MISBAH BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

Ni dai duk da haka ina tausayin ta bana son yana

-sakata kuka nasha ganin tana kuka ko naji suna fada tana yin kuka.”

Ni dai babu ruwana yau dai sai na fada da kyar

Muhammad ya roke shi yayi shiru kada ya fada

Sannan ya yarda. .Ashe duk abin nan da suke yi akunnen Farida taje daki duba Nuren ta tarar baya nan jikin ta ya bata cewa ya fito neman Muhammad ne, ta biyo bayansa ne taji suna wannan maganár.

– .

Take taji nadamar abinda tayi wa Muhammad da

• dukkan tarin wahalar da ta dinga bashi wanda daga ita sai Allah sai shi kuma amma bai ta ba gayawa kowa ba a haka yake nunawa yana tausayin zaman da take shi da Deeni yayanta na cikin ta babu wanda ya taba nunawa yana jin ciwon abin da yake mata sai shi hasalima yayanta na ganin ita ce mai laifi bashi ba, lallai Deeni yayi mata illa ta ko ina.

Tundaga wannan lokacin tayi nadamar abinda ta yiwa Muhammad ta kira shi ta bashi hakuri a gaban Nuren da Aisha: maimakon ta ga farin ciki akan fuskarsu sai wani bata rai suka yi shi kadai ne Muhammad yayi murmushi yace babu komai Mama.

Wannan Kenan haka suka ta so ta cigaba da kula da su babu babbanci ko daya ya dawo bata da wanda tafi jituwa da shi irin Muhammad idan sun samu matsala da Deeni shine mai bata hakuri. dama haka rayuwa take ka haifa baka san wanda zai jikan ka ba naka ko na wani. Allah yasa mu dace.

Shirye shiryen komawar su makaranta suke yi a gobe komai sun gama hadashi sai gobe su dau hanya inda suke karatu a can ABU ZARIA.

Nuren Shamsu Umar na karantar LAW inda ya shiga shekararsa ta karshe a can duka duka shekarunsa Ashirin da biyu. Nuren ya dakko kamanin mahaifinsa sak wato Shamsu tundaga yanayin kamaninsa har jikin duk na mahaifinsa ne.

Yayin da Muhammad Mislihu yake karantar

Madicine wanda Deeni ne da kansa yace ga abinda zai karanta don ya zama ya gado mahaifinsa da mahaifiyarsa da kuma shi kansa Deeni a yanzu shima yana shekararsa ta hudu a nan ABU din shida Aisha suna SAMARU yayi da shi Nuren yake can Congo.

Aisha Shamsu Umar ita ma tana science din take

Phamarcy take karanta a yanzu haka wannan komawar da zasu yi ne zata shiga Level two. Aisha kana ganin ta ka ga Farida futuk sai da yanayin jinni da kaga Nuren zaka san yayanta ne domin wani lokaci suna diban kama.

Haka suka taso komai nasu a hade abokan juna koda yaushe tare suke gida guda DR. Deeni ya kama musu nan cikin garin Zaria ya kuma basu mota idan sun tashi tsakanin su wanda zai gama lacture da wuri ranar motar a hannunsa take tsakain Nuren da Muhammad ranar shike da alhakin dakko su idan kowa yagama sai su tafi gida tare. haka dai suke rayuwar su cikin hadin kai da kaunar juna babu mai jin kansu.

Washegari suka tattara suka taho makaranta suka bar iyayensu Deeni da Farida. wanda Farida taji gidan ya dai na mata dadi dama walwalarta idan yara sun dawo hutu suna tafiya kuwa za su dawo kamar da kowa yana harkokinsa shi kadai wandà dama tuni suka saba har yau babu canji sai dai hakkin aure Deeni baya wasa da shi mu’amala ta wani soyayya da nuna SABO DA JUNA tun tuni suka haramtawa junansu kowa hakuri yake da dan’ uwansa. can Gombe Aisha ne ta kasa zaune ta

kasa tsaye na murnar tafiyarta makaranta inda ta samu Admission a can ABU ZARIA. Inda take burin zama likita. A yanzu Aisha Nuraddeen Umar ta zama budurwa a yanzu tana daf da shiga shekarunta na shashida tsananin basirarta da kwakawalwa da take da shi da kuma samun makaranta mai kyau shine ya janyo mata shiga jami’a da wuri saboda

Foundation da ta samu. gashi da dan banzan kokarin da take dashi a makaranta wannan yasa tun tana Ss2 aka gwada ta ta zana WEAC da NECO sai gashi cikin ikon Allah duk cikin daliban ita ce ta biyu a jerin da suka fi kowa result mai kyau. ga kuma JAMB taci da kyau don haka yasa tayi saurin shiga jami’ a kafin shekarunta su cika shashida.

Ga kuma wani irin girma da tayi bana shekarunta ba kawai jin dadine da kwanciyar hankali. tsananin kamar ta da Deeni kuwa sai dada bayyana yake a tare da ita sai kawai fatarta da sumar kanta duk irin na Bahijja ne.

Shi ma Muhammad Umar ma a A.B.U. yake karatunsa.

DR. Bahijja ne ta shigo falon ta sameta wanda idan ka dubeta babu wanda zai ce ita ce ta haifeta kamar yaya da kanwa suke maganar gaskiya Allah ya bawa Bahijja jiki mai kyau da kuma sura da wuya ka ganta kai tsaye ka canki shekarunta.

Bahijja tace “Aisha naga almar ba zaki iya saka komai a bakin ki ba, sai wani doki da zumudi kike tayi kamar ma so kike ki tafi ki barmu nu kadai muke nuna damuwar tafiyarki.”

Murmushi tayi tace “Haba Mama ya zaki ce haka kawai ni kadai nake jin abinda nake ji, Mama wannan shine lokaci na farko da zan yi wata tafiya mai nisa da zan barku wanda ban taba yi ba a rayuwana ba sababa kuma na tabbata zan shiga damuwa idan bana ganinku.

Wannan murnar da dokin da kika ga ina yi bana komai bane na son zuwane naga sabbin

AL’UMMA da ban taba gani bane ban kuma taba rayuwa da suba zan je na gani nasan zan koyi darasi daban daban zan koyi iya zama da mutum sanin halin mutum zan rayu da kabilu daban wanda ma ban taba tunanin gani ba. Mama wannan shine dokina da zumudina amma tunaninku da kewarku sunanan makale a kasan zuciyata na boye ne kawai.” Bahijja tayi murmushi ta ji dadin kalamanta, ta kalli diyarta ta kara jin sonta da kaunarta a ranta. nan tace “Kin yi gaskiya jami a gurin daukar darasi ne kala kala sai yadda kika tsara rayuwarki zaki gudanar da ita, har kullum ina son ki zama mace mai kamun kai ki duba karancin shekarun da kike tare da su ki mutunta kanki ki zama yarinya ta gari bana son ki canza hali ki kula da kanki da ibada bana son kina sakaci da sallah duk mai kike yi idan lokacin sallah yayi ki ajje ki yi kamar yadda na hure ki a nan gida.

Bana son kula kawaye ko kadan domin suneke canza ma mutum tarbiyyar da kazo da ita daga

Hmmm

Show More

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE