ALLURA CIKIN RUWA BOOK 3 CHAPTER 21 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

hayayyafa tana yawan ziyartar su Inna, bai dace son da zilai ta nuna ba mu barta haka Ina dariya ya jawo ni ya ce, “In Kyale ki har yanzu baccin bai ishe ki ba?’

Nace Na gama na nawa sai dai na Bebin. ka” Ya ce, Ni kin ga ma yau kwana uku ban zauna na ji lafiyarsa ba”

Na ce, “Wai don Allah Yaya duk wata matar likita sai idan tana tsakiyar soyayva ake mata awo?*

Ya Kara rungumata yana dariya. yace. A a, sai yar lele kamar ki

El-Bashir ya hada mu da Reina wadda mijinta ya sakar mana motarsa tana zagawa dan wurare da dama na ban sha’awa, har irin wuraren da ake shirya fim ta kaini.• Itama yarinya ce karama kamar ni, shekarunta biyu da aure bata taba haihuwa ba. Ta kan zauna ta zuba mana ido ni da Yaya Aminu, wai ita sha awa muke ba ta, saboda ta dauka bakar fata kamar soyayya ba ta cikin ra’ayinsu, amman ta lura yadda Aminu ke nuna min ko su Indiya sai hakan. Kuma bata taba ganin bakar fatar da suka dace da juna ba irin mu. Wata rana da hira ta kasance a tsakaninmu na tambaye ta Shin wai da gaske ne duk duniya babu wanda ya kai soyayyar Indiya?”

Tayi murmushi ta shiga bani labarin tarihin wadanda suka yi suna a fagen soyayya, inda har sun bar tarihi. Ta yi min alkawarin raka ni wani gida na musamman in ga ainihin tarihin wadannan masoya

Na sake tambayarta cowa.

Har yanzu kuna nan

bisa aladunku wanda in iyayee sun ki amincewa da auratayyar yara, sai su fada wani kogi na musamman wanda ake kira • Muntansun Muhabbat?

Ta yi dariya tace ” A-siya na yarda kin karanci tarihi a Kasarku. Wannan zance maki anyi shi amma a da zamanin iyayenmu masu gaskiya da rikon amana. Yanzu abin duk ya zama shirme, ko yaran sunyi alkawarin suna isa saiya bar yarinyar ta fada yace yana yar kwalla yace ya yi yayi amma ta Ki, shi kuma ya canza shawara, bazai  Kulla wata daya ba sai da wani auren Sai dai ba duk aka zama daya ba”.

Da yamma kamar kullum su Yaya Aminu su kan fita Da misalin Karfe tara saura kwata na dare, nayi kwance-kwance na tsala ado saboda za mu wata  liyafa da aka gayyaci su Yaya Aminu.

Na zuba wata babbar riga da shadda mai ruwan hoda tasha ado daga gaba da wasu duwatsu masu ruwan hoda da farare masu daukar ido, inda duk na gilma suna walkiya. Shi ainahin dinkin a Kasar dakar wata kawar Mama Inki ke daukowa.

Na gyara gashina sannan na murde dankwalin ya zama kamar rawani na zizara shi. Na fito falo inda Yaya Aminu ke ‘yan rubuce-rubucensa, ga shi kuma bai taba ganina cikin wannan babbar rigar ba.

Ya dago kai ya dube ni, ya aje biro ya ce. “Ranki ya dade amarya kin sha kamshi”.

Na yi murmushi nace Angona nayi kyau ne'”

Yace, “Kada ki yi shakkar hakan, sai kace matar gwamna ba matar likita ba

Nace haba Doctor yadda kowacce, matar kwarai ke ji lokacin da take Kokarin farantawa mijinta rai ai mijin nan ko gyartai ne yafi gwamnan a wajen matar”

Ya yi murmushi ya ce, , haka ne. amma zo nan in baki tabbacin jin dadin wannan adon

Na zauna bisa cinyarsa ya sanya hannayensa ya

– tallafo ni, na dan sunkuyo masa da kaina ya lalubo harshena. Bamu farga ba sai da wl- Bashir ya danna mana Kararrawa.

Duk da Kasar Indiya muke a gaskiya babu na biyuna wajen tsarin adona, har El-Bashir ya ce in yi masa alkawarin dauko wa yarinyar da zai aura, na’ ce na yi masa insha Allah. Ita ma. Reina ta nuna min matukar sha awarta, na daukar mata alkawarin in har zata iya sakawa zan aiko mata, ta sha alwashin sanyawar.

Ana saura kwana biyu mu bar Kasar Indiya, su

Yaya Aminu suka yi amfani da mukamansu na likitoci, inda suka tabbatar da magungunan da suka yi oda lalle babu algus, sannan sun ga tahowar su Nigeria don kada mu taho wani abu ya auku.

Yaya Aminu ya bani makudan kudi don in sai abin da raina ke so, da tsarabar ‘yan’uwa, na nuna masa kudin sun yi yawa, ya yi murmushi ya ce, tunda ina dasu basu yi ba. Na yi godiya.

Ya saka rigar baccinsa yazo gabana ya tsaya yana daure bel din rigar, ya zauna a gabana bisa kafet ya rinka ja min yatsun Kafafu, ya ce, “Insha Allah zan amsa maki tambayar iyakar sanina, kuma ba zan ki fadar gaskiya ba

Na yi masa kyar da idanu, na dube shi cikin kwayar idonsa sannan na ce,.Wai shin ka taba shan

giya?”Shima yayi min kallon cikin kwayar ido, ya yi murmushi ya ce,

“Asiya a da kam na sha giya farkon

shekarata a Rasha, saboda al’adar Bature ke nan, idan a ofis ka same shi ko a gida abin da zai fara kawo maka kofin giya, sai daga baya na waye da hakan na guje mata saboda addininmu Islama”

Na dube shi na nisa sannan na janye Kafata daga hannunsa, tun a nan ya san tambayar da zan masa mai radadi ce, amma kuma a fuskarsa babu alamar damuwa a bisa tambayoyina. Na ce, “Ya ya harkar wajen cudanya da ‘yammata?”

Ya gyara zama ya dan lumshe ido kafin ya bude, ya dube ni da kyau ya amsa min, “Asiya na riga na san komi dadewa za ki yi min wannan lambayar, ko don saboda hoton da na baki tare da wata yarinya.

A bisa gaskiya Asiya bata yiwuwa in ce miki ban yi harka da ‘yammata ba, saboda duk namiji baligi lafiyayye dole’ya bukaci diya mace. A nan ku mata kunfi mu hakuri, amma ina son ki yarda da abu guda daya, wallahi-wallahi ban taba son wata diya mace ba wadda

Hmmm

You cannot copy content of this page