KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 19 BY JAMILA UMAR TANKO

da yan’ uwanki da duk wani mai sonki cikin, damuwa da bacin rai dauwamammiya. Idan kika gudu kin tashe mu tsaye musamman ni da mahaifinki, zaki tasar mana da ciwon da zaj iya zama ajalinmu.

Ga mahaifinki ya tsufa ruf daya zuciyarsa zatà iya fashewa, nima gashi girma ya zo kece abokiyar shawarata tamkar gawata nake hira dake ga dan karamin kaninki yahuza duk inda ya fita ya samo

• labari wajenki yake nufowa kai tsaye ya fesa miki. Idan kika tafi kika bar mu yaya zamu yi?”

Ummma furera ta fashe da kuka. Sajida ma kukan ya kece mata. Har tsawon lokaci babu mai iya lallashin wani. Sajida ta dago da jajayen idanuwanta ta dubi mahaifiyarya.

Ta ce “Umma, ina tunanin yarinyar nan Zahra da ta zo

kwanakin baya, turo ta aka yi ta zo taga halinda nake ciki da Abdulmajid ta kai rahoto domin ita tasan ina lekawa ta katanga ina aron waya in bugawa Abdulmajid.”

Umma furera ta tsagaita da kukan ta dubi Sajida

fuskarta cike da rudani. Tayi doguwar ajiyar zuciya.

Ta ce “Sajida ban fahimce ki ba. Wacce yarinya kike magana?”

Sajida ta ce “Zahrar nan wacce Baba ya shigo da ita.

kwananakin baya ya ce-*yar gidan mai daukar karatu ce a kofar gida. Har na ari wayarta na bugawa Abdulmajid. A dalilin bamu bata kunu ba Baba ya hana ki yin kunun siyarwa har sati guda.”

Umma Furera ta ce “kwarai kuwa na tuno ta tabbas anyi haka. Ba lallai ba ne ita ta fada amma akwai alamar tambaya. Da farko ma a ina ya santa har zai kawo ta ya tafi ya barta a cikin gida? Na biyu bayan tafiyarta ne ya shigo yayi miki wannan dukan har muka dauki alhakin Yahuza. To ko budurwa Abdulmajid ce take bibiyarki don ta san ya fi sonki, Ko daman ita take hada miki tuggu don babanki ya raba ku duk motsin da ki kayi da Abdulmajid sai an fadawa mahaifinki?”

Sajida ta girgiza kai ta ce “Abdulmajid bashi da

budurwa, ni kadai ce budurwarsa a duniya haka ni kadai ya taba so kuma yayi min alkawari har karshen rayuwarsa ba zai taba son wata ‘ya mace ba. Yayi min

rantsuwa tun sanda ya hadu dani bai taba jin yana son wata ba. Umma, wallahi na rantse da ubangijin daya halicce ni tunda Zahra ta zo har gida tayi min gulma tayi min sanadiyyar da na daina samun damar yin magana da Abdulmajid a waya har tsawon wata guda kenan. Asanadiyyar wanna na daina cin abinci, na daina bacci sai kuka, ga zazzabi da ciwon kai. Na yi alkawari duk ramar da na yi ido hudu da Zahra sai nayi mata rashin mutuncin

“da’ ban taba yiwa kowa ba Idan ma son

Abdulmajid take ko a dangin Abdulmajid take daman da yawansu basa sona hakika sai na nakasta ta, nakasar da itama nata sauranyin zai daina sonta ta ji yadda nake ji data rabani da nawa masoyin.

Umma furera ta rike baki ta ce “a’a Sajida kada ki jawo

mana abinda za a maka mu a kotu daga mu har ke. Kada kiyi kisan da saki jawo a kashe ki a dalilin wani Abdulmajid. kinga yarinyar nan daga gani ‘yar gidan masu kudi ce, ko bata da gaskiya ubanta ya na da halin da zai fada aji a hukunta mu balle ma ki nakasta ta ko ina aka je ke ce marar gaskiya. Sajida ina raba ki da wannan banzar zuciyar taki, saurin fushi da yawan dacin rai, tsiwa da futsara.”

Sajida ta hasala ta mike tsaye tana gatsine, tana murguda baki, tana zare ido irin na tsantsar fitsarar da ta saba. Ta ce “Umma, me naji kina cewa? Kina nufin in hadu da Zahra ta wuce in wuce ban tanka mata ba? Haba ashe ba’a haifeni da jini ba, daga sama na fado. Don ubanta yana da kudi sai tayi min laifi in kyaleta? Wallahi na yarda in dauwama a daure a kurkuku har karshen rayuwata da in zubawa makiyiyata ido. Ni kuwa a rayuwata me zanyi da mutumin da baya kaunata da Abdulmajid?” Kafin Sajida ta rufe bakinta mahaifinta ya sako kai

cikin gidan, domin har kofar gida yake jiwo tsiwar

Sajida duk da cewa baya gane abunda take fada amma ya san zancen bana dadi ba ne.

Sajida na ganinsa tayi shiru amma taci gaba da harare-harerenta. Ya dubeta cikin fushi Ya ce *ke kuma hayaniyar me kikeyi kamar, kina magana da sa’arki? Mahaifiyar taki kike dagawa murya har kofar gida?”

Sajida tayi shiru tana ta fuse fusgen kai alamar ko a

mutu ko ayi rai, ayi duk wacce za’ayi wai da bera ya zubar da garin mage.

Umma furera tayi caraf

Ta ce “ah, ba wani abu ba ne malam. Zafin zazzabi ne yake sakata surutai barkatai.”

Malam ya’ ce surutan zazzabi daban haka rashin kunya daban. Nasan dalilin zazzabin nata ai shiru nayi muku kawai, a dalilin raba ta da dan iskan yaron nan Abdulmajid shine yasa take kokarin kashe kanta saboda taurin kai irin nata. To bari kiji in fada miki Sajida ko ki warware ki ci gaba da walwalar ki, ko ki ci gaba da takura kanki cikin kunci ki hadiyi zuciya ki mutu a wajena duk daya ne kuma ina nan akan bakata har abada ba zaki sake haduwa da Abdulmajid ba balle ya lalata ki, daman ba aurenki zai yi ba.” Sajida ta fusata ta murguda baki ta fada cikin tsiwa “an

takurawa rayuwata a gidan nan, gara in mutu ma in huta. Haka kawai kowacce yarinya ana barinta ta kula wanda take so sai ni za’a takurawa. An kulle ni a gida, an hana ni karatu, an hanani fita makarantar Islamiyya da makarantar dare sai duka da zagi

• Kullum ba kakkautawa..”

Ba ta rufe bakinta ba ta ga- ya wurgo tabarya ta gefen

fuskarta, saura kiris ta same ta a kunci. Malam ne a fusace ya wawuro tabaryar ya wurgo mata bai damu da ko zai fasa mata kai koma ya kasheta ba. Da turmin zai cicciba ya wurga mata, yaji da nauyi ba zai ya dauka ba.

Ihun Umma Furera ne ya gara tunzura shi ya ji dama ace ya same ta tayi ihun da hujja.

Sajida ta zura da gudu ta shige dakinta da gudu ta

sakale da sakata. Malam na huci yana ta “har fitsarar taki ta dawo kaina ina fada kina fada saboda kin raina kowa. To wallahi ba’a gidana ba, inyi wahala dake tun da aka haifeki zuwa girma sannan kice ban isa in fada miki ki ji ba to sai dai idan ba’a karkashina kike. ba ki tattara kayanki ki tafi kiyi zaman kanki tunda kina ganin ke kika haifi kanki, kin girma kinfi karfin kowa. Ni kuwa idan ni na haifeki kuma da sauran numfashina a duniya wallah ba zaki auri Abdulmajid ba ko zaki mutu.

Ya juva ya dubi furera ya ce “ke ce uwar banza da ba kya tsawatarwa ‘yarki. Banga amfanin zama da ke ba tunda ya’ya biyu kin kasa ba su tarbiyya da sun kai guda goma ma ban san tabarar da za’ayi min a gidan nan ba. To bari in fada miki zamanki a gidan nan ya kusa karewa, ke ki rasa aurenki itama ta rasa Abdulmajid din kuyi biyu babu. Dan haka kisa ido, idan na sake jin maganar dan iskan yaron nan Abdulmajid a gidan nan zaku ga yadda zanyi muku. Sajida albishirinki a cikin satin nan zan yi miki miji ko kina so ko bakya so shi zaki aura kuma dole ki zauna, ba zaki sake yin wata guda a gidana ba insha Allah”

Ya Kade babbar rigarsa ya fice yana huci ya bar umma furera a takure a lung ta buga tagumi. Zuciyarta sai dukan uku-uku take saboda tashin hankali. Yayin da Sajida ta kwalla ihu ta fada kan katifa tana rusa kuka kamar ranta zai fita. Umma furera tayi ta buga kofa tana magiya Sajida ta gi

bude kofa. Sai da tayi kuka ta gaji da kanta sannan ta bude kofar. Umma furera ta shiga lallashinta akan ta daure ta ci abinci amma Sajida taqi ci.

Bakura ya iso kofar gidan Malam Yakubu daf da

magariba kamar yadda ya saba zuwa. Ya iske™ Malam tare da dalibansa wato manyan mazan da suke daukar karatu tsakanin sallar magarib da isha’i. Kamar yadda su ka saba bayan sun idar da sallar magariba sai suka shiga daukar karatu, har zuwa lokacin

– da Isha’i ta yi, su na idarwa sai kowa ya watse.

Bakura da Malam ne kadai su ka rage. Hira suke kamar abokai, hirar dai ba ta wuce hirar siyasa ba. Da aka fito da abinci sai Bakura ya nemi afuwa akan yau dai sai dai Malam ya yi masa hakuri ba zai ci abinci ba saboda duk randa ya je gida cikinsa a goshe rigima ake da uwargida.

Malam yayi dariya ya ce “kwarai kuwa na fahimce ka,

mata su na da wannan dabi’ar. “

Malam ya bude kwanon tuwo da miya kamar kullum

tuwon tsari da miyar busashshi kubewa ce babu nama a cikin miyar sai dai qamshin wake da daddawa ne ya ke tashi. Bakura yana hira ya na satar kallon Malam. Tausayinsu ya rufe shi ya shiga sake-saken yadda zai taimakawa wadannan bayin Allah. Sai ya yanke shawara a ransa in dai ya tashi tafiya yau zai yiwa Malam alkawarin wani kudi mai tsoka da buhunhunan abinci wanda zai agaza masa wajen samu ya ciyar da iyalinsa da abinci mai kyau.

Malam cin abincinsa yake kai kace ba garau- garau yake ci ba kamar wanda yake cin naman talo-talo.

Malam ya gyara zama ya dubi Bakura ya ce “Alh.

Babura na yaba da hankalinka, ka zama tamkar d’a na cikina ko in ce dan uwana na jini. Na yarda da kai sosai ina so ka bani shawarar da zata amfane ni. Bakura ina so ka tsaya cikin nutsuwa ka bani shawara akan wata matsala da ta addabe ni”

Bakura yayi quri yana duban Malam zuciyarsa cike da

tsananin mamaki ya na tambayar kansa shin wacce irin alfarma ce haka Malam yake nema a wajensa yake jero irin wandannan kalamai?

Malam ya ci gaba da cewa “Bakura, ka bani shawara

akan Sajida.”Shawara akan Sajida?” Bakura ya tamabaya cikin murya mai tafe da tsananin mamaki. Ya gara da cewa “me yake faruwa ne game da Sajida?”Malam ya nisa ya ce “so nake in aurar da Sajida domin in sami nutsuwa da kwanciyar hankali. Saboda yaron nan Abdulmajid ba zai barta ba. Kuma duk garin nan kowa ya san ba aurenta zai yi ba lalata ta yake niyyar yi. A dalilinsa na hana ta karatu, a dalilinsa na hana ta fita amma duk da haka basu rabu da juna ba kwanciyar hankalina shine kawai in sami wani babba mai hankali wanda zai riqe min Sajida a matsayin matarsa. Wallahi Bakura ko baccin kirki bana iya yi saboda kullum gani na ke Sajida zata bude kofa cikin dare ta je wajen Abdulmajid.”

Bakura yayi shiru kamar wanda ruwa ya cine ya rasa

abunda zai ce. Can ya misa ya dubi Malam ya ce- “bayan Abdulmaiid akwai wasu masu neman ta?”

Malam ya girgiza kai ya ce bayan Abdulmajid ba ta tsayawa da kowa. Akwai wani mai naci da ya qi tafiya duk wulakancin da za tayi masa baya fasa zuwa shima yanzu ya hakura ya daina zuwa. Yanzu al’amarin Sajida ya kai ya kawo akan

Abdulmajid za ta iya rufe ido tayi tsiwa a gabana ta ce babu mai hanata auren Abdul Abdulmajid.”

Sai hawaye ya surnano daga idanuwan Malam.

Hankalin Bakura yayi mutuwar tashi yayi shiru ya na tunanin irin shawarar da zai bawa Malam a matsayinsa na mai ilmi

Malam ne ya katsewa Bakura tunani, ya ci gaba da

cewa “ranar wanka ba’a boyen cibi. Bakura,

-KAI KA FI CANCANTA ka auri Sajida.”.

Jin wannan kalma ta fito daga bakin Malam sai ya ji tamkar an harba bindiga a kirjinsa, ya ji kamar wani abu ya harba a cikin zuciyarsa saboda firgicewa. Ya dago da’ sauri ya dubi Malam, duba irin na rashin fahimtar abunda yake nufi.

Malam ya dubi Bakura duba na fuska da fuska. Ya ce “kai nake so ka auri yata Sajida idan kayi haka ba karamin jahadi kayi ba, ka taimaki rayuwarta ka taimaki rayuwata ni ubanta. Babu wanda ya fi ka sanin illar haduwar Sajida da Abdul majid. Saboda a hanya ka

Hmmmm

Show More

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE