NUFIN ALLAH CHAPTER 8 BY AYSHA DANSABO HAUSA NOVEL

📱 *NUFIN ALLAH…!* 🤲🏻
_*Arewabooks@ayshadansabo*_

*Paid book:500*

*Chapter 8*

_Free page_

Bayan Adamu ya ci abinci ya gabatar da sallar azuhur anan cikin zauren gidan Inna Mairo, sai suka yi sallama da juna ya juya don komawa garin kaduna.Inna Mairo ta juyo zuwa cikin gidan daga yi masa rakiya da tayi,tana ji zuciyarta na cigaba da yi mata matsananci zafi. A nan tsakar falonta ta samu Najma na fiddo kayan da ke cikin waɗannan paper bangs ɗin.Ta nemi guri ta zauna tana cigaba da kallon kayayyin da Najma ke fiddowa.Kayayyaki ne da aka raba wajen bikin irin cups da su plate, sai su towels na wanka da su mafitai masu kyau da sauran tarkace. Ɗaya bag ɗin kuma turmin atamfa ne mai tsada haɗe da wani laces mai shegen kyau, sai takalmi flat shoe product ɗin CHANNEL. Najma ta dinga juya kayan tana yaba kyawunsu, yayinda Inna Mairo da ke kallonta ta dinga ji zuciyarta na karyewa.Hawaye suka fara taruwa a idanunta ,ta dinga jin ƙaunar Hajiya Zainab na sake samun waje a zuciyarta. Cikin wani irin sanyin murya ta dubi Najma ta ce, “Watakila ta siya mini waɗannan kayan ne a tunaninta zan isa da wuri sai a ɗinka mini inci biki dashi.Ki taya ni yi mata fatan alkhairy domin yadda take nuna mini ƙauna ta fiye mini ƴan uwana da sam bana cikin zuciyarsu.” Inna Mairo ta ɗan dakata da maganar wani abu mai mauyi na sake danne zuciyarta. Da ƙyar ta iya cigaba da faɗin, “Najma aurar Yara biyu fa aka yi amma ban yi darajar da zanji koda labari ba, wata iriyar ƙiyayyace Gwaggo ke mini har haka? Meyasa idan ita ba zata sanar min ba Yaya Kabeeru da kansa ba zai iya aikowa a sanar mini ba? Sabida ni ɗin basu damu dani bako? Suna ƙyamar na raɓi hidimarsu don za a nuna ni a ƙasƙance ace ni jininsu ce dana fito daga ƙauye ko? Meyasa zumunci ya yi lalacewar da ɗan uwanka na jini ke maida kai bakomi ba matuƙar aka ce kai ɗin ba kowa bane, ko wanda ka ke tare da shi ba kowa bane? Zafi nake ji sosai a cikin zuciyata Najma,na rasa yadda zanyi na cigaba da yin sabo da irin wannan tozarcin da ake yi mini don anga ba idanun Abbah a raye….” Inna Mairo ta kasa cigaba da maganar sakamakon kuka mai ƙarfi da ya taho mata, ta dinga yinsa har da shashsheka tana ji tamkar ƙirjinta zai buɗe sabida zafi da ciwon da take daga cikin zuciyarta. Hankalin Najma ya tashi da ganin irin yadda Inna Mairo ke kuka,wani irin tausayin Inna ya kamata. Hawaye suka dinga zarya a fuskar Najma tana rarrashin Inna Mairo.Tsana da jin zafin Gwaggo da Ƴan uwan Inna na sake zama a zuciyarta. Da ƙyar tayi nasarar tsaida kukan da Inna Mairo ke yi,ta sanya hannu tana share mata hawayen da suka kasa tsayawa. Cikin tsananin raunin muryar da tausayi da zallar damuwa suka kassarashi Najma ke faɗin, “Inna kiyi haƙuri, ki sake akan wanda ki ke yi.Komi zai wuce, zasu yi nadama wataran, domin sun cutar da zuciyarki a lokacin da kike matuƙar buƙatar su nuna tausayi da kulawarsu gareki. Kina dani Inna kuma In Sha Allah sai na share miki hawayenki na sanya farin ciki a zuciyarki,farin cikin da zai wanke damuwa da ƙuncin da suka cusawa zuciyarki.Don Allah Inna karki saka wannan baƙin cikin a zuciyarki ta yadda zai tada ciwonki, domin ni kaɗai kike sanyawa cikin firgici da ɗimuwa a duk sanda zan ganki cikin halin ciwo.” Najma ta dakata da maganar hawaye na cigaba da zarya akan fuskarta. Inna Mairo ta dubi ƴarta tana sake jin tausayin kansu na kamata, ta miƙa hannu ta riƙo na Najma tana faɗin, “Ba zanyi hakan ba Najma, amma ki sani dole zuciyata da shiga ƙunci da irin wannan abinda aka yi mini.Ki tayani addu’a Allah ya danne zuciyata domin bana ji a yau zan iya koda rintsawa ne. Zuciyata zafi take yi ina jin ciwo mai yawa a cikinta Najma.” Inna ta dakata tana zare hannunta daga riƙon da tayi wa Najma ta nufi ɗakinta jiri na ɗibarta. Hankalin Najma sai ya sake tashi,tabi bayan Inna da kallo wasu hawayen masu zafi na sake ɓalle mata. Duk yadda ta yi ƙoƙari wajen tausar zuciyar Inna Mairo ta kasa, domin ko abinci cokali uku Innar ta kai baki ta ce ta ƙoshi. Da ƙyar ta sha ruwa ta haɗiyi maganinta na rana ta kwanta,tana cigaba da jinyar zuciyarta da ke mata tsananin ciwo har lokacin. Zuwa yamma bayan Najma ta kammala yiwa Inna ɗan faten tsaki da yakuwa, sai ta juye a kula ta nufi ɗakin Inna dashi ta aje.Ɗakinta ta nufa ta zuro dogon hijab ɗinta har ƙasa kalar sararin samaniya,kalar ya yi mata kyau matuƙa tare da haske black beauty face ɗinta. Ta leƙa ɗakin Inna ta sameta a kwance har lokacin bisa katifarta,ta rufe idanunta tamkar mai yin bacci.Amma a zahiri idanunta biyu ta dai rufe idanun ne kawai, don bata buƙatar barinsu a buɗe sabida yadda idanun kansu sukai mata wani irin nauyi. Najma ta sanyaya murya ta ce, “Inna zan ɗan leƙa gidan Baba Hakimi, zan dawo yanzu bada jimawa ba.” Kai kawai Inna Mairo ta gyaɗa wa Najma, ba tare da ta iya buɗe baki tayi mata magana ba. Najma ta juyo ta fice zuciyarta cike da damuwan halin da Innan ta shiga sanadiyyar kawai ba a sanar da ita bikin Ƴaƴan ɗan uwanta Yaya Kabeeru ba. Tafiya take yi cikin sanyin jiki har ta isa ƙofar gidan Hakimi, ta samu mutane zaune daga wajen zauren bisa shinfiɗu. Ta risina ta gaidasu ta wuce zuwa cikin gidan, tana ji ƙafafunta na faman harɗewa sakamakon idanun maza da suka yi mata rikiya. A tsakar gida ta samu Inna Karima na gyaran gyaɗar da za ta zuba a miyar taushe. Da fara’a ta ɗago tana amsa sallamar Najma tana faɗin, “Lale Najma, yanzu Hanne suka gama zancenki ita da Lubah.” Najma ta ƙarisa inda Inna Karima ke zaune bisa kujerar tsugunno, ta gaidata cike da ladabi tana faɗin, “Alllah sarki, na tsaya na kammala yiwa Inna fate ne shiyasa ban fito da wuri ba.” Inna Karima ta jinjina kai tana faɗin, “Ya jikin nata Najma, da fatan dai tana shan magungunan? Ɗazu Hakimi ya gama maganar cewa Auwalu zai je a sayo cikon ɗaya maganin.” Najma ta saki murmushin yaƙe tana cewa, “Jiki da sauƙi Inna, tana shan maganin bisa ƙa’ida. Amma yanzu haka a kwance na baro ta, tana cikin ɓacin rai mai tsanani Inna.” Inna Karima tayi saurin aje tray ɗin hannunta tana duban Najma ta ce,”Subhanallahi! Mai ya sameta Najma, ana murna jiki ya yi sauƙi kuma?” Najma ta sake narke fuska alamun tana cikin damuwa, ta dubi Innarsu Hanne cike da sanyin murya ta mayar mata da yadd aka yi. Inna Karima ta sauke zazzafar numfashi bayan ta gama sauraren Najma, ta buɗe baki cikin ɓacin rai ta ce, “Wannan Gwaggo wai wace iriyar zuciyace gareta? Meyasa ba zata mance abinda ya faru a baya ta gane cewa komi fa NUFIN ALLAH ne, yadda duk yaso hakan dole zai kasance. Mairo bata da laifi domin ba ita ce ta sanya mahaifinta auro Innarta ba, ba kuma ita ce ta zaɓawa kanta auren Malam Mahmuda ba. Allah ne ya yi nufin hakan zai kasance, don me ba zata saduda ta gane komi yin Allah bane? Ki kwantar da hankalinki Najma, zan yi magana da Hakimi domin lokaci ya yi da ya kamata ace ya shiga cikin wannan lamari ya daidaita tsakanin Mairo da Ƴan uwanta koda son ran Gwaggo ko babu. Domin idan aka cigaba da tafiya a hakan, tabbas watarana za a wayi gari baƙin cikinsu ya yi ajalin Mairo.Wanda mu ne za a yiwa asara basu ba, domin su ɗin basu san daraja da ƙimarta a matsayinta na mace tilo a cikinsu ba.” Inna Karima ta kai ƙarshen maganar fuskarta na bayyan zallar ɓacin ran da ke zuciyarta. Najma da tayi zuru tana saurarenta,ta ɗaga manyan fararen idanunta tana duban Inna Karima ta ce, “To Inna da ko na gode idan ki kai wannan taimakon, domin ina cikin matsanancin damuwa. Ina jin tsoron ciwon zuciyar da ke barazanar samunta ya sameta, idan hakan ya faru na shiga uku Inna.” Najma ta kai ƙarshen maganar cikin rawar murya. Inna Karima ta dinga rarrashin Najma tana kwantar mata da hankali, daga ƙarshe ta ce ta tashi ta isa ɗakin su Hanne suna nan a ciki. Ta ja ƙafa a hankali ta isa ɗakin amininan nata su Hanne, zuciyarta na yin sanyi da kalaman da Inna Karima tayi mata na kwantar da hankali. Shafin hira suka buɗe da ƙawayen nata su Hanne, waɗanda take kallo a matsayin ƴan uwa na jini da bata dasu. Sun ɗauki lokaci suna raha a tsakaninsu, sai da Najma ta kalli agogo ta ga lokaci ya ja sosai, sannan ta miƙe tana sanar dasu cewa zata wuce gida ta baro Inna ita kaɗai bata jin daɗi kuma. Cike da alhini suke tambayarta me yasamu Innar? Najma ta basu amsa da cewa jikin ne dai ya ɗan motsa mata, bata sanar dasu gaskiyar abinda ya kawo ɓacin rai a zuciyar Inna Mairon ba. Suka yo mata rakiya har zaure bayan tayi sallama da Inna Karima da Amaryar Hakimi mai suna Ladiyo.

Ta isa gida ana daf da kiran sallar magriba, ta wuce direct ɗakin Inna Mairo don duba halin da take ciki. Bata sameta a ɗakin ba hakan ya bata tabbacin ta fita zuwa bayi ne, sai ta nufi ɗakinta tana zare hijab ɗin jikinta ta aje bisa katifarta. Fitowarta falo ya yi daidai da shigowar Inna Mairo, ta dubi Najma tana faɗin, “Sai yanzu ki ka dawo Najma?” Najma ta ɗan narke fuska tana faɗin, “Inna kiyi haƙuri, wallahi ban ankara ba naga lokaci ya tafi.Inna Karima suna gaidaki sun ce ai miki sannu da jiki, sannan Baba Hakimi ya bai wa Auwalu kuɗin maganinki da ba a sayo ba.” Inna Mairo dake sauraren Najma sai tayi murmushin yaƙe tana faɗin, “Alhamdulillah! Allah ya biya shi da gidan aljanna Najma.” Najma ta amsa da cewa, “Ameen.” Tana mai wucewa waje don zuwa ta ɗauro alwala.

Suna zaune tare da Inna Mairo bayan sallar isha’i suka jiyo sallamar Hakimi da Inna Karima. Najma tayi saurin fita tana musu barka da zuwa. suka ƙariso cikin ɗakin Inna Mairo Hakimi na amsa gaisuwar da Najma ke masa cike da kulawa. Inna Mairo tayi saurin shigewa ɗaki ta sanyo hijab, kafin ta fito ta zauna daga kusa da Najma tana yiwa su Hakimi barka da zuwa. Bayan sun gama gaisawa da tambayarta jikinta, sai Hakimi ya ɗaura da yi mata nasiha kamar ko yaushe akan ta cigaba da haƙuri da rayuwa. Inna ta dinga gyaɗa kai tana jin ƙarin nauyi a zuciyarta, musamman da ya ambato mata sunan Gwaggon kaduna. Hakimi ya cigaba da duban Inna Mairo yana faɗin, “Mairo lokaci ya yi da zamu je gani gaki gaban Gwaggo ta gaya mana mi kika yi mata da ta riƙeki haka a zuci? Meyasa ba zata gane cewa komi mai wucewa bane, sannan Ubangiji na son masu yawan yafiya da manta sharrin mutum su rungumi alkhairinsa.Zaki tasa ƴarki Najma mu je gani gaku domin kawo ƙarshen wannan ƙiyayya,don naga alamun lamarin kullum sake lalacewa yake yi maimakon ya gyaru. Bai kamata ace an kawo lokacin da har za a aurar da Ƴaƴan Kabeeru amma ace baki yi darajar da zaki sani ba, sabida an kai maƙura wajen nuna miki cewa ke bakomi bace. Abin ya yi mini ciwo matuƙa Mairo, amma ina miki nasiha da ki ɗauki dangana ki kuma maida komi ba bakomi ba. In Sha Allah! Komi zai daidaita, ni dai alfarmata kawai ki amince da buƙatata karki ce mini a’a.” Hakimi ya kai ƙarshen maganar yana duban yadda hawaye ke gudu akan fuskar Inna Mairo. Cikin rawar murya ta saci duban Hakimi tana faɗin, “Ƙafi ƙarfin ka nemi dukkanin alfarma in kasa yi maka,sai dai ina matuƙar jin tsoron kar taci mutuncinka idan mun je gareta. Kayi haƙury abar maganar har zuwa lokacin da ita da kanta zata gane gaskiya ta nemeni.” Inna Mairo ta ɗan dakata tana duban fuskar Hakimi, wanda ya kafeta da ido yana jin dukkanin ƙaunarta da yake binnewa tsayin shekaru na neman fallasa kansu. Ya yi gyaran murya yana faɗin, “Mairo ba za ai haka ba, ke ce ƙarama kuma ke ce kika yi fushin da kika daina bibiyarsu sabida gujewa tozarci.Wanda hakan ba cikakkiyar hujja bace da zaki yanke zumunta da ƴan uwanki, ko gurin Allah baki da hujja Mairo don shi ya faɗi cewa ku sadar da zumunta koda ga waɗanda suka yanke muku ne. Don haka zamu je gareta ki durƙusa ki bata haƙurin ƙauracewa zuwa garesu da kika yi tsayin shekaru, ni kuma nayi miki alƙwarin zan bi miki hakkinki wajen hutumarta ta sanar damu aibunki ko wani abu mara kyau da kika taɓa yi mata a rayuwa da har kika cancanci ta nuna miki irin wannan ƙiyayyar ta son zuciya da take nuna miki.” Hakimi ya dakata daga maganarsa yana jin ciwo da zafin irin yadda tsohuwar take treating ɗin Maironsa, wacce tun bayan rasuwar amininsa yake ɗawainiya da soyayyarta a zuciyarsa. Ba don ta jima da sanar masa har abada ta haramtawa kanta aure in dai shi ne zai zamo mijin ba, da tuni ya jima da mallakarta a matsayin matarsa. Inna Mairo da zuwa lokacin take kuka har da shashsheka, sai ta ja hanci tana magana cikin rawar murya ta ce, “Allah ya kaimu lokacin da zamu je ɗin,Allah kuma ya fisshemu tozarci daga gareta.” Hakimi da ya ji daɗin kalaman Inna Mairo, sai ya saki murmushin jin daɗin amincewarta cikin sauƙi yana mai faɗin, “Madallah Mairamu! Allah ya yi miki albarka ya ƙara miki juriya da haƙurin fuskantar dukkanin jarabawa ta rayuwa. Allah ya raya mana Najma ya yiwa rayuwarsu albarka. Ba zaki nadama ba Mairo domin Allah yana tare da masu yawan haƙuri da yawan yin yafiya ga bayinsa da suka zaluncesu. Zamu tafi a ranar asabar mai zuwa idan Allah ya kaimu, domin ina fata ya kasance mun yi sa ar ganin shi Alhaji Kabeerun tunda ƙarshen mako ne da ƴan boko ke zama tare da Iyalansu.” Inna Mairo ta kai hannu tana share fuskarta ta dubi Hakimi ta ce, “Hakane kam, Allah yasa muyi farar tafiya.Ubangiji ya duba gaba da bayanka ya kuma raya Iyali. Bamu da bakin godiya bisa ga hidimar da ake yi damu tsayin shekaru ba tare da gajiyawa ba,tabbas samun amini na gari irinka sai an tona.Don haka tsakaninmu daku duka kai da Iyalanka sai dai addu’ar fatan gamawa lafiya.” Inna Mairo ta juya ta dubi yadda aminiyarta Inna Karima ke tayata matsar ƙwalla ta cigaba da cewa, “Karime a tayani sake yin godiya, Allah ya biyaku da gidan aljanna domin kuma kun kasance mataye nagari,waɗanda ke ƙarfafa zuciyar mazajensu da basu goyan baya wajen aikata alkhairy ba tare da kushe ko hassada ba.Tabbas ku ɗin abin a yabeku ne a kuma gode muku, musamman ke da kika zame masa jajirtacciyar uwar gidan da kike tsaye wajen ɗaurashi akan hanya madaidaiciya.” Inna Mairo ta ƙarisa kalamanta cikin raunin murya sosai. Hakimi ya bita da kallo yana jin wani irin yanayi na mamaye zuciyarsa, yayinda Inna Karima ta kama hannun Inna Mairo ta riƙe tana faɗin, “Kome muka yi muku bamu faɗi ba Mairo, domin duk ɗan halak ba zai mance alkhairy ba. Marigayi Malam Mahmuda ya kyautata mana a lokacin yana raye, ya kuma hidimta mana da dukkanin iyawarsa. Don haka idan ma bamu duba bayansa ba tamkar munci amanar zumunta da ƙaunar da ya nunawa Hakimi da mu kanmu ne. Ki daina gode mana Mairo domin abinda ya dace muke yi, kuma muna fata kada Allah ya nuna mana lokacin da zamu gaza. Allah ya ƙara miki lafiya, yasa wannan tafiya da zaku yi ya zamo silar yayewar baƙin cikinki da damuwarki. Allah ya daidai tsakaninki da ƴan uwanki su gane cewa ke ɗin amanace a garesu, kuma baki da waɗanda suka fisu kamar yadda suma har duniya ta tashi basu da tamkarki. Domin kece jininsu da zasu nuna suyi alfahari dake bayan ƴaƴansu da suka fito daga jikinsu.” Inna Karima ta kai ƙarshen maganar cikin nuna tsantsar kulawa ga Inna Mairo, wacce ke jinjina kai dukkanin kalaman Inna Karima na ratsa jiki da zuciyarta. Cikin yin ƙasa da murya Inna Mairo ke zubawa Inna Karima godia, tana mai yi mata fatan alkhairy duniya da lahira. Sai wajen tara da rabi suka yi sallama da Inna Mairo don komawa gida,bayan Hakimi ya aje mata ledar maganin da Auwalu ya siyo a cikin garin shika.Inna Mairo ta sake yin godia tana mai yi musu rakiya har bakin zaure bayan Najma ta fito daga ɗakinta tayi musu sai da safe…….✍🏻

 

*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *Evidence of payment to this number:08167768704*

🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA’AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*

*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻

 

#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰

You cannot copy content of this page