman wanda aka hadu dasu social media. Idan kuma kawar yar jam’ice, wata sa’in har lectures Ruma tana rakata daga nan a wuce

gantali.

Bukokuwa kuwa ba’a kirga yawan wanda taje, bata sati biyu bataje biki ba. Wata sa’in a wani bikin take haduwa da amaryar da za’a yi bikinta sati mai zuwa. Ba’a wuce hotuna biyar a Instagram na yan mata wanda suka yi cinkoso na kamu watau group pictures baka hangeta ba.

“Kankana war ruwa, Kankana abin sanyaya rai. Kowa yana marmarinki saboda bakida abin da za’a zubar, kwallon ki da bawon ki duka magani ne. Koda kudin mutum saida rabon sa. Matar manya, ganin ki yafi zuwa Dubai,” Lala ta soma mata kirari yayin da suka rungume juna.

“Rahina Bulala ashe zaki iya gogewa” Ruma tace cikin izgili, Lala ranta ya sosu amma tayi fuska. Janyo mata hannu tayi suka shiga cikin gidan. Anan Ruma Sa’u ta saki baki, gidan ya kawatu. Domin yafi na sauran Kawayenta na social media haduwa.

“Ya kamata da Lala zan kulla aminta bada yan group din

One Love ba” ta ayyana cikin ranta. One Love ya shahara a WhatsApp, asali Big Boys and Girls ke ciki, ajebo masu kayan alatu da duniya. Amma yanzu ta dauki alwashin zata koresu duka domin ance zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai. Kulla alaka da Lala zai sa itama ta goge tayi

arziki wata rana. Tabbas Lala alheri ne a rayuwar ta.

Karewa dakin Rahina tayi tsab tana yabawa, pink ne komai cikinsa. Gashi kal kal dashi komai yana inda ya dace. Sanyin

AC yana ratsata ga Samosa wanda yaji kayan had tana _watsawa bakinta, nan take haushin mahaifinta ya diran mata. Wai ya rasa duk sana’ar duniya da zaiyi sai malunta.

Shima din wai malamin firamari. Baida mota baida sutura, duk kayansa ya kode.

Sai dai a haka yakai yaransa biyu jami’a. Aliyu yayan Ruma Sa’u sai kanwarta Fa’iza. Aliyu ya hada karatu da aikin typing, printing da photocopy. Ita kuma Fa’iza tana kananan dinki kamar su huluna, hijabi da sauran su tana siyarwa. A haka suke rufa ma kansu asiri.

Canza kaya Ruma Sa’u tayi a gidan su Rahina, saita dauki iPhone dinta taje farfajiyan gidan tana hotuna, anan taga mai aikin gidan saita mika mata wayar domin ta dauke ta.

Riga ce off shoulder wanda ya bala’in matse ta, sai pencil skirt. Duka sansan jikinta a bayyane, gashi tanada diri mai kyau. Daurin ture kaga tsiya tayi inda yayi masifan mata kyau.

Anan ta saka a Instagram dinta. Sunan da take amfani dashi shine “Kankana” kuma kafin kace kwabo maza harda mata sunata vabon ta.

‘Kankana uwar ruwa’

‘Kankana mai sanyaya rai’

‘Ajebo dan Allah kizo ki aure ni’

‘Hurul ayn din duniya. Bakida matsala babban yarinya’

Sai kuma wanda sukayi ta ajiye account number dinsu suna

mata maula.

Ita kam ba abinda ya dameta ba kenan, jira takeyi wani babban yaro a Instagram mai suna Qwaro yayi liking hoton.

Ta dauki alwashin zata kulla alaka dashi tunda shima dan masu dashi ne.

Ko’ina akwai yarensa, yasa daga kudi sai kyau kadai ne yaren da Ruma take ganewa.

You cannot copy content of this page