
MISBAH BOOK 4 CHAPTER 22 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
tayi da ke, sai ki yi mata alkawarin ba zaki sake ba maganar Hubby kuma dole ki hakura don haka ki tashi ki je ki bata hakuri daga baya mayi Magana ko idan mun koma makaranta tunda hutun yana daf da karewa.”Zata yi wata Magana ya dakatar da ita yace “Kiyi kawai abinda nace da ke Aisha.”
Haka kawai taji tace “To.”
Bai jira yaji mai zata ce baya kasha wayar abinsa.
A haka dai suka yi hutun ya kara suka koma makaranta amma kafin ta koma sai da suka shirya da Maman ta sai dai ta jamata kunne sosai akan bata son ta kara yin haka. Kwanci tashi babu wuya gurin Allah a yau ga shi
Aisha tana daf da gama Level one wanna wanda tuni ta yi nisa a kaunar Nuren domin babu wanda ya san yadda lokacin da soyayyarsu ta yi karfi haka, cikin dabara da wayo Nuren ya gama shiga zuciyarta bata sani ba saboda shi mutum ne mai hikkimar gaske shawarwarin da yake yawan bata akan ta bi abin da mahaifiyarta ta so ta hakan ya gama siye zuciyanta da kuma dadadan lafazinsa hakan yasa tuni tayi tsamo tsamo a cikin son shi sai lokaci guda ta Ankara.
Tashin hankalin Yaya Muhammad ya karu a lokacin da ya gama gano tsakanin Aishansa ga wanda take so ba fada masa tai ba wata rana ne ya zo gurin ta a cikin School don yazo ta raka shi cikin gari gaisuwar Baban wani abokinsa da ya rasu a nan ya hango su suna ta dariya suna hira kai da ka ganin ka zaka gane cewa su masoya ne.
Tasananin kishin Nuren ya taso masa kamar zai halaka shi domin dama ba sa shiri da juna duk ranar da suka hadu basa wani gaisawa sosai kamar yadda zai tsaya da Muhammad. A hankali ya gano cewa soyayya don haka ya ji duk duniyar ta yi masa zafi sai dai kawai ba zai iya fitowa fili ya fada mata abin da yake ransa ba.
Daf da za’a fara jarabawa ne sun gama karatu kenan suna hira ita da Yaya Muhammad tace.
“Yaya Muhammad ina son yin magana da kai amma ni kai na ina jin shakkar fada maka amma idan na tuna a duniyar nan bani da wani dan’uwa sama da kai bani da abokin shawara sama da kai, kai ne aminina kai ne best Friend dina komai na ba na yanke hukuncin komai sai da saninka.
Cikin kaguwa ya katseta yace “Oh Aisha naji na kuma jima da sannin haka please go to the point.”
Nan ta kale shi cikin jin kunya tace “Nayi wa
Mama laifi bayan na yi mata alkawarin bazan yi abinda bata so ba amma na san idan ta sani ba zaka bari ba zat tayi min fada ba don haka sai ka kare ni.
Yaya Muhammad ba komai ba ne illa Yaya
Nuren da yace min yana so na ban kuma yi shawara da kowa ba na amince masa tashin hankali na daya idan Mama ta ji bayan ta min kashedi da kada na yarda na bata lokaci na akan samari duk karya ne babu wata soyayyar gaskiya a nan duniyar.” Daga mata hannu yayi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa yace “Me yayi saura kuma me kike so nayi miki bayan kin amsa masa, kin manta da alkawarin da kika yiwa Mama me kike so nayi miki yanzu bayan kin zartar da hukunci da kike gani shi ne dai dai.”
Babu wani abu da yayi saura a yanzu zan ce ki fasa son Nuren ne kome, abinda zan fada miki ba lallai ne yayi mik dadi ba don haka ni a wannan maganar babu abin da zan iya fada miki sai dai nace a yi soyayya lafiya.”
Yanayin da Muhammad ya shiga yayi mutukar daga mata hankali domin tunda take a rayuwarta bata ta ba ganinsa cikin wanna yanayin ba domin idonsa ya kada ya yi jazur ga wani irin fushi akan tuskarsa.
Mikewa ya yi tayi saurin ta shi ita ma tace
“Yaya Muhammad wannan maganar da na fada maka ita ta daga maka hankali har kake so ka yi fishi da ni haba Yaya Muhammad dina na sani ban kyauta ba da na amince da soyayyar Nuren ban nemi shawarar kaba ni kai na ban san ya akai na yi hakan ba.”
“Kin sa ni mana ke da bakin ki kika fada kina son shi tunda kuwa kina son shi kin ga babu wanda ya isa ya dakatar da ke tunda kin yi nisa.”
Haka ne naji ni na fada don na fadi haka bashi ne zai san a kasa iya canza furucin da na yi ba ina son shi ba mutukar Yaya Muhammad ba zaiyi farin ciki da shi ba, domin na san duk abin da nake so shi Yaya Muhammad yake so don haka don naki abin da baka so ba zai taba cutar da niba tunda a haka muka taso duk abin da dayan mu yake so shi dayan yake so don haka. Idan baka son tarayyata da shi a yau zan dakatar da shi duk da kuwa irin son da nake masa mutukar yin hakan zai sanya ka farin ciki.”
Mursmushin karfi hali yayi yace “Aisha na ki kwantar da hankalin idan nine bazan taba kushe abin da kike so ba sannan zan yi iya yi na naga Mama bata yi fishi da wanna abin da kikayi ba babu komai kada ki ta da hankalin ki akan wannan al’ amarin ni Yaya Muhammad ina tare da ke da kuma abin da kike so HAR ABADA.”
Wani irin dadi ya kama ta ta shiga murna tare da yi masa godiya. yace “karki damu ina tare da ke.”
Da wannan furucin ya kwantar mata da hankali ta fada cikin exams din ta sai dai shi din da ya fada cikin zafin son ta da yake kwana yake tashi gashi bai iya furta mata abin da yake ransa ba har wani ya zo ya bayyana mata abin da yake ransa.
Tabbas ya san ba laifin kowa bane nashi ne da ya fada mata tuntuni baya kawo wasa cikin al’amuransa da tuni komai ya dai dai ta don haka zai ajje son ta a ransa ya kuma cigaba da bata karfin gwiwa a kan Nuren din saboda zai iya sadaukar da komai akan ta don kawai ya ganta cikin farin ciki shi kadai da zuciyarsa suka san irin tarin son da yake mata amma bai iya furtawa ba har wani ya zo ya fada mata. Makale take da waya cikin dare bayan ta gama karatun ta Nuren ne ya kira ta suna hira kamar yadda suka saba nan take gaya masa yadda suka yi da Yaya Muhammad din ta yaji dadi sosai kuma ya yarda da abinda yace zai yi domin Muhammad Gentle ne babu hayaniya a tare da shi nan ya ji yagama samun nutsuwa ya saki ransa ya fara zana final exams dinsa.
Muhammad kuwa damuwa ne yayi masa yawa ya rasa yaya zai yi da zuciyarsa domin yana jin bai kyautawa zuciyarsa ba mai yasa bai fadawa Aisha abinda yake ransa ba, haka ya din ga jin kamar ba zai iya yafewa kansa da zuciyarsa abinda yayi ba.
A ranar ya samu Muhammad wanda a yanzu yake babban abokinsa nan ya zayyana masa komai ya kuma fada masa babu yadda zai yi dole ne ya boye abinda yake ransa domin ya ga tuni Aisha tayi ni sa akan son shi.
Ganin irin yanayin damuwar da ya shiga yayi mutukar tausaya masa nan yace ya bar shi zai yiwa
Nuren bayani yadda zai gamsu ya bar masa ita kada ya bari ya rasa ta.
Cikin damuwa yayi saurin dakatar da shi yace
“kada ka yi haka Muhammad idan nayi haka ban yiwa kai na adalci ba bayan da baki na, na fada mata zan taimaka mataba zan taba bari ta rasa abinda take so ba.
Idan na yi mata haka ban kyauta ba zata dauke ni makaryaci mara cika alkawari zanyi kokarin yadda zan yi na danne kishi na nayi kokarin ta ya ta son
Hmmm