WAYE ANGON MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 20 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 20 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

Inna lokacin da ta fito taga abin da aka mata, ta dinga fada in da take shiga ba ta nan take fita ba, bala’i take har zani na faduwa.

“Iskancin da aka min kenan kan wata amarya can! To wallahi ba zan yarda ba, duk abin da aka lalata min sai an biya ni, amaryar banza. To za ka zo ka same ni, kaje ka

auro. “yar mahaukata ba da ni ba wannan abin kunyar, kazo ka sakar musu ‘ya wallahi an zo an tarwatsa min gida an lalata shi, to ban yarda ba. Sai da safe sannan D.P.O yake jin abin da ya faru, ya tambayi kowa. Abin

ya daurewa ‘yan sandan kai,

wadanda ke gun, D.P.O ya ce,

“Wannan abin yafi karfina, sai dai a tura

ku kotu, ita ce zata yanke muku hukunci aba mai mata matarsa ko kuma kowannanku ya hakura. Har dare ba su dawo ba, daga bisani ne aka sallami kowa don ba mai laifi, babu mai laifi a nan sai iyayan Mabarukan,; don haka su kotu zata kama da laifi su za’a

tuhuma, meye dalilinsu na yin hakan? Sai dare can sannan suka komo gida, kowa ya kama

gabansa. Gidan su RafI’atu ta wuce, don ba za ta iya zama daya daga gidan iyayenta ba, don su suka jefata wannan masifar.

Duk amarya ana mata aure a kaita gidanta a ranar tana farin ciki amman ban da ita, tazo iya wuya matuka, bakinta ya kulle bata da abin cewa. Ta sha maganin ciwon jiki ita da Rafiar bayan Maman Rafi,a ta matsa mata tasha ruwan lipton don kar maganin ya dame ta, rabonta da cin abinci har ta manta.

Ta kwanta lamo ita ba bacci ba ita ba tunani ba, sai dai hawaye dake zarya, ta rasa me ke damunta ta dora kanta saman cinyar Rafiatu, a hankali take shafa mata kai donta samu bacci, amman idonta kamas babu alamarsa

Daga angwayen nata guda biyu Sulaiman da Imran zuwa iyayenta ba wanda bai isheta da kira ba amman ba kiran wanda ta dauka, daga karshe ma ta kashe wayar

gabadaya ta wullar da ita can gefe.

Ranar da suka fara zama kotun Musulunci, Alkali ya bukaci ganin Babanta, Mamanta, Baba Haruna, Baba Hamza, Imran, Sulaiman tare da Mabarukan. Duk suka fito gaban kotu suka tsaya, sannan Alkali

ya ce su koma su zauna. Bayan sun zauna ne sannan ya bukaci ganin Baban.

Ya fito ya tsaya inda ake tsayawa, akwai Lauyoyi masu kare bangaren Imran da ya dauka jin an kai maganar kotu, shi ma Sulaiman baisa wasa ba ya dauki

Lauya. Alkali ya bukaci sanin meye sunansa.

Ya gyara tsayuwa ya ce, “Sunana, Yusufu Ali Daura. Alkali ya Kara cewa,Wane addini ka ke bi?” Ya ce,Musulunci.Ya kara cewa’

“Daga baya ka Musulunta ko ko da shi

kataso?”Da shi na taso, na tsinci iyaye da Kakanni suna yin shi, ni ma da na gan su sai na ci gaba da bin shi har zuwa yanzu.”

Alkali ya ce, “A takaice ko za ka iya fadawa kotu tarihinka, waye kai?”

Ya ce, “Eh, ba laifi zan iya. Kamar dai yanda nace sunana Yusufa, asalina dan garin Katsina ne cikin garin Daura, iyayena da Kakanni duk a can suke, nazo wannan garinne tun ina saurayi neman kudi da ilimin

Muhammadiyya. Alhamdulillah na samu ilimin, sana’a kuma ba wacce bana yi in ta samu ce, naji dadin zama garin nan, saboda ci gabansa da yanda ake samun ilimi. Na ci gaba da zama a gidan Malaminmu tare da abokaina, Allah cikin ikonsa har nayi aure na samu

hayar daki daya na tare da matata. A lokacin

ina sana’ar wankin hula kuma Alhamdulillah ina samu, Allah yasa min albarka a

cikinta har zuwa yanzu kuma da ita nake cin abinci. Bayan aurena da shekara uku na samu karuwar haihuwa ta da namiji, a nan take ya koma, Bayan shekara na kara samun haihuwar shima sati biyu taron sunansa ya koma.

Sai bayan shekaru uku sannan na sami ‘ya mace,muna ce mata Salaha. Watanta hudu Allah ya amshi abinshi. Muna nan muna nan dai kamar ba za a kuma ba can sai ga wata haihuwar, a nan muka samu haihuwar

Mabaruka, to Allah ya rataya Alhamdulillah wannan shi ne a takaice.Alkali ya kira Mahaifiyarta ta tsaya a dayan gurin ya

Ce,Atakaice ko za ki fa da wa kotu tarihinki?”

Ta ce,Eh! Sunana Halima Bello, ‘yar nan garin ce ni, mahaifina shine Mallam Bello, gidanmu duk mata ne nice mace ta farko agidanmu.

Ina da kanne biyar, nayi aure tare da Mal. Yusufa kamar yanda ya ce, Allah ya bamu ya’ya hudu tare da shi amman Allah bai sa sun tsaya ba sai Mabaruka. Alkali ya ce,

“Meye rayuwar aurenku da shi?”

“«Eh, lallai kam an sha fadi-tashi na rayuwa tsakanina

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE