ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 31 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Sai da muka ji maganar mutane suna cewa,

“Ya ya dai yallabai bakuji ciwo ba ko?” Sannan ya ce, “Wallahi wani mahaukaci ne ya gifta ta gabamu, saura kadan na taka shi”.

Nayi ajiyar zuciya, sannan na zare jikina daga jikinsa na koma mazaunina, na hada kai da. gwiwa ina mai karantu addu’a a raina har muka isa shi ke nan babu wanda ya ce uflan. A nan ya fita ya sawo mana ruwa, yazo ya bani na sha, sannan ya sha muka zauna shiru zuwa can ya ce, “Har yanzu jikinki na rawa”

. Na ce, “Ya dan rage kadan

Sai ya rika bani labarin ban dariya har hankalina ya dan kwanta, sannan muka isa Zariya.

To yanzu na samu haske daga Zahra’u da Aliyu a kan Aminu, sai na ji zuciyata ta yi mani Kuna, na ce,

“Insha Allah ba zai yi nasara a kaina ba”

  • Lokacin da muka isa Malumfashi mahaifina na gida, bayan mun yi masu gaisuwa har za mu shige Kuka-Sheka sai Inna ta ce, “Har kun shiga
  •   wajen Inna Hafsatu? Hadiza ma tazo jiya yau da safe Aminu ya wuce da ita Katsina”
  •   Na ce, “Inna a ce muna gai da ita wallahi sauri muke yi yau Aliyu zai wuce Kano”

Zahra’u ta ce, “Asiya zancen banza kike yi, wane irin sauri zai hana mu shiga wajen Inna?” Muka shiga ba don raina ya so. ba, muka gaisa, sai na lura da wasu saitin akwatuna har saiti biyu, da masu ruwan bula da masu ruwan zuma wato guda shida. ke nan.

Can gefe kuma ga wasu guda biyu masu ja, sai mai rawul gida daya irin wanda ya bani. Sai na yi

haka?”murmushi na ce, “Kai Inna duk tsarabar taku ce

Ta ce, “Uhm! Wannar ba tawa ba ce wai don . shirme ba a sami matar ba, amma wai an hado lefen

aure”Zahra’u ta ce, “Inna ai ba shirme bane yana da gaskiya, idan ya ce a nan zai saya zai kashe kudi kwarai”Nima na ce, “Amma ya yi farar dabara”

Ita kuma Inna ta ce,Ba don kuna sauri ba da

kun sha kallo”Na ce, “Haba Inna abin da ma ne ‘yan kai lefen, mun gani a hankali”• Muka yi dariya tare da

sallama. Mun biya Shagalinku Restaurant mun ci abincin rana, Karfe biyu ne daidai Aliyu ya wuce Kano. Muka mai da hankalin wajen karatu gadan-gadan bamu da wani lokacin hutawa.

Bani mantawa da wata rana muna kwance bisa gado daya ni da Zahra°u, mun yi karatu mun gaji, sai muka ji ana mana sallama an turo kofar an shigo, to ashe Raula ce wadda a kwanan baya Yaya Aminu ya aiko ta neman mu. Ita Raula mutuniyar Sokoto ce, ajinsu daya da Zahra’u. Da muka gama gaisawa ta nemen da in bata hotuna za ta yi kallo, bayan ta gama ta ce, “Ya ya ban ga hoton wannan yayan naki ba wanda yazo ran nan?Na ce; “Kina son ganin, hotonsa ne?” Ta yi. dariya ta ce, “Eh”. Sai Zahra’u ta tashi za ta bakin shago ta sawo mana nama.Na fiddo wá Raula hotunan Yaya Aminu, amma ban da wanda ya. dauka da yarinyarsa. Bayan ta jima tana kallonsu, sai ta ce, “Asiya a bisa amana ko za ki yarda ki yi mini arziki guda”

Na yi murmushi na ce, “Ki fada mini in zan iya zan yi mik”.Ta ce, •NI dai gaskiya tun lokacin da

Yayanki yazo na kasa sakin raina in yi karatu, ba don komi ba sai don kawai son da nake wa dan’uwan nan naki, shine na kasa daurewa zuciyata.

Idan kin san ba shi da wadda zai aura, ki taimake ni ki hadani da shi, idan ma yana da mata da ‘ya’ ya, ni dai in har zai aure ni, ina son shi ko ya ya kika

gani?” Na yi shiru, sannan na ce, “Raula kin san sha’anin aure na Allah ne, amma zan miki taimako guda daya, shine zan gayawa mahaifiyarsa kin ga saita shawarce shi idan ya amince, to amma ni ba zan iya tunkararsa da wanna maganar ba”

Ta ce, “Eh, haka ya yi daidai, amma sai ki san yadda za ki yi ‘yar dabararmu ta mata”

Na ce, “Insha Allah zan yi kokari tunda za ni

Malumfashi kwanan nan”.

Muna cikin magana Zahra’u ta dawo, muna cin nama ana Kara shirya yadda zan gayawa Inna Hafsatu.

Bayan ta tafi ne Zahra’u ta ce, “Ni kuwa Asiya bani son irin wannan sakarcin, ban da wulakanta kai mene ne abin zuwa ka ce wai a roki namiji ya so ka, idan har yana sonta ba ya ganta ba?

Kuma ke don rigimar tsiya kin daure gindin za ki taimaka”

Na ce, “Ai shi ne fa, to ya ya zan yi, sai ta dauka kamar bana sone, kin ga idan na gaya ma Inna in yana so shi ke nan, idan bai so kuma an huta, tunda mace ake matsawa ba namiji ba”.

Bayan sati da yin wannan maganar sai na sami wasikar Aliyu yana shaida mani in shirya zai zo ranar Jumma’a don mu je Malumfashi bisa daidaituwar maganar aurenmu.

Ana sauran kwana biyu mu tafi, ita kuma

Zahra u aka aiko Shehu. kanin mijinta a kan ta shirya

za a z0 daukar ta ranar, Jumma’ a saboda sunan da za’ayi ranar asabar na matar, Yaya Ahmed da ta sami

yar budurwa.

Hmmm

Show More

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE