
NI DA MIJINA PART 1 BY MAMAN NUR
Kallonta yayi cike da nuna ya isa da ita yace”ke zo nan”
Mikewa tayi jiki na rawa tace” k b waya fada maka ina nan?”
Yace”yaushe raini ya Shiga tsakanina dake da har kike tambaya ta?”
Tace”sorry my k b”
Hanun ta ya kama zai ja ta kawai ya ji khady ta rike hanun d’ayan tana jefa me kallon tsana
Wani mugun kallo ya jefa mata yace”zaki saketa ne ko sai ranki ya b’ace?”
Tace”bazan saketa ba yi abinda zaka yi”
Kokarin janyo mukram yayi sai ya kasa domin wani mugun riko khady tayi mata
Ganin ya kasa janta kuma babu alamun tsoronshi a idon khady
Hade rai yayi yace”ke zaki saketa ne ko sai na b’ula miki ciki?”
Kallon shi khady tayi tace”da rabon yau ka kwana bayan kanta”
Ai yana jin haka ya sake mukram dan ya tsane police station
Jakar hanun mukram ya kwace ya cire kudi ya kara gaba
Mukram ko kuka ta fashe dashi tace”zuciyata baka min adalci ba da ka kamu da soyyayar k b”
Rungumeta khady tayi tace”my friend you still have time wallahi kabir ba mijin aure bane”
Cikin kuka tace”iam trying my best”