AKWAI KADDARA CHAPTER 1 BY PHATYBB HAUSA NOVEL

Safiyar Ranar Litinin Karfe takwas dai-dai da agogon Nijeriya. Ranace data kasance ranar aiki ga ko wani ma’aikaci, dalibai ya zame musu ranar makaranta.

Hayaniyane ke tashi cikin gidan Malam Yusuf Mai Kanti, in da sabo sun riga da sun saba, gidane cike da yara manyan Yaya mata da samari, kanana da kuma masu tasowa, wasu na shirin tafiya makaranta yayin da was suke shirin tafiya waien sana’ar su was kuma sun kasance tasu sana’ar a

gida suke yinta.

Mata uku ne cikin gidan, matar farko lya Ramma ta biyunta Babar Yara sai ta uku Mamar Murshidah, matane ga Mallam Yusuf Mai Kanti wanda kowa gidan rabi shi ya rike kansa da Ya’Yansa, uba ga yaya goma sha shida inda Allah ya azurasa da mata goma maza shida, yakan kokarta ko wani karshen wata ya jinginar musu rabin shinkafar tsinta dasu gero, dawa, masara daga nan kuma sai wani watan in ko babu sai watan gaba.

lya Ramma takan dama koko da wainar hatsi kullum safe na saidawa dan taimakawa kanta da yaranta, tana da yaya shida maza uku mata uku, Babbar Yara nata sana’ ar shine suyar awara safe da yamma Allah ya azurtata da yara shida mata hudu maza biyu, sai Mamar Murshida yaranta mata uku sana’ar wanke wanke da shara take gidan Alhaji Mudassir Timber da kitso ma mutane a gida.

Yaya Goma sha shidan sune Muftahu, Kabeeru, Rufaida, Fauziyya, Amal, Ameer, Yaya ga lya Ramma.

Yunus, Batul, Aneesa, Khairiyyah, Musaddik, Jamila sune

Yayan Babar Yara.

Murshida, Khausar, Laila Yaya ga Amarya mata ga Kanin Mallam Yusuf Mai Kanti (Hudu), bayan rasuwarsa da sati biyu ta haife Murshida, bayan ta gama wanka da iyayenta

da lyayen Mallam Yusuf Mai kanti suka hada aurensu, kuma suna zaune lafiya sai abinda ba’a rasa ba.

Gidane da ba mai ragawa wani ko mai girmanka ko

Kankanta kowa gashin kansa yake ci, dai-dai gwargwa Mallam Yusuf Mai Kanta na bawa Vayansa ilimin addini dana boko, Muftahu, Kabeeru, Yunus suna degree inda su suka saka kansu da Var sana’ar hannunsu, Rufaida, Fauziyya, Batul, Murshida shekaran nan suka gama Diploma inda suke jiran sakamako, Laila, Aneesa, Khairiyyah suna aji uku na sakandare sai Ameeer, Musaddik, Khausar na aji hudu a firamare.

“Murshida!!!

Kiran mahaifiyarta ya farka da ita karo na uku, farkawar tayi tana mutsetseke idanunta kafin ta amsa kamar bata so.

“Yanzu ke shikenan kuma daga gama makarantar sai baccin asara haka ki kaga yan uwanki nayi? Ko wacce na Kokarin taimakawa mahaifiyarta, amma ni kin barni kullum ina hanyar zuwa gidan aiki, in na dawo ga masu kitso suna

¡irana.”

“To Ni Mama mai zan miki, dame zan taya ki, kinga Ni ba kitso na iya ba, wancan kuma aikin ni gaskiya…” Fadin Murshida na bata fuska.

“Gaskiya mai..?”

Mahaifiyarta ta are numfashinta kafin taci gaba da cewa

“Kina bani mamaki Murshi, kina sassauta wa wannan jin kan naki, ke ba yar kowa ba amma kin dau jin kai kin daurawa kanki.”

“Yi hakuri Mama ba hakana bane, mai zan miki yanzu.”

Fadin Murshida tare da saukowa daga kan gadon Mamarta.

Murmushi tayi tana kallon Yarinyartan kafin tace.

“Ki kamamin aikin can kafin jarabawar ku ta fito musan abin yi, dukka mahaifinku dakyar ya yarda kucii gaba da karatun, Ni kuma sai inji da masu zuwa kitso kinga zamu kara samun wani abun.”

Bata fuska Murshida tayi tana cewa “Mama.’

“Za kije ko baza ki ba.”

Fadin mamar na mayar da murmushi ta zuwa bacin rai.

“Zanie.” Ta fada tana turo baki.

“Yawwa Yar albarka.”

Ba tace komai ba tayi hanyar fita a dakin, Mama murmushi tayi a zuciyarsa tana cewa ‘Allah ka shirya min Murshi.’ Fita Murshida waje taga kowa na harkar gabanshi a gidan kamar yanda aka saba, yara sun tafi makaranta sai wanda basa zuwa sune yan matan da suka gama.

Kwaskwarima tavi saboda yanayi na sanyi da ake zubawa, cewar ta ba zata iya wanka da ruwan sanyi ba, ga ba Mamarta bace da girki balle ta daura ruwa ko da a gawayine, duk wacce bata girki bata zuwa wajen murhu daga ita har yayanta.

Tana gamawa ta shige daki tayi shafe shafen ta in kaii yanda kamshi na tashi, kaga fuskanta kayi zaton tayi awa biyu tana wanka, bayan ta gama ta jawo kwanon Silva data gani a dakin da alama kannentane suka rage, kosaine da awara da dan yawa, ci tayi ta koshi kafin tana mahaifiyarta sallama ta fita ta kama hanyar gidan Alhaji Mudassir Timber.

Tana isa kofar gidan taja ta tsaya, Kwankwasa kofar tayi ta tsaya kusan mintina uku ba’a zo an bude mata ba, bugar kofar tayi iya karfinta wanda shi ya fargar da mai gadin gidan ya taso cikin sauri ya bude mata, da kallo ta bishi tana cewa.

“Mutanen gidan na nan?”

“Bismillah shigo suna ciki.”

Fadin Mai gadin na kallonta da karfi halinta, ba sallama bare gaisuwa.

Gefen shi ta raba ta wuce tana nufin kofar data hango a zatonta nanne kofar falon, kwankwasawa tayi shiru ba’a zo an bude ba ya sata juyawa tana kallon mai gadin alamar ya zata yi? ganin kallon da take mishi ya sashi karasowa gurinta ya danna door bell na falon yana barin gurin, da barinsa da buder bai fi minti biyar ba aka bude falon, matashiyar budurwace wacce Murshida zata girme mata da shekaru biyu ta bude, da kyakkyawar murmushi a saman fuskarta.

Ganin hakan yasa Murshida sakin nata fuskan.

“Bismillankii. “

Fadin yarinyar, tana bata hanya, bayan Murshida ta shiga yarinyar ta rufo kofar tana juyawa ga Murshida.

“Ina kwana.”

Ta fada mata wanda yasa Murshida jin wani iri tsammaninta duk masu kudi girman kai ne gareshi amma yarinyar nan ta bata mamaki, hakan yasa ta kwakulo murmushi tana fadin.

“Ah lafiya lau, dama Mamana ne zan kama mata aikin kafin zuwan wani lokaci.”

“Laah kece Murshi kenan.”

Fadin yarinyar na matsowa kusa da ita.

“Eh nice.” Murshida ta fada da nata murmushin saman fuskarta.

“Bari in Kira Aunty Ani nasan ta farka war haka tazo taga

Murshin Mamar Murshi.”

Murmushi Murshida tayi tana mamakin kenan har sunanta sun sani.

Tana tsaye inda take har ta sauko tare da kyakkyawar Mace mai kamala da ganinta za tayi dattaku da nutsuwa, murmushine kwance saman fuskarta, gain sun iso kusa da ita yasa Murshida dan rissinawa tana fadin.

“Ina kwana Hajiya.”

Murmushi Aunty Ani ta fadada tare da amsa.

“Lafiya kalau, Murshida ce yau a gidanmu?”

“Eh Hajiya Mama ce tace in kama mata aikin kafin wani lokaci.”

“Ba komai wallahi amma nafi so ki kirani Aunty Ani kamar yanda sauran yaran ke kirana zan fi son hakan.”

Kara sunkuyar da kanta Murshida tayi tana mamakin karamci na matar.

“Shikenan Haji.. au Aunty”

•Dariya dukkansu su kayi kafin tasa yarinyar ta nuna mata aikinta, sharane da goge goge sai wanke wanke, akwai mai dafa abinci, zata fara yi yanzu, aikinta ta tayi inda ta fara da sharan babban falon kasa dana saman tayi mopping tayi goge goge kafin ta shiga kitchen ta wanke kwanuka da akayi amfani dashi na girka da abincin karin safe.

Sai wajajen sha daya ta gama ta fito babban falon lokacin duk iyalan suna zaune, kallon daya ta musu ta sunkuyar da kanta tana Karasawa wajensu, mata biyune cikin gidan kenan kuma da alama suna zaman lafiya, bayan ta karaso ta zauna gefe tana fadin.

“Aunty na gama.”

“Murshida.”

Cewar dayar matar da suke zaune da Aunty Ani, idanuwanta ta dago ta kalli matar tare da sunkuyarwa dan yanda ta mata kwarjini, murmushi tayi tare da amsa tana gaisheta.

“Na’am Hajiya ina kwana.”

“Murshidan mamar Murshi.” Fadin Hajiya Maryam.

Sunan dariya yake bata hakan yasa ta murmusa har hakwaranta suna bayyana.

“Murshi duk yanda kika so ba laifi zakina wuni ko zaki zuwa safe da yamma.” Cewar Aunty Ani.

Kan Murshida kasa tace “Aunty zan so ina zuwa safe da yamma, in kuma bani da abin yi za ina wunin wani lokaci.”

“Ba komai Murshi, ki gaida Mamanki.”

“Za taji inshaAllah.” Cewar Murshida na kokarin tashi, bayan ta musu sallama ta nufi hanyar fita, sallamar da a akayi a wajen data bari shi ya sata kokarin juyawa, ko mai ya hanata ta fasa taci gaba da tafiyarta har ta fita a falon.

Bayanta kawai ya gani ya zauna kusa da Hajiyarsa, idansa ya lumshe kwana uku bacci ya kauracewa idanunsa, tin ranar da Mahaifinsa ya mallaka masa abubuwa mafitsada a garesa tambayoyi suka cika kwakwalwarsa ya rasa mai amsa masa, wa zai tunkara da dimbin tambayoyinsa? Wa zai bashi gamshasshiyar amsa?.

“BAGUS.”

Fadin Hajiya na kallon yaronta ta kula kwana biyu kwata kwata baya da walwala, lumshashshun idanuwanta ya bude can kasa ya amsa.

“Meke damunka yarona, baka da lafiyane.”

Girgiza kansa yay yana tashi, alamar ba komai.

Murshida tafe take tana mamakin mutumcin mutanen gidan lalle ba’a shaidan mutum, tsammaninta duk gidan mai kudi za’a samesu da girman kai da ji da kai amma wadannan sun bata mamaki, da tunane tunane har ta isa gidan, tin daga kofar gidan kana jin hayaniyar cikin gidan dan ma yara sun tafi makaranta, da sallama ta shiga ciki ciki, wanda su kaji sun amsa wanda basu ji ba suka share, Mamarta na zauna a dan barendansu tana ma wata kitso, kusa da ita ta zauna tana cewa.

“Wash Mama na dawo.”

“Raguwa kawai tafiyarne ko aikinne ya gajiyar dake.”

Mamar ta fada tana kallon Yarinyartan.

“Dukka Mama.”

“Kwadayi dai…” Fadin Fauziyya ga Mamarta da suke zaune a barendansu.

Zumbur Murshida ta tashi ta nufi gurinsu dan maganar tamkar a gabanta tayi, bata tsaya ko ina ma sai kan

Fauziyya kyam.

“Ki kace me?”

Fadin Murshida na kankantar da idanuwanta.

“Mai nace, Ni kinji nace wani abu tin shigowar ki, ke ko na fada akwai abinda za kiyi.”

“Ke ta fada me za kiyi, ba kwadayin bane ya kai ki aikin gidan Alhaji Mudassir Timber.” Cewar lya Ramma mahaifiya ga Fauziyya.

“iya! lya da Yarki nake ba ke ba, ina ganin mutunci ki.”

Murshida ta fada ta nunata fada yatsa.

“Mahaifiyar tawa Murshida.” Fauziyya ta fada tana tashi cike da masifa.

“Ni nace ta tsoma tsamin bakinta, ke kuma Fauziyya..:

Marin da ya sauka saman fuskarta shi ya hanata karasa

maganar ta, Yaya Muftahune tsaye a gabansu, zai kai mata wani ta kwace, cike da masifar ya fara magana.

“Ke Murshida har wuyanki yayi kaurin zagin mahaifiyarmu? tsabar fitsara, zany maganinki, Bari Baba ya dawo.”

Haka yayi ta bambaminsa ya fita a gidan, yana fita ta karasa kusa da Fauziyya ta kwasheta da mari.

“Marin da Yayanki yamin, ki sani ba’a tabani na bari sanin kankine.”

Fauziyya zata rama Murshida ta riko hannunta ta kara kai mata wani.

“Na zagina da ki kayi na farko.”

Tana fadin haka ta yarfe da hannunwanta tana barin gurin, daki ta shige sai a lokacin hawaye ya zubo mata, sosai marin Yaya Muftahu ya shigeta.

A waje ko Fauziyya kuka take dirgaza cewa take bazata yarda ba yaza ayi yarinyar data girme mata da shekara guda tazo ta daketa, Mamarta sai lallashinta take cewa bari

Babansu ya dawo.

Mahaifiyar Murshida tana zaune inda take tana kitsonta tun farawar abun ba tace komai ba, inda sabo sun saba da halin gidansu.

You cannot copy content of this page