KAFIN IN ZAMA LAWYER BY NABELERT LADY COMPLETE HAUSA NOVEL

Wata bakar mota ce me tsadar gaske tashiga wani hadaddan gida, daga gani babu tambaya kasan gidan masu akwai ne.

A parking space ya aje motar ya fito, masu gadin gidan se mika gaisuwa sukeyi, yana daga masu hannu fuskarshi dauke da fara,a.

Alhaji Lamido Jaye kenan, babban dan siyasa me rike da matsayin Director Na house of assembly a Abuja.

Alh. Lamido babban mutum ne, yana zaune a garin katsina tare da matanshi guda 3, biyu suna zaune a garin katsina, amarya kuma suna tare dashi a Abuja.

Yana da matukar kula da iyalanshi, mutum ne wanda beda son kanshi, yana kokarin kwatanta adalci atsakanin yaranshi da matanshi.

Week end kawai yake zuwa katsina. Uwar gidanshi Haj. Maryam, mace ce me kirki da saukin kai. Diya ce ga Alh. Garba Mekaita, yar asalin garin Funtua ce.

Tana da yara 2 da mijinta, Babban danta shine ANWAR LAMIDO JAYE, yagama karatunshi a A,B,U Zariya inda ya karanci Dr. Yana aiki a Medical Center fannin yara.

Dr. Anwar yana da nutsuwa, duk da yanda mahaifinshi yake da kudi sam baya takama da su. Yana da son yara shiyasa ya bada duk kanin lokacinshi ga aikinshi.Beyi aure ba haryanzu.

Kanwarshi Zaituna, yanzu tana karatu a school of nursing katsina. Itama tana da hankali da nutsuwa.

Matarshi ta 2 itace Haj. Falmata, yar asalin garin kaduna ce, iyayenta suna da hali, yaranta 2, duka mata Laila da Ilham. Laila tana karatu a B,U,K kano. Ilham kuma tana S,S 3 a F,G,C, Bakori.

Haj. Falmata tana da son yaranta, batason abinda ze tabasu, sede kuma sam basa fitina ita da Haj. Maryam, suna zaune lafiya harda yaransu.

Amaryar Alh. Suhailat, yaronta daya AMMAR yana primary school a abuja, sam baruwanta da sauran kishiyoyinta, asalima babu abinda yake hadasu se idan sun hadu a hidimar mijinsu.

Ganin bata kulasu yasa suma suka fita harkarta, kowa yana hidimarshi. Sanin mijinsu baya son fitina yasa acikinsu babu wanda yake kawo wata damuwa acikin gidan.

Da sallama Alh. Lamido yashiga cikin falonshi, Umman Anwar da Aunty Mahaifiyarsu Ilham suna zaune suna kallo, tashi sukayi suna fadin sannu da zuwa Alh.

Umma ce ta amshi jakar hannunshi kasancewar itace keda girki. Zama yayi, Aunty tace ina wuni Alh, ya hanya? Murmushi yayi yace lafiya lau Auntyn yara, na sameku lafiya da yara?

Tace lafiya lau, suna ciki ma ba suji zuwanka ba. Tashi tayi ta wuce dakin yan mata domin ta kirasu. Umma ce tafito dauke da tire, bayan ta zuba mashi tazauna tana gaisheshi.

Hannunta ya kamo yana fadin lafiya lau Umman yara ya aiki ? Murmushi tayi tace lafiya lau, ya mutanan Abujan? Yace kalau suke suna gaisheku.

Hannunta tazame jin sallamar yan mata, amsawa Alh, yayi sannan yabasu izinin shigowa. Kasa suka zube suna gaishe shi, yace lafiya lau, ya makaranta Laila? Tace lafiya lau Abba,muna hutu ma.

Kallon Ilham yayi yace saura sati 1 ku koma ko? Tace E Abba kuma daga wannan hutun bazamu kara dawo wa ba se mungama. Dariya yayi yace ashe muna da yan Candy agidan nan.

Umma tace sosai ma, kinga se adena kukan komawa makaranta. Ilham tace kai Umma ai yanzu seniors ne mu babu sauran wahala kuma.

Abba yace to Allah yatemaka, seki dage kifito da result me kyau, kina ganin sauran yan uwanki babu wanda yasamu matsala da secondary result dinshi.

Kallon Umma yayi yace Zaituna batazo gida bane cikin week end din nan? Umma tace wai practical suke dashi gobe asabar. To Allah yatemaka, wannan karon baza tazo gida ba kenan.

Bakomai kafin intafi zanje makarantar tasu semu gaisa dan idan nakoma senayi 2 weeks banzo ba, akwai wani aiki da zamuyi.

Ina Dr. Fa? Murmushi Umma tayi tace ai kasan shi se dare ze dawo. Murmushi Abba yayi yace dan yasan be aje nauyi agidan ba shiyasa ya bada duka lokacin shi a asibiti, da yana da iyali ai dole yarika dawowa da wuri.

Shigowa Aunty tayi tana fadin kaima de kafada Alh, ina ganin semun samo mashi da kanmu sannan zeyi aure. Murmushi Umma tayi batace komai ba.

Abba yace rabu dashi, zezo yasameni, idan ma tsoron matan yake zan baki dama kinemo mashi wadda ta dace. Tashi yayi yana fadin bara inshiga ciki inyi wanka se nazo muci abincin. Ilham tace Abba afito lafiya.

Rayyana! Rayyana! Na,am Amma ganinan hijabita nake nema. To ai gara kiyi sauri kada yamma tayi kije kisiyo mani kayan miya indora abincin.

Fitowa Wadda aka kira da Rayyana tayi tana kokarin saka hijabinta. Amsar kudin tayi, Amma tace kisiyo mana kifi na 200 dan Allah kiyi sauri banaso Babanku yazo bangama ba.

Rayyana tace Amma bara induba idan Nabila tana nan tarakani. Amma tace kinsan data dawo nan zata shigo ai, amma leka kigani kota dawo dan Ummanku taleka makota.

Rayyana tace to bara intafi amma idan Nabila tashigo kice tabiyoni semu dawo tare. Amma tace naji maza kitafi, fita tayi tana fadin sena dawo Amma.

Rayyana da Nabila kenan su biyu Allah yabama mahaifinsu, Alh, Lawal me Hula, kusan kansu daya, yan watan nine tsakaninsu.

Alh, Lawal yana da mata 2, Karima da Saude, Karima itace uwargida, kuma itace mahaifiyar Nabila, tunda ta haifeta bata kara haihuwa ba, dama kuma seda ta shekara 5 bata samu ciki ba.

Ganin haka yasa Alh, Lawal yakara aure, cikin ikon Allah ana auren Karima tasamu ciki,alokacin da Alh, Lawal yasani bakaramun jin dadi yayi ba, haka suka zauna zaman lafiya ita da kishiryata Saude.

Alh. Lawal babban dan kasuwa ne, yana da kudi na rufin asiri, gidanshi yana kofar kwaya cikin garin katsina, sede sam beda sha,awar barin yaranshi su wuce gaba da secondary.

Yana kula da iyalinshi sosai, hakan yasa hankalinshi yake kwance a koda yaushe. Cikin Karima yanada wata 2, Itama Saude tasamu ciki, murna agurin Alh. Lawal ba,a magana.

Haka suka cigaba da renon cikinsu, har lokacin haihuwar Karima yayi ta haifi Mace, kyakkyawa fara tas da ita. Ranar suna aka samata Nabila.

Bayan wata 2 da haihuwar Karima Saude ta haihu itama mace, Alh. Lawal yaso ace namiji yasamu, amma ganin mace ce yasa yayima Allah godiya da addu,ar Allah yashiryar dasu.

Ranar suna akasama yarinya Rayyana. Haka suka cigaba da renon yaransu hankali kwance, kome suke so mijinsu yana yimasu.

Karima tana sana,ar saida kayan sanyi, irinsu zobo kunun aya, anan cikin gida take saidawa. Ganin Saude bata saida komai yasa tayima mijinsu magana akan yabama Saude jari seta rika saida aya, zobo, da sauran kayan hadinsu, ita kuma tana yi.

Sosai yaji dadin abinda Karima tayi, haka yaje yasiyo ma Saude duk abinda Karima tace yabata, godiya sosai tayi mata, haka suka cigaba da sana,arsu.

Sede tunda suka haihu so daya babu wadda takara haihuwa, Saude ce kawai tayi bari bayan haihuwar Rayyana tun suna damuwa har suka hakura ganin shi mijin nasu yabarma Allah komai.

Karima yar garin Mani ce, ita kuma Saude yar Kankiya ce. Zuwa yanzu yaransu suna da shekara 24, sungama secondary islamiya kawai suke zuwa, ajinsu guda, duk inda zasuje tare suke zuwa, wasu har dauka suke yan 2 ne, duk da basa kama sosai amma kusancinsu yasa ake ganin kamar yan 2 ne. Dan Nabila tafi Rayyana kyau, kuma ita fara ce.

Da Sallama suka shigo, Amma ce ta amsa tana fadin ai dama tunda naga baki dawo da wuri ba nasan kinhadu da Rayyana. Dariya Nabila tayi tace wlh kuwa Amma tana shawo kwana muka hadu shine na rakata.

Umma tadawo kuwa? A,a bata dawo ba, amma nasan yanzu zaki ganta. Ku dauki kayan miyan ku gyara daya kuma ta wanke kifin ta soya. To Amma yau mezaki dafa mana? Koma menene ai tare zamu dafa zaku gani, ku wuce muje, hijabinsu suka aje suka nufi kitchen.

Dan Masani lafiyarka naga kabuga tagumi, ko yau ma ba,a dace ba? Ajiyar zuciya wanda aka kira da Dan Masani yayi tare da cire hannunshi daga kumatunshi yace kaide bari Abdul.

Wlh har nafara cire rai da samun aikin nan. Wai ace yanzu mutum da takardunshi da komai amma samun aiki yayi mashi wahala. Tunda nake fita neman aikin nan babu ranar dana ji haushi kamar yau.

Wata babbar Chamber ce naje ta Babbar kotu, akwai wani babban lawyer kowa yasanshi agurin,ya iya aiki sosai, sede nayi sati 2 ina neman yanda zanyi inganshi.

Da kyar nasamu wani masinjanshi ya karbi number ta, ganin yanda nake zuwa bana samunshi, yace duk ranar dayazo zekirani. Kasan wani abun haushin? Wai ina zuwa na bashi takarduna.

Kasan meyace? Cewa yayi wai tunda banida experience akan Law sede yadaukeni amatsayin masinjanshi, amma tunda inada kwalin degree matsayina zefi na tsohon masinja kadan.

Kuma ma private aiki ne zanyi mashi. Wlh lokacin daya gama fada mani wani kululun bakin ciki ne ya tokareni. Kamar in karbe takarduna infito, haka de na tsaya yagama fada mani komai.

Wannan takardar yabani yace incike idan na amince zanyi aikin to inmaida mashi, nan da kwana 2, idan kuma ban amince ba, idan kwana 2 ya wuce beganni ba, ze bama wani aikina.

Ina fitowa kamar in yaga takardar dan haushi, haka de nasamu guri nazauna na kara karanta takardar, kasan ko nawa zerika bani? Dubu 15 fa, wai seyaga yanayin aikina sannan zekara mani.

Yanzu Abdul kasan irin yanda nasha wahala kafin in kammala wannan karatun nawa. Tunda nagama secondary iyayena suka rasu, kakata bawani karfi gareta ba, kana ganin saboda rashin kudi seda na bata shekara 1 kafin nasamu nashiga University.

Admission dina na farko sede asararshi nayi saboda rashin kudi. Har dako nayi, nine aikin karfi dan kawai insamu in kammala karatun dana sama raina. A kullum Kaka tanamun fada akan in hakura da wannan karatun, inkoma kasuwa tunda ba dole bane.

Haka na rufe idona nace mata a,a yanda nafara shan wahala ai bazan iya hakura ba. Kafin ingama itama tarasu. Haka nazamo maraya gaba da baya, Kawuna kadai yarage mani, kuma nayi alkawarin bazan ze in nemi wani abu na kudi agurinshi ba.

Domin shima bawani karfi gareshi ba. Haka nazauna acikin gidanmu ni kadai, amma saboda son Zuciya ace wai dubu 15 shine albashi na. Ai gara inje inkoya a wata private school nasan ko banza zasu bani dubu 20.

Amma yanzu nida ba abun hawa gare ni ba, ko a kudin abun hawa ai zasu tafi, yazanyi da sauran hidimomina? Hawayene suka sauko mashi. Dafashi Abdul yayi, cike da tausayi yace Sageer.

Inaso kabani hankalinka nan, sanin kanka ne baka da wani aboki koma ince dan uwan daya wuce ni. Yau munkwashe kusan shekaru 20 muna tare, babu abinda baka sani nawa ba.

Dan haka zan baka shawara guda 1, wadda idan har ka dauketa zakaji dadinta, kuma ko bayan rai na insha Allah nasan zakayi alfahari dani, amatsayina na wanda yabaka shawara da kabi har ka samu biyan bukata. Goge idonshi Sageer yayi yace ina jinka, kuma nayi maka alkawarin zan dauki duk shawarar dazaka bani matukar bazata sabama Allah ba.

Sageer Alee inaso kasani duk wani dan Adam na duniya daka gani da arziki to seda yasha wahala kafin ya tarashi. Kai yau ko mutum harkar tsafi yakeyi dole seya sha wahala kafin yatara kudi.

A kwai masu kudi da yawa da zasu fada maka ta yanda akayi suka zama yanda suke ayanzu wlh se kayi matukar mamaki.

Kai sekaji ai kai baka sha wahalar komai ba. A binda akeso mutum yarike arayuwarshi shine hakuri, idan karike hakuri babu abinda bazaka samu ba.

Hakuri yanada matukar wahala, amma daga karshe babu abinda ya kai shi dadi. Kai ko mutuwa kayi batare da kaci ribar hakurin da kayi ba, tabbas ranar gobe kiyama Allah ze linka maka akan hakurin dakayi a duniya.

Koshi wannan Barrister da kake fada shima na tabbata seda yabiyo ta irin matsayin daya baka, kai kilama naka yafi nashi daraja, ai ni agurina, duk abinda zan samu arayuwa nafiso nasha wahala kafin insame shi.

Koba komai nasan zanfi rikeshi da daraja, kuma bazan taba bari nayi wasa da damar dana samu ba. Dan haka ina baka shawara akan kada kayi la,akari da yawan kudin daza,a baka.
Ka kalli muhimmancin aikin ka.

Kudi komin yawansu suna karewa, amma kima da daraja basa taba gushewa koda bayan ranka, wata kila katara dukiya, wadanda katara dominsu kila surika amfani da ita ta hanyar banza.

Amma idan ka tsaya kayi aikinka tsakani da Allah, ko mutuwa kayi aikinka da addu,ar jama,a zasu bika har kabarinka, koda baka aje kowa ba.

A binda nakeso ka cike wannan takardar kuma kamaida mashi ita, kasa aranka zakayi wannan aiki da zuciya daya, koda wata zezo ba,a biyaka kudinka ba, kada kayi saurin fushi.

Ni nasan abinda zaka samu agurin da wanda zaka karu dashi yafi kudi. Kuma shima yanada gaskiya, yanzu idan aka dauki shari,a aka baka, nasan bazaka taba sanin yanda zaka tafiyar da ita ba.

Saboda abinda aka koya maka amakaranta daban, duk da kasamu experience a school of law amma baze kai wanda zaka samu agurinshi ba, kai da kanka kacemun Babban lawyer ne.

Kaga kenan yasan aikinshi, kada ka koyi abinda yakeyi, kawai kadauki abinda yakoya maka, kasan kamar malamin addini ne, da ake cewa kayi aiki da abinda malaminka ya koya maka, amma kada kayi aiki da abinda yakeyi.

Wannan maganace me harshen damo, ba kowane me hankali bane ze iya fahimtar abinda ake nufi, kasan da yawa akwai wasu malaman da zasu koyama dalibansu abu, amma idan ka kallesu sekaga su basa amfani da abinda suka koya.

To kaima haka nakeso ka kasance, Sageer tun muna makaranta kake da ra,ayin kazama lawyer, wannan dalilin ne yasa muke kiranka da DAN MASANI.

Gashi haryanzu wannan suna yabika, kana da gaskiya, acikinmu kafi kowa riko da gaskiya da amana, hakan yasa akoda yaushe nake fada maka kaine kadace ka karanci Law acikin mu.

Dan Allah kada kabari wasu su canza maka ra,ayi, kasan irin wannan aikin naku, babu abinda kudi besawa ayi inde a harkar shari,a ne, babu wahala wajen maida karya tazama gaskiya, kamar yanda ake iya maida gaskiya tazama karya.

Nasan duk wanda yace zeyi riko da gaskiya a fannin aikinku to ko acikin abokan aikinshi beda wani tasiri, bare kuma gurin wasu mutanan, musamman masu kudi.

Karike Allah, ze te makeka, kayi gaskiya Allah ze kareka, ina me tabbatar maka ko bana raye wata rana se kazama babban mutum a wannan harkar. Nide fatana kayi amfani da shawarar dana baka.

Kuma seka kwantar da kai ne zaka iya fahimtar abinda kakeso ka koya, duk wani aiki na duniya dole zaka samu akwai wanda yafika iyawa. Yanzu misali, mutane nawa ne kasani wadanda suke aikin kanikanci, ayanzu sunzama manyan kansu?

Amma da zaka tambayesu wlh nasan akwai wanda zece maka daga mika sifana yafara koyon aikin, wani ma aikinshi mikama ogansu abinci ko ruwa. Amma da sukayi hakuri daga karshe me suka zama.

Akwai wanda zakaga idan ya kware a aikin ma seyafi oganshi iyawa, shima ze bude gurinshi kuma yasamu yaran daze koya masu, ahaka suma zasu iya harsu koyama wasu.

Kaima idan kayi hakuri wata rana seka bude taka Chamber wadan da mutane zasu zauna akarkashinka. Dan haka kayi hakuri dan Allah Sageer.

Hannu Sageer yasa ya goge kwallar da take zubo mashi tun lokacin da Abdul yafara bayani. Gaba daya jikinshi yayi sanyi da maganganun da Abdul yafada.

Tabbas ada yamanta da alkawarin daya daukarma kanshi zeyi aiki ko badan kudi ba, ko dan ya temaki talakawa, wadan da ake danne masu hakkinsu saboda kawai talaucinsu.

Kallon Abdul yayi, ya kamo hannunshi yace nagode Abdul, hakika banida wani dan uwa daya wuce ka a duk duniyar nan, bayan iyayena banida wanda ze fadamun farar gaskiya babu son zuciya a cikinta kamar kai.

Tabbas kayi mani tuni akan abinda namanta, kuma ka kara mani wani ilimi wanda bansanshi ba na rayuwa. Ina maka albishir da cewa insha Allah zanyi wannan aikin kamar yanda kace.

Kuma zanyi amfani da abinda kafada mani, idan ma akwai kari tozan kara akan hakan, bazan kara kallon abinda za,a bani ba. Fatana Allah yashige mani gaba a wannan aikin.

Murmushi Abdul yayi yace amma gaskiya naji dadin maganarka, Allah yabamu sa,a gaba daya. Tashi muje kaga ankusa kiran magriba.

Dr. Anwar ne yafito harabar asibitinsu hannunshi rike da jaka, haduwa sukayi da abokinshi Dr. Shamsuddeen, hannu yabashi suka gaisa yana fadin bade har katashi ba?

Murmushi Dr. Anwar yayi yace kasan yau Abba yake dawowa, kuma harma ya iso, dazu Umma takirani take fada mani. Dr. Shamsu yace hakane, shikenan se Allah ya kaimu, nasan gobe bazaka fito da wuri ba tunda Boss yana gida.

Dr. Anwar yace ya danganta, idan aka kawo patients urgent ai dole nafito, amma de zamuyi magana da Abba, hannu Dr. Shamsu yabama Dr. Anwar sukayi sallama ya wuce gida.

Seda ya tsaya suka gaisa da masu aikin gidan, sannan yawuce ciki, haka al,adarshi take, shiyasa kowa agidan yake yabonshi, sam bashida girman kai.

Da sallama yashiga fuskarshi dauke da fara,a zaune yasamesu asaman table suna cin abinci. Kusa da Abbansu yaje ya duka har kasa yana fadin sannu da zuwa Abba.

Hannu yamika mashi suka gaisa, yace Dr, na sameku lafiya? Tashi yayi yana fadin lafiya lau, Abba ya hanya da gajiya? Alhamdulillahi gajiya tabi lafiya.

Kallon iyayenshi yayi yace sannunku da gida, sukace yauwa Dr, ya aikin. Su Ilham sukace Yaya sannu da dawowa. Yace yauwa yan mata na ya aikin gida ina fatan baku kyalesu Aunty na da aiki ba.

Murmushi Aunty tayi tace a,a ai basa laifi, sun tayamu aiki. Zauna ga abincinka nan in zuba maka. Murmushi yayi yace Aunty zanshiga ciki in danyi wanka, idan nafito zanci.

Bayan kowa yagama cin abinci suka koma falo domin fira, dan aka,idar Alh, Lamido baya ganin baki aranar daya dawo, sede washe garin ranar, shiyasa iyalenshi suke samun lokacin shi.

Kallon Dr. Anwar yayi yace Dr. Wai ya maganar mu ne, haryanzu naji shiru, ko semun kebe? Dariya suka saka Anwar ya dukar da kai yana murmushi. Aunty tace a,a Alh, nace kabar komai a hannuna yaron nawa kunya gareshi baya son magana agaban yara.

Alh, yace a,a nikam hakurina yakare, shekarar ka 35 fa, amma ace haryanzu kana zuwa cin abinci agidanku. Haba Dr. Kayima kanka fada mana, kaifa likitan yara ne, na tabbata saboda kanason yara yasa ka karanci wannan fannin.

Meyasa bazakayi ma kanka fada ba, kaima kayi kokarin samun naka yaran. Dan haka nagaji, ayau dinnan ba gobe ba, senaji wata magana dazan tafi da ita me dadi.

Inaso kafin indawo ace matar dazaka aura kawai zangani. Aunty tace shikenan insha Allah kafin kadawo zakaji waya medadi. Kallon Anwar tayi tace Dr, akwai wadda kakeso ne ko ka bamu zabi?

Murmushi yayi yace Aunty kunfini sanin mata, kawai kuzaba mani wadda kuka ga zata dace dani. Amma fa wadda ta iya girki kuma me tsafta. Bandamu da kyawunta ba, inde tafito daga gidan mutunci, tana da tarbiya.

Kuma akwai ilimin addini ni babu ruwana da talaucinta ko kudinta, wadan nan abubuwan nafiso, domin mu kudi ba damuwar mu bace, to banga abinda yar masu kudi zata nuna mani ba.

Dariya suka saka, Laila tace ah! haba Yaya, shima kyau ai yana cikin abubuwan da annabi yace a auri mace danshi. Anwar yace amma daga karshe me yace? Ilham tace addininta.

Anwar yace yauwa yar gari, Aunty kawai kizaba mani irin wadda nace. Aunty tace to idan takasance gidansu suna da kudi kuma tana da abubuwan da kakeso yaza,ayi?

Murmushi yayi yace, aidama nace baruwana da kudinta, kawai asamu me wadannan abubuwan. Tace angama, ammafa gaskiya bazan zabo maka mummuna ba, koda tana da fin abinda kace.

Dariya suka saka gaba daya, Anwar yace dama Aunty saisa saisa zaki nemo. Aunty tace angama, kallon Umma tayi tace Umma kawo mana taki mufara zaba.

Dariya tayi tace a,a wannan maganarku ce, mude addu,a itace tamu, munbaki wuka da nama, keda danki. Laila tace Umma nizan kawo yan makarantar mu guda 4 se azaba.

Anwar yace waike waya fada maki zaben mata kamar zaben kayan sawa ne? Dariya tayi tace emana, ai nasan halinsu. Yace to nide bansaki ba, kije kizabo naki, tukunna, dariya sukayi, Alh, yace to nide nabada zabi, kafin indawo inji labari medadi.

Kwance Nabila da Rayyana suke adakinsu kowa yayi shirin kwanciya bacci. Rayyana tana ta charting, tana dariya. Fige wayar Nabila tayi tana fadin wlh shiyasa banaso azo kwanciya babu wuta, kawai seki damu mutane da dariya.

Da akwai wuta nima se in kunna kallo in kyaleki. Dariya Rayyana tayi tace wayace kema kibama kawarki aron wayarki kawai dan tace maki zataje biki kuma kibata aron waya.

Wlh ni bazan iya kwana 1 batare da waya ba, bare kuma kwana 3. Nabila tace enaji ba komai, ai mutunci kesa ayi komai, kuma kinfi kowa sanin yanda muke da Zarah, ba waya ba, abinda yafi waya ma zan iya bata.

Itama ai tana da ita kawai lalacewa tayi, kuma kinsan kowa yanaso yaje biki da babbar waya ko? Rayyana tace to naji, sarkin tsara magana, yanzude bani wayata.

Duka Nabila ta kai mata tana dariya tace wlh yarinyar nan kinrainani, kinsande na girmeki ko? Rayyana tace da wata 2, ko? Oho koma da second daya ne, aide narigaki shakar iskan duniya.

Rayyana tace tonaji dan Allah kibani haba yar yayata ko sokike aganni online kuma bana maida amsa? Kallon wayar tayi, tace bara inga abinda yake baki dariya to.

Rayyana tace babu kyau fa kallon sirri, Nabila tace sena gani, wayar tafara kallo, murmushi tayi tace kice sabon saurayi kikayi shine baki fada mani ba.

Rufe fuska Rayyana tayi tace kai Yaya duka fa jiya muka hadu dashi, dana fita, nafiso sena gama saninshi sannan infada maki. Nabila tace to kide kula, kinsan halin samarin yanzu,

Yanzu zakiga yafara fadin kitura mashi hotunanki, daga nan kuma se abinda yayi gaba. Rayyana tace insha Allah ma bazan biye mashi ba.

Nabila tace anshi wayarki ga wannan mararjin kawar taki nan tayi maki magana, ni banga abinda kika gani agurin Hidaya ba harkike kawance da ita.

Yarinyar da tafiki komai, ita a university ma take, kawai dan tana dan zuwa islamiya shima ba sosai ba, amma kin wani like mata. Dariya Rayyana tayi tace kai Yaya banga dalilin dayasa kika tsani Hidaya ba.

Kalli yanda take girmamaki amma ke bakya gani, e bana ganin nide kawai jinina be hadu da nata ba. Rayyana ta anshi wayarta tana fadin dama hakane.

Wani zakaga jininku behadu dashi ba, nima ai jinina be hadu da Zarah ba. Nabila tace ammade kinsan Zarah tafi Hidaya kyan hali ko?

Rayyana tace yanzu de abar maganar, kowa ya kwanta. Nabila tace to kema ki kashe wayarki mu kwanta. Rayyana tace kinsan wani abu Yaya? Nabila tace sekin fada.

Wlh na kagara inga nayi aure kodan inga wai agidana nake zaune, komai nacikin gidan nawa ne, inci abinda nakeso, babu wanda ze hanani.

Dariya Nabila tayi tace lallai Rayyana da alama wannan sabon saurayin naki yazo maki da wani sabon salo, inafatan de shima ya isa aure ko?

Rayyana tace karatufa yakeyi kuma duka wannan shekarar yafara. Nabila tace bakida magana, kawai kirabu dashi, dan wlh irinsu babu abinda suke sa mutum se son aure.

Kinsan samarin jami,a akwai iya kalamai, yanzu zasu canza maka akida, ga soyayyarsu akwai tsayawa arai, tunkafin kuyi nisa kirabu dashi mucigaba da addu,a Allah yakawo mana mazaje nagari.

Rayyana tace amin, amma bazan rabudashi yanzu ba, kinga koba komai zerika debe mani kewa. Murmushi Nabila tayi tace to Allah yasa mudace, amma ki kula. Kwanciya tayi tana fadin seda safe.

A yau ne Sageer Alee ya koma office din babban brr. Yusuf. Seda yayi jiranshi na kusan awa daya kafin yazo, masinjanshi ya karbi takardar yabishi da ita.

Bayan yagama abinda zeyi ya amshi takardar ya duba, kallon masinjan yayi yace kace mashi yashigo. Bayan sun gaisa yace Sageer Alee ina tayaka murnar fara aiki dani, zan fada maka dokokina idan kaji kuma zaka iya binsu, daga gobe zaka fara zuwa aiki. Dan haka kabude kunnuwanka kaji abinda zan fada maka.

DOWNLOAD COMPLETE BELOW 

KAFIN IN ZAMA LAWYER CMPLT BY N.R.Z (1)

You cannot copy content of this page