BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE

BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 14

A hankali ummul ta yayibo wani farin hijabi amman tsabar tsufan dayayi yasa ya koma milk colour ta sanya ajikinta.
Tare da amsar hamsin ɗin ta fita waje garin tsit sabida lokacine na sanyi ahankali take jan ƙafafunta harta ƙarasa wajan mai sayar da kokon ta tsugunna ta gaisheta haɗi da bata gudar hamsin ɗin
Juya kuɗin mai kokon take don hamsin ɗin bazata amsu ba amman tsabar tausayin yaran yasa ta amsa tare da zuba mata,kokon daya fi na kuɗinta ma yawa.
Sosai ummul tai mata godiya ta yo hanyar gida.
Adai dai ƙofar gidan hajja taga mota fara a fake wadda tun lokacin fitowarta ta farko taganta amman tsabar sauri yasa bata tsaya kallon motar ba, Allah ya bawa ummul son kallo dakatawa tai tana kallon kyan motar kamar wata ƴar ƙauye.
Sannu Ahankali ta nufi gate ɗin gidan hajja yaushe rabon data shiga gidan tun ranar datai mata fitsarin kwance yau kusan sati biyu kenan bata ƙara leƙawa ba ko hajjan tazo gidansu ɓuya take.
Tafiya take cikin gidan kamar munafuka har ta ƙarasa tsakar gidan tana gab da shiga cikin falon hajja taga namiji zaune saman kujera ƴar tsugunno yana brush.
Da sauri taja baya tana ƙifta idanu sam bata kawo zataga wani ba.
Matashin saurayine black colour kyakykyawa mai manyan idanu haɗi da kwantaccen saje daya haɗe da gemun shi jikinshi ba riga se guntun wando daya tsaya iya cinyar shi.
Kwantaccen gashine baƙi ya ƙewaye ilahirin fatar jikinsa har cinyarsa da hannunsa ga wani irin baƙin gashi a saman kirjinsa ya kwanta ya zagaye nippy ɗinsa.
Rintse idanu ummul tai jikinta yana rawa zuciyarta na bugawa dana sanin shigowa gidan hajja ya cikata.
Aguje tayi ɗakin hajja tana mai yarda kokon hannunta wanda ta fallatsawa wannan matashi ajikinsa shi sam bai ma kawo da mutum a wajan ba zafin kokon ne yasa ya ɗago da dara daran idanunsa yabita da kallo taɓe bakinsa yayi tare da wanke inda ta ɓata mai ya wuce ciki.
Dayake hajja tana ɗaki yasa ummul tabita can.
Dan haka yana shiga falon hajja bai ganta ba ya wuce ɗakin daya sauka ya shirya sauri yake sabida kar lecture ta wuce shi yazo yin wani course ne nan bayero!akan aikin shi na lauya, duka duka wata ɗaya kawai zeyi ya koma.
Ƙamshin daddaɗan turarensa yasan ya ummul ƙara maƙewa a bayan gadon hajja tana ƙifta idanu sanye yake cikin manyan kayan dasuka fito da surar kyansa na yaren hausa fulani ya zauna bakin gadon hajja suka gaisa .
Hajja ce ta nuna mai ummul wadda taƙi yarda ta haɗa idanu dashi.
“Ka ganta ita ce ƴar raino ta taimin fitsari ta gujeni”
Dariya ya saki marar sauti batare daya ce komai ba.
Ya zira hannu cikin aljihunsa ya ɗauko ƙatuwar chocolate ya bawa hajja yace ta bata.
Kana ya soma magana cikin ɗan faɗa kaɗan.
“Amman hajja wannan ƴar renon taki bata sallama sannan bata iya gaisuwa ba yakamata a koya mata”
Yana gama faɗin haka ya wuce yayi tafiyarshi bayan shi ummul tabi da kallo a haƙiƙanin gaskiya bazata ce ga kamannin saba sedai tace mai yana da faɗa yana da kyauta.
Hajja ce take dariya ta janyo ummul ta bata chocolate ɗin haɗi dayi mata faɗan rashin sallama.
Se lokacin ummul ta tuna da aiken Bamu kallon hajja tayi tare dacewa.
“Hajja bamu ce ta aikeni na siyowa ihsan koko wallahi agarin kallon wancan ƙaton na zubda”
Tafaɗa tana mai ƙoƙarin zubo da hawaye!
Hajjace ta dube ta a tsanake tace.
“Karki ƙara ce mai ƙato jikana ne sunan shi baffa! sannan kije kicin ki ɗauki taliya a kula ki kai mata sannan ki bata haƙuri”
Ƙifta idanu ummul tasoma cikin tsoro tace.
“Nikam hajja tsoro nake ji kar naje bamu tace na biyo tanan na roƙe ki”
Faɗa hajja tahau mata wanda yasan ya ta ɗauko kular ta fice.
Koda taje gidan bamu faɗa tahau yi mata kamar zata ari baki.
Kuka ummul ta sanya tana bata haƙuri da ƙyar ta amshi taliyar tare da makawa ummul worning akan kada ta ƙara biyawa ta gidan hajja da safe.
Alhamdulillahi kowa yaci taliyar ya ƙoshi harma tai saura.
Ƙarfe sha biyun rana talatu tazo domin jin yadda bamu sukai da baba aikam bayan zaman talatu hassana tana kuka tana wassafa mata halin data ke ciki.
Shawarwari talatu ta bata sannan tace mata tazo suje gidan,Data samar mata anan gaban sune can ciki.
Hassana ce ta shirya tare da barwa ummul amanar ƙannenta suka rankaya suka fita.
Sosai suka sha tafiya sabida shi gidan da zata fara aikin acan cikin unguwar yake ɓangaran masu hannu da shunin arean haka suka ƙarasa cikin layin gidane na gani na faɗa na masu hannu da shuni.
Talatu ta buga ƙofar gate mai gadi yazo ya buɗe masu.
Gaisawa sukai da talatu sanin yasan ta tana kawo wa masu gidan ƴan aiki yasa yace su zauna a saman banci domin masu gidan basu tashi ba.
Zaro idanu hassana tai cike da mamaki ƙarfe 12 amman basu farka ba amman ga mamakinta setaga talatu tace mata.
“Taso ki rakani gidan nawa aikin ki tayani kafin nan sun tashi,kinsan ita matar gidan nan ƙawar uwar ɗakina ce wadda nakewa aiki to ina kawo mata ma’aikata basa zama ne”
Ba musu hassana tabi talatu wanda layika uku suka rabasu da wannan gidan dasuka bari.
Abin mamaki talatu da kanta taje ta zubo musu abinci suka ci sannan sukai wanke wanke bayan sun gama sukaje falon matar gidan suka zauna ƴaƴan gidan sunata tsokanar talatu ahaka matar gidan tazo itama cikin barkwanci suka gaisa da talatu har tana janta itama.
Sosai abin ya bawa hassana sha’awa lallai ba kowani mai kuɗi bane yake da wulaƙanci wani zakaga yasan darajar ɗan adam gadai uwar ɗakin talatu da ƴaƴanta kamar bama su kuɗi ba sam basu da reni bare girman kai.
Tambayar talatu matar take akan hassana tas talatu ta kwashe komai ta gayawa matar.
Sosai matar ta tausayawa hassana cikin kwantar da murya tace.
“Hajiya timo bata da matsala tana da kirki xakiji daɗin ta matsalar ta ƴaƴanta ita da mijinta basa ganin laifin ƴaƴansu amman indai kika iya zama da ita xakiji daɗinta”
Sosai ta bata shawarar yadda xata zauna da uwar ɗakin nata daza’a kaita wajanta.
Har azahar suna gidan amman rabin hankalin hassana yana kan ƴaƴanta.
Seda sukai sallah sukaci abinci har talatu tai guzirin wani sannan sukai sallama uwar ɗakin talatu ta bawa hassana taliya kusan leda goma da dubu uku da sabulai.
Sosai hassana tai mata godiya suka wuce gidan da za’a kaita ɗin.

1 2 3 4 5Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE