MISBAH BOOK 4 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

gono, mai yasa baki ji tausayinsa ba a wannan lokacin.

Na tabba da kin barshi gurin mahaifiyarsa da ta rikè abinta ta rayu da shi ya dauke mata radadin zafin mutuwar mijinta amma duk baki duba wannan ba sabo da son kai irin naki. baki san wane irin hali ta shiga ba lokacin da ta rabu da mijinta da kuma danta duk ta cinye bata taba biyo ku ba don ganin danta ta barshi tunanin ta dangin ubansa za su yi masa adalci su bashi uwa su bashi uba, ashe abin ba haka bane, wani sabon maraici za su jefa mata shi.

Hakika da ana mutuwa a dawo da DR. Mislihu ya ga bakin cikin da bai taba gani ba a rayuwarsa zai yi bakin ciki sosai zai ce dama uwarsa abin hannunsa take so ba abin da ya Haifa ba, idan dama kun karbi Muhammad ne domin tarin dukiyar mahaifinsa na tabbata babu wanda cikin ku bai san illar cin gadon maraya ba amma ni dai ba wannan ne a gabana ba. sai Magana ta gaba na tabbata baki zauna da Bahijja na kwana daya kun fahimci juna ba da na tabbata ba zaki taba kullatar ta ba domin Bahijja mutunce mai mutukar mutunci da daraja jama’a ko daga ina suke ta san mutuncin kanta bare na wasu.

Da kin san wane irin baiwa ke tare da ita da baki yi mata haka ba amma bazan hanaki tsanar Bahijja ba domin abin a jinin ki yake amma na tabbata da zaku rayu da Bahija ba zaki san lokacin da zaki

nemi tsanarta ki rasa ba domin ba zaki gane ta ba sai wata mu’ amala ta shiga tsakaninku da ita.

Tunda haka ta faru komai ya wuce ni zan koma amma idan da hali ina son wani ya raka ni gidan marayun naga Muhammad ko sau daya ne.”*

Gabaki dayansu na gurin babu wanda jikinsa bai mutuba tare da tarin nadama a fuskokinsu musamman ma Hajiya Babba. babu wanda ya iya cewa komai nan ya mike yace “idan bazan samu wanda zai raka niba a bani number ta file dinsa da cikkaken sunan da akai mai amfani da shi.” Sulaiman ya mike yace “Mu je na raka ka.” Babu wanda ya sake tankawa ya mike ya fice yana bada baya ya ji Hajiya ta fashe da wani irin kuka mai cike da nadama bai tsaya sauraron kukan baya ya fice ya dai ji lokacin da suke bata baki.

Tare suka taho da Sulaiman wanda bayan sun fito yake fada masa uwarsu daya ubansu daya da

Dr. Mislihu nan ya shiga fada masa irin halin mahaifiyarsu duk haka kowa yake hakuri da ita kuma duk wanda ya gani a nan duk Kannan Docter ne. yace “Allah ya kyauta.”

A nan ne ya kara masa haske cewa tun

Muhammad na da shekara uku ta kai shi gidan marayu ba kowa ne ya sani ba idan ba su ‘ya’ yanta ba kowa ya tambayeta sai tace “Bahijja ne ta zo ta karbe shi was kuma tace ita ta maida mata da shi. shima wata rana ya ji gurin yayarsu wadda da tayi niyar karbarsa Hajiyan ta hana da yake babu wanda

yake kawo mata wargi duk cikin mu dole kowa ya zubawa abin ido. A yarda yake fadi dama yace da zarar yagama karatunsa yayi aure babu abida zai hanashi dakko Muhammad ya rike shi koda Hajiya zata tsire shi. ta kuma tara su ta fada musu badan kowa tayi haka ba sai don kawai bata kaunar Bahijjaa da wannan suka isa gidan maryu na kano da ke nan Nasarawa G. R. A daura da Asibitin Nassarawa.

Basu sha wahala ba aka fito musu da

Muhammad wanda dama kowa yasan cewa yana da gata wani dalili ne yasa aka kawo shi nan ajiya. kuma da yake dama Sulaiman shine yake zuwa lokaci zuwa lokaci dan haka tuni suka saba da kowa a gida.

Yaro ne da kimanin shekaru shida kana kallonsa ka ga Bahijja komai irin nata ne tun dagafata har fuska. wani irin razana Deeni yayi da yaga tsananin kamar da yaron yake da Misbah dinsa nan take yaji wani irin hawaye ya zo masa yayi kokarin kare sun a tausayin Muhammad da kuma kaunarsa da yaji duk a lokaci daya. Muhammad yana ganin Sulaiman da sauri yazo ya rungumeshi yana cewa “Uncle Sulaiman oyoyo kace zaka dawo tunda ka tafi baka zo ba sai yau.” nan ya rungume shi.

Jin hakan ya kara karaya zuciyar Deeni take hawayen ya zubo masa domin a wanna karan ba zai iya tsai dasu ba tsabar tausayin Muhammad da jin furucinsa.

Sulaiman ya lura da halin da Deeni va shira haka kawai shima yaji wani abu ya taba masa zuciya.

Muhammad ya lura da Deeni sai dai kafin ya ga hawayen fuskarsa tuni yayi sauri ya goge yace

“Uncle Sulaiman wannan wanene ko shima wani

Uncle ne ya zo ganina?”

Cikin Murmushi yace “eh Muhammad shi ma uncle dinka ne yau shima yazo zai ganka.”

Kallonsa yayi yace “Uncle mai yasa kai ban sanka ba baka taba zuwa ka gani ba kuma uncle Sulaiman bai taba fada min wata rana zaka zo ba, ba baka sona ne kamar yadda Uncle Sulaiman yake sona.”

Wani irin tausayinsa ya kama shi bai san lokacin da ya sake wasu hawaye ba duk dauriya irin ta

Deeni sai da zuciyarsa tayi rauni yana Magana yana hawaye yace “Muhammad ka yi hakuri bana nan ne ina son ka sosai fiye da kowa nazo ne na tafi da kai daga gidan nan na kai ka gurin Maman ka ba zaka kuma zama a gidan nan ba HAR ABADA.”

Mama na kuma a ina mamana take ba Aunty

Amina ne Mama na ba (yana nufin yayar sulaiman wadda take zuwa wajansa duba shi). To me yasa kake kuka haka ka share hawayenka Uncle Sulaiman baya kuka idan yazo guri na ko Uncle Sulaiman.”

Zan dai na Muhammad nima ban san ina yin kukan ba Aunty Amina itama Mamanka ce amma dai zan tafi da kai kana so zaka bini.”

Murmushi yayi cikin jin dadi yace “Eh zan bika ni dama bana son zama a nan kullum idan nace zan bi Uncle Sulaiman sai yace min ba yanzu ba sai wata rana.” nan ya kalli Sulaiman yace Uncle

Sulaiman yau wata ranar ta zo Kenan?.”

“Eh Muhammad tazo Deeni ya zuba ma Muhammad ido yana kallon yadda Allah yake ikonsa komai nashi irin na Bahijja hatta yadda yake murmushinsa duk iri daya. haka ya dinga jin wani irin farin ciki a ransa ya dinga jin kamar Bahijja ce ta dawo cikin rayuwarsa rabon da ya ji farin ciki irin wannan tun da suka bar gidan Gonarsa shi da Misbah rabon da ya samu wani farin ciki sai yau haka ya dinga jin wani irin son Bahija da kewarta na shigarsa cikin ransa yace “Allah na gode maka da ka baiwa Bahijja na Misbah na haihuwa ko ba da ni ba.”

“Uncle Sulaiman shi wannan Uncle din ya sunansa?”abinda yaji Kenan wanda ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya shiga. da sauri yace

“Sunan Uncle Deeni.”Murmushi yayi yace “To.”

Gabadayansu suma suka yi murmushin ganin yadda Muhammad din ya bashi amsa.

Deeni yaga Director na gidan bai boye masa komai baya fada masa dukkan abinda ya faru aka

Akayi yarjejeniya duk wasu dokoki da kaida na gidan

Hmmm

Show More

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE