KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 21 BY JAMILA UMAR TANKO

Yarinyar nan, Ki taya ni fada mata ko ni wacece ko kuma yaya nake. Dan rainin hankali ma wai tambayata take me ya faru? Ba ta ma san me ta yi min ba ko? To bari ki ji Zahra babu yadda za ki yi da ni da Abdulma sai dai kallo da Ido babu mai raba mu, ke ko uban daya tsugunna ye haifeni ma sai dai ya yafe min amma ba zai iya hana ni son Abdulmajid ba.”

Gaban Zahra ya sake faduwa ta shiga sake-sake ranta “tabbas Sajida ta ji labarin Abdul majid ya nã yi min waya ada.”Sajida ta rike kugu sai girgiza take tana huci tana hararar Zahra, tamkar mayunwacin zakin da yaga nama. Zahra ta juya ta dubi Ibrahim ma’aikacin da yake biye da ita a baya. Ta ce ya matsa ya bar wajen ta na son ta yi magana da qawarta, ya amsa mata cikin ladabi ya tafi da sauri ya bar wajen.

Zahra ta matso kusa da Sajida ta ce “Sajida, wallahi ban san Abdulmajid ba, ban taba sanin yaya kamanninsa su ke ba, ba ni da wata alada da shi dan haka ne ma nake mamakin tuhumar da kike yi min a akansa.” Sajida ta ji tamkar Zahra ta soka ma ta mashin wuta a gahon

zuci. Ta fada a fusace “dubi bakin gofar shigowa.”

Zahra ta waiga da sauri, sai ta hango wani dan kyakykyawan saurayi a tsaye.

Sajida ta ce to Abdul majid dina kenan, ki koma ki sake fadawa Babana kin ganmu tare.”Saida ta kwallawa Abdul majid kira nan da nan ya garaso in da suke. Tace da shi “ga Zahrar da nake fada maka wacce na taba kiranka da wayarta, daga qarshe ta hada min tuggu wajen Baba.’ Abdulmajid ya ji gabansa ya yanke ya fadi kamar yadda na Zahra yake faduwa lokaci guda suka Zubawa juna ido har wani lokaci mai dan tsawo kowannan su ya na tunani a ransa. Abinda ya fara fadowa Zahra a ranta sai kalmar “inna lillahi wa’inna ilaihi rajil’un. Yau me ya ke shirin faruwa da mi ne haka? Na rabu da

Abdulmajid a waya ga shi na gan shi yau a zahiri?”

Abdulmajid kuwa’ kan ka ce kwabo farin ciki ya lullube

zuciyarsa da Allah ya nuna masa Zahra a zahiri, kwakwalwarsa ba ta taba kwatanto masa haduwar Zahra ta kai haka ba, ba makawa Zahra itace irin kalar macen da yake burin ya mallaka a rayuwarsa. Tum fitowarta daga motarta tun ma bai san wacece ita

ba zuciyarsa ta fara muradinta domin ta cika gaba daya abubuwan da namiji yake bukata a wajen mace. Nan da nan ya ji kafarsa ta kasa daukar jikinsa. Ya kidime ya fita daga hayyacinsa, amma

gudun kada Sajida ta gane halin daya shiga sai ya juya da sauri ya fice ya nufi wajen motarsa ya shiga ya zauna ba tare da ya ce uffan

ba. Iyayye ta ce “au daman itace munafukar da kike fada min ta na hada miki tuggu?”

-Idan hankalin Zahra yayi dubu ya tashi, nan da nan

idonta ya cika da hawaye. Ta girgiza kai ta ce “actually I don’t understand what is happening here…

Kafin ta rufe bakinta Sanida ta daka tsalle ta kinkimo

qaton gwangwanin madara babba wato (giant size) ta datsa mata” wajen kaifin a goshi, ko sakon daya ba’a gara ba jini ya wankewa Zahra fuska.

Zahra ta kwalla ihu mai tsanani ta yanke jiki ta fadi

Kasa. Kafin kiftawar ido Sajida da kawarta lyayye sun bace daga cikin kantin.

Ma’aikatan shagon kacokan dinsu suka taru su ka

zageye Zahra su na mamaki, su na al’ajibi yadda gwangwanin madara zai fado mata a goshi. Daya daga cikin ma’aikanta ne ya ke

bayani wato Ibrahim cewar akan idonsa wannan budurwar ta jawo gwangwanin madara ta rotsa ma ta a goshi Sauran ma’ aikatan gaba daya suka yiwa Ibrahim caaa akai su na tuhumar sa da cewar me yasa bai dame yarinyar ba har ya bari ta gudu?”

Hankalinsu a tashe suka garzaya da Zahra asibiti dan

tsayar da jinin da yake zuba, aka kuwa ci sa’a ba a yi mata dinki ba, lodine da plasta aka saka mata aka lige suka kawo ta gida. Samira suka iske a falo, ta na ganin goshin Zahra sai ta dauki salati mai hade da kuka dadin dadawa ma bushashshen jinin

– da ta gani a jikin tufafinta. Abinda ya fara fado ma ta a rai shine ko hadari ta yi a hanya, amma ganin ma aikantan shagon sai ta fara tunanin ko a bakin kantin hadarin ya faru. Zahraa rungume mahaifiyarta tana rusa kuka, Samira ta zaunar da Zahra akan kujera itama kukan ta fara yi tana tausayin

‘yarta tana tausayin kanta, domin arangamarta da Bakura ba zai yi kyau ba dalilin da ya sa ta bari Zahra ta dauki mukullin motarta ta fita ita kadai.

Ga gargadin da yake yi mata cewar ta sa ido sosai akan Zahra, yana fatan, yana kuma addu’a Zahra bata fita ta ragashe a bayan idonsa. Cikin karkarwar jiki

Samira take tambayar ma’ aikatan da suka rako Zahra har su hudu. Daya daga cikinsu ya ce “ina jin tuntube tayi ta daki jikin kanta gwangwanin madara ya datso mata a goshi.” Daya yayi karaf ya ce “ba gaskiya bane babu yadda za’ayi dan mutum ya dan daki kanta gwangwani ya fado, wannan ba abin rufa-rufa ba ne don idan muka rufa mu kuma zai iya shafar aikinmu, idan maigida ya zo zai iya korar dukkan mu ya ce bama lura. Akan idon Ibrahim abin nan ya faru dan haka Ibrahim ka yi bayani.”

Ibrahim ya matso ya ce “îna biye da Zahra a baya sai

wasu ‘yan mata suka haù zaginta sai ta ce da ni in matsa daga wajen zasu yi magana. Matsawata ke da wuya sai na ga daya daga cikin ‘yan matan tayi tsalle ta ciccibo gwangwanin madara qato ta kirba mata a goshi amma ko Sama ko gasa ban ga ta inda ‘yan matan suka bi suka gudu ba.”

Samira ta juya ta dubi Zahra ta ce “wadanne ‘yan mata ne wadannan? Me kika yi mu su haka har da zasu fasa miki kai?

Ke da baki da abokin fada tun ki na yarinya. Me kika yi musu har ya tunzura su suka fasa miki kai?°

Zahra hawaye take ba tare da ta iya bada amsa ba.

Ana cikin wannan hali.

Bakura ne ya kira wayar Samira tana jin ringing sai tace yauwa ga Abbanki nan ya kira bari na fada masa tunda ni kin qi fada min gaskiya.”

Samira na dannawa ko gaisawa basu yi ba ta ji Bakura

ya na fada har da kumfa baki, hankalinsa a tashe. Yace “wai me yake faruwa ne aka yi min waya aka ce wata yarinya ta fasawa Yagana kai a cikin Super Market? Wacce yariya ce, kuma waye

Ubanta a Kano?” Samira ta ce “yanzun nan su ka shigo min da ita ban ma gama jin abinda ya faru ba. Yagana kuka take ta qi yin magana, sai dai ga Ibrahim wanda abin ya faru akan idonsa zai yi maka bayani.”

Samira ta migawa Ibrahim kan waya, Ibrahim ya karba gami da yin sallama.

“Me ya samu ‘ya ta?’ tambayar da Bakura ya yiwa

Ibrahim kenan kafin ya amsa masa sallamar. Ibrahim ya haù bayanin iya abinda ya gani akan idonsa.

“ina yarinyar take?” in ji Bakura.

[brahim ya ce “kafin na ankara na neme su na rasa sun

gudu.”

Nan da man Bakura ya hau Ibrahim da bambamin fada

yi yake yana dukan teburin da yake gabansa. Ya na yiwa Ibrahim barazanar rasa aikinsa akan wannan sakacin da yayi. Malam Yakubu ‘ ne a zaune a gefen Bakura yana

lallashinsa, yana bashi baki cewar ya kwantar da hankalinsa abi abin a hankali.

Bakura ya kashe waya sai huci yake yi, wani gumi mai

zafi ne yake ta keto masa.

Ya ce da Malam Yakubu “wallahi, wallahi sai na dau

fansa akan wannan yarinyar da ta bi Yagana har cikin kantin Mahaifinta ta dau katon gwangwani ta fasa mata kai, sai na ga

mahaifin yarinyar nan inji ko shine ya sa take rashin mutunci a Kano. Ban taba rigima akan yarana ba, ban taba rigima da kowa ba tun sanda na zo Kano, amma zan fara akan wannan yarinya.”

Malam Yakubu ya ce “daman bai kamata a bar

maganar nan ba, saboda idan aka bar maganar nan gaba waya san.

abinda zata yi mata idan taga ba’a dau mataki ba, amma abi abin a hankali saboda yanke hukunci cikin fushi yana jawo dana sani ko nadama.”

Bakura yayi ajiyar zuciya ya ce “to malam, na ji zan bi

a hankali amma Ko me Yagana ta yiwa yarinyar nan bai kamata tabi ta har cikin shagona ta fasa mata kai ba, har da jini face-face. A° iya sanina Yagana ba ta fada, ko an tsokane ta bata tankawa. Ba ta

iya fada ba, bata ma san yadda ake yinsa ba. Haka kawai ta bi ta har cikin kanti ta fasa mata kai ni kuwa sai na ji da wa take tagama a gasar nan kuma sai na ga mahaifinta inji dalilin da yasa

Hmmmm

Show More

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE