KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 18 BY JAMILA UMAR TANKO

Ya iske Samira a falo tana tsaye, ya zo ya wuce ta da

sauri ya nufi kofar fita gami da ce mata “Mun tafi, sai mun dawo.”

Ta bi shi a baya tana masa fatan alkhairi har sai da ta ga fitarsu daga cikin gidan, Sannan ta dawo ciki, ta dawo zuciyarta cike da mamakin irin wanna hali na maigidanta. Wani murdadden mutum ne, mai rikakken ra’ayi, kamar ba yanzu ta dinga yi masa maganar rashin lafiyar Zahra ba, ya yi shiru kai ka ce da dutse take magana. Amma gashi da kansa ya shiga ya duba ta. Tayi murmushi ta Ta fada a bayyane”Malam •Bakura kenan, Kanuri na’ Samira sarkin mulki.”

Tafi-tafiya kwanaki uku kenan da Abdul majid ya fara

takurawa Zahra ta waya, , don haka kwanaki uku kenan da susucewar Zahra. A takure take ta kasa sukuni, ba ta kaunar zama a cikin ‘yan gidansu, saboda takura ma ta da Abdulmajid yake a waya. kullum tana qunshe a daki tana cutar karya. Tana ji tana gani aka kai ta asibiti aka tulo mata magunguna iri-iri tana sha, dan dolenta. Don haka take yawan kwanciya, jikinta duk kasala, sai yawan barci kullum. a kwance a daki.

La’asar sakaliya Samira da Bakura za su fita unguwa, gaisuwar mutuwa zasu je gidan wani abokin™

Bakura da mahaifiyarsa ta rasu a unguwar Na ‘ibawa. Samira. ta iske Zahra a kishingide akan doguwar kujerar falonta ta kafawa akwatin talabijin ido, amma hankalinta baya kan abin da yake gudana, babu abin da take fahimta tunaninta na kan halin da Abdulmajid ya jefa ta. Wayarta na gefenta ta saka ta a silent saboda damun da Abdulmajid yake yi mata da kira da text massages.

Samira ta dubi Zahra ta ce “Ya ya jikin naki, kin sha

magani?” Zahra ta langwabe kai ta yi magana cikin marainiyar murya ta ce “Mama da sauki.”

Samira ta dafa kanta ta ji ba zafi. Ta yi murmushin jin

dadi ta ce “Yau babu ciwon kan, na ji kan ki ba zafi. Za mu fita nida Abbanki, za mu je gaisuwa gidan su Maman Zulai yau kwana uku. Ki fito babban falo ki zauna tare da yara ki kula da masu shigowa. Ki fadawa cook abin da kike so su dafa miki, kada ki zauna da yunwa, ba’a son masu ulcer su dinga zama da yunwa.”

Zahra ta mike tsaye ta yi murmushin karfin hali.

• Ta ce “To Mama sai kin dawo.”

Su ka dunguma suka fito tare. Kafin su fito har

Bakura ya shiga mota yana jiran Samira, don haka da sauri ta fice.

Zahra ta kishingida akan doguwar kujera tana kallon

talabijin yayin da Abubakar ganninta yake Zaune akan kujerar gefenta yana kallon shi ma, ta jima kadan ya dube ta ya girgiza kai don tausayin yanayin da yaga take ciki. Ya ce,” Sister Zahra sannu.”

Ta amsa da “Yauwa.” Sauran kannenta kuwa Umar da

Usman suna farfajiyar gidan su na kwallo. A hankali a hankalin bacci mai nauyi ya kwashe Zahra. Kamar daga sama take Jiyo muryar Abubakar yana ta magana. Inda hankalinta ya sake karkata da sauraron abin da yake cewa ambaton sunanta da ta ji yana yi a hirar. Dakyar take bude idonta ta hango shi a zaune da alama waya ce a hannunsa. Abin mamakin shine tasan Abubakar• ba shi da waya. A ina ya sami waya yake ta magana tun dazu? Me yake cewa kuma da wa yake magana har yake ta ambaton Zahra, Zahra? Cikin magagin bacci ta laluba gefenta za ta dauki wayarta sai ta ji wayam babu komai. Ta zabura ta mige zaune ta dubi Abubakar ya dube ta shima. Ta tambaye shi “Wayata ce a hannunka?”

Ya gyada kai ya ce “Ita ce kina barci ake ta kira ba ki ji

ba kin saka a silent? Ya sake kara wayar a kunnansa ya cewa mutumin da suke magana a waya “hold on ga ta ma ta farka daga barcin bari in bata.”

Ya taso da sauri ya dungura mata a kunne-gami da

cewa “Sunansa Abdulmajid.”

Kafin Abdulmajid ya yi magana Zahra ta yi sauri ta

dauke wayar daga kunnenta kai ka ce garwashin wuta aka dana mata. Ta yi sauri ta katse wayar. A fusace take yi wa Abubakar magana.

Ta ce “Ba ka da hankali, ya zaka amsa waya? Ba ka san mutum ba, baka san lamba ba ka hau hira da shi. Watakila ma wrong number ya kira don ni ban san wani Abdulmajid ba.” Abubakar ya ce “Shi ya sanki har ya fadi sunanki.”Zahra tayi shiru ta kasa magana don ta rasa abinda zatace masa.

Cikin sanyin jiki tayi ajiyar zuciya. Ta ce “meya ce

maka?!Abubakar ya ce”ce min yayi ni kaninki ne, a wacce makaranta muke? In ne gidan mu?”

Zahra ta zabura ta dafe kirji ta ce “meyasa zaka bashi

address dina har ka fada masa makarantarmu?”

Abubakar ya rude gaba daya ganin yadda idanuwanta suka firfito suka cika da hawaye saboda damuwa.

Ya ce “ban fada masa ba, mun fara wayar kenan kika

farka.”Ta ji zuciyarta tayi sanyi kadan, hankalinta ya kwanta.Ta mike ta nufi dakinta dauke da wayarta a hannu. Tana shiga daki ta bude wayar ta zare sim card din ta balla shi gida biyu taje ta jefa a toilet ta kwara ruwa ya tafi. Ta dawo ta kwanta a kan gado tana huci don takaici. Can ta tuna a ranta ai kuwa tayi aikin banza da ta karkarya sim card shi kadai. Ya za’ayi ace sim card ya bata waya bata bata ba? Ai hankali ma ba zai dauka ba. Tayi zumbur ta mike zaune tana tunanin hanyar da zata bi ta salwantar da wayarta ta hanya mafi sauki ba tare da an gane ba. Da farko tayi tunanin ta jefa wayar a toilet tayi flushing; sai ta tuna ashe ba zai wuce ba zai toshe toiet din. Tayi tunanin ta je swimming pool ta jefa, Sai ta tuna ai za a tsinta idan aka tashi wanke wajen. Idan ta jefa a shara masu zubar da shara zasu tsinta su kawo. Sai ta yanke shawara ta tafi bayan Katanga ta wurgar. Da ta isa bayan katangar sai ta cire bayan wayar daban, sannan ta wurga ta cire batir din wayar ta koma wata kusurwar ta wurgar ta sake koma wata kusurwar ta wurgar da fuskar wayar. Haka ta aiwatar amma sai da ta faki idanuwan ‘yan gidan ta tabbatar babu wanda yake ganinta ta je ta wurgar ta dawo ta kwanta tana mai shakar iskar farin ciki da kwanciyar ta hankali. Ta ci gaba da tunanin karyar da zata. zabgawa iyayenta a game da batan wayarta. Ba ta damu ta fada musu ba ta san babu wanda zai yi mata fada a cikinsu. Matsalarta® su gane Abdulmajid yana yi mata waya amma ba ta batan wayarta ba, waya ba komai ba ce. Jinta take wasai tamkar ta sauke wani kaya daya dame ta da nauyi a kanta. Salwantar da wayar da tayi ta farfado mata da dumbin farin ciki da walwalar da ta rasa a kwanakin baya a sanadiyyar takura mata da wayar da AbdulAbdulmajid yayi. Kan kace kwabo Zahra ta dawo kamar da,ta sa karatunta a gaba. Kuma tuni ta tsara mahaifanta akan batan wayarta babu wanda ya tuhumeta ko ya tsareta da tambaya akan dalilin batan wayarta.

Bayan kwana biyu Bakura ya siyo mata sabon layi na

Glo da kan waya kirar Iphone.

**********

Sajida ce a zaune a cikin rana tana Juye-juye. Kallo daya zaka yi mata ka tabbatar bata jin dadin jikinta ga tsananin damuwa. Umma furera ce ta fito daga dakinta dauke da katuwar fanteka a cike da geron kunun kanwarta na Siyarwa zaa kai mata Surfe. Dakyar take tafiya saboda nauyi, ta cije baki ta ajiye a kasa yayin da ta dafe kashin bayanta tana sallati.:

Ta juya ta dubi sajida. Ta ce “yanzu Sajida ba zaki tashi daga rana ba? Tun dazu nake faman yi da bakina amma kinki tashi, hantsin har ya fara zafi. Idan sanyi kike ji ki shiga daki ki lulluba, rana ciwon kai da zazzabi zata sake jawo miki.”

Sajida ta dago da luhu-luhun idamuwanta wadanda

suka kumbura a sanadiyyar koke-koke da zafin zazzabi ta dubi mahaifiyarta. Ta ce “Umma, tabbas kun kusa ku nemeni ku rasa

-kuma idan na tafi na tafi kenan.”.

Umma Furera tayi kasake a tsaye ta hada hannu ta rike ciki tana duban Sajida. Can ta karaso inda take ta ciccibo hakarkarinta ta daga ta tsaye. Tana fadin tashi daga rana mu koma inuwa sai muyi maganar. Umma Furera ta mayar da Sajida inuwa ta zaunar da ita akan wata tsohuwar tabarma ta jawo kujera ta zauna a kusa da Sajida.Ta ce “yanzu Sajida ba zaki hakura ki fauwalawa Allah komai ba, akan Abdul majid ki ringa kokarin ki kashe kanki. Babu ci ba sha har kike tunanin guduwa a nemeki a rasa ki jefa iyayenki

Hmmm

Show More

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE