ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 16 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 16 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

mahaifiyarsa na kuma tabbata hoton Innar tamu ce, saboda na lura kuna kama da ita, shine na ga ka aika mini da hotonka ba ka bani nata ba, ni ko shine nake so in tambaye ka ka bani Yayi murmushi ya nuna mini a zahirn cewa nayi masa Wata magana wadda ta faranta masa rai wadda kuma na yi imani ta Kara mini kwarjini a „ zuciyarsa.

Sannan ya ce, “Na ji dadi Asiya ko ban aure

kIba na godewa Allah da ya hada ni dake saboda na san son Allah kikeyi mini, amma nima zan nemi wata alfarma a wajen ki kafin in baki wanna hoton da Kika bukata Na Ce,

‘”To Aliyu fadi nima idan batafi  Karfina ba zanyi Ya Ce, Za ki yi Asiya sai dal idan bakiyi

niyya ba, bukatar ba wata mai tsanani ba ce, so nake don Allah ki yi mini tausa da hannayenki masu taushi kamar auduga

Na yi tagumi na yi shiru ina tunanin wai duk

maza haka suke ba su da hakuri, ko kuwa dai Aliyu ne kawai yake mini haka? Ina Kara kawo maganar mahaifiyata cikin zuciyata, inda kullum take mana gargadi ni da Hadiza tana cewa, “Kada ku kuskura ku saki jiki da

namiji duk yadda kuke son sa. Yawancinsu mayaudara ne, idan sun gane kuna CIWon SOn Su, babu wuya su tilasta muku su rinjaye ku, har ku kaiga alkata akin shedan. A duk inda namiji da mace suka kebe in dal ba

maharramarka ce,ba to lallai shedan shine na uku a tsakani yanayi muku hudubar

Iblis. Kuma ku kasance masu kunya ga samarinku, saboda an ce kunya adon dan halak idan namiji ya sa ku yi masa abin da bai dace ba kuka yi, to wata ran zai sa ku yi abin da mafarkinku bai taba nuna muku ba.

Daga nan mutunci ya zube, K0 kun aure su yarda da amincewa za ta yi wuya tsakanin ku. Amma idan sun buga sun

raya kukaki to ina tabbatar muku har abada ba zasu taba zarginka da Komi ba, tun da sunga sun haddace halayenku tun kafin su mallake ku’Ina cikin wannan hali ne na tuna hudubar mahaifiyata, sai naji Alyu ya ce,

“Asiya ya ya naga fuskarki ta canza nan da nan, ko abin da na ce ya bata miki rai ne?

Na ce, “Aliyu irin wadannan abubuwan basu

dace da rayuwar dan musulmi ba, idan irin haka na faruwa a tsakaninmu ina tausayin kanmu nan gaba. Mu duka ba Annabawa ba ne ko wasu Manzanni da aka tsarkake daga fadawa kowane irin mugun aiki, cimma biyan bukata.Idan harna zama mallakarka, wallahi tausa na daga cikin Kananan abubuwan da zaka samu daga gare ni, wadanda ina ganin sun zama dole in yi maka ba har sai ka Bata bakinka ka roke ni ba Aliyu ina rokonka ka rika sanyawa zuciyarka hakuri, kada ka bari shaidar na zuga ka a bisa wani

abin jin dadi na Kalilan, karshe ya zame maka abin bakin ciki nan gaba.

Yanzu kana ganin idan har na yi maka tausa,

nan gaba ba zaka nemi abin da ya fi haka ba a gareni? Aliyu na san kana so na, so kuma na hakika, saboda haka babu abin da zan yi maka ka gamsu a halin yanzu dama zai zame maka kamar ina yi maka susa ne bisa rauni. Ka ga babu maganarwarkewa sai

raunin ya kara kwakkwabewa. dan kuma ka ga

wadannan maganganu nawa shirme ne, to bismillah sai in yi maka tausa har barci ya dauke ka ba zan daina ba Sai ya tashi zaune tsam ya ce,Ada Asia na dauke ki yarinya kwarai, ban kuma taba zaton za ki iya shirya maganganu irin wadannan masu shiga jiki

ba. Wallahi kin sa kafafuna sun yi sanyi, kuma ina mai tabbatar miki ina alfahari da hankalinki, kuma na sakankace ashe ke yarinya ce mai halin manya. Na yi imani zan samu iri na kwarai a gidana, kamar yadda kika ce ne, so in ya yi yawa halaka ne,ni kuwa yanzu yaddah nake ji Asiya kamar in dauke ki in hade, in rika jinki cikin jikina. Kuma babu namijin da zai ganki har sai ya cimma burinsa na ya mallakeki” Na Ce,

“Idan Allah ya yarda kada ka sa

shakkar komi a zuciyarka, wata rana za ka ganmu tare” Sai ya ce,Don Allah Asia shiga kicin ki damo mini fura ki káwo mini”

Na bude “firij na fiddo ledar fura da jakar

nono, na sami kwano na saka, sannan na leka falo nace,Aliyu ban ga koshiya ba, ko in dama da hannuna?”Sai ya yi dariya ya ce,

“Asiya ya ya zan ajiye Koshiya tun da ban iya amfani da ita ba, balle kuma

yarona shi ma ba zai iya amfani da ita ba; wannan sai ku mata, ki sa hannu ki dama mini kawai Na kusa gamawa kenan sai dankwalina ya sunce, a daidai wannan lokaci Aliyu ya shigo, sai yayi sauri ya dauke mini shi daga Kasa ya rataya wuya yana kallon gashina.

Ya Ce,Amma Asiya gashinki bai kitsuwa

ko?”Na ce,Me ka gani?” Ya Ce,

“Na ga zai yi sulfi kuma yana da

Tsawo da yawa”Na yi murmushi na ce,

“Ko na yi kitso bai kwana biyu sai ya warware

Ya Ce;Yauwa kin ga na samu yadda nake so

ke nan, daman ba na son kitson nan, sai dai in sawo miki kayan gyaran gashi, kullum ina ta kallo yana sheki. Wai shi leshi babu wani dinki da ake masa ne sal riga mai hannu?”

Nace A’a, ana yi masa dinki kamar yadda

ake yi wa shadda ko atamfa, ya kasance ne yadda mutum ke da sha’awa”

Ya ce, “To ni dai na fi sha awar mai hannu

saboda ya dace da leshin da kuma yadda kirar jikinki take, komi naki ya yi das, ban ki ba in ta ganin ki cikin wadannan kayan Asiya”

Na dube shi na yi murmushi na ce,

“Kai Aliyu komi sai ka yi magana a kansa®

Sai ya yi yar dariya yace Kai

. Sai na yi sauri na dauki kwanon furar na

nufi falo na aje masa. Bayan ya gama sha ya ce, sai in sha sauran, akan dole na dauka na sha. A nan muka ci gaba da hira, a inda na nemi sanin ko kannensa na wa

Sai ya ce.Asiya ki godewa Allah da ya baki

‘yan’uwa maza da mata wadanda kuke daki daya.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page