MISBAH BOOK 4 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

babu wanda Deeni bai cike ba. haka ya bada komai nashi da address da komai na Lagos da na Kaduna.

Basu gama komai ba sai washegari ya gama komai koda wasa Sulaiman bai fadawa su Hajiya abinda yake wakana ba sannan dalilai da cikakkun shedu da ya kawo yasa ko ta kansu hajiya ba’ a biba sai dai Aunty Amina tazo ta saka hannu ita da Sulaiman haka aka bawa Deeni Muhammad suka taho tare da Sulaiman dan yaga gidansa sai dai bai fada masa cewa sun rabu da Bahijja baya dai fada masa tana can Kaduna taje wani aiki zata dawo.

Da yake jirgin safe suka biyo yamma nayi

Sulaiman ya bio jirgin yamma ya dawo kano zuciyarsa cike da nutsuwa dama tuni ya yarda da

Deeni badan shi ya takura a taho da shi ba da ba zai biyo shi ba.

Kuma abinda ya kara kwantar masa da hankali ganin hotunan Bahijja birjik cikin gidan hakan yasa ya kara samun nutsuwa. sai da bai je bangaran

Farida ba bare ya ganta haka suka rabu cikin jin dadi tare da tarin kyauta mai tsoka da ya bawa

Sulaiman.

Zaune take tana hutawa yau sam bata gidan tana makaranta tun safe sai yamma lis ta dawo. sallama yayi ya shigo falon nata a kaikaice ta amsa masa sai dai abinda ya fisgi hankalinta shine yaron da ta gani tare da shi da sauri ta kara dubansa.

.Kallon da tayi masa na Karin son bayani ne. ga yaro na nan na kawo miki shi ki hada da su Deeni karami ki rike kamar yadda zaki rikesu.

Yaron ta kurawa ido sosai gabanta ne ya fadi.

“Ban gane mai kake nufi ba ina son jin Karin bayani amma ba wai haka kai tsaye ka ce min ga yaro bana rike ba tare da kayi min bayani ba.”

“Kada ki daga hankalinki yanzu kuwa, nasan kina da labarin cewa Bahijja na da da mijinta da yarasu ko to shine yanzu na karbo shi wurin dangin ubansa na dawo dashi gurina zan rike shi da zuciya daya.”

Cikin kakkausar muryar tace “Deeni wai yaushe zaka dai na yaudarar kanka da ganganne sannan kuma yaushe zaka dai na raina min hankali ni yarka ce da zaka je ka dakko min dan wata kace min na rike maka shi to wallahi baka isa ba, ni fa wannan abin naka yagama isa ta yau kuma ta nan ka biyo min kai Kenan burinka ka sanyani bakin ciki zuciyata ta kumbura ta fashe wallahi ka gama ba zan tsaya kana min abinda ranka yake so ba.”

*Na ji ban isaba amma baki da ikon hanani rike yaron nan a cikin gidan nan tunda ba naki bane, ni nake da iko akan gidana sannan idan har zaman aure na kike dole ne ki yi min abinda nake so.” Deeni kana mutukar bani mamaki cikin al’ amuranka ka cika son kai da so ganin ka yi abinda zai taba zuciya wanda na fuskanta yin haka na saka farin ciki da nishadi. ka tuna a yanzu Bahijja bata tare da kai ko dan son gani na cikin bacin rai yasa kayi min haka.

Yanzu kagama hora zuciyata ta saba da dukkan wani bakin ciki da zaka nuna min amma a wannan

karan ko mai zaka yi bazan rike yaron nan ba sai dai idan saki na zaka yi kamar yadda na tsani

Bahijja haka naji na tsani yaron nan yanzu a rai na.’

Shi Kenan muzu ba dani da ke wannan yaron sai dai ki mutu amma ban ga mai iya raba shi da gidan nan ba ko iyayena basu da hurumin hanani rike shi domin ganin jinin Bahijia a tare da ni zai sanya na dinga jin saukin raradani rashinta da nayi, sannan ki adana kalaman kina batun na sake ki ina mai tunatar da ke tun abaya na fada miki babu saki a tsakaninmu a haka zamu karasa rayuwarmu ni da ke.

Yana gama fadin haka ya ja hannun Muhammad suka yi ciki. nan kuwa kuka ya zo mata ta dora hannu aka tana yin mai isarta ita dai ta ga ta kanta lallai ba ta san lokacin da Deeni zai dai na loda mata wannan kayan bakin cikin ba.

Nan ta kirawo Mama ta fada mata irin tarin takaicin da Deeni yake tara mata ta kada baki tace

“Farida sai dai fa kiyi hakuri babu abin da zan iya yi akan wannan halin na Deeni kuskure dai mun riga da mun yi tún farko nayi alkawarin bazan kara shiga harkar rayuwar gidansa ba tsakanin mu da ke sai dai mu baki hakuri.

Kuka ta saka mata ta kasha wayar tana tunanin yadda Mama sam yanzu bata samun goyan baya a gurin ta duk lokacin da ta zo mata da matsala sai da tace ta yi hakuri ko kuma ta goyi bayan dan ta a nan dai ta gaji da kuka ta har ta rarrashi kanta ta hakura.

A hankali Deeni ya kirkiri danganta tsakanin

Yaransa duk da yana yi Farida tana warwarewa ta kasa ranar da ya farga yayi mummuna bata mata.

Cikin kankanin lokaci suka saba domin yadda ya sabarma yaran karya ne Farida tayi nasara akan ta raba yaran da kowane irin makircin da zata yi musu.

Haka dai rayuwar tasu ta ci gaba suna girma bata dai na abinda take masa bashi kuwa dukkan masifa da azabar da zata yi masa baya taba gayawa kowa domin yasan idan Abban su ya sani ba zai gyaleta bashi kuma ba yason ganin fadan da yake mata.

Akwai wata rana da lokacin Deeni karami bashi da lafiya zazzabi ya kwantar da shi yana daki haka ma Aisha a ranar tun da gari ya waye Deeni karami bai ga dan uwansa Muhammad har yamma. nan da

Farida ta zo bashi magani ya tabbayeta yana ina tace ita bata ganshi batun dazu ko yawo ya tafi.

Tana fita ya mike da yake yaji dadin jikinsa nan ya shiga neman Muhammad cikin gida loko da sako na gidan yana neman su amma bai ganshi ba nan ya nufi can loko inda suke wasan buya a nan ya iske Muhammad kwance cikin inuwa ya galabaita sai nishi yake. Yana ganinsa yayi sauri zuwa gurinsa ya tambaye shi yace mai yake a nan a kwance bai shiga gida ba. Nan yace “tun safe mama ta koro ni nan tace idan naje inda kuke sai ta yi min dukan tsiya ta kuma hanani abinci tunda safe har yanzu ban ci komai ba ruwa kawai na sha shine ciki naya kulle na zo nan na kwanta.”

Cikin damuwa yace “Muhammad wallahi sai na fada ma Abba dama kai ne komai zan fada sai ka hanani kace kada na fada idan na fada zaka ce karya nake yau ko zaka karya tani sai na fada.”

Rike hannunsa yayi yace “haba yaya Nuren wai kai kullum baka tausayin Mama ne baka ganin yadda suke da Abba kullum kowa cikin damuwa babu wanda ya damu daga kai har Aisha ni kadai abin yake damuna, ya kama ta mu hadu mu bawa Abba hakuri su dai dai ta ka ga idan ka fadama Abba haka nasan zai kara fushi akai.’Muhammad idan kana son zaman lafiyarka kada ka kuskura ka yiwa Abba wannan maganar tun ba yau baya kira ni yayi min magana yana cewa babu ruwana da irin Zaman da suke da Mama idan nayi kokarin saka baki zai mutukar bata min tun ban kai haka ba yake min magana bare yanzu da zan shiga shekara goma.

Ni dai babu ruwana ban san mai yasa suke haka ba bana kuma so na sani tunda Abba bai nuna na sani ba kai ma ina mai baka shawara ka saka musu ido, amma dai a yadda na san Abba da halin da kirkinsa sai nake ganin laifin duk na Mama ne ka ga dai yadda take maka kuma kana gani tana yi ne bata so ya sani.”

Hmmm

Show More

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE