A daren karfe takwas da mintuna Mallam Yusuf ya aika kiran
Murshida, sosai ya mata fada cewarsa aure ma zai mata tinda tayi graduation, ya hutu da jaye-jayen fadarta, kuka tasha sosai jin furucin mahaifinta kafin bacci ya dauketa a daren.
Washegari kafin takwas na safiya ta bar gidan dan zuwa gidan aikinta tare da kannenta ta fito bayan sun wuce makaranta ta wuce gidan aikinta, basu farka ba hakan ya bata damar yin aikinta a tsanake, bayan ta gama guraren karfe tara ta yanke shawarar wuni kawai tinda in ta koma gidan banda bakin ciki ba abinda zasu tusa mata, kowa ma haushinsa take ji a gidan.
Bayan ta gama tana shirin fita a falon Aunty Ani ta sauko.
“Murshida!”
Juyowa tayi tana kai kallonta wajen da taji muryarta, murmushi tayi wanda shine murmushinta na farko tun safiyar ranar.
“Aunty! Ina kwana?”
“Lafiya kalau Murshida, yaya mamanki?”
“Lafiyarta kau.”
Ta fada tana sunkuyar da kanta kasa sosai take jin son
matar.
“Kin gama aikinne?”
Aunty Ani ta fada ta katse mata tunanin ta.
“Eh, dama.. nace dama zan wuni yau in ba damuwa.”
Fadin Murshida na son jin mai Aunty Ani za tace, murmushinta ta fadada tare da riko hannunta.
“Zan so hakan Murshida, kece dai kawai da farko ki ka nuna bakya so.”
Kallon mamaki da al’ajabi Murshida ta bi hannunta dashi yada yake sakale cikin na Aunty Ani, hannune fari, kamshi, laushi, cikin nata hannayen da yanzu suka gama dilmeyewa a cikin kumfa, kallon ta ta sake yi har yanzu murmushinta bai gushe ba.
“Ba komai Aunty.”
Hannun Murshida ta jawo tabi bayanta basu tsaya ko ina ba sai saman dinning table dake sheke da warmers na abinci, zama Aunty Ani tayi tana cewa.
“Bude mu gani mai Baba Saude ta dafa mana, ni kam naci kafin sauran su tashi dan yunwa nake ji.”
Bubbudewa tayi tasa ta zuba mata dankali da kwai ta hada mata tea tana kokarin barin gurin mutanen gidan suka karaso, Alhaji Mudassir Timber ne tare da Hajiya Maryam da alama itace da girki, gefe ta matsa tana gaishesu, zata bar gurin Hajiya Maryam ta tsayarta.
“Murshi mu fa? Wato Auntynki kadai kike so.”
Murshida murmushi tayi cike da kunya, ta fara zuba Hajiya Maryam, kafin Hajiya Maryam ta zuba Alhaji nasa, ta kula hatta Alhaji gidan ba ruwansa, tana Kokarin barin gurin suka karaso gurin budurwar jiyace tare da ita BAGUS ne, kallo daya ta musu ta kawar kanta, bayan sun karaso yarinyar ta gaisheta, a kunyace ta amsa zata bar gurin
Hajiya Maryam ta tsayarta.
“Murshi tsaya ki zubawa yarona.”
Wanda aka Kira da yarona tama kallo daya ta watsar, can kasa yace.
“Hajiyana ta bari bana jin yunwa.”
Fadin Bagus na jawo kujera zai zauna.
“Kai wai mai ke damunka, na fa lura kwana biyu ka zama silent.”
Hajiya Maryam na fadar haka tana juyawa gaba daya tana fuskantarshi.
Hannun yasa ya shafi kansa yana kirkiro murmushin dole.
“Ba komai Mamma.”
“Anya ko yarona, Aunty ki masa magana ko zai ji naki.”
Murmushi Aunty Ani tayi ta kallo Bagus tace.
“Ba ruwana tsakaninku.”
“Haka kika ce shikenan.” Fadin Hajiya Maryam.
Gurin Murshida ta bari ganin abin nasu tsakanin sune family, tana mamakin zaman lafiya da suke a tsakinsu, ganin tana jefa kanta cikin tunanin da ba’a sata ba ta kamo wani yanda zata ci gaba da karatunta na Degree.
Duk abinda suke da hiran da iyayensu ke jan shi dashi ganin ya saki ransa hankalinsa na ga bakuwar fuskar da ya gani, ko wacece?.
Bayan sun gama breakfast dashi da mahaifinsa suka kama
hanyar wajen sana’arsu, Alhaji Mudassir Timber ya wuce aikinsa daga nan zai yi tafiyan kwana biyu, shima ya wuce asibitinsu.
Bayan ya isa anan ya tarar da abokinsa amininsa Abubakar har ya iso, inda shi yake likitan kunne, Bagus likitan Ido.
Patients suka duba basu samu kansu ba har karfe 2 sallah
su kayi suka ci abincin da aka aiko musu daga gidan
Abubakar, sai karfe uku da rabi patience suka kare kafin suyi sallama da juna suka kama hanyar gida.
Da sallama ya shiga falon ba kowa falon sai hayaniya a falon sama da alama suna can, can yaji an amsa kasa kasa, kallonsa ya kai gurin, plate ne a hannunta tana tattarewa daga amsa sallarmar taci gaba da aikinta, hanyar dakinsa zai yi sai kuma ya fasa ya nufi wajenta…
Tana gain yana kusanto gurinta zuciyar ta ya bada wani irin bugu, amma ta dake ta ci gaba da harhada plates din, har ya karaso kusa da ita yana kallon yanayin ta akwai tsoro a tattare da ita amma ta dake.
“Kina bukatar taimako?”
Ya fada yana kokarin daukar warmers, kallon daya ta masa ta girgiza kanta alamar ah a, bai kulataba ya dauki manya manya biyu ya nufi hanyar kitchen, ajiyewa yay ya dawo itama ta gama deban sauran ta kai kitchen, gain ba abinda ya rage ya sashi barin gurin.
“Nagode.”
Ta fada can ciki tsammaninta ma ba zai ji ba, juyawa yayi ya kalleta da murmushi kwance saman fuskarsa kafin ya wuce dakinsa, ajiyar zuciya ta sauke ta fara goge gurin, duk iyalan gidan sun san daraja da girman Dan Adam.
Sai biyar da rabi ta gama ayyukanta tama Hajiya Maryam da
Aunty Ani sallama ta kama hanyar gida.
Da isarta abinda aka mata ya dawo mata, ranta taji ya baci, dakinsu ta shiga Khausar da Laila suka nufota.
“Oyoyo Yaya.”
Rungume kannenta tayi tana ajiye food flask a hannunta.
“Na kawo muku abu mai dadi amma baza kuci ba sai muni sallar magriba.”
Tana fada tana cire hijabin jikinta ta rataya saman kofa, Khausar da Laila har rige rigen fita suke, murmushi tayi ta bi bayansu ganin Mama na sallah bare ta gaisheta.
Bayan sun gabatar da sallah ta bude flask din tuwone daya
tuku na semovita da miyar igushi yaji bushashshan kifi,
bayan ta dibarwa Mama ta zauna ita da su Khausar da Laila
suka ci abinsu ko ta kan tuwon gidansu basu bi ba, anan
take duk bacin ranta na gidan ya wuce, burinta taga
mahaifiyarta da kannenta na farin ciki.
Washegari.
Da farin cika ta tashi wanda ta rasa dalilinsa amma tabar
abin abin akan yanayin da taga Mama da Khausar da Laila,
karfe takwas ya mata a kofar gidan Aunty Ani, aikinta ta fara
ganin ba wanda ya farka a gidan, mamaki take ace mutum
har karfe takwas bai farka ba sabanin nasu gidan tin
asubabi babu mai komawa, wanke wanke ta ke yi bayan ta gama shara da mopping.
Jikinta tane ya Bata ana kallonta, tsaye yake wajen kusan
mintuna biyu da shigowarsa, kanta ta juyar kamar basa za
tayi magana ba tace.
“Ina kwana? Kana bukatar wani abu ne?”
Karasowa ciki yayi yana amsa.
“Lafiya lau, Ya kike? Hadamin tea sauri nake yanzu aka kirani emergency.”
Yayin da yake mata duk wannan maganar ita kuma ta bar
wanke wankenta ta fara kokarin hada masa batace kala ba, bayan ta gama ta mika masa ya amsa tare da fadin. “Thank
you.”
Bata ce komai ba sai murmushi da tayi ta koma wajen sink
taci gaba da aikinta, a inda yake ya fara sha burinsa yasha
ko kadanne ya fita, juyawa tayi taga yana sha a tsaye, kamar baza tayi magana ta juya.
“Ba kyau shan abu a tsaye.”
•Ya tsinci muryarta a dodon kunnesa, gurinta ya kallo kamar ba ita tayi maganar ba, karasawa gurinta yayi tare da ajiya cup din ya kalli agogon hannunsa tara ta gota.
“Nagode da tunatarwa, sai anjima.”
Yana fadin haka ya fita a kitchen din sakamakon saurin da yake, bin bayansa tayi da kallo, kamarsa da Van gidan daban.
Share zancen da take yi tayi ta ci gaba da aikinta, bayan ta gama ta iyalan gidan suka fito ta gaishes suka amsa mata kamar yadda suka saba da fara’a da murmushin da baya wucewa a fuskokinsu.
Bayan sun gama suka koma falo ta tattara wajen goge, tana cikin yin aka rangada sallama tare da shigowa cikin falon, matashivar budurwace da baza ta wuce shekaru ashirin da biyar ba tare da ita karamar varinya da shekarunta zai kai
goma.
Amsa wa mutanen falon su kayi da gudu karamar tayi gurin
Hajiya Maryam ta fada jikinta “Mamma.”
Rungume ta Hajiya tayi tana son yarinyar.
“My sweet daughter Barka da dawowa.
“Nayi kewarki Mammana.”
“Nima haka My Raudah”.
“Ni fa Rau?” Cewar Aunty Ani tana kallonsu.
Murmushi Hajiya Maryam tayi tace.
“Ke naki gaisuwar sai antima.”
Dariya Aunty Ani tayi tana kallon masu shigowa yar suce
Noor da yar yayan Babansu Zaituna, da sallama a bakinsu suka karaso wajen iyayensu, bayan sun amsa musu suka tambayi yan gida, kasancewar Noor da Raudah da Sanjidah sun samu hutun makaranta, Noor da Raudah suka tafi gidan Karin babansu hutun sati biyu yau suka gama suka dawo tare da Zaituna sa’ar Noor.
Da sallama ta karasa wajensu hannunta dauke da faranta ruwa da abin motsa baki, Noor da Zaituna ta gasar gain zasu girme mata da kadan, ba laifi suka amsa mata cikin fara’a kafin tabar wajen.
“Wacce ita?”
Noor ta fada tana tsiyayan ruwan da Murshida ta ajiye.
“Murshin Mamar Murshida.” Aunty Ani ta fada.
“Itace Murshidn?” Noor ta fada tana neman karin bayani.
“Eh ba ruwa ta yarinyar aikinta kawai take yi.”
“Yafi mata ai dan was masu aikin basu da kamun kai.”
Cewar Zaituna na Kokarin kawar da maganar.
Karfe biyar ya shigo gidan da sallama ya shigo da gudu
Raudah ta gurinsa ya dagata sama.
“Little sister.”
“Am back big brother.” “Welcome back my dearest, Amma gaba gaba baxan iya daukarki ba kinji nauyinki.”
Turbine fuska tayi tana cewa “Ni dai bani da nauyi”
“Uhm uhm fa Raudah.”
Yayin da yake zaman a daya daga kujerun falon, Zaituna da Noor suka gaishesa ya amsa yana musu Barka da zuwa, bai jima ba yayi hanyar bedroom nasa, mintuna arba’in ya fito cikin doguwar jallabiya.
Ta musu sallama tana kokarin barin gurin ya fito gain ta nufi hanyar fita shina ya fasa karasawa ya dan d’aga murya.
“Mamma zanje masallaci magriba ta kusa.”
“Bakaci komai ba fa.” Ta fada dan tsayarsa.
Bai bata amsa ba ya fita yabi bayanta, tana fita ya fito ba tayi tsammanin zasu hada hanya ba, ganin shi kawai tayi gefenta yana tafiya, dan dakatawa tayi ta kallosa, hanya yake kallon.
“Ina wuni Ya aiki?”
Ta fada tana ci magana da tafiyarta.
“Lafiya kalau ya naki aikin.”
Ba tayi tsammanin amsa daga gareshi ta tsinkayi muryarsa cikin kunnenta.
“Ummu Allahamdulillahi.” Ta fada tayi gum da bakinta, tafiyar kurame su kaci gaba day har ya iso bakin masallaci dake layin unguwar su, anan taga ya tsaya. Wato dama masallaci zaije shine ya jera tafiyarsa da nata.
“Sai gobe ko, ko kina bukatar rakiya?”
Maganarsa ya dawo da ita sai yanzu taga ashe itama ta tsaya ganin ya tsaya.
A kunyace ta girgiza kanta sosai taji kunya. ‘To ina hankalin ta ya tafi, ganin ya tsaya, me zai tsayarta ita?
‘Dama ina ke ina hada tafiya dashi, hanyane kawai ta hadalu ba yanda ya iya.’
Tafiya ta fara kokarin yi tayi taku uku ta tsinkayi muryarsa.
“Don’t worry gobe zan miki rakiya har gida, yanzu ina sauri ne.”
Da hanzari ta dago idanuwanta tana juyowa, murmushi yayi mata yana daga kansa alamar eh.
Cike da kunya ta juya taci gaba da tafiyarta ji take ma tana hardewa da irin kallon da yake mata.