BAKAR KADDARA

BAKAR KADDARA CHAPTER 4

Dayake nasihan Umman yashige ta sosai shiyasa koda Adda rukayya tafito mata da kayan da zata saka batare da tayi wani gardama bah ta amshi kayan tasaka,
Riga da skirt ne na wani hadaddan lace me shegen kyau da tsada dayake ita din farar mace ce kuma me diri mekyau sai kayan sosai suka zauna mata a jiki sukayi mata wani mugun kyau kalar kayan yana daya daga cikin abunda yakara fitowa da ita,
Adda lauratu dayake ita din professional ce wajen makeup da kanta ta zauna ta tsantsara ma yar kanwar tasu kwalliya me Dan banzan kyau kada kuso kuga yanda Buddu tayi wani kyau duk dama bawani heavy makeup akai mata bah amma still yanda Adda lauratu ta mata kwalliyan sai yayi matukar yin kyau da fuskar tata,
Walima aka hada nagani nafada anan farfajiyan gidan sosai wata malama tayiwa amarya tuni akan yanda zata kula da mijin ta da duk wani hakkin sa akanta harma da albarkam daren farko saida malamar nan ta fayyace komai ba Buddu kadai ba duk wata yarinya data fara tasowa saida wa’azin malamar nan yashige ta,
Karfe hudu dai-dai aka tashi daga walimar aka fara shirye shiryen kai Buddu gidan alhaji babba dan wannan al’adar suce duk wata ko wani daza aiwa aure tofah dole ne sai an kaishi wajen Alhaji babba yamai nasiha,
yanzu ko wata ratsassiyar super na atamfa tasaka green color sai ratsi ratsin blue black a jiki sosai tayi wani kyau fuskar ta tayi wani dan banzan haske sabida wannan karan koh powder ba’a shafa mata ba a cewar Umma tunda gidan Alhaji babba za’a kaita baikamata ai mata wani kwalliya ba sabida tasan alhaji babba bai rabo da korafi saidai idan akayi la’akari da tsufar daya somayi sai ai masa uzuri,
A bangaren Jimeta saida yayi bacci yatashi sannan yaji dan sauki duk da har a lokacin Bawai ya najin wani dadin jikin shi bane amma babu yanda ya iya haka shima ya shirya cikin wani hadaddan farin shadda wanda yasha aikin farin surfani me mugun kyau,
Hatta hular daya saka fara ce saidai akwai dan digo digon blue blue a jikin hakan sai yakarawa hular kyau dashi karan kanshi me sanye da hular,
A al’ada dole shima namiji sai anyi mashi rakiya kamar yanda za’aiwa mace rakiya itama a kusan tare motocin gidajen biyu suka dira a kofar gidan Alhaji babba nandanan wajen ya kaure da hayaniya hade da hada amarya da ango a guri guda Adda bilkisu ita da kanta ta dauki hannun Buddu tasaka ana Jimeta tuni wajen yadauki buda,
Ko irin murmushin nan da ango yakeyi ranan auren shi babu shi ko kadan a fuskar Jimetan saima wani dau’daure fuska yakeyi yana shan kamshi itako buddu dayake an lullube mata fuska dawani katon gyale ne sai babu wanda ya fahimci halin da take ciki
Kai tsaye bangaren Alhaji babba akai masu rakiya sai kowa yaja ya tsaya akabar Jimeta da Buddu suka shiga cikin babban falon daya kayatu sosai da kujeru na alfarma hade da sauran kaya masu kayata waje,
Tunda suka shiga falon Alhaji babba yake sakin murmushi danba karamin kauna yakewa Buddu da Jimeta bah sune jikoki mafi soyuwa a cikin ranshi yana masu kaunar da baima ya’yan cikin shi shiyasa ya yanke hukuncin hada auren su dan tuni yahango alkhairi sosai a auren nasu,
Samun waje sukayi suka zauna Kan Buddu a kasa tabude bakin ta dakyar tace,
“Kaka barka da warhaka mun sameka lafia”
Daga haka sai taja bakin ta tayi shuru tana wasa da zoben dake hannun ta,
Fuskar shi dauke da murmushi ya amsa da lafia lau yar albarka Allah yayiwa rayuwar ki albarka yabaki ya’yan da zasu maki biyayya kamar yanda kika mana biyayya nida iyayen ki,
Muryar ta har rawa yakeyi wajen cewa Amin Kaka,
Cikin Nuna isa da fadin rai Jimeta yace,
Dafatan mun same ka lafia Allah yakara maka lafia”
Murmushi kawai Kaka yayi hade da girgiza kai a zuciyar shi yace me hali dai baya fasa halin shi yarasa wane kalar zuciya ne da Faruqu amma yana addu’ar Buddu tazama silar canzawar shi tazama garkuwa a cikin rayuwar sa tazama jikon rayuwar sa tazama Farin cikin rayuwar sa,
Gyaran murya kaka yayi kana yace, Alhamdulillah nagode ma Allah daaya nuna mun wannan rana dana jima ina jiran zuwan sa babu abunda zance maku saidai Allah yabaku zaman lafia yakuma baku zuri’a nagari yasa Alkhairi a rayuwar auren ku, daga nan kuma yafara masu nasiha me matukar ratsa jiki saidai a bangaren Jimeta ta inda take shiga tanan take fita Buddu ko sosai nasihar take shigar ta saidai kuka takeyi a hankali yanda babu me iyaji kuma gyalen da aka rufe mata fuskar ta dashi bazai samu daman tona mata asiri bah,
Bayan Alhaji babba yagama masu nasihan ne yakara da jawa Jimeta kunne akan kula da Buddu yace,
“Faruqu nasan kokai waye nasan abunda bazaka iya ba nasan kuma abunda zaka iya aikatawa ina rokon ka badan niba karike Buddu amana kazamar mata uba kazamar mata uwa kazamar mata dangi sabida zaku tafi garin da Buddu batasan kowa ba kaine zaka zame mata garkuwa kaine zaka zama me kula da lamarin ta”
sannan yajuya kan Buddu yace, Nasan kedin me biyayya ce dan haka kiwa mijin ki biyayya kiyi koyi da halin Umman ki dan macece tagari’ da ganan kuma yace Allah yabaku zaman lafia yabaku hakurin zama da juna,
Sannan yakara dacewa,
Daga nan bana son ku tsaya ako ina ka dauki matar ka kutafi sabida babu wanda zai mata rakiya tunda dai gari ba kusa bah daga nan yace su tashi sutafi ai tunda kaka yace babu wanda zai rakata taji hankalin ta yatashi dakyar suka fito daga Falon kakan,
Suna fitowa kuma yan uwa suka hau yimusu nasiha karfe shida dai-dai motocin da zasu rakasu airport suka karaso kofar gidan nanfa hankalin Buddu yakuma tashi shikenan baza takara ganin Umman taba sai zuwa nanda wani watanni kilama shekaru kuka sosai takeyi wanda har saida sautin kukan yafara fitowa dan dakyar tashiga motar aka tafi su adda rukayya suka sanyata a tsakiya,
suna karasawa airport din flight din yana gabda tashi shiyasa a gurguje ko wannan su yafito nanfa hankalin Buddu yakara tashi ganin lallai lallai da gaske Tafia su adda rukayya zasuyi su barta batasan sanda tafasa kuka ba hade da fadawa jikin su tana wani kankame su cikin muryan kuka tace,
“Dan Allah adda kada kutafi kubarni wallahi bansan kowa bah wayyo Allah adda kada kubari natafi”
sai takuma fashewa da kukan suma kukan tausayi da kuma rabuwar da yar uwar tasu sukeyi ganin da gaske takeyi zata bata mashi lokaci sai kawai ya daka mata wani rikitaccen tsawan daya sanyata janye jikin ta daga nasu Adda rukayyan ta dukar da kanta karasawa yayi inda take ya sanya hannun shi ya rike mata nata hannun gagam yanda bazata iya kwacewa bah sannan yafara janta da sauri,
Kuka sosai takeyi tana juya bayan ta tana kallon su Adda rukayya da suma kukan sukeyi har saida suka bacewa ganin ta kana ta daina juyawa sai kawai ta dukar da kanta taci gaba da rusa uban kuka,
har suka shiga cikin flight din bata bar kuka ba ganin lallai ba zata daina bane ya sanya hannun shi yaja mata kunne kana yace,
“kimun shuru tun kafin naci uban ki a wajen nan”
Tsit kakeji kamar anyi ruwa an dauke sai shasshekar kukan da takeyi hade da sakin wani ajiyar zuciya,
Hour daya ne yakaisu har cikin garin Lagos flight din na sauka kowa yafara fitowa hannun shi yasanya yariko nata hannun suka fito daga cikin jirgin,
tun kafin su karasa fitowa tuni ya hango driver dinshi sai yakuma damke hannun ta irin na muguntar nan yakara sauri suna karasawa driver din yagaida Jimetan sannan yabude masu gidan baya suka shiga,
Har suka isa gidan jimetan dake cikin Victoria island Buddu bata sani ba saida taji motar ta tsaya sannan ta tabbatar da an kawo ko kallon inda take bayyi ba yabude murfin motar yafita ganin yafice daga cikin motar yabar tane ya sanya ta rushewa da kuka hade da sanya hannum ta tabude murfin motar tabi bayan shi saidai tun kafin ta karasa tuni ya bacewa ganin ta sai tarasa inda zata bi dan kofofi ne suka kasu kashi kashi daya daga cikin ma’aikatan gidan ne wata takaraso ta nuna mata kofar da jimetan yabi,
Muryar ta har rawa yakeyi wajen furta “nagode”
Sannan tayi saurin bude kofan tafara tafia a hankali wani dogon corridor ne wanda aka kaya tashi da furruni masu mugun kyau da daukar ido sai wa’insu frame da aka man manna a jikin bangon sosai corridor din yayi mata kyau,
tsintar kanta kawai tayi a wani babban falo wanda kujeru ne masu matukar kyau farare tass dasu sai yazamana komi dake cikin falon fari ne hakan sai yayi matukar birge ta da mata kyau sai wani katon Hoton Jimetan dake manne a jikin falon Tsurawa Hoton ido tayi a zuciyar ta tace mutum har mutum amma bakar zuciya ne dashi,
kofofin da taga sun rabu kashi uku ne ya sanyata rasa inda zata nufa kawai saita samu gu akan daya daga kujerun falon ta zauna tafara rusa kuka tana kiran sunan Umman ta a hankali hade dana abbun ta sosai ta kejin wani mugu mugun kewar su.
Kamar daga sama taji an daka mata wani mugun tsawan daya sanyata mikewa tsaye a rikice tana zazzare idanuwa hade dabin Hamma Faruq din da kallo ganin yanda yahade girar sama da kasa ne yayi mugun kara rikita ta tuni jikin ta ya dauki rawa,
A hankali yafara takowa har inda take tsaye kana yaja ya tsaya yana jifanta da wani mugun kallon data kasa tantance kona menene,
Cikin rikitacciyar murya shi yabude bakin yace,
“Uban ki akai maki da zaki budewa mutane baki kina kuka Ko dukan ki akayi”
Dukar da kanta tayi tana share hawayen dake saukowa akan fuskar ta,
A karo na biyu yakuma daka mata wani tsawan yace “tambayar ki nakeyi dukan ki akayi kike barewa mutane baki kamar wata jaririya”
Saurin girgiza mashi kai tayi sai kuma takasa yin magana tafara ja dabaya dan tasan ba karamin aikin sa bane ya make ta,
A karo na uku yakuma bude bakin shi yace” waike dan uban ki bakida baki ne koke kurma ce kosai na tattaka ki sannan zaki bude bakin kiyi magana”
Yarfe hannayen ta tafarayi tana girgiza kai hade da rarraba maganar,
i… in.. a..yi
Dogon tsaki yaja kana yayi Hanyar waje hade da dacewa, ” bana sonna nadawo na sameki a falon nan inko na Tatar dake na lahira sai yafiki jin dadi sakara kawai.
Rasa inda zata dosa tayi sai kawai tafara matsan hawaye tana wani yarfe hannu a hankali tafara takawa harta isa kofa na farko hannun ta takai tabude kofar hade da cusa kanta cikin dakin da katon hoton Jimetan tafara cin karo yana sanye da kakin sojoji batare data bari taga kalar dakin da kuma yanayin shiba tayi saurin janyo kofar dakin ta rufe hade da kara matso wa’insu hawayen masu zafin gaske,
Dayar kofar dake cen dayan gefen takarasa cikin sarsarfa sabida tsoro duk yagama kamata bata kaunar Hamma Faruq din yadawo ya sameta a falon kamar yanda yafada,
Tana karasawa bakin kofar takai hannun ta tabude hade da cusa kanta cikin dakin ganin yanayin dakin da kuma yanda aka tsara komai ne ya tabbatar mata danan din ba dakin Hamma Faruq bane sabida komi na dakin purple and white ne favorite color’s dinta kenan batasan sanda murmushi ya subuce akan fuskar tata ba koda bata saniba tasan aikin Mami ne wato mahaifiyar Hamma Faruq sabida ita da kanta tace zata ma Buddu kayan daki,
maida kofar tayi tarufe hade da sanya key sannan tasaki wani wawan ajiyar zuciya saidai tuni taji cikin ta yana mata kukan yunwa bata damu da hakan bah tawuce bathroom ta dauro alwala tafito komi cikin sauri take yinshi sabida sallan Isha da taji ana kira kuma sannan batayi Magrib bah,
wardrobe din dake cikin dakin takarasa tabude duk da bata tunanin zata samu hijab a ciki saidai bisa mamakin ta tana budewa taga kaya ne jere reras a cikin wardrobe din gefen veil daban gefen hijabai daban gefen su tarkacen under wears daban sai gefen su gowns da abaya shima daban sannan gefen su atamfa da laces shima daban,
Murmushi tasaki wanda batasan sanda ya subuce mata bah saidai ko bata saniba tasan aikin Mami ne sabida daman taji su Adda rukayya suna hirar Mami ta tura da kayan dakin ta harma da kayan sawan ta wanda ita da kanta ta dinka mata su,
Hijab da sallaya kawai ta dauka sannan ta tada sallah saida tayi har isha’i tana idarwa tamike ta ninke sallayan hade da maida shi inda yake sannan hijab dinma ta maidashi cikin wardrobe,
samun bakin gado tayi ta zauna tuni cikin ta yafara mata wani mugu mugun kukan yunwa wanda har takejin gefen cikin ta yana mata wani irin ciwo
Kofar dakin da taji antaba ne yayi mugun rikitar da ita tuni jikin ta yadauki rawa sanin babu wanda zai shugo dakin sai mutum daya rintsa idanun ta tayi hade da juyar da kanta gefe hawaye na tsiyaya akan fuskar ta,
Muryar shi kawai taji yana cemata tafito taci abinci tun kafin tace yana barin ta da yunwa daga haka sai yajuya kamar zai tafi sai kuma ya dakata ya zuba mata idanu ganin yanda duk ilahirin jikin ta yana wani irin rawaa sai hakan yayi mugun bakanta ranshi,
Cikin daga murya yace mata,
“ba dake nakeyi ba ko sai nazo naci uban ki a wurin”
sai yakare maganar da takowa har zuwa tsakiyar dakin kana yaja ya tsaya, a nutsu tamike tsaye hade da gyara mazaunin rigar ta data dan sabule akan kafadar ta sannan cikin yar karamar muryar ta tabude baki tace,
“Hamma Koda ace Abbu ba mahaifin ka bane baikamata ko wane lokaci ka dinga zagin shi haka ba Abbu mahaifi nane kuma ina sonshi sosai ina daraja shi Hamma Abbu kamar mahaifi yake a wurin ka kuma sannan zagi bai kamace kaba”
Duk da a tsorace tayi maganar amma saita kauda tsoron nashi a cikin ranta a wannan lokacin dan sosai takejin wani mugu mugun zafi a cikin ranta a duk sanda yazage ta barin ma yace sai yaci uban ta,
Buddu yarinya ce me matukar hankali da gudun abunda zai bata ran mutum danko lokacin da suke zuwa hutu gidan su Hamma Faruq din sosai take kiyaye duk wani abunda zai jawo harya duke ta saidai duk da haka bata kaucewa dukar nashi dole dole idan su Zaliha sukayi laifi saiya hada da ita wajen duka,.
Sosai maganganun yarinyan yabashi mamamki bai taba tunanin zata iya bude baki tafada mai irin magana har haka ba lallai raini yana son yashiga tsakanin su kuma dole zai kawo karshen abun a yau dinnan kuma a daidai wannan lokacin,
ka’da kanshi kawai yayi hade da juyawa yakoma ya rufe kofar dakin kana yafara takowa a hankali har zuwa inda Buddun take tsaye cike da tsoro a cikin ranta barin ma da taga yarufe kofan dakin toh me hakan yake nufi bata ankara bah sai ji tayi yayi mata wani mugun fincika hade da fisge Gyalen dake yafe a jikin ta hade dayin wulli dashi gefe guda,
Nandanan jikin ta yadauki wani irin bari tsoro yadira a cikin zuciyar ta muryar ta har rawa yakeyi wajen furta,
“Hamm” Tun kafin takaiga karasawa yakai hannu yabige mata baki hade da mata wani irin cakuma ihu tasaki me dan karfi hade dafara kuka baiko saurare taba ya matseta sosai a jikin shi yanda bazata taba iya kwacewa ba yafara kiciniyar cire mata rigar dake jikin ta kuka takeyi sosai tana bashi hakuri amma kamar kara tunzura shi takeyi saida yasamu nasarar cire mata dukkan kayan dake sanye a jikin ta kana yadauke ta kamar wata yar baby yayi wulli da ita akan gado ihu tafasa hade da rintsa idanun ta tana sakin wani rikitaccen kuka,
baiko lura da yanayin yanda si!an jikim ta yake bah yahau cire kayan jikin shi hade da cewa” daman amfanin ki kenan a cikin wannan gidan”
Bata ankara ba sai ji tayi anwani finciko ta tuni sautin kukan ta yakaru tafara rokon shi tace,
“Wayyo Hamma kamun rai kayi hakuri wallahi Allah natuba bazan kara ba”
Ko sauraren ta bayyi a gaggauce yakeyin komi cikin mugunta yake mata harya samu daman fasa budurcin ta wani rikiccen ihu tafasa hade da dan kara mai cizo tana yakushin shi taki ina tana kiran sunan duk wanda yazo bakin ta tun tana iya magana har yazo ko motsi bata iyayi a hankali jikin ta yafara saki,
Saida ya tabbatar ya gamsu sosai sannan yadaga ta baiko kula da halin da take ba ya sanya wandon shi hade da daukan kayan shi yafice daga dakin,
Kai tsaye dakin shi yakoma yayi wanka sannan ya shirya cikin kananun kaya wa’inda sukayi matukar yimasa kyau sannan yadaura p-cap akai turaren shi kadai zai tabbatar maka da cewan Jimeta ba karamin mutum bane dan duk wanda yake shafa turaren hundred dollars toba karamim mutum bane,
Mukullin motar shi kawai yadauka yafice a lokacin wajen karfe goma ne na dare daya daga cikin motocin dake jere a cikin gidan yashiga yabar haraban gidan da mugun gudu,
Pablo by cubana yana daya daga cikin manya manyan club’s a cikin garin na Lagos dan duk wani shege daya isa dawuya kaga baije pablo ba dan hadaddun manyan yara ne masu ji da naira suke zuwa club din,
Tun daga bakin gate din shiga cikin club din yammata da samari suka tabbatar da isowan Jimeta dan dawuya Jimeta yaje club ba’a san da zuwan shiba sabida barin naira da yakeyi dan har gasar rawa yake sakawa tsakanin yammata duk wacce rawar ta tafi kyau tofah a take a wurin zai dire mata 2hundrend thousand,
Yana faka motar shi yammata suka soma zagaye motar saida yadauki mintina kamar goma sannan yafito yana wani busa hayakin sigarin dake bakin shi ko kallo yammatan basu ishe shiba yafara takawa har zuwa door din dazai sada shi zuwa cikin ainihin wajen clubbing din,
Tunda yashiga sai idon yammata da dama yadawo kanshi shi kuwa samun wuri yayi ya zauna ya daura kafa daya kan daya yana zukan sigarin dake hannun shi cikin kwanciyar hankali
sosai yanda yakeyi yayi mugun tafia da imanin yammata da dama a wurin ciki ko harda phendo wacce ita din yar asalin garin maiduguri ne mahaifin ta wani babban attajiri ne me matukar jida naira sosai yagama tafia da imanin ta dan tunda ta tsira mai ido takasa kauda idonta akan shi duk da tayi mu’amala sosai da maza daban daban amma yanayin Jimeta daban ne da sauran maza,
koda wata waiter ta tambaye shi meza a kawo mai sai cewa yayi yau ba zaisha Beer ba a kawo mai Malt kawai,
tunda yafice daga dakin bata farfado bah harsai wuraren karfe sha biyun dare sannan tafara bude idanun ta a hankali hawaye na tsiyaya akan fuskar ta mikewa tafara kokarin yi sai taji gabaki daya bazata iya mikewar ba kuka tafashe dashi sosai tana kiran sunan Umman ta saida ta gwada mikewar harso uku takasa sabida kasan ta dake mata wani irin mugun zafi daga karshe dai hakura tayi ta sawa sarautar Allah ido dan har tayi kuka tagaji ganin kukan bazai fishshe ta bane ya sanyata mikawa Allah Lamuran ta,
Sosai lamarin Hamma faruq yabata mamaki bata taba tunanin muguntar tashi har takai haka ba kenan wane irin zama zasuyi da Hamma Faruq din zama kenan zatayi na irin matan da basuda yancin kansu a gidan mazajen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE