KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 20 BY JAMILA UMAR TANKO

tsince su kaga halin da zasu shiga ka garzayo ka fada min don in tsawatar ba karamar gaunarmu kake yi ba. Na yarda da tsananin tsoronka, saka ido akan tarbiyyar iyalinka. Na yi sha’awar hada zuri’ata da taka ba don komai ba, ko don wani abu ba sai don saboda Allah. Idan kana gain baka da ra’ayin kara aure ko baka da ra’ayi akan Sajida kar ka boye min Bakura ka fada min, wannan magana muke ta fahimta.

Na yarda a cikin jama’arka ko daga cikin abokanka zuwa yaran gidanka ko Malaman masallacin gofar gidanka ka zabi mai hankali, mai addini mai tsoron Allah ka bashi Sajida. Na mince maka na san ba za ka cuce mu ba, ko ina raye ko ina a mace.

„Sajida ‘yarka ce, kanwarka ce ka dauke ta tamkar Zahra.” Bakura yayi shiru kansa a sunkuye a kasa kamar wanda

aka saka igiya aka daure shi tamau ko yatsa baya iya dagawa saboda rikirkitaccen tunanin, kwakwalwarsa ta kasa warwarewa.

Malam ya ci gaba da cewa “wanda zai auri Saida ba na bukatar ya kawo min komai in banda sadaki. Sadakin ma kalilan ya isa kamar yadda sharia ta yarda, ina da filina anan ringi road zan saka shi a kasuwa in sayar na san zai isa in yi mata gado da yan kujeru da zannuwan daurawa. Me kuma ake nema a rayuwar aure dai? Burina a killace min ita ta zauna lafiya ta cire ranta daga kan dan iskan yaron nan. Na fada ma ta nan da sati guda zanyi ma ta miji ko ta na so ko bata so, nan da wata guda ayi biki. Hankalina bai kwanta da masu zuwa wajena ba ne.

Da yawa sun sha nuna min su na son auren Saida na qi amincewa saboda ban yarda da rikon da za su yi mata ba haka ina tantama da tarbiyarsu. Kudi ba komai ba ne, mutunci shine ya fi komai. Ko dan dakon da yake neman halalinsa mai tsoron Allah, wanda ya san Allah ya san yadda zai bautawa Allah mai ilimin addini, wannan mutum shi ya fi cancanta a zauna da shi ba mai kudin da yake takama yana da kudi ba don haka yake ganin yafi karfin ya bautawa Allah ba.”

Bakura har yanzu kalma guda daya ta gagari bakinsa ya na kallo, yana sauraron Malam babu abinda yake sai kada kai alamar yana gasgata zancen Malam.

Daga karshe malam ya ce “na baka wuka, na baka nama Bakura ka je kayi tunani nan da sati-biyu ka zartar da duk hukuncin da ka ga yayi daidai akan ‘yata Sajida.” Ba tare da Bakura ya furta wata kalma ba ya mike zuwa wajen motarsa. Malam ya raka shi har jikin mota yana maiyi masa addu’ar Allah Ya kai shi gida lafiya. Bakura ya duga ya cewa malam “na gode malam, zan tafi sai kuma gobe idan Allah Ya kaimu.”

Ya shiga motarsa ya ja ya tafi. Malam ya dawo kofar

gida ya ci gaba da tunanin shin wacce shawara Bakura zai yanke akan Sajida? Bakura kuwa tsabar tunani sau biyu yana shiga layin

daba layin gidansa ba, bayan fadawa a ramuka da kwatoci ba adadi. Ya rasa abinda zai zaba wanda yafi cancanta a ciki game da Sajida. Na farko a sanadiyyar tsanananin kamar da sajida take yi da Zuhuriyyarsa ya

ji baya gajiya da kallonta tamkar wata talabijin haka Idan ya tuna tsantsar rashin kunyar Sajida sai ya ji gabansa ya fadi saboda shi yana da kunya kuma baya son ayi masa rashin kunya.

Kalmar farko da Sajida ta fara furta masa ido da ido

tawa Bakura ita ce “na tsaneka.”

Dan haka babu tantama wanna tsanar tana nan a

dauwame a cikin ranta babu mai goge ta. Zahra yarinya garama ba ta san Sajida ba amma har ta gane halin Sajida bashi da kyau a take ta ce bana son Sajida bata da tarbiyya. Ga matarsa mai tsananin kishi muddin ta sami labarin Bakura zai kara aure tabbas zata iya hadiyar zuciya, ta suma idan ma bata zarce gaba daya ba.

Bakura ya sake Juyawa ya dubi amintar da take tsakaninsa da mahaifin Sajida Malam Yakubu ya san zai ji nauyin ya ce masa baya son ‘yarsa. Yaya za’ayi kenan? Sajida ta zame masa kadangaren bakin tulu.

*******

Washegari da yamma Bakura ya koma daukar karatu gidan Malam, har suka yi hira suka gama babu wanda a cikinsu yayi maganar Sajida. Sai dai sun sha hirarsu har Bakura ya shaidawa Malam cewar sati na sama ba zai sami damar zuwa ba saboda zai je Abuja kuma a kalla zai yi kwanaki goma a can.

Malam yayi addu’ar Allah ya kai shi lafiya ya dawo da shi lafiya ya samo abinda ya je nema.

Bakura ya gyara zama ya ce “Malam ka san ina harkar

man fetir, ina da gidajen mai kala-kala a garin nan da super market wato

ZUHURIYYA STORE da ZUHURIYYA PETROLIEUM STATION. Shekaru biyu da suka wuce na bude branch a Kaduna, yanzu kuma uwargidana Samira na gina

-babbar plaza – Abuja.

“A unguwar gwarumpa mai suna ZUHURIYYA PLAZA. To shine zan je ayi bikin budewa.”

Malam ya gyada kai ya ce “au kai ne mai gidan man

nan zuhuriyya? Yanzu zaka bude a Abuja kuma?

Bakura ya ce “Eh, plaza ce, ma’ana qatan gini ne mai hawa-hawa har hawa hudu kowanne hawa akwai kantina manya-manya guda hamsim ka ga kantina dari biyu da hamsin kenan.

Kantina hamsim na kasa duk ni zan zuba kaya amma hawa na daya zuwa na hudu dukka haya zan bayar shine, zan je ayi bikin budewa. Malam ya gyada kai yace “wane mutum, ikon Allah. Kantina maka-maka har guda dari biyu da hamsim a waje daya wannan ai itace kasuwar duniya.”

‘ Bakura ya bushe da dariya ya ce “haba kasuwar duniya, sai dai kasuwar uguwar dai.”

Malam ya ce “wanne irin bikin budewa kuma za’ayi?”

Bakura ya ce “ni da matata da ya’yana da abokaina da matansu da ‘ya’yansu ne zamu had mu je wani hotel mai tsada mu ci abinci a yanka kek.”

Malam yayi dariya ya ce “ka ga turawa ‘yan boko. yanzu meye amfanin a yanka kek ayi tafi ayi dogon turanci, ina aibarka take? Shawarar da zan baka

Bakura shine kar ka tara jama’a ana wani yanke-yanken kek bai yi tsari ba ace ka hada matarka ta aure da wasu mazan ana cin abinci ga ‘yarka baliga a cikin maza, abokanka ba muharramansu ba ne. ka kalli matar wani a kalli matarka wanda yake haramun ne.

Me zai hana ka dibi mahaddatan alkur’ani daga masallacinka su bazu cikin shagunan su sassauke kur’anai a ciki da zummar Allah Ya kawo ciniki, da kariya daga sharrin barayi da ‘yan damfara.

Matarka kuwa da ‘ya’yanka ba’a hanasu su taya ka murna ba sai suyi tasu liyafar a cikin gida iyakacinsu mata kadai su gaiyaci yan’uwa da abokan arziki su zo su ci, su sha, ayi karatun kur’ani.

Ka dauko mace tayi musu wa’azi a cikin gida. Haka baifi ba?” Bakura ya gyada kai ya ce “gaskiya ne Malam, tabbas na yarda cewa abinda da babba ya hango daga zaune yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango ba. Sai dai ina neman wata alfarma a wajenka Malam. Babu wanda ya fi cancanta ya je. ayi saukar nan sai kai da almajiranka.”

Malam ya girgiza kai ya ce “a’a tunda ka na da naka malaman da almajiran ai su suka fi cancanta su je bani ba. Ni fa ban taba zuwa Abuja ba, idan aka ce za’a kashe ni akan sai na nuna hanyar Abuja to sai dai a kashe ni ban san inda take ba. Ga tsufa ina zan iya jure zaman mota daga Kano zuwa Abuja?”

Bakura ya ce “zaman mota ba matsala ba ne daman da jirgi zamu tafi. Zancen cancanta kuwa KAI KA FI CANCANTA kayi min saukar-kur’ani saboda bajintar dake tsakanin mu. Zan iya samun daci da quna a cikin zuciyata idan ka bijirewa bakata.”

.Malam yayi shiru ya na dan murmushin jin dadi ya nisa sannan ya ce “Bakura babu wata bugata da zaka nema in qiyi maka ita. Ba damuwa zan baka yardaddun almajiraina dana yarda da kwazonsu su je suyi maka sauka ko ta kwana nawa ce sai dai ina so in ja hakalinka karka biya su kudin aikin da suka yi maka, Baya da ci da sha ba ma bugatar ka basu wasu kudi na daban domin tsakanina da kai babu wannan.

Bakura yayi murmushi ya ce “Malam har yanzu baka yi

min abinda nake so ba, zan so tafiyar

nan a tafi da kai don kasa min albarka da bakinka.”

Malam yayi dariya ya ce “to shikenan Bakura ba zan qi zuwa ba tunda zuwan zai gara maka farin ciki.”

Bakura ya ji dadi sosai ya tsayar da ranar tafiya, nan da kwanaki uku su shirya zai sa a zo a dauke su zuwa filin jirgin sama zasu acan Abujar zasu same shi don shi washegari zai tafi.

Kamar yadda Malam ya bashi shawara haka Bakura ya umarci iyalansa su aiwatar, wato su hada walimarsu a gida mata kadai ba sai sun bi shi Abuja ba.

Ya bawa Samira da yaransa izinin su je Zuhuriyya super market dinsa su dibi duk abinda suke bugata komai yawansa, komin tsadarsa daga naira daya zuwa naira million daya ya yarda su kashe. Su gayyaci kowa da kowa daga kan masu kudi zuwa talakawa a dangi da makwabta.

Ya umarce su da su ware abinci tukunya daban wacce za’a tara almajirai a gofar gida a rabar sadaka saboda Allah. Sannan Bakura ya tafi Abuja, bayan tafiyarsa da kwana biyu yayi waya Kano ya ce direbansa ya kwaso Malam yakubu da almajiransa guda goma zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu

Kano suka hau jirgi zuwa birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda aka yi a kano a Abuja ma Bakura yana da gida da direbobinsa don haka tun kafin su Malam su sauka daga jirgi direbansa ya zo yana jiransu.

“Su na sauka daga jirgi ya kwaso su ya kawo su gida. Bayan sun gama hutawa a kwana daya washegari suka kama karatu a cikin plaza, suka yi ta saukewa qur’ani su a maimaitawa.

** *******

Zahra da mahaifiyarta Samira kuwa su na kano Su na ta faman shirye-shiryen walima. Don karfin hali har wani dan karamin katin gayyata Zahra ta buga ta rarrabawa qawayenta na makaranta.

Ranar asabar ne ranar da za’ayi walimar. Don haka ranar Juma’a da yamma washegarin ranar da za’ayi. Samira ta iske Zahra a falonta a zaune ta na kallo. Ta ce da ita ta je Zuhuriyya super market ta hado mata kayan qamshin girki (spices) kamar curry, thyme, dakekkiyar citta da dai sauransu.

Zahra ta shirya tsaf ta fito caras sanye take da wani

dandantsetsen leshinta shudi any masa zanen fulawa ruwan goro. kallo daya za ka yiwa leshin ka gasgata tsadarsa duk da daman dallar aka siyi …leshin idan aka kiyasta kudinsa zai kai Naira dubu dari da tamanin.

Kwararren telan da ya sarrafa dinkin leshin da ace gasar America zata sami labarinsa data dauke shi aiki a kamfanin dinka kaya (English wears).

Domin idan ka kalli kayan a jikin zahra sai ka rantse daga kamfani leshin ya fito a dinke. Yankan siket din das a jikinta haka rigar, abinka da marar jiki, doguwa santaleliya kai ka ce taliya ce ke nutso a cikin ruwan zafi, idan Zahra ta na tafiya. Duk da tsayin da Allah yayi mata ta qara da wani cogen takalmi mai tinin gaske a gafarta shima takalmin kalar ruwan goro ne. Ta nada daurin dankwali a gaban goshi, gashi keyarta kuwa lallausa mai laushi ne ta tufke shi da ribbon ruwan goro. Ta dauki dan siririn mayafi ta yafa a jikinta. Ta na rike da mukullin mota a

hannunta. Samira ta dubi Zahra ta yi murmushi ta ce “baby kinyi kyau yau Sosai. Ko za ki bar leshin nan gobe ki saka? Kamar zai fi na gobe kyau.”

Zahra ta ce “a’a mama kin manta kudinsu ne? Ai yellow da zan saka gobe ya fi wannan tsada kudinsa da na kiyasta naira dubu dari biyu ne da hamsim wannan kuwa dmdubu dari da tamanin ne. Kin ga ai ba kudinsu daya ba. Allah Ya kaimu goben shima za ki ga yadda zai yi min

• kyau.” Samira ta ce “Magaji deriba ne zai kai ki ko?”

Zahra ta ce ” sabuwar motarki Discussion continues zan tuga da kaina.”

Samira ta ce “ba wai ban yarda da tukinginki ba ne amma fa har vau mahaifinki bai san kin koyi tuki ba, kada ki je wani abu ya faru

Allah ma Ya kiyaye ya ce yaya aka yi ma ki ka fita ke kadai?”

Zahra ta ce “Allah ma Zai kiyaye yanzu zan je na dawo.”Samira te ce “Allah ya kiyaye mamana.”

Zahra ta saka bakin gilashinta saboda hasken gari, ta sakala hands free a kunnuwanta saboda amsa waya, ta shiga tsaliliyar motar nan

-mai launin silver nufi ZUHURIYYA SUPER MARKET.

_Daf da kofar Zuhuriyya Surper Market ta ja ta tsaya a inda ta dubi gefanta wata bagar mota ce qirar Brama mai bakin gilashi, ko kafi quda na ci ba za ka iya hango abinda yake ciki ba.Tabbas it ma motar ta hadu domin irin sautin kidan da yake

tashi daga cikin motar da irin daukar idon da motar ke yi saboda da shegi.

Kamar yadda shekin motar Zahra take daukar idanuwan masu kallonta har ‘yar karamar rigima ce ta tashi tsakanin saurayi da buduwar da ke cikin motar saboda yadda yake kallon Zahra har da lege.

Ba tare da Zahrar ta san abinda ke gudana ba.

Zahra ta yunkura ta fito daga cikin motar in da ta danna remote alamar ta rufe motar. Ta na fitowa ta fuskanci wasu’yan mata guda biyu sun fito daga cikin wannan bagar motar, daya daga gaba ta fito daya kuma daga gidan baya.

“Yan matan dukkansu sanye suke da wandon

jeans da riga iya gwaiwarsu, sai dan gyale yalolo a magale a kansu da cogen takalma a gafafuwansu. Nan da nan suka dunguma tare da Zahra suka shiga cikin Super market din. Daga yadda ‘yan matan nan biyu suka ga ma’aikanta super market su na dukawa Zahra su na kwasar gaisuwa Hajiya sama Hajiya kasa sun san tabbas yarinyar nan ‘yar wani ce a gasar nan. Inda su ka sake tabbatar da hakan sai sanda suka ji ta umarci daya daga cikin ma’ aikatan cewar ya samu leda ya je ya zabo mata spicês kala-kala masu gamshi daban-daban kamar roba ashirin ya kai mata

mota.Yan matan biyu sun ci gaba da zazzagayawa su na zazzabar abinda suke so. Kicibus su ka yi da Zahra a daidai kantar greeting cards.

  • Yayin- da su dukka ukun suka dugufa wajen karantawa don su zabi wanda yayi dai-dai da kalaman da suke buqata, kamar daga sama Kunnuwan Zahra su ka jiyo mata daya daga cikin ‘yan matan ta ce da dayar. ” Iyayye, kin ga wani kati wanda yayi daidai da wanda zan bawa Abdulmajid.” Jin sunan Abdulmajid ne ya sawa Zahra wata mummunar faduwar gaba ta dago da sauri ta dubi mai maganar. Zahra ta zare bakin gilashin dake fuskarta ta dube ta sosai inda ita ma mai maganar ta tsaya cak ta na duban Zahra yayin da su ka dauki ‘yan dakikai ba su daina kallon juna ba kowa ya na gogarin tuno inda ya san wannan fuskar.
  • Lokaci guda kwakwalwarsu ta sanar musu cewa wannan Zahra ce, Kwakwalwar Zahra ta sanar mata wannan Sajida ce: Qara-gara- ga-qa; ga Zahra, ga Sajida. Ya za’ayi kenan!?ba?”

Zahra ta yi murmushi ta ce “kamar na sanki, ba ke ce Sajida ba Cikin gadara Sajida ta ce “Sajimajid ce, kwarai ashe kin tuna ni kamar yadda na tuna ki Zahra. Ina neman ki daman tamkar ruwa a jallo. Na dade ina addu’ ar Allah ya nuna min irin wannan rana.”

Sai Zahra ta ji gabanta ya yanke ya fadi kan ka ce kwabo

zuciyarta ta fara harbawa tana dukan uku- uku.

Ta tambayi Sajida cikin kidemewa “me ya faru?” Sajida ta yi murmushin mugunta ta dubi kawarta lyayye ta ce “ki taya ni duban

Hmmm

Show More

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE