ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 33 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Sai ya ce, “Ta yi rashin sa’a bani da sha’awar mata da yawa, mace daya ta ishe ni”. Yana dariya.

‘Inna ta ce, “Kai wannan maganar fa mai Karfi ce ba maganar wasa ba ce. A ina ka sami matar?”

Ya ce, “Zan kawo ta kwanan nan ku ganta”.

Ya dube ni ya yi murmushi, sai gabana ya rika dar-dar, na bata fuska amma sai ya ce, “Inna amma fa banufa ce”. Yana dariya a gare ni, sai raina ya yi mini dadi.

Na ce, “Kai Yaya nufawa fa mayu ne?”

Ya kyalkyale da dariya ya ce, “Shi ke nan na yi maganinki ke nan sai ta fara cinye ki, tunda na lura ba kya son aure, ko kuwa wasan Katsinawa da

Nufawa za ki kawo” Na ce, “Don Allah Yaya ka rufa mani asiri ka ga Raula ta shiga wani hali ka rabu da banufar nan”Ya ce, “To ke wai ina wasa da ke ne? To ki bari idan na yi shawara da ita banufar tawa zan zartar da hukunci”

Ita Inna da ta ga ya mai da maganar wasan yara sai ta fice ta barni da shi, ya fiddo wasu saitin hankici masu kyan gaske har guda shida, ya dube ni ya ce, “Ko kina so?” Na ce, “Eh, na gode”

Ya ce, “Hala saurayinki za ki bai wa?” Na ce, “Eh to yadda nake son shi dole ne ma in ba shi, amma ita ma Raula zan dibar mata in ce in ji ka”

Sai na ga nan da nan ya zare ido, ya ce,

“Asiya kada ki ga kamar na sa maki ido, cikin wannan hutun ki tsai da ruwan idonki ki fiddo miji domin ba ta yiwuwa a aurar da Hadiza ita kadai, shi Aliyun da kika barshi ya hana kowa magana, za mu zauna da Baba mu yanke shawara, kin ji da kyau?”

Kaina na sunkuye na ce, “Eh, na ji”.

Inna Hafsatu ta shigo suka yi sallama zai tafi, ya kawo kudi masu dama ya ba ta, sannan ya shiga wajen Innata ita ma ya bata.

Na koma gida na yi wanka na zauna na shirya kwalliyar da ko ‘ya mace ta dube ni ta yi sha’awa ta ballantana da namiji. Inna ta ce, “Ina za kine kike ta sau ri ga hadari nan yana niyyar hauhawa?”

Na ce, “Wallahi Inna Aliyu ne ya matsa mani a kan muje gidan Yaya Rabi tana son ganina”.

Sai ta daure fuska ta harare ni, ta ce, “Ke ce me neman gidanta ita ba ta san naku gidan ba? Allah ya kyauta da halin sayar da kai”.

Sai na ji jikina ya yi sanyi, na koma gefe guda na zauna na yi tagumi ina gaya mata duk yadda muka yi da shi.

Tace, “Kin riga kin amince masa ni yanzu na sauya maki ra’ayi? Ki dai sani ba za ki taba mutunci ta idonsu ba, ina ma laifin a ce suma suna zuwa naku gidan, to in kin je nasu babu laifi. Ki tuna fa gaisuwar mutuwa ba su zo mana ba, ni na ma taba ganin neman aure irin wannan. Dubi ‘yan’uwan ” Mukhtar haka suka dinga

jele bisa hanya tun da aka yi mutuwar nan, amma shi nasa dangin a gari daya kuke,,

‘Allah ya kyauta.

Komi kwakwarki wannan hutu dole ki tsai da mana da magana”

Na yi shiru Kwalla suka cika mani ido, amma

don kada in bata kwalliyata na yi kokari suka koma.

Larai ta shigo ta ce, “Aliyu na kira na”. sashen Inna na sunkuyar “da kaina kasa.

Ta ce, “Tunda na amsa masa inje daga wannan ba zan sake dauka ba, nayi na karshe”

Na same shi a zaune a mota, na yi taurmushi ya bude mani na shiga, ya ja muka tafi. Na ce, “Ni na yi zaton ma ba za ka zo ba sai gobe ganin wannan hadarin da ya taso?”Ya ce, “Haba ina, so nake a fara zartar da komi a yau kin ga gobe sai in gama da Galadanci a can Katsina’Na dube shin nayi murmushi nace “Kamar kaSan ni ma an fara matsa mini akan maganar aure yace Wallahi suna da gaskiya aini ba karamin mutunci iyayenki suka nuna mani ba. Yadda mutane ke damunku amma kuka ki sauraron kowa sai ni ake jira, babu abin da zance sai allah ya saka musu da alheri, ke kuma babu abin da zan ce miki a game da toshe kunnunki da ki ka yi sai dai ince ran da duk na ci amanarki ni ma Allah ya ci tawa.

Na san, kina da samari wadanda suka fini kyau ko mukami ko kudi amma duk basu rude ki ba, . ni dai kika yiwa alkawari kin sanya mini ido, kin kuma bar wa Allah ikonsa. Insha allaha Asiya za ki zama daya daga cikin mata masu sa’a a duniya ta fannin aure, kuma za ki gani, Allah ya ba mu rai da lafiya yadda nake jinki a jikina Asiya, bana iya fassara miki amma mutane sai su dinga _maganar banza.

Ni kadai na san yadda kike a raina babu komi ni dai burina a yau in ga an daura mana aure”

Na ce “Aliyu mutane maganar me suke maka’?

Ya ce “A°a babu komi, kin san halin dan adam. kowa da ra’ayinsa”

• Mun isa gidan su Yaya Rabi muka same ta a falo, na durkusa na gajshe ta, ta dube ni kamar zata lashe ni, ta umarci yaringar gidan ta kawo mani lemun kwalba da cin-cin da danbun mama. Na rika kallon dukiyar da aka shirya a falon. Ta tashi ta shiga daki Aliyu ya bita.

Tun suna magana a hankali har ya zamanto na fara jin abin da suke fadi. Ita Yaya Rabi ana jin abin da take fadi amma shi Aliyu a hankali yake maganar. Da farko kunnuwa na ba su yadda da abin da suke ji ba, ya yin da zuciya ta ta yi mini kunci ta rika bugawa uku uku, idanuwana suka lullube don tsananin bakin ciki. Ga hadari ya babbako saboda tsananin duhun hadari sai mutum, ya dauka karfe tara na dare ne, amma duka-duka shidda da minti biyar. Ga abin da ya Rabi ta fadi.

“Wallahi Aliyu, a iya gaskiya na yi na’am da’ wannan yarinyar sai dai kuma kamar yadda na sha gaya maka, ni mai iya zartar da komi ce amma ba zan taba sanya kaina abin da zai jawo mini bacin ran Baba ba. Tun da na yi imani idan har na yi abin da ka ke so, to lallai Baba zai zo har cikin gidan nan ya. ci mani mutunci, kuma don dai ka ki bin ra’ayina ne da tuntuni ka hakura ka auri Dokta Mairo, daga bisani sai ka auri ita Aisya.

Hmmmm

Show More

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE