MISBAH BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

MISBAH BOOK 4 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

•hakuri da son jin abinda ya zame mana sirrinmu. na farko dai Bahijja bata da aure a yanzu haka idda take bata fita daga ciki ba tunda tana dauke da ciki don haka bayyana mata kana son ta a yanzu zai zama haramun, dole sai ta sauka na fada maka haka ne don kada ta haramta gareka.

Sai na biyu ni ba ni na haifeta da cikina ba amma a matsayin uwa nake a gareta. wadannan abubuwa kadai zan iya fada maka amma banda wannan babu wani abu da zaka iya ji a tare da mu.

Na fada maka ne don kasan yadda zaka yi, amma ina mai baka shawara da ka janye maganar aure a tare da ita mutukar kana son ku zauna lafiya.”

Ya bude baki da niyar zai mata Magana Kenan wayarsa ta fara ringing da sauri ya zaro wayar daga cikin aljihunsa sunan Hajiya da ya gani akan screen din yasa yayi saurin dagawa yace””Haiiya barka da

gida.”

Cikin karaji tace “Farouk kana ina ne Bahijja babu lafiya kuma daga dukkan alamu haihuwa ne ka ganta nan sai cewa take a kira mata Baba Audi ko kana kusa ka zo gamu mun fito zamu tafi asibiti.”

Arude yace “Innanillahi wa’ inna ilaihir raju’un

Hajiya zama ku wuce asibitin gani nan zan taho da Baba Audi din insha Allahu gani nan yanzun nan.”

Jin wannan furucin ya ta da hankalin Baba Audi a rude tace “Dana mai ya faru da Bahijja din don

Allah ka fada min ko hankalina ya kwanta “Baba ki kwantar da hankalinki ina zaton haihuwa ne domin Hajiyata haka ta fada min yanzu kawai ki shiga ki fito sai mu karasa asibitin mu same su.”

Aggaggace ta shiga ta fito tana addu’ a akan Allah ya sauketa lafiya. cikin tashin hankali suka iso asibitin da yake bayan ya kira Hajiya ya tambayeta a wane asibin suke nan ta fada masa.

Lokacin da suka karaso tuni har an shiga da ita sai dai yana zuwa yake tambayar ya ake ciki nan

Hajiya ta fada masa har yanzu babu wani labari tunda suka shiga babu wanda ya fito ya fada mana ga halin da ake ciki.

Jin haka ya kara jin hankalinsa ya tashi nan ya din ga kai komo. Ana cikin haka sai ga wani likita ya zo cikin gaggawa.

Farouk yana ganinsa kai tsaye ya nufi inda yake yace “Doctor don Allah a wane hali take ciki” ya fada ciki kaguwa.

Nan likitan ya dube shi yace ko kai mijinta ne?”cikin sauri ya fada “Eh nine.”

Likitan yace “kar ka damu insha Allahu muna sa ran haihuwarta nan da dan wani lokaci kadan yanzu haka muna son jini.”

“Likita muje ka dauki nawa a saka mata idan har zai yi.”

“Ok babu matsala zamu iya zuwa a gwada amma kafin nan mu shiga ciki ina son Magana da kai.”

Ya wuce ya bishi a baya kafin ya tafi ya juyo ya kalli Hajiya da Baba Audi yace “Bari na je na bada jinni na amma don Allah ku cigaba da addu’ a Allah ya rabata lafiya da abinda da yake jikinta.”. yana gama fadin haka ya juya ya bi likitan suka yi ciki.

Baba Audi cikin kuka ta amsa da “Amen ya

Allah.”

Hajiya ta cigaba da bata baki akan cewa *kiyi hakuri ba kuka zaki tsaya yi ba addu’ a ita ce gaba.”

Baba Audi tace “To Hajiya zan yi.” Nan ta shiga mamaki da tunanin ganin yadda Farouk ya rude akan halin da Bahijja take kici ko mijinta iya kar abinda zai yi gashi da kansa yace a dibi jininsa a saka mata, kai gaskiya Bahijja tana da masu son ta komai a rayuwa idan zaka yi gaskiya a cikinta to lallai ba zakataba rasa masoya na arziki ba.

kuma dama dama kyan hali irin na Bahijia babu abinda ba zata samu ba a rayuwarta sabo da ita kowa da zata zauna da shi da zuciya daya take zama da shi. nan da nan taji kaunar Farouk a zuciyarta taji ya kwanta mata ya kuma burgeta don haka zata yi iya kokarinta ta ga bai samu matsala akan Bahijja ba duk da kuwa tasan irin kafiyarta da tsatstsauran ra’ ayinta da babu mai iya canza mata.

A can office din likita hankalin Farouk ne yayi mutukar tashi jin likita ya fada masa suna tunanin nan da wasu lokuta kadan idan bata haihu da kanta ba za’a yi mata CS, don haka muna bukatar saka hannunka idan yuwar hakan yayi.

Bai tsaya tunanin komai baya nemi ya bashi ya saka hanun. sai da suka gama komai yaje aka gwada jininsa a ka diba daga nan bayan ya dan huta kai tsaye masalaci ya wuce yayi alwala ya shiga nemar mata sauki akan Allah ya kawo mata sauki cikin gaggawa.

Zaune yake cikin masallacin ya daga hannu yana addu’ a Hajiya ne da Baba Audi bakin masallacin suna tsaye suna jiran fitowarsa domin ya fada musu yaje masalaci don haka suka taho cikin doki don yi masa albishir.

Suna tsaye suna hango shi cikin masalacin ya daga hannunsa sama yana addu’a. ganin ya jima a haka Hajiya ta gaji ta je bakin masalacin tace.

“Farouk addu’ar ta karbu haka maza kazo ta haihu da kanta.”

‘ jin muryar mahaifiyarsa yaji wani

dadi ya kama shi bai iya juyowa ya kalleta ba sai da ya mai da kansa ga sujjada yana kara godema

Allah. Duk abin da yake Baba Audi na hango shi haka taji ya kara shiga ranta tare da kara ganin kimarsa.

Jin kadan ya dago ya fito cikin sauri fuskarsa dauke da fara’a, yace “Masha Allah Hajiya mai aka samu?”

Hajiya tace basu fada mana ba amma maza mu koma kada su fito suga bama nan. cikin murna suka juyo ya kalli Baba Audi yace Baba

barkanmu.

Cikin murmushi tace “Barkan mu dai.”

Zuwan su Kenan babu wuya likita ya zo kurin tare da wasu Nursesguda biyu daya dauke da jariri a hannu. Da sauri ya nufi gurin Nurse din ya karbi jaririn yace “Doctor mai muka samu.

“Ranka yadade an samu Baby girl.” Ya fada yana murmushi.

“Masha Allah”ya fada sannan ya kai maBaby sumba sannan yayi mata addu’a kamar yadda addini ya tanada. sannan yace “Doctor ya maman

Baby din.”

“an gama gyarata ne sannan kuma tana karbar

Karin jinin da ake mata kasan ta yi zubar jini sosai kuma jininka yayi dai dai da nata amma cikin ikon

Allah iya jinin naka kawai ya wadatar da ita.”

Wani irin farin ciki ya kama shi yace Doctor ina godiya goran albishir dinka na musamman ne ku kuma sisters ga naku goran.” nan ya saka hannu a aljihunsa ya zaro kudi bai san ko nawa bane kowa ya bata yan raina dubu dubu ne. nan suka shiga godiya hade da murna.

Da kyar ya bama Hajiya da Baba Audi Babyn nan suka shiga tsokanarsa likatan da suran sisters din. ana cikin haka sauran mata biyun suka karaso gurin suna mai sanarwa likitan sun gama shiryata zasu iya shiga.

Nan suma ya basu nasu kason suka shiga murna da kara yi masa godiya wani dadi ya dada kama

Baba Audi cikin ranta ta shiga yi masa addu’ar samun nasara a rayuwarsa. gaba dayan su suka nufi dakin.

Kwance suka sameta ta daga idanunta sama tana tunani ganin Baba Audi ya sakata tsananin farin

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE