KAI KA FI CHANCHANTA BOOK1

KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 39 BY JAMILA UMAR TANKO

ta kula da ci da shan Sajida da kula da gyaran dakunanta da wankin bandakuna. Kai hatta undies dinda Bakura ya ce Grace ta dinga wanke mata zai biya.

Tsawon wata guda kenan da zuwan Sajida bai fi sau biyu ba Zahra ta ga Sajida. Shi ma à kofar dakin Sajida suka’ hadu, Sajida ta leko kiran Grace, Zahra kuma ta zo wucewa za ta shiga dakinta suka yi kallon-kallo kowa ya dauke kai. Duk ranar girkin Samira, Bakura zai kame a dakinsa, Samira ta zo, amma ranar kwanan Sajida sai dai ya bi ta daki, shi ma datse kofar falon take sai dai ya shigo ta kofar baya wacce shi. kadai yake da mukullin. Kada ku ce idan ya shiga dakin wani abu ne zai faru, a’a a gaba take sa shi sannan. ta danno lambar Abdulmaid su yi ta soyayya don ta kular da shi ya gaji ya sake ta, amma sai ta ga Bakura ‘ko damuwa ba ya yi. Kai har in credit din wayarta ya kare sai ta ga ya zaro recharged card na dubu daya da dari biyar ya ba ta ya ce ta ci gaba da wayarta, yana gefe yana kallonta cike da, murmushi.

Al’amarin, Bakura wani lokaci yana ba ta tsoro, don ba ta san abun da yake hada mata ba akan wannan kasaken da ya yi mata.

Sajida ta ga an doshi watanni biyu da aure, babu alamar gajiyawa a tare da Bakura, ba shi da niyyar jin haushi, balle ya sake ta. Sai ta yi yunkurin hada kaya ta gudu cikin dare, amma abu ya ci tura. Ta kalli tsawon katangar gidan nan ta ga ba irin katangar

gidansu ba ce da take iya haurawa ba. Ta nufi get ta

tabbatar masu gadi suna aikinsu tun karfi ko da yaushe

.get a datse yake da manya-manyan kwado. Kafin a bude mata get sai sun gama tambayoyi, balle a ce su ganta da kayanta a hannu ba a motà ba ta ce za ta je unguwa, ko daya ba za su bar ta ba. Gashi an hana.

kowa zuwa daga gidansu.

Wata rana da daddare, dare har ya fara nutsawa

Bakura bai dawo gida ba. Sha daya na dare, har ta

wuce ba Bakura babu wayarsa, don haka hankalin

Samira da ‘ya’yanta ya tashi, ko barci suka kasa yi. Yi

suke suna kara yi wajen buga wayarsa, amma wayar a kashe. Babu abokinsa da ba ta kira ba, sai su ce ba sa

tare da: Bakura a yau. Sha biyu daidai wayar Samira ta

yi kara alamar ana kiranta, ita da Zahra suka hau rige-rigen dauka. Samira ta danna wayar, gami da kadawar hanta da fargaba. Ta fada

“waye yake Magana”

Cikin harshen turanci mutumin ke magana da alama inyamuri ne, ya fara da gabatar da kansa.

Ya ce, “Sunana Doctor Isreal daga International

Hospital. Dan Allah ina magana da Samira ne Mrs.

Bakura?”

Ai tuni Samira ta rusa kuka ta fara kwakwazo.

-“Doctor ni ce Samira. Me ya faru da maigidana,

ya mutu ne?”

“‘Bai mutu ba, amma ya sami raúni “

Ta sake fashewa da kuka ta ce, “Hatsari ya yi ne?”.

Ya ce “A’a an kawo mana shi dai ana tunanin

‘yan fashi ne suka dake shi har an farfasa motarsa. Ki kwantar da hankalinki ga shi nan ya mike yana magana, shine ma ya ba ni lambarki ya ce in kira ki.”

Doctor ya sawa Samira muryar Bakura yayin da ita ma ta danna speaker yadda yaranta za su jiyo muryar mahiafinsu, don su duka kuka suka zo suka kewaye ta suna yi. Cikin kuka suke kiran.

“Abba, Abba me ya faru da kai?”

Cikin sanyin murya Bakura yake lallashinsu fadi yake,

“Na ji sauki, ku daina kuka.”

Duki wannan abun da ake Saida na bayansu a tsaye ta jingina a jikin bango ta kama Kirji ta kame kamar soja. Da alamar sanyin jiki a tare da ita. Amma da ta ga sun juyo gaba daya suna kallonta, sai ta tabe baki ta harare su sama da kasa ta wuce zuwa dakinta, . don kada ma su dauka ya dame ta. Samira ta aika Zahra da Abubakar, Boy’s quater su taso Lurwanu direba ya zo ya kai su asibiti wajen Bakura. Da gudu Zahra da kaninta suka nufi Boy’s quater suka taso shi, a gigice ya dauko mukullin mota ya fito. Ba tare da bata lokaci ba Samira da ‘ya’yanta suka duru a mota suka nufi asibiti, sai addu’a suke suna koke-koke.

Sajida na shiga falonta ta jawo wayarta ta bugawa Abdulmajid, zuciyarta cike da bacin rai, domin tana zargin da sa hannunsa a cikin wannan al’amari, Yana

amsawa ta harbo masa wannan

tambaya.Abdul majid me kasa a yi wa Bakura?”

Ya tabe baki ya ce so.

•”Me ki ka ga an yi masa, wannan wacce irin tambaya ce kike yi min? Kar ki raina min hankali mana.

Ta fada cikin tsawa da bacin rai, “An ce ‘yan fashi sun tare shi sun dake shi, har sun fasa masa mota.

Ina tunanin kai ne kasa a yi masa haka.”

Ya ce, “Ki daina tunanin nasa an dake shi, nine da hannuna na tare shi ni da su Shehu abokaina muka farfasa masa kai dazu da Magruba a Hotoro G.R.A.

Kin fara sonsa ne, ina ruwanki ko mutuwa ya yi?”

Ta fada a fusace, “Kaga Abdul majid ba na son haka, ya za ka nemi ka kashe mutum ba da hakkinsa ba. Me ya yi maka? Mutumin nan ya ba mu damar mu yi magana har ma katin waya yake siya ya ba ni in kira ka. Me ye laifinsa?”Ya fusata ya ce

To ki je police station ki yi Kara na da kan ki kafin ya warke ya sa a nemo mu, don na fada masa ko mu su waye, kuma na haska masa fuskata tangararai ya ganni, kuma zai shaida ni. Tunda kina sosa kada ki

Kara kira na a waya.”

Ya yi, tsaki ya kashe wayar, Sajida ta dade a zaune tana, ta tunani tana zullumin abun da zai je ya dawo. Hakika har cikin ranta ba ta ji dadin abun da •Abdulmajid da abokansa suka aikatawa Bakura ba.

Don haka babu irin kiran da Abdul majid bai yi mata ba a cikin daren nan Sajida, ta ki amsa wayarsa, daga karshe ma ta kashe wayar gaba daya ta yi kwanciyarta.

Tana jiyo motsin dawowar su Samira har da

Bakura, amma ko lekowa kofar dakinta ba ta yi ba, balle ta yi masa sannu. Haka washe gari Bakura ko falo bai fito ba, yana dakinsa a kwance ya hana Samira. ta fadawa kowa, ba shi da lafiya, don haka masu aiki ma ba dukkansu ba ne suka san Bakura na kwance ba lafiya ba. Wannan al’amari na Sajida ya yi matukar batawa Samira da ‘ya’yanta rai, sai shige da fice take tsakanin dakinta, falo zuwa kicin tana nuna halin ko in kula bai dame ni ba. Rashin lafiyarsa ku ta dama

A fusace Samira ta zo shiga kicin yayin da a fusace Sajida ta zo fitowa daga kicin suka bangaji juna a bakin kofar kicin, Sajida dauke take da katan kwalin juice da kofi a hannunta.

Samira ta ce, “Mutum ko dabba ne ai ya san mai ba shi abinci, don haka baya samun sukuni idan ya fi kwana biyu bai ga mutumin nan ba. Ma’ana shi mai ciyar da ke, mai tufatar da ke, mai siyo wannan juice din da ki ke yini kina sha, ba shi da lafiya a ce ko sannu, yaya mai jiki baki iya ba. Duk rashin tarbiyyarki ai kya tausayawa rai, saboda idan mutumin nan ya fadi ya mutu, sai dai fa ki koma gargajiya zancen juice ya kare.”

Hmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE