WAYE ANGON CHAPTER 13 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 13 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

 

Ya ji kamar ya yi kuka saboda takaicin tsare shi da. tayi, da tuni ya yi nisa da tafiya. Kuma bai isa ya tafi ba

ba tare da ta sani ba, dole sai ya ce zai fita.

Ta ce, “Zaka zauna ko sai na mike nima?” Ba shiri ya koma ya zauna, sam ba yunwa yake ji ba, dokin da yake

ma bai bar shi ya ji yunwar ba.

Ta kwalawa Samira kira, budurwa ce kanwarsa ta shigo tana gyara daura zani, kanta ba dankwali sai gashi

da ya tashi buzuzu, ta ce

“Gani Inna.” Ta ce,Zubo

mishi kokon da dumamen.

.” Ta ce, “To.” Ta fice tana

Kwalkwalar tasona.

Shan koko da cin dumame dole ne farilla sai ya ci shi sannan ya tafi duk in da za shi, duk da yana da mata bata

yarda yaci na matar ba sai dai nata.

Sai dai ya ci wancan a boye, sannan ka’idarta ba a mata sauran abinci in ta zubo maka dole sai ka cinye shi.

Ta dawo dauke da kofi na roba cike da kokon, sai

kwanon dumamen tuwo miyar kuka shar sai kwandala-Kwandalan waken da ka ke hangowa, da ganin shi bai

dahu ba, guda-gudanshi yake. Ta ajiye a gabansa ta fice.

Haka ya ci gaba da karyo tuwonnan yana ci saboda

dan banzan taurinsa kamar ya fasa ihu. Sai da ya tura

tuwonnan duka tumbinsa, ya wanko hannu ya dawo yana cewa, “Ni na tafi.”

Ta ce,

“Ina kayi kenan?” Yayi jim! Sannan ya ce,

‘”Akwai wasu abokaina da zamu hadu da su to can nayi.”

Ta ce, “To jeka Allah ya tsare.” Ya ce, Amin.’

“Har yana

hardewa wajen sa takalmi, kar ta Kara tsayar da shi.

Har ya wuce ta kira shi ya ji kamar ya runtuma kar ya

dawo, ya dai daure ya dawo din. Ta ce,

“In ka fita ka ce

wa Saddiku mai shago in yaga yara da kwanon siyen koko ya turo su.”

Ya ce, “Koko kuma Inna? Ana bikin ba za ki hakura

ba?” Ta dago da bala’inta ta ce, “Ka ji min dan iskan yaro, auranka din banza zai hana ni neman kudi, za ka ba nine?”

Ya yi saurin cewa,

“A’a yi hakuri.

.” Daga haka ya

juya. Ta ce, “Kai zo nan.

.” Ya juyo ta ce,

“To in gaya maka ko ranar da aka kawota sai nayi ba fashi kajiko?”

Ya ce, Naji sosai Allah ba da sa’a.

” Tace,Amin, jekato.”

Ya juya har ya kai zaure ta kara Kwala masa kira. Ya

dafe kai “Oh ni Sulaiman! Na shiga uku.” Ta Kara dago

murya, “Sulaimanu kana jina kayi shiru ko nasan ba ka isa ficewaba.”

Ya juyo dole yana kumburi. Ta dube shi da kyau tace, “Wai saurin me ka ke ne, in fa kayi wasa wallahi za a daga bikinnan.” Ya zaro ido “Dagawa kuma Inna?”Ta ce, “Eh! Ko ban isa ba? Sai a fasa ma gabadaya

Ya yi saurin cewa “Kin isa mana sosai, ayi hakuri.” Tayi kwafa ta ce, “Jeka to Allah ya tsare, ka duba in mai

kosan nan ta fito.?Ya ce, “To.” Da sauri ya wuce. Ta dago murya “Karka yi dare fa.”

Shi ma ya dago “To an gama Inna.

Da gudu ya karasa fita. Ya saki ajiyar zuciya da dafe Kirji.

“Wai, Allah ya fito da ni! Inna jaraba.” Bai saurari ya duba mai kosan ba, don ba dawowa zai yi ya gaya mata

ba abin da ya gani. Ya tare mashin ya bar unguwar zuwa hidimominsa.

Koda suka tashi ita da Rafi’a, tun sannan mai gyaran

jikin da aka dauko ta fara aikinta, in da ta hau darzar

mata jiki tana yi tana zoBara baki da musu,

Idan mai gyaran ta ce tayi haka ta ce a’a, ita ga yanda za ta yi. Abin ya kai matar bango ta ce, “Shin ke wace

irin yarinya ce da kafiyar tsiya? Na ce haka kin ce haka,

a gyara ki ne ba kya so ba ki ga kudaden da Mamanki ta

kashe ba a kan gyarannan?”

Ta turo baki ta ce, “Yo ina ruwana.

“‘ Rafi’atu ta ce,

“Don Allah kiyi hakuri kar ki ga laifinta.

Ta dube ta. ta ce,

“In tambaye ki don Allah?” Ta ce,

“Ina jin ki.? Ta ce,

‘”‘Amman auren dole za a yi mata ko?”

Ta kasa bata amsa, sai dai Mabarukan ta ce “Kwarai

kuwa, auren dole auren maza biyu kuma.

Mai gyara ta kasa fahimta. Rafi’ar ita ta mata bayani,

abin ya bata mamaki matuka, ta dubi Mabarukar ta ce,

“Eh lallai kam dole kyayi kumbure-kumbure, Allah ya sawake.”

A dakin da suke kusa da na Imran ne, ya shiryo tsaf

cikin dogayen kaya farare sol yasha hula da farin glass,

ya zauna a saman dogon hancinsa.

Haka kuma ya yi wa kyakkyawar fuskarsa kyau, mai

haske. Dakin bude yake suka yi ido biyu da ita lokacin

da yake tsaye a falo suna magana da Momy.

Tayi masa kyau sosai, ya saki fuska yana mata

murmushi, ya yi mata alama da “kin yi kyau” daga can ta

gallo masa harara tasa Kafa ta banko kofar ta rufe.

Ya yi dariya abinsa ya wuce. Motarsa tayi ready an

wanke an goge, ya shiga ya zauna ya turo mata text.

Kin yi kyau my light, you will receive millions kiss from me, Insha’Allah.

Urs husband,

Imran Umar.

Ya yi dariya yaja motarsa, Maigadi ya bude masa Gate ya fice.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page