ALLURA CIKI RUWA BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 3 CHAPTER 13 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Na rika tuno da Aliyu a inda ya taba ce mini,

“Asiya ranar da na ganki a dakina na mallake ki a wannan rana zan nuna miki son da ba a taba nunawa Wata mace a duniya ba, amma a tawa aljannar duniyar.

A ranar zan yi miki abin da mafarki ko tunaninki bai taba nuna miki ba, zan tabbatar miki ni maraya ne na ainahi, wanda bai samun jin dadi a wajen kowa ba a duk fadin dunivar nan sai ke da Allah ya. rataya zuciyata a gare ki.

A wannan ranar dai dogara rayuwa ta gare ki, zan kuma nuna miki hanyoyi wadanda na san a rufe suke a fanninki sai ni ke da mallakinsu. In kuma Allah ya yarda da asubar fari zan samar mana abin da zai tsayar mana da so da Kauna, watau Allah zai mana baiwa da diya mace, wacce harna riga na rada mata suna

Fadima” Na yi ajiyar zuciya na saukar da kaina Kasa kamar yadda na yi a lokacin da yake mini wannan

magana.

Yayin da nake kokarin tuno amsar da na ba shi ne, saiga Yaya Aminu tsaye a gabana ya zuba hannayensa cikin aljihu. Nayi zumbur na mike tsaye da nufin in gudu zuwa gidanmu, sai ya yi caraf ya rike ni.

Na ce masa,

“Wallahi ka sake ni kada mu yi

bala’ in da baka taba zaton zan iya aikata maka shi ba”

Ya lura hankalina ba ya tare dani, ya ce, “Haba Asiya kwantar da hankalinki kada wata cuta ta sarke ki, in don na shigo dakinki ne bari in fita”. Ya fita jikinsa na

rawa ya koma dakinsa ya kwanta.

*Bayan na yi sallar asuba na kunna kaset din

suratul yasin na zauna na bude Alkur’ ani mai girma ina bi.

Da misalin karfe takwas na ji ana Kwankwasa

Kofa, na ce, “Wane ne?’

Ya ce, “Nine ina Madam’.

Na bude Kofar ya gaishe dani, sannan ya shigo da

tiren kayan shayi. Ina zaune ina tunani ko ina Yaya Aminu yake? Sai Allah ya turo mini Larai, na tambaye ta. Ta ce, “Yana bisa dakali shi da Babana”

Na ware gyalen atamfata na sha lulludi na nufi

sashen Inna Hafsatu don in gai da ita, saboda laifin wani baya shafar wani.

Na same ta tare da Baba Ladidi a falo, na durkusa. har Kasa na gaishe su. Inna Hafsatu ta matsa mini in

zauna bisa kujera amma na ki. Ni kaina na yi mamakin

yadda na kasa hada ido da Inna Hafsatu, duk da yadda take wasa damu.

A bisa kan hanyata komawa sashemmu na yi

kicibis da Yaya Aminu, ya ce, “Kowa na gaishe shi ban da Aminullahi ko?” Na wuce abina.

Da la’asar sakaliya na ji Aminu na kirana daga falo. Da farko na yi shiru amma da na ji maganar su Maikaita sai naje ba tare da na amsa ba. Na samesu su

uku na yi sallama muka gaisa. Yaya Aminu ya umarce ni da in kawo musu alkaki da nakiya. Na amsa “To”. Na sami faranti na zubo masu, sannan na zubo wasu a cikin leda na kai musu.

Abbati ya ce, “Wadannan na cikin leda fa?”

Na ce, “Na iyalanku ne”

Suka nuna farin cikinsu ainun, inda na lura Yaya Aminu har wata rangwada ya rika yi don tsananin jin dadi.

Na juya zan koma daki suka nemi da in tsaya mu yi hira, nace Aiki nake yi”.

Hakika zamana a gidan Yaya Aminu na

Malumfashi bai kunshi komai ba face bacin rai, in ka debe gaisuwar da nake yi da abokai da kuma ‘yan’ uwana babu wani abin arzikin da ya taba hada ni da shi. Hutunsa na sati biyu ya cika, a daren washegarin da zai koma Katsina da misalin karfe sha daya, ina kwance ina karatu sai ga shi ya shigo, ya mayar da kofa ya rufe, yana sanye da wata tafkekiyar rigar bacci yana rike da belt din rigar.

Yadda na hango kirjinsa sai gabana ya fadi, da ya lura da hakan ya lattara rigar ya mayar da bel din ya tsuke, ya nemi kujera ya zauna.

Ya yi murmushi ya ce, “Kina kallona kamar kin ga wani kumurci, haba ‘yar lelena ina son in shaida miki sai ki shirya gobe za mu koma Katsina”.

Na daure fuska na ce, “Da wa za ka Katsina? Ba dai ni Asiyar ba”. “Haba Asiya ki fa rage tsanata ko ‘yar hira mu rika yi mana

Na dube shi, “Tsana yanzu na fara, hira dani kuwa har abada, har sai ka yi nadama ka sallame ni”

Sai ya kyalkyale da dariya ya ce,Ni duk

bakaken maganganunki basa damuna, tunda babu hirar arziki bari inzo mu yi ta tsiyar, a wajena mai zaki ce”.Ya taso ya nufo ni, ya rike ni yana neman ya zaunar dani bisa gado. Sai muka rikice da kokawa. Da ya lura ban damu ba don an kashe tangaran din da ke dakina, sai ya sake ni ya koma bisa gado ya kwanta, ya ja lallausan bargona ya Kudundune. Da na tabbatar idan.

•ban dauki mataki ba zai aikata wani abu dani ta kowacce hanya, sai na bude kofar bandakina wanda yake cikin dakina, na bude shi na ce, “Da in kwana da kai gara in kwana a bandak;”

Ya bude ido kawai yana duba na, ya nemi kalmar da zai yi amfani da ita ya rasa, zuciya ta kule shi ya yi mani wani irin kallo wanda rabon da in ga irinsa tun yana koyar damu lokacin ina firamare.

Yayin da ya mike na san irin kallon da ya yi mani lalle ya dauki maganata da zafi. Babu ruwansa dani, na kuma tabbatarwa kaina daga wanna rana ba sauran wani wasa da zai yi dani, balle har ya nemi wani abu a gare ni.

Ya bude kofa ya fita zuwa dakinsa..

, Daga wannan rana na fara samun ‘yan natsuwar hankalina kadan, abin da kawai ya rage mani shine ya sallame ni in koma gidan Gwaggo Juma a can Katsina, har mu yi aure da Aliyuna.

A kwana a tashi na sami kimanin ‘yan watanni a gidan Yaya Aminu. Ran nan kwatsam Yaya Abubakar yazo mini da tabbacin jarrabawarmu la fito, na kuma cinye takardun.

Saboda haka Yaya Aminu yazo ranar asabar kamar yadda ya saba duk sati ya koma ranar lahadi, Yusuf ne ya shaida masa maganar jarrabawarma. Ya yiwa Inna Hafsatu magana a kan ta roke ni ya kai ni amso takarduna.

Babu yadda zan yi dole na bi shi Zariya na amso.

Bayan sati daya da amso sakamako, sai Yaya Aminu yazo mini da takardar fara hidimar kasa a inda zan yi a can Katsina, a makarantar koyon aikin shari’ a ta Katsina.

Washegari da la’asar muka doshi hanyar Katsina, na rika tunanin yadda zamanmu zai kasance a Katsina.

Na tuno da yadda aka sha artabu dani a kan in shiga in yiwa iyayena sallama, amma na ki don na san ko na shiga hararata za su yi. Na kalli Yaya Aminu nayi tsaki ina juyayin yadda ya hada ni da iyayena.

Muka isa gidan Yaya Aminu na Katsina, mun sami yaronsa Ino yana girka abinci. Ya yi mana sannu da Zuwa tare da shigar mana da kaya.

Na sami daya daga cikin kujerun falon na nutse, shi kuma Yaya Aminu ya shiga wanka, ya shirya ya fito sanye da jallabiyya fara, ya tsaya a falo yana sanya takalmansa, ya kwalawa Ino kira ya shaida masa cewa,

Hmmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE