DA MA NI CE CHAPTER 27 BY JAMILA UMAR TANKO

Shamaki gami da tausayin Malaika, ga haushin jin danyen hukunci da Malaika ta yanke na zuwa wajenta.

«Ta zo wajena Abuja ta zauna akan me?

Meye hadinna da ita?” Nasrin ta fada a cikin zuciyarta.

Nasrin ta dakatar da ita, ta ce, “in takaice miki mijinki yana zargina da kashe muku aure gani yake ni nake zuga ki saboda ina turo miki katin waya, dan haka Malaika kada ki sake nemana a waya balle kice za ki zo gidanmu.Ki je iyayenki da iyayansa su yi muku sulhu ku* zauna lafiya, babu in da zaki je ki zauna kiyi daraja wanda ya wuce gidan mijinki, ki rungumi ‘ya’yanki dan babu mai rike miki su ki ga daidai idan bake da kanki ba. Dan Allah Malaika ki cire ni daga cikin mutanen da kika taba sani a rayuwa, matsalar gidanki ta dame ni ta tsaye min a rai, gashi ta jawo min zargi da wulakanci daga Shamaki.”Nasrin ta tsiyayo da hawaye ta katse wayar, tana katsewa ta yi sauri ta goge lambar Malaika daga cikin wayarta. Ta kashe wayar

gaba daya ma dan taga Malaika tana ta sake kiranta.

Ta rubutawa Dr.Jalo sako ta ce, “daga

karshe wannan auren da muke kokarin ceto rayuwarsa Allah ya yi masa cikawa a yau da yamma.”

Ta rufe computer ta, ta kwanta cikin gagarumin bacin rai.

RANAR TALATA…ABUJA

Dr. Jalo da Nasrin sun dade suna

hira a facebook kasancewar ta ga

wadansu sakonninda abokansa su na

tura masa suna yi masasannu da jiki. Ta

tabbatar bashi da lafiya, dan haka ta damu tana

ta tura masa sakonninfatan samun lafya cikin

gaggawa.

Ya yi mata godiya saboda kulawarta

ya nuna ya ji dadi. Amma ta matsa ya fada mata abinda ya ke damunsa, sai bai ce mata

komai ba ya ma canja hirar. Gudun kada ta bata masa rai sai ta bar zancen, dan taga alamar

baya son yawan tambaya.

Daga nan ta shaida masa tana yawan

zazzabi da ciwon kai kwanan nan. Ta tambaye

shi wanne irin magani ya kamata ta sha dan ta warke?

Ya tina bai ba ta amsa ba, daga baya yace ta je asibiti mana. Ta ce tana so ta je amma aiki ke hanata

zuwa, kasancewar

zazzabin dare ne kafin safe ya sauka sai ta manta ta fita ofis.

Sai yau ya tabbatar mata shi ba likitan asibiti ba ne likitan karatu ne kawai. Nasrin ta yi mamaki matuka dan ya yi mata kama da cikakken likita mai farde mutum ya dinke. Sai ta ji ta rage mamakin yadda ya zama kwararren marubuci, rubutu masu ma’ana ashe likitan karatu ne.

Ya shaida mata ya karanci English Literature? yana koyarwa a jami’ar Lagos. Nasrin ta ji dadi kwarai da ta fara sanin wani abu nasa.

Ta yi mamaki da ta ji yace ta bashi taribin rayuwarta yana so ya sani.Ta karanta sakon nan daya tura, ya fi sau biyar dan ta tabbatar haka din yake mufi dan kada ta fara zuba alhali bai ce ba. Ta gasgata haka yake nufi, sai ta gyara zama. Ta rubuta ta tura masa ta ce idan ba zai damu ba zata Kira shi suyi magana a waya, zai fi dadi idan suka yi magana baki da baki, ta shaida masa kada ya damu bata biyan kudin katin waya. Nan da nan ya bata izinin, zata iya kira ba damuwa. Farin ciki ya

rufe ta kafin ta kira shi sai da ta kira Dinah ta bata labario yadda suka yi da Dr. Jalo, ta tabbatar mata yanzu ma zata .kira shi su yi labari.

Dinah ta yi mamaki ta kuma ta taya ta murna ta tabbatar mata ita ma ba zata yi bacci ba har sai sun gama wayar, tana jiran ta kira ta fada mata yadda suka yi,Nasrin ta yi mata alkawari zata kira ta fada mata komai.

Dinah ta yi mata alkawarin zata dauki carbi mai dubu ta taya ta da addu’a Allah Ya sa atattauna abubuwa masu alkhairi.

Maganar Dina ta bawa Nasrin dariya kwarai, dan haka ta yi ta dariya ta kashe waya. ca Ta fada abayyane. “Dina shakiyiyar yarinya ce wallabi.”

Nasrin ta tashi ta bude firij ta dauko lemon kwali da kofi ta dawo kan gado ta zauna ta nutsu sannan ta kira lambar Jalo, bayan da ta karanto kula’uzai ta tottofa a kowacce kusurwa ta dakin, ta na neman Allah ya tsare ta da bata masa rai ko ta fadamasa abinda zai sa ya janye daga gare ta.

Hmmm

You cannot copy content of this page