ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 20 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 20 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Mai kaunar ki,

Alhaji Kahir.

Aliyu ya ce, “Lalle Asiya kwanan nan za ki

zama Hajiya Naira, Allah ya hada ki da dan karya” Yana dariyar yake gaya mini haka. Ya ci gaba da neman in ba shi wasikar ya gani, na so in hana shi gudun ka da ransa ya baci ganin abin da Kabir ya rubuto, kuma ina tsoron kada ya dauki wani abu a ransa, sai na mika masa. Ya karanta ya yi tsaki.NaCe da za ka taimakan na baka

wadannan kudi ka mai da masa, maimakon in bai wa Mama Inki ta basu abinsu”

Sai yace Ba zai yiwu ki ba za a mai da ba,

ai shi ya baki, da bai dasu ba zai baki ba. Saboda haka ki dai yi shawara da Mama Inki”

Na lura Aliyu hankalinsa ya tashi kwarai da

ganin wannan kudi daidai kwatankwacin bacin ran da muka yi kwanan ba ya. Aliyu ya mike tsaye bayan ya duba agogo, yaCe,

“Gara in tafi sai mun z0 gobe”

Ba tare da ya dube ni ba, har ya kai tsakiyar daki sai na daure na kira sunansa cikin murya mai nutsuwa. Ya tsaya Kyam a a tsakar daki, ya amsa mini yayin da ya saka hannunsa na dama a cikin aljihun wandonsa. Na, tashi na je daf da shi inda yake tsaye, na ce,Aliyu ba na son ka tafi zuciyarka na cike da zafi game da ni, saboda na lura ko murmushin sai da safe

ba ka yi mini ba, don Allah ka daina sanya wanda bai taka kara ya karya

zuciyata ba yana kuntata maka rai”

A wannan lokaci sai nayi masa abin da ban

taba yi ba, na jawo hannunsa na rike a yayin da na dora kaina bisa barin kafadarsa. Sai nan da nan ya fiddo hannunsa ya tallafo ni, ya kara jan hannuna ya zuwa bisa Kirjinsa, har na tsawon lokaci. Sai da na ji ya fara rawar jiki sannan na daga kaina sama muka yi ido

hudu da shi na lura idanuwansa sun kada sunyi jawur, sai muka yi murmushin so da kauna. Can sai ya ce,Asiya na riga na san yadda nake son ki ke ma ina ji a jikina kina so na, amma nayi mamaki yadda ba ki son raina ya baci, tunda na ga kin yi mini abin da bakya so, amma don ki kwantar mini da hankali yau kika yi. Asiya ina mai tabbatar miki da

cewa, ba karamar gagarumar nasara ba ce a gare ni idan har kika zama matata, haka kuma zai kasance babbar asara a gareni idan na rasa ki, saboda kina daya daga cikin mata masu kaifin imani da hankali da Kwakwalwa mai zurfin tunani Ban ga laifin Kabir ba, tun da duk namiji mai son kwanciyar hankali a gidansa da son samun zur ta gari zai so samun mace kamar ki, ba wai don kyau

da Allah ya yi miki kawai ba maza ke kwadayi a gare ki, a’a, har da Karin nutsuwa da kamun kai da kike da su

Sai ya jawo hannuna na dama ya sumbaci

tsakiya, ni kuwa na kara rusuna kaina bisa kirjinsa. A haka na makale a bangaren jikinsa, na ce,Aliyu mu je in raka ka kada Baba Suraj ya gaji da jiranka”Muka yi dariya muka nufi falo. Sai da muka isa daf da falo sannan na zare jikina daga jikinsa, ya Kara murza mini yatsu, fuskar Aliyu na cike da annurin farin cikin da ban taba gani ba sai a wannan

dare. Da safe bayan mun gama kalaci, muka shiga dakin Mama Inki da ni da ita na bayyana mata komi da komi., na ce tasa a mayar wa da Alhaji Kabir kudinsa. Amma ta nuna mini sam wadannan kudi ba za ta iya mai da wa Kabir su ba, sai ma ta hada mini har da wadancan dubu  dari biyar da ya taba ba ni, ta ce in kai wa mahaifina shi ya san dabarar da zai yi a kai

ba tare da ya bata wa kowa rai ba. Kin ga idan sun amince da Aliyu shi ke nan faduwa ta zo daidai da zama

Da kyar ta shawo kaina na yarda zan tafi da

wadannan makudan kudì, amma ina ma dai ace ita ta tafi da su idan ta tashi zuwa Malumfashi ta kai musu ta yi musu bayani da kanta. Na yi tunani a wannan zamani wadannan kudi sun isa mahaifina da

mahaifiyata su ziyarci aikin Allah mai girma da su, amma saboda kin da nake yiwa Kabir bana ko bufatar abin hannunsa.

Da misalin karfe daya da rabi muka isa.

domin ba mu bar Kaduna da wuri ba

Suraj ya ce,Asiya za mu biya gidan tawa amaryar ku gaisa kafin ku isa Malumfashi”

Na ce,To’Sai Aliyu ya juyo ya ce mini,

“Ba ki cewa ya tambayeni inna yarda sannan

a kaiki ganin amaryar?” Na yi murmushi na ce,

“Àliyu ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne”

Suka tuntsire da dariya. Lokacin da muka

isa unguwar su Jamila da ake kira Gangaren Ammani, a nan Suraj ya ja birki ya gyara fakin din motarsa ya aje ta cikin karkashin

darbejiya inda wasu dattawa ke zaune.

Wannan unguwa na da yawan yara kanana,

kafin ka ce haka yara sun rufe motar ruf. Dattawan nan suka rika tsawata masu, yayin nan ne Suraj yaCe,

“Idan kin shiga ki nemi Jamila ki shaida mata

tare muke Na yi sallama kamar sau uku kafin a amsa mini, saboda babban gida ne, wanda da alama yana

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page