
NOOR ALBI CHAPTER 5 BY MAMUGEE
Guraren la’asar Rana ta Dan bude kadan daga hadari da ruwan da aka tashi dasu
Tana ganin ranar ta Dan bullo ta kwaso kayan wankin jiyan datai Wanda iska ya lalata tasake wankewa sama sama ta shanya
Tana gamawa ta sakarwa abbanta labulan palonsa sbd magriba datai danma yau Bata fito dashiba Shan iska tsakar gida kamar yanda tasaba kullum take fitowa dashi yasha iskan yamma sai magriba ta turasa ciki
To yau sanyi sanyin ruwan da akai yahanata fitowa dashi Dan ita kanta dannewa tayi Amma zazzabin dukan ruwan datashane yake cinta sosai Amma ba amfanin kwantawar Dan haka ta danne sai idanuwanta ne dasuka ja
Sai Wanda yakeda zurfin ganewane zai gane zazzabi ne ajikinta.
Alwala tayi bayan tasake share tsakar gidan tas ta shigarda komai kicin tarufe kicin din Dan dama abinci daya sukeyi har dare basa abinci biyu matuqar ba baqi Momy tayiba aka cinye abincin Amma abinci daya akeyi har dare sbd lallabawa da neman da take.
Dakinta ta Isa ta tayarda sallah cikin dauriya tayi sallar tazauna tana adhkar har tsawon lokaci saidataji zazzabin na neman fin qarfinta ta miqe batareda ta cire hijabin sallartaba ta nufa kofa tafice zuwa gurin Abba Dan bashi abincinsa da magani kafin ta kwanta jikin ya hanata tashi.
Cikin qarfin hali tagama bawa Abban abinci tabasa magani ta maida kayan kafin tadawo ta zauna tana goge Masa fuska sai alokacin Abban yaji tsananin zafin hannuwanta da har wani siracin zafi sukeyi
Ya zuba Mata idanuwansa kafin ya Dan motsa hannunsa alamar mgn
Ta kallesa tana kawarda abunda ta fahimci yaji Wato zafin jikinta.
Cigaba da gage Masa fuska tayi tana qin Bari ya kalla idanuwanta dasukai laushi
Tana gamawa ta miqe tana Masa addua Tai Masa Saida safe ta fito takoma daki Kai tsaye Tai sallar ishai ta kwanata take baccin wahala ya dauketa a gefen katifarta ko rufar arzki bataiba.
Washe gari sbd zazzabin data dauka zai sauka kafin safiyar yasa tayi lattin tashi jikinta a matuqar zafafe da zafi Amma hakanan ta tashi taje tayo alwala tazo tayi sallah
Tana gamawa ta miqe ta fice Dan ayyukanta data Saba dasuke gabanta.
Kunun abbanta tafara damawa kafin ta soya doya tadafa ruwan Lipton ta juye a qaramin flask ta Kai Palo tadawo ta dauki na abbanta takai masa.
Cikin dauriya tayi aikin gyaran koina ta zauna tana bawa Abban abinci,
Daga fuskarsa Yana iya Jin hucin zafin jikinta dake hurowa
Take jikinsa yayi matuqar sanyi zuciyarsa ta narke da tausayin kansu dagashi har itan
Ya zuba Mata idonuwansa dasuka sauya Yana danne hawayen Dake kokarin gangaro Masa Dan karya qara Mata damuwa akan wannan halin datake cikin.
Tana Gama basa ta gyarasa ta fice zuwa gyaran palon Momy da dakunansu,
Daqyar tagama gyaran ta dauki kasko ta fita tasamo garwashi maqota tadawo ta zuba turaren wutar kadan ta aje palon Saida ya Kama koina har dakunansu kafin ta dauka takaiwa abbanta shima ya samu tadawo da kaskon tsakar gida ta aje.