GIDAN ARO BY Sameena Aleeyou COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin k’warewa da sanin makamar aikinta budurwar mai kimanin shekaru 29 taci gaba da kwararo bayanai tana mai nuni da Farin allo wanda hasken k’wan wutan projector ya haskesa, Ko ba’a fad’a maka ba zaka fahimci cewa cikin d’akin gudanar da binciken manya manyan laifuka suke musamman irin laifin da ya shafi kisan kai, fyad’e, Garkuwa da mutane da sauransu..

Hoton wani matashi ne na’urar Ta hasko, kwance yake a k’asa tamkar bai numfashi, ga dukkan alamu babu rai tattareda shi.. Ko ina na wajen a kewaye ne da Doguwar igiya mai launin ruwan d’orawa, jikin igiyan an rubuta _Restricted Area_ da manyan bak’ak’e…

Budurwar ta k’urama hoton idanu Wanda ya bayyana Babba gabansu kasancewar da na’uarar projector ake hasko hoton.. Ta matso sosai tana mai rage girman idanunta tana kallon hoton, a hankali take furta “Da hannun hagu ya rik’e bindigar, direction d’in da bindigar Ta kalla bai kamata harsashi ya samu k’irjinsa direct ba, ya kamata harsashin ya huda ribs d’insa kafin ya ratsa cikin k’irjinsa indai har da hannun da aka sami bindigar a ciki yayi harbin..”

Wani matashi mai kimanin shekaru 32 ya taso yana k’arasowa kusanta wanda shima d’aya ne daga cikin ‘yansanda masu gudanar da bincike da suke zaune a madaidaicin Zauren gudanar da binciken.. Hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa, idanunsa naga hoton yake furta “Well done Agent Maleeka.. But wani hanzari ba gudu ba.. Baki tunanin idan mutumin nan ya kasance bahago zai iya karkata hannunsa har harsashin ta iso daidai tsakiyar k’irjinsa ta hudasa..?”

Karkatowa Maleeka tai tana duban wanda Yai maganar kafin ta d’an tab’e baki tace “Bani da tabbaci Inspector Assad.. Amma hakan nake tunani..”

Bata Kai aya ba wata murya ta katsesu da fad’in “Oh shut up.!”

Gaba d’aya suka juyo suna dubansa, kusan tun shigowarsu d’akin kansa a k’asa yana aikin murza zoben dake mak’ale yatsarsa guda wanda yin hakan kusan d’abi’arsa ce musamman idan yana nazarin bincike..

Ya d’ago kai yana dubansu, kallon da yake sanyata daburcewa ta rasa mai take ciki, tunaninta duk su sakwarkwace shi ya jefata dashi kafin yace “Tunani kikeyi.? Ko kuwa kin tabbatar..?”

Kasa furta komai tai sai yin k’asa da idanunta da tai

Hannayensa biyu sakale cikin aljihun wandon jeans d’insa, yana tsaye gabanta yana iya hango tsakiyan kanta sabida ratan tsawo dake tsakaninsu.. Cikin muryarsa da yake tsakanin kashe mata jiki lak’was wanda yake sanyata losing kanta gaba d’aya ya soma furta “We are investigating a murder  here, in case you forgot.. There’s nothing like you thought, everything here must be known.. You must Know.. I want results and  not assumptions.. Kin fahimta..” Ya k’arashe yana kwanto da fuskarsa kusan nata, idanunsa da suke matuk’ar furgitata dab kusan nata…

A hankali take jinjina kai cikin yanayi na d’an daburcewa “I..I’m sorry Inspector, Sir..”

“I don’t need your apology.. Just do your work correctly.. Or else, you’ll be kicked out of this team..!”

Yanda yake maganar cikin tsananin zafin rai zaka fahimci ransa a matuk’ar b’ace yake..

Mutumin dake tsaye gefen Maleeka ya d’an girgiza kai kad’an kafin yace “But..”

Katsesa yai da fad’in “What do you mean but.?.. You know me quite well Assad, you know I hate incompetence.. And I easily get irritated by people like her around.”

Assad ya d’an shafi kansa dan yasan Wanene abokin nasa da kuma yanayin da yake ciki “MU’AZZAM.. will you please calm down.. I was only asking you to go easy on her..”

“Oh really..! Da gaske Assad..  Am I really being too strict?.. Let me remind you idan ka mance.. Mutuwar k’anwata muke bincike a nan Assad.. K’anwata was found dead tareda wannan d’an ta’addan.. And you’re asking me to go easy on her… My sister Assad.. My only Sister.. An kasheta in a cold blooded murder.. Someone murdered her Assad.. Sannan na kasa aiwatar da komai domin wad’anda suka kasheta su biya abinda suka aikata.. Tell me, a haka ne kake ce min na natsu.. A haka ne kake ce min I should calm down and go easy on her Assad.!” Ya k’arashe cikin tsananin d’aga murya gashin jikinsa na kuma mimmik’ewa

D’akin yai shiru sai hucin fitar numfashin Mu’azzam kakeji.. Cikin rarrabewar kalma yake ci gaba da furta “If she’s not competent enough to work with this team, the door is widely open..”

Cikin zafin nama Assad ya katse sa da fad’in “But the man who killed your sister is dead too.. He committed suicide after he killed your sister Mu’azzam..!”

Ya k’arasa jikin k’aton allon ya shiga nunawa yana fad’in “Look.. Look here, look at the suspect, ya kashe kanshi bayan ya kasheta.. Bindiga d’aya yayi amfani dashi.. Ga finger prints d’insa a jikin bindigar an samu.. Duk iyaka binciken da za’ayi anyi Mu’azzam but still babu wani abinda yake canzawa.. Until now we couldn’t figure anything out sabida bamuda wani dalili Ko hujja…Amsa  d’aya muke samu a k’arshe shine mutumin nan kashe kansa yayi bayan ya kashe Ikram.. Sannan inaga ya kamata mu saki mutumin nan dake tsare cikin interrogation, babu amfanin detaining d’insa a nan..”

Wani irin duba yake ma Assad da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja, lokaci guda yake jinjina kai kafin ya mik’a hannu saman Table dake gefensa ya d’auko k’aramar bindiga piston.. Cikin tsananin huci yake furta “I’ll proof to y’all that that man didn’t kill himself.. Someone killed him..” Yai maganar yana pointing Assad da bindigar zuciyarsa na kuma tafarfasa..

Maleeka kame baki tai idanu a warwaje take duban Assad da Mu’azzam..

“Sir.. What are you doing.. Please don’t..” Maleeka tai maganar cikeda tsoro..

Ko kallo bata ishi Mu’azzam ba balle ya amsata.. Pointing bindigar yai daidai saitin k’irjin Assad, yana kallonsa yana huci kaman mai shirin d’ana harsashi..

Lokaci guda ya karkato da bindigar saitin ya juyo da Ita saitin nasa k’irjin, bindigar tana rik’e ne cikin left hand d’insa kasancewarsa left handed, shid’in bahago ne.. Bai daina sakin huci ba yana rik’e da bindigar idanunsa tar akan fuskar Assad.

Maleeka Ta kuma zaro idanu waje ganin Mu’azzam yayi pointing kansa da bindiga, cikin tsananin daburcewa take girgiza kai tana k’ok’arin rintse idanunta, dan gani take kaman d’ana ma kansa harsashi yake da niyya

D’aya mutumin dake zaune saman kujeransa wanda shine cikon na hud’unsu a cikin d’akin wanda ya d’an fisu gaba d’aya a haife dan shi zai kusan shekaru 39 sai sannan ya taso ya k’araso yanda suke a tsartsaye..

Ya isa jikin board d’in yana nuna hannun mutumin yanda ya rik’e bindigar ya d’ana ma kansa harshashi cikin hoton, kafin ya kaikaito yana duban Mu’azzam dake rik’e da bindiga yayi pointing kansa daidai yanda wannan mutumin yayi.. A hankali ya saki murmushi yana ma jinjina kafin tunani da jajircewa a aiki irin na Mu’azzam.. Rik’e bindigar da yayi so yake ya masu proving cewa mutumin nan baiyi committing suicide ba kaman yanda ya bayyana masu cikin hoton.. Wani ne ya kashesa sannan ya saka bindigar cikin hannunsa dan idan ba haka ba babu yanda za’ayi ya harbi kansa a wannan position d’in…

Tafe hannunsa mutumin ya shigayi yana furta “Impressive.. Bravo Officer MA Gamji..” Yai maganar yana mai tafe hannayensa lokaci guda yake duban Mu’azzam..

Assad ya kai dubansa ga hoton yana yanda mutumin ya rik’e bindigar sannan yakai dubansa ga Mu’azzam, ko shakka babu wannan rik’on bindigar saka masa akayi sannan ya tabbata bashi ya harbi kansa ba..

Jinina Kai Assad yai murmushi saman fuskarsa yake duban aminin nasa.. Lokaci guda ya k’araso gabansa kafin ya d’aga hannu yana sara masa alamun jinjina.

Officer Maleeka ma wani irin murmushi ne taji ya kufce mata cikeda jin dad’i dan har Ta fara tunanin idan basu samu komai out of this case ba watsi za’ayi da binciken and bazata samu lokacin da take so Ta samu dan Ta kasance da Mu’azzam ba.. Sabida son kasancewa taredashi ne yasa tayi yanda tayi akayi assigning nata to case d’in…

A hankali mutumin ya zare bindigar daga hannun Mu’azzam yana mai furta “Weldon Mu’azzam har na fara tunanin idan bamu samu komai ba anything can happen.. Za’a iya rufe case d’in…”

Sai sannan Mu’azzam ya dubesa ya sara masa kafin yace “Believe me Yusuf babu  wanda ya isa ya rufe case d’in nan until I get to the bottom of everything.. Is a promise, Alk’awari ne da na d’aukarwa mahaifiyata dake cikin tsananin jinya wacce batasan d’iyarta Ta mutu ba.. Wacce duk randa ta farka daga wannan jinya nata zata farka ne ta tadda babu d’iyarta.. Babu Ikram..” Ya k’arashe wane irin gumi na karyo masa tin daga cikin sumarsa har zuwa karan hancinsa da ya dace da kyakkyawan fuskarsa…

Lokaci guda yaci gaba da furta “Yanzu da duk muka fahimci abu guda nida ku.. I’m goin to make that imbecile talk..!” Daga haka cikin sauri ya juya ya fice daga cikin d’akin..

Assad yabi bayansa yana kiran sunansa inaa Ko zarafin tsayawa bai samu ba balle ya amsa sa..

Yana isowa ya bud’e k’ofan interrogation d’in ya shige ciki saidai yana shigewa ya maida k’ofar ya danna mata lock yanda Assad Bazai iya shigowa ba…

Girgiza kai kurum Assad yayi dan yasan waye abokin nasa idan ransa ya b’aci..

Wani mutumi ne zaune saman kujera nan cikin interrogation d’in, Mu’azzam ya d’ibi lokaci yana dubansa cikin tsananin tsimewa..

Murmushi ne saman fuskar mutumin, yana murmushin yana shafa hab’arsa, cikin muryarsa da yafi kama da ta ‘yantadda yake furta “Officer MA Gamji, you’re not going to get anything from me.. zaifi kyau idan ka sakeni nayi tafiyata dan idan ba haka ba zan iya shigar da k’ara an ajiyeni a police station babu dalili..”

Cikin takunsa irinta cikakkun mazaje da suka sha training suka k’oshi ya soma takowa, hannayensa dafe da belt d’in wandonsa.. Saida ya k’araso har gaban mutumin kafin ya zauna a kujera mai fuskantar mutumin.. Zoben dake hannunsa ya cire ya wainata saman table d’in da ya raba tsakaninsu da mutumin, saida yayi hakan kusan sau uku k’afarsa d’aya bisa d’aya kaman bazai ce komai ba, har lokacin idanunsa naga zobensa da yake faman wainata saman table..

Mutumin ya kuma murmusawa kafin yace “Mr Officer, if you think you’re goin to get something from me you’re quite mistaken..” Cak ya katse maganar nasa sakamakon ganin hoton da ya aje masa saman table d’in..

“Im gonna ask you for the last time.. Tell me everything you know about this guy..!” Mu’azzam ya k’arashe yana mai matso da fsukarsa dab kusan na mutumin yatsarsa manuniya na saman hoton yana nuna hoton da Ita….

K’uri mutumin yai yana dubansa kafin ya saki murmushi kad’an yace “You won’t get anything from me, Mr Officer..?”

Wani irin zabura Mu’azzam yayi saida yai fatali da table d’in da ya raba tsakaninsu da mutumin.. Ya finciko wuyan mutumin ya matse ya had’uda da garu yana mai ci gaba da sakin huci “I am not playing games with you.. Now tell me.. Ka fad’a mun mai ka Sani akanshi..? Wanene shi..?”

Mutumin da yaji matsa idanunsa sun firfito waje yana neman hanyar da zai shak’i iskan numfashi ya fitar da k’yar yake jinjina kai ma Mu’azzam alamun ya sakar masa wuya zai fad’i abinda ya Sani…

Jifa dashi Mu’azzam yai yana yarfe hannunsa kafin ya isa gabansa ya d’an duk’a kad’an “Tell me..” Ya fad’i idanunsa akan mutumin..

Da k’yar mutumin ya d’an iya mik’ewa ya zauna dirshan a k’asa kafin ya soma fad’in “Baida kowa.. D’an ta’adda ne.. Baida kowa a garin nan, sannan bansan daga Ina yake ba.. Amma nasan a nan yake running businesses d’insa..”

Cikin zak’ewa Mu’azzam yace “Ya akai kasan d’anta’adda ne…?”

“Sabida ni kad’ai yake zama yayi min firan da bai wuce mintoci….”

Ya jinjina kai kafin yace “What was his business..?”

Girgiza kai mutumin yai kafin yace “Komai ma business d’insa ne as far as wannan kasuwancin ta’addanci ne…Iyakacin abinda zan iya fad’a maka kenan..”

Mu’azzam ya kuma gyara tsugunonsa idanunsa nakan mutumin kaman mai tsoron kar yayi losing sight d’insa kafin yace “Baida kowa.? Baida tak’amammen aboki ko wani abu mai kama da haka.. Tell me..”

“As I  told you , mutumin nan ganinsa kawai muke yazo ya sai sigari yasha ya k’ara gaba.. Amma wata rana naji yana waya kaman da wacce zai aura ne..”

“Wacce zai aura..?” Mu’azzam ya tambaya cikin son jin yaji komai.

Mutumin ya jinjina kai yace “K’warai wacce zai aura.. Dik a wanann daban ni kad’ai yake zama yayi hira dani da bai wuce na tsawon minti uku zuwa biyar.. “

Tura masa kujera Mu’azzam yai yace “Tashi ka zauna sannan ka sanar dani firan taku..”

Saida mutumin ya d’an fuzar da huci kafin yace “Amma Rankaidad’e bazaka bari a ajiyeni a police station ba dan ka gani da idanunka shago na bana sayar da komai, bana sayar da tabar wiwi sannan bana sayar da k’waya.. Karan sigari kawai nake saidawa Rankaidad’e.. Dan Allah ka taimakeni kar a ajiye ni a nan.. Bana komai illegal I promise..”

“Kar ka damu idan muka tabbata baka running wani illegal business na maka alk’awari bazamu ajiye ka a nan ba.. Yanzu ka fad’a mun hiranku na k’arshe da wannan mutumin..”

Saida ya gyara zamansa kafin ya soma fad’in “A satin da ya gabata yazo k’ofan shago na, as usual ya sayi sigari na kyauta masa lighter.. Kaman ko yaushe bai shiga cikin mutanen dake zama a daban k’ofan shago na ba.. Ya koma gefe ya soma zuk’ar sigarinsa.. Ya gama shan sigarinsa yazo wajena karb’an canji dan dama sanda ya sayi sigarin ban basa canji ba dan babu canji, nace masa ya gama sha kafin a samu canji.. Toh tsayuwarsa yana jirana na had’o masa kan canji na basa yai daidai da fara ringing d’in wayarsa..Ya ciro wayar yana amsawa. Cikin maganganun nasa a waya na fahimci da wacce zai aura yake waya.”

Mu’azzam yace “Bakaji wani abu ba gameda budurwar tasa.. Maybe a ina take kokuma wani abu mai kama da haka..?”

“Inspector I told you I was only his smoking buddy.. How would I know all the details..!”

Murmushi Mu’azzam yai kafin yace “Do you really want us to play this game..? I can assure you I know exactly when to throw my card..” Ya k’arashe yana mai waina zobensa saman table. Lokaci guda yake ci gaba da furta “Nasan baka Sani ba, but I do know a lot of things about you.. I know about your criminal records.. Nasan abubuwan da kake aikatawa wanda zasu kaika jail ka shafe shekaru da Dama.. But If you cooperate with me, zanyi iya k’ok’arina a kotu to make sure anyi reducing sentences d’inka.. So ina shawartanka don’t let me lay my cards first.” Ya k’arashe yana tsaida zoben dake faman wainuwa saman table da yatsarsa guda…

Murmushi mutumin yayi yana mai jinjina kai dan yasan business na drugs da yakeyi zai iya kaisa gidan yari.. Yai k’uri wa Mu’azzam yana dubansa wanda babu alamun tsoro Ko d’ar a tattare dashi.. Kaman bazaice komai ba Sai kuma yace “I need protection..”

Mu’azzam yai masa k’uri yana dubansa kafin yace “So you do know something..?” Yai maganan yana jinjina kansa yana kuma tabbatarwa plan d’insa really works.. Gyara zamansa yai had’ida d’aura k’afa d’aya bisa d’aya still yana fuskantar mutumin yace  “I knew it.. I was right all along..”

K’uri mutumin yai masa gajeriyar murmushi saman fuskarsa “But you  need to guarantee my safety first, Inspector..”

Mu’azzam ya jinjina masa kai yana mai furta “We will give you protection here.. I promise.. Just tell me what you know..”

Ya jinjina kansa a hankali idanunsa akan Mu’azzam sann ya tura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya ciro k’aramar takarda a nannad’e.. Lokaci guda ya mik’a ma Mu’azzam yace “Wannan zai iya amsa maka duka tambayoyin ka.. Duk abinda kake so ka Sani gameda mutumin nan..”

Mu’azzam yasa hannu ya amshi takardan ya warware.. Address ne na wani gida a jiki..

Ya d’ago yana duban mutumin da alaman tambaya..

Jinjina masa kai mutumin yayi yace “Kaje wannan Address d’in zaka sami amsoshin da kake nema…”

Mik’awa tsaye Mu’azzam yayi yana juya address d’in wanda yake a garin SULEJA…

Bai kuma ce ma mutumin komai ba yasa kai ya fice kaman zai kifa da k’asa.. Mutumin na kiransa yana fad’in yaushe za’a sake shi ya tafi gida.. Inaa ko zarafin juyowa Muazzam baiba balle ya amsa Sa.. Yana fitowa ya tadda Assad yana jiransa.. Cikin sauri Assad ya take masa baya yana fad’in Ina zasuje..

Bai tsaya amsa Assad ba har saida suka k’araso yanda motocinsu Ke ajiye.. Ya dubi Assad yace “You drive..”

Assad yace “Destination.?”

Takardan dake hannunsa ya d’an warware ya nuna masa..

“Suleja..?” Assad ya maimaita a hankali kafin ya girgiza kai kad’an yana mai capke d’an makullin da Mu’azzam d’in ya jefo masa..

“Do we have a mission there Inspector.?” Cewar Assad dake k’ok’arin key wa Mota..

“Idan munje zaka gani..” Mu’azzam ya basa amsa yana mai kuma duban takardan dake hannunsa..

Maleeka da tin fitowarsu take hangensu, Ta nufo waje cikin sauri amma saidai bata cimmasu ba, cikeda takaici take ciza baki kafin Ta koma cikin building d’in..

**

SULEJA

Wata matace zaune tsakar gida tana tsintar wake, yara guda biyu maza zaune gefenta saman tabarma suna cin abinci.. D’aya bazai gaza shekaru 12 ba d’ayan kuma bazai gaza 9 ba.. Sai cin abincin suke hannu baka hannu k’warya alamun yunwa taci ta cinyesu…

“SADIYA..! SADIYA..!! Ke SADIYA..!!” Matar Ke fad’i daga nan yanda take zaune tana tsintar wake..

Ganin wacce ta kira d’in bata fito ba ya sanyata yin k’wafa tana mai gyara zamanta saman kujerar had’ida daidaita zaman parantin da waken Ke ciki saman cinyarta “Kar Allah Sa ki fito daga cikin d’akin nan.. Idan yunwa ta azalzaleki zaki fito.. Ke kanki farau ake saka aure a fasa..? Ai ke abinma ki gode ma Allah ne da yanzu kin je kin auri wanda ba’a san danginsa ba.. Wa yasani ma ko d’anta da ne Ko d’an fashi da makami ne, ko kuma ma Dan garkuwa ne da mutane.. Ki gode ma Allah baki da rabon shan wahala ne tinda gashi har shagulgulan bikunku aka fara d’aurin aure kad’ai ya rage aka nemesa aka rasa sa, Allah kad’ai yasan shid’in wane irin mutum ne dan ko danginsa bamu tab’a gani ba sai wannan Kawun nasa.. Da yanzu kin aure shi d’in Allah kad’ai yasan irin masifar da zai janyo miki, ke da gidanki saidai ki rayu ciki tamkar kina a GIDAN ARO ne..” Ta k’arashe tana bushe waken dake cikin parantin…

Tana busar waken take ci gaba da furta “Ni duk bama wannan ba uban bashin da mukaci ne na fitan biki ya tsaya min a wuya da yanda zamu kwashe da d’inbin mutanen dake binmu bashi… Oh Allah dai ya fiddamu..”

Bataji sallamar ba sai Muryar data jiyo tana furta “K’warai kuwa Uwani gwara ki nemo hanya tun wuri dan yau bani fita cikin gidan nan sai kin lale min kud’ad’e na.. Yo Ai ni bani nace kiyi bukin k’arya ba.. Harda cewa d’an gidan Babban k’usa a k’asar Amurka  ‘yarki zata aura.. Toh maza maza idan ma guduma ne ba k’usa ba a fiddo mun kud’ad’ena yanda suka shiga suka fita ehe..” Ta k’arashe tana wane irin jijjiga

Mata mai tsintar waken murmushi ta saki wanda hausawa Ke ce ma kafi kuka ciwo

“Tabawa kece tafe, k’araso k’izauna mana, ga wajen zama..”

“Ank’i a zauna d’in.. Nace bazaa zauna d’in ba.. Yo ni naga wajen zama ne a nan..”

“Haba Tabawa mu shiga daga ciki sai muyi maganar..”

“Bazan shiga ba..!” Tabawa Ta fad’i tana mai fatali da parantin waken da matar Ke tsincewa Ai ko sai cikin abincin da yaran ke mamuk’a…

Wane irin kuka k’aramin ya fashe yana birgima yana fad’in sai an biyasa abincinsa da aka b’ata…

Tagumi Ta rapka tana duban yaran yanda suke kukan basu k’oshi ba.

“Oh ni Uwani naga takaina, yanzu ta Ina zan samo kud’ad’en nan..”

“Umma bamu k’oshi ba..” K’aramin yaron ya fad’i yana mutsuke ragowar hawayen dake idanunsa..

Janyo yaran tayi jikinta tana lallashi tana fad’in suyi hak’uri yanzu zata girka masu ragowar waken data tsince..

“Umma nidai ba zanci wake ba, ni abinci mai dad’i da Aunty Sadiya take kawo mana zanci.. Kuma ai Umma kince idan tayi aure Gidanta zamu koma dukanmu.. Kince gidan Babba ne kuma zai d’auke mu gaba d’aya.. Abba kawai zamu bari a nan gidan..” Ya k’arashe daidai sanda wani magidancin mutumi ya fito daga wata d’aki dake can gefe, goge bakinsa yake da karar aswaki ya isa ya d’auki buta ya d’ebi ruwa a famfo dake filin tsakar gidan ba tareda yaceda matar komai ba.. Ta bisa da idanu tana jira taga ko zai mata magana amma shiru baice komai ba, kodashike tasan za’a rina haka.. Bazai ce komi d’in ba dan tinda aka soma hidiman bikin baya saka kansa ciki dan Dama ba’a saka shi ba dukda duwa cewa Sadiya d’iyarsa ce ta cikinsa amma baida ta cewa a gidan sai abinda Sadiya da mahaifiyarta Uwani sukace akeyi.. Uwani irin matan nan ne masu bala’in son abin duniya wanda kwad’ayi ya rufe masu idanu basa gane daidai daga abinda yake ba daidai ba koda kuwa gaskiyar Ta bayyana masu k’arara..

Tun aurensa da Uwani haka nan take, da yana dashi da baidashi sai ta tursasa masa ya kawo mata, koda suka haifi yara ma Uwani bata fasa halinta na kwad’ayi da tsaban son abin duniya had’ida hangen na sama da ita ba.. D’iyarsu Ta fari itace Sadiya Sai Ashiru da Habib d’an autansu.. Sadiya kyakkyawa ce ta gani a fad’a dan tun tana k’arama ake mata lak’abi da Sady pretty a layinsu.. Tinda ta soma zama budurwa Uwani mahafiyarta da suke kira da Umma ta maida ita hanyar samun kud’inta.. Tuni Umma ta hure ma Sadiya kunne cewa ta dinga karb’o masu kud’i hannun samaruka, hakan yasa Sadiya bata raina samari hardai zata samu ta tatsesa ta rariki rabonta.. Kowa a unguwar yayi shaida ma Sady pretty da Ummarta indai akan tara samari barkatai ne da amsan abin hannunsu.. Babu yanda Malam Ibrahim mahaifin Sadiya da suke kirada Abba baiyi ba wajen ganin ya karkatar da Uwani da kuma mummunan d’abi’ar data d’aura d’iyarsu amma abu yaci tura.. Tsaf Uwani take tsefe masa ruwan bala’i tace bazata zauna tanaji tana gani d’iyarta ta k’are a auren matsiyaci ba kaman yanda ita ta k’are.. A haka har Sadiya ta sami gurbin karatu a Jami’ar babban birnin Tarayya.. Idanun Sadiya sun kuma bud’ewa yanda Ta soma gogayya da manyan ‘yanmata masu ji da kansu da kuma yaran masu hannu da shuni.. Tuni Sadiya Ta kumaji Lallai batada miji sai mai Kud’i ko d’an mai kud’i musamman ganin yanda daga shigarta samaruka sukai mata chaa sabida kyaun halitta da Allah yayi mata.. Idan tayi wanka ta shiga makaranta sai ka rantse d’iyar wani hamshak’i ne, daga nan duk wasu situru da abubuwan more rayuwa da take amfani dasu maza Ke bata su.. Daidai da registration da kud’in samari tayi.. Hoto kuwa idan zatayi posting a social media saidai ta tafi can layin bayansu gidan su wata k’awarta Sabeera a nan take hoto dashike mahaifin Sabeera yanada d’an rufin asiri dan babban d’an canji ne cikin Abuja amma gidansa na nan Suleja.. Gida mai d’an karan kyau ya cancad’a.. Kullum Sady pretty tana gidansu Sabeera dan dama tare suka sami gurbin karatu a nan Jami’ar Abuja, course d’aya suke tare suke tafiya tare suke dawowa, a motar gidansu Sabeera ake kaisu a d’auko su wasu sunyi zaton ma ‘yan gida d’aya ne wasu kuma sukanyi zaton Sady ce d’iyar mai Kud’i Sabeera ce ‘yar k’wak’warta.. Bugu da k’ari Sabeera irin ‘yanmatan nan ne da abun hannun iyayensu bai rufe masu ido ba, Sam abun duniya bai d’ad’areta ba kaman k’awarta Sady pretty.. Sady sam bata bari k’awaye suzo gidansu saidai Su had’e a gidansu Sabeera.. A haka Sabeera Ta zamto Aminiyar Sady, sau tari Sabeera takanyi nasiha ma Sady kan irin rayuwar data d’aukar ma kanta amma ko a jikinta takan ce lokacinta gwara taci duniyarta da tsinke.. Bazata bari kyaun da Allah yayi mata ya zamto a wofi ba tinda basu da kud’i zata iya amfani da kyaun da Allah ya bata ta sama masu rayuwa mai inganci itada iyayenta..

Duk wasu kayan more rayuwa da Sady zata kawo gidan Abba baya amfani dasu bai kuma fasa masu nasiha ba musamman ga Uwani mahaifiyar Sadiya.. Ita kam Sadiya ya mata nasihar ya mata fad’an har duka yasha mata amma babu abinda ya canza dan Tuni mahaifiyarta ta hure mata kunne.. K’arshe Umma ce masa tai idan dai bazai bar mata d’iya ta sakata ta wala ba toh wllhi zata kwashe yaran ta tafi taredasu kuma bazai sake ganinsu ba Eritrea zasu koma da shike dama Mahaifiyar Sady ‘yar asalin k’asar Eritrea ce, haka nan take  kyakkyawa kaman mutanen k’asar Eritrea masu kusanci da Ethiopia dan a wajenta Sady ta samo tsantsan kyaun halitta da Allah yayi mata, saidai Ita Sady har ta d’ara mahaifiyar tata.

Sosai Malam Ibrahim ya  samu matsala da Umma akan Barin Sadiya da tai sakaka tana Yawo dan har Dattijan unguwa sun gaji sun soma masa magana, yayi dik yanda zaiyi ya hana hakan abu yaci tura..K’arshe dai shine yace saidai Sady ta fiddo da miji a mata aure kafin ta k’arasa shekararta ta farko a jami’a.. Ana haka ta had’u da wani saurayi mai suna Sagir a Yanargizo.. Nan da nan Sagir ya samu gurbi mai girma a zuciyar Sady dan sosai yake mata b’arin kud’i kuma yace da aure yake nemanta.. Sady ta gama sakankacewa ta yarda ta amince Sagir masoyinta ne Tuni tace masa ya turo ayi maganar aurensu dan Dama Abbanta ya saka mata takunkumi.. Nan Sagir yake sanar da ita cewa iyayensa US suke  basa zama a Nigeria.. Shima abinda ya kawosa zuwa yayi dan ya nemi mata ‘yar k’asar Nigeria ya aura ya d’auketa su koma can US suci gaba da zama.. Haba nan fah Sady da Umma suka kuma susucewa akan Sagir.. Ya turo masu wani mutumi guda d’aya a matsayin Uncle d’insa akai maganar aure.. Sagir yace kar suji komai shi zaiyi komai na aure, nan suka kuma jin dad’i.. Nan da nan zance ya d’auka Sady zata auri d’an gidan k’usa bama cikin Abuja suke zama ba cen k’asar Amurka suke da zama shida iyayensa neman macen aure ya dawo dashi gida Nigeria, iyayensa zasu Zo da zaran ya samu mata an soma shagulgulan biki..

Hakan yasa Uwani cin alwashin yin Bikin kece raini ga Sadiyarta, Ta shiga ciwo bashi dan tayi Bikin kece raini, Bikin yaran masu hannu da shuni Bikin nunuwa a shafukan sada zumunta na yanar gizo..

Ana biki kwatsam aka nemi ango aka rasa har rana mai kaman Ta yau basu san abinda ya faru da ango ba.. Ga wayar salulansa ta dena shiga.. Tun Sady na damuwa har dai Umma tace ta daina damuwa k’ila America ya koma dan ya taho da iyayensa tinda an soma shagulgulan biki.. Sabeera ma cewa tayi k’ila US d’in ya tafi kuma ba lallai wayarsa Ta shiga ba.. Hankalin Sady sosai ya tashi, taci kuka tana fad’in Maiyasa bazai kirata ba da zaran ya saka layinsa na k’asar Amurka, Sabeera tace k’ila surprise yake son mata.. Abu kaman wasa babu Sagir babu dalilinsa har zuwa ranan d’aurin aure da aka rasa ango aka rasa mai karb’awa ango aure.. Toh daga nan ne fah Umma da Sadiya suka fara shakku da yinin wane irin mutumi suka jajib’o…

Umma Ta nusa tana duban Abba da har ya ida alwalansa yana d’auraye slippers d’insa da sauran ruwan butar har lokacin karan goge bakinsa na cikin bakinsa..

“Abban Sadiya yanzu bazakace komai ba.. Kana jin yanda ake shigo gidan nan sahu sahu ana d’aga min hankali sai na fidda kud’ad’en dana ciwo bashi..”

Sai sann ya d’ago ya dubeta “Toh ki biyasu kud’insu mana sai su daina miki sintiri a gida..” Ya fad’i yana k’ok’arin mik’ewa.

Ta k’walalo idanu waje “Ina zan iya kashin  tulin kud’ad’en nan Abban Sadiya..?”

“Aw dama Kinsan Bakida hanyar samu Kika ciwosu.. Kan wane dalili.? Dan ki birge mutane..? Ai sai ki jira mak’aryacin da ya yaudareku d’in yazo ya biya miki bashin dan nikam Kinsan Ko kud’in haya na shekara da nake biya idan an had’a bazasu isa ba..”

Umma ta dafe fuskarta da hannu tana salallami tana furta “Oh ni Uwani na shiga uku, Sadiya kin d’ebo mana ruwan dafa kanmu..”

Tana jiyo muryar mijinta na kiran Ashiru da Habib suzo su shige masallaci…

Umma ta nufi d’aki yanda Sadiya Ke kwance tana aikin abu guda..

“Ki tashi ki daina wannan koke koken mu soma tunanin yanda zamu samo mafita.” Umma Ta fad’i tana mai zama gefen katifar da Sadiya Ke duk’unk’une tana zuban hawaye, sautin kukan ma ya daina fita.. Idanunta sunyi luhu luhu haka nan ma fuskarta tayi jajazir, tsinin hancinta shima yayi ja har kaman ya k’ara tsawo.. Kallo guda zakai ma Sadiya ka fahimci cewa tana cikin tsananin tashin hankali wanda tinda tazo duniya bata tab’a shiga irinsa ba.

“Umma.. Sagir..” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka, sai kuma ta kasa ci gaba da magana sakamakon kukan da ya dad’a taso mata

Nan ta kifa kanta tana mai isarta yayinda Umman tai tagumi Ta zuba mata Ta mujiya..

**

Suna tafe saman kwalta Assad naci gaba da jefo masa tambayoyi wanda akasari ba samun amsarsu yake ba shidai kawai damuwarsa su isa wannan location d’in da Danger ya basa..

Wayar Mu’azzam d’in Ta soma ringing.. Yai saurin ciro wayar a aljihu yana duban mai kiran nasa, a d’an kasalce ya k’arawa a kunnensa dan yasan mai kiran nasa matsala zai kunno masa.. Shiru yai ga dukkan alamu yana sauraren d’aya b’angaren ne..

A hankali ya lumshe idanunsa yace “Tell me your location..?” Alright alright I’ll be on my way.. Don’t call a cab just wait for me there..” D’if ya kashe wayar yana mai fuzar da fuci..

“Pull the car over Assad.”

Assad da kacaukam hankalinsa kega kwalta d’an kaikaitowa yai yana dubansa “Wait what..?”

“Stop the car, zan sauk’a a nan.. I need to go back..”

“You mean to the station..?” Assad ya kuma tambaya yana k’ok’arin parking motar gefen kwalta..

Yana k’ok’arin ficewa daga motar yake fad’in “No..MUSADDIQ ne… Daga yanda yake mun magana nasan ba cikin hayyacinsa yake ba..”

“Musaddiq kuma..? Na kwana biyu  banji kana tare tare da gagaransa ba.. What really happened..?”

D’an tab’e baki Mu’azzam yai kafin yace “How would I know.. Abunda na sani kawai shine ya kasa karb’an k’addarar cewa Ikram ta tafi kuma bazata tab’a dawowa ba.. I’m afraid rashin Ikram ka iya jefa Musaddiq halinda ya riga ya bari a baya..” Ya k’arashe damuwa saman fuskarsa..

Cikeda tausayawa Assad yake duban abokin nasa, yasan d’awainiya ne da dama zasu kuma hawa kan Mu’azzam d’in…

Daidai lokacinda cab ya tsaya.. Mu’azzam ya shige yana fad’in “Kaje kayi sauri ka isa location d’in zamuyi waya..”

Baki sake Assad Ke dubansa yana kuma juya ‘yar k’aramar Doguwar takardan mai d’aukeda address d’inmu.. D’an girgiza kai kurum yai kafin ya shige ya d’auki hanya…

**

-Star lake street, Maitama_

Tsaye tayi saman kan matar dake kwance saman gado wacce idanunta Ke bud’e tarau saidai gefen jikinta guda tamkar a shanye yake, bakinta dake karkace miyau na fitowa.. A tak’aice dai kallo guda zakai mata ka fahimci matar tana cikin tsananin jinya ne…

A hankali matar dake tsaye kanta ta duk’a tana mai ci gaba da k’are mata kallo, lokaci guda ta saki murmushi tana mai ciro tissue paper dake ake gefe cikin kwali ta shiga goge mata miyau d’in dake fitowa daga cikin bakinta. Lokaci guda take furta “Na shafe tsawon shekaru ina jinyar kishiya.. Shin zan samu riba nan gaba..? Shin hak’ata zata cimma ruwa.. They say everything in life has a price, Nuratu.. Could this be my punishment..?” Tai fasali tana mai duban matar wacce ta kirata da Nuratu kafin ta saki murmushi tace “No wait.. How could this be my punishment bayan ni ban aikata komai ba.. Kece kika aikata mun komai Nuratu.. Kece kika d’auke komai daga gareni.. A baya ked’in matar d’an uwan mijina wacce na miki lak’abi da kishiyar Dinga sannan Hausawa sunce ita d’in tafi zafi..  Kin kasance wacce tafi soyuwa cikin dangi musamman wajen Inne Mahaifiyar mazajenmu..” Ta k’arashe maganar tana mai disposing used tissue paper d’in kafin ta d’auko wani tana mai kuma goge wanda yake gangarowa, lokaci guda take ci gaba da furta “Nayi zaton idan mijinki ya mutu zaki fita daga rayuwarmu.. Zaki koma yanda kika fito.. But then I was wrong.. Ashe mutuwar mijinki ba komai zai k’ara mana ba face kusanci da juna..” Kukanta ya k’aru sanda taci gaba da fad’in “Kin aure mun miji Nuratu.. Kin aure mun miji bayan naki mijin ya mutu.. Kin zamto shalele mafi soyuwa a wajen mijina.. How could you.. Ta yaya zaki aikata mun haka..? Ta yaya Nuratu..” Tasa hannu tana goge hawayen da ya wanke mata fuska kafin taci gaba da fad’in “This is what you deserve.. Keda mijina bazaku tab’a kasancewa ba balle har Kuji dad’in yin rayuwar aure tare.. Bazan tab’a bari hakan ta kasance ba Nuratu.. Ked’in bazaki tab’a warkewa daga wannan ciwo ba.. Kar ki mance da furucina… Dama na gaya miki gidan mijina tamkar GIDAN ARO yake a wajenki… Babu Ke babu sukuni balle samun natsuwa a cikin gidan mijina.. Na fad’a miki aron gidan na baki na d’an wani lokaci.. Zaki fita daga gidan domin kuwa akwai babban shiri da nake miki.. Zaki fice daga wannan gidan  kaman yanda na miki alk’awarin cewa shid’in GIDAN ARO ne a wajenki..” Tana kaiwa nan ta kece da wata irin dariya hawaye na fito mata.. Saida har dariyar nata ya koma tamkar kuka kafin ta kifa kanta gefen majinyaciyar tana kuma sakin kuka mai ban tausayi.

K’amshin turaren mijinsu da yaima k’ofofin hancinta sallama ya tabbatar mata cewa shid’in ne ya shigo.. Nan fah ta dad’a narkewa tana sakin kuka mai ban tausayi..

DOWNLOAD COMPLETE BELOW 

GIDAN ARO COMPLT

You cannot copy content of this page