MISBAH BOOK 3 CHAPTER 20 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 20 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

maganin Barci ta sha amma kamar bata sha

komai ba daga karshe ta mike ta dauko labtop dinta ko za ta samu rubutu ya dauke mata hankali amma sai ta kara tsintar kanta a yanayin da yafi na da duk

wani soyayya karya ce duk wani alkawarin amana karya ce babu shi a duniya duk kowa mayaudara ne maci amana duk da namiji ya iya maka dadin baki da alkawarin karya har ya rufe ma ido ka yadda da shi

sai daga bayan aure ya nuna asalin halin,nan tayi wurgi da system din ta ce.

“Nayi bankwana da rubuta love story dama ko

wani irin labari ina rubuta abin da na yadda da shine kuma nasan zai iya faruwa amma yau na wayi gari na fahimci abin duk karyan banza ce.

Haka nan tunanin Mislihu ya fado mata ta fashe da kuka tare da fadin “Allah ya jikanka gwarzo na mai gaskiya namijin duniya Allah yasa Aljanna ce makomarka da dukkan sauran musulmai da suka rigamu gidan gaskiya.

Haka ta haye gado tana ta juye-juye da barcin

ya gagara ta mike tayi bayi ta dauro alwala tazo ta fara sallah haka ta kwana sallah da addu’oi tare da karatun AL-KUR’ANI mai tsarki har gab da asuba sannan tayi raka’atainin fajir da aka Kira sallah tayi

bata mike ba har sai da ta gama azkar din safiya tare da karatu har rana ya fito.

Sannan ta mike ta nufi bangarensu Baba audi ta Fada musu irin Breakfast dim da za’ayi a kaiwa amarya da ango da farko tasa hannu sumayi tare amma sai taji barci na fisgarta saboda kwana da tayi ido biyu dan haka ta barwa su baba audi ta koma ciki tayi wanka ta shirya tab irin shirin fita asibiti da tà saba sanna ta koma kicindin taga sun

hada komai sai da ta tabbatar an kai musu sannan taja motar ta tayi asibiti,tabi kan marasa lafiya ta dubasu sama-sama sannan ta nufi gidanta na cikin asibiti ta kulle ta haye gado tare da kuna A.C tuni barci mai nauyin yayi gaa da ita

Al,amarin Deeni da Farida kuwa abubuwa sunki dai-daituwa duk iya kokarinta da jan hankalinta akan Deeni ya kwana da ita tasamu ta mallakeshi su zama abu guda abin ya gagara,na farko gani yake yaya zai fara kwanciyar aure da matar yayansa duk

da baya duniyan kuma addininsa bai hana masa ba amma duk da haka abin ya gagareshi a tun lokacin da Farida ta auri wani soyayyarta da sha’awarta ya fice masa a zuciya lokacin da yake son ta da muradinta bai samu ba sai lokacin da bashi da

bukatarta. Sannan abu na biyu tabbas ya tabbata yaci amanar Misbahn shi ya runtse ido yana tuno alkawarin da yayiwa Misbah irin alkawaran da suka yiwa juna wanda ita har yanzu bata karya ko daya ba har da kuwa alkawarin da ta masa na cewa duk randa ya auri Farida ita kuma za ta bar shi

HAR ABADA. Duk da ba saki su kayi ba amma sallamashi da tayi hakane ta yafewa Farida kwanakinta to ba komai tunda haka ta zaba ni zan iya binta a haka a wannan dare dai Farida bata samu yadda ta ke so ba.

Saboda halin da Deeni ya tsinci kansa bashi da wani sauran sha’awa ko natsuwar da zai iya kwanciyar aure da ita,duk makaman yakinta ba wanda Farida ba tayi amfani dasu ba, wurin jawo hankalin Deeni gareta amma ta lura bai sanma tanayi ba sai dai ya kalle ta ya kau da kai wata zuciyar kuma ta ce masa duk wannan dan’uwankane akayiwa kafin kai to meye abin birgewa aciki ina ma Farida wani ta aura wanda ban sani ba,hala abin yazo min da sauki tunda na auri Farida sauke hakkin

aurenta ya zame min dole haka karya alkawarin da nayi tsakanina da Misbah ya tabbbata. Tsawon sati guda suka dauka a haka sannan da kyar ya samu ya iya sauke nauyin hakkin Farida dake kansa,ba dan ya so ko yaji dadin hakan ba rayuwa ke nan duniya juyi-juyi akwai wani lokaci abaya da bashi da buri ko muradin da ya wuce yaga

sun zama abu daya da Farida. Sai gashi yau ya tsinci kansa da tsanar yin haka

gaba daya haushin kansa da kansa ya kamashi ya tashi ya fita yabar gidan ya nufi gidan gonarsa ya hada kai da gwiwa yana jin zuciyarsa na masa kuna gaskiya ne Misbah na naci amanarki ban san da wani ido zan kalleki ba duk matakin da kika dauka a kaina dai-dai ne. Al’amarin Farida kuwa abin ya tabata yadda ta zaci irin zazza fan soyayyar da Deeni yake. mata a duk randa suka hada shimfida zai gwada mata irin soyayyar da yake mata sai gashi shamsu ma da ba auren soyayya sukayi ba yafi nuna mata kauna da

riritata a daren su na farko da gaske Deeni ya daina sona? da gaske Deeni yafi son Bahijja fiye dani da gaske Deeni ya aure nine abisa dole ne? Tabbas yau na ga zahiri tuni ta fashe da wani irin kukan bakin ciki anya akwai abin da yafi ciwo da zafi ga ya mace irin ace mijinki baya sha’awarki baya jin kusantarki sai dai ya kwanta dake dan kawai ya sauke hakkin aure nan ta zauna tayi kuka har taji ba dadi a nan ta fahimci wancan soyayyar da take gadara da shi a baya ya rushe babushi sai dai tayi kokarin,gina wani shin ta ina za ta fara?

Bahijja ta riga da ta mallakeshi bayaji baya

gani sai Bahijja shegiyar marar asali nayi alkawari sai na rabaki da Deeni ko ta girma ko ta arziki saboda muddin kina gidan nan

ba zan taba samunkan Deeni da hankalinsa ba Deeni kuwa nawa ne ni daya mallaki nane ba zan bar maki shi ba nan ta mike ta share hawayenta tare da kaiwa da kawowa tana tunanin hanyoyin da za tabi haka

rayuwarsu ta kasance kowa yana bangarensa yana harkarsa wani lokacin Bahijja da Deeni sai su dau tsawon kwanaki basu hadu ba in ma sun hadun gaisuwa ke hadasu tare da tambayar lafiyar juna

duk wani hakkinta na aure akan Deeni tana

saukewa tun daga kan masa girki kula da gidansa da kuma tsare amanar aurensa.

Dukkansu sun zama tamkar bakin juna

ba sakewa ba wani sauran shakuwa tamkar ba Deeni da Misbah ba,yawanci in dai anji wani hayaniya a gidan to nasu Deeni karami da Aisha ne,nan ma Farida na jin sunyi bangaren Bahijja za ta koro su.

À kwana a tashi ba wuya Farida ta samu

gurbin karatu aji daya a uni lag bangaren

turanci,dan hakagidan ya zama ba kowa daga safe har yamma sai masu aikin Farida da kumasu Baba Audi da ma’aikatanta Misbah sai masu gadi wani

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page