ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 14 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 14 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Da gari ya waye bayan mun yi duk abin da

muka saba, sai Mama Inki ta ce in shirya zan rakata kasuwa. Kafin mu isa kasuwa sai da muka biya gidan abokin Alhaji mijin Mama, ana sunan matarsa wadda ta haihu.

A kasuwa Mama Inki ta yi sayayya, amma ni

ribon na saya na daure gashi kala-kala, bamu dawo ba sai bayan azuhur. Ina dawowa Ummi tace mini, “Aliyu yanata  bugo waya

Na yi bakin cikin zuwa na kasuwa, saboda na

huce ina son magana da shi. Bayan na yi sallar magariba na zauna ina ta rokon Allah ya sa Aliyu yaZo idan har baizo ba ban san irin kukan da zan yi ba, sai Kwalla suka dinga fito mini. Na shiga bandakin da ke cikin dakina na sa sabulu na wanke fuska ta, na zo na shafa gazar da hoda saboda kada Mama Inki ta gane na yi kuka. Zuwa can sai ga Ummi ta shigo, ta ce, Anti gasu Aliyu can da Baba Suraj sunzo wajen Mama”l- Na ji wani irin sanyi ya sauka cikin zuciya ta irin wanda naji lokacin da Suraj ya z0 ya gaya mini Aliyu yace yana sona. Na tashi na kara gyarawa, na daure gashina na sake shi bayana, ya kwanta lambam

bisa kafadata. Sannan na gyara daurin dan kwalina yadda ta ko ina ana iya hangen gashin. “Zuwa wani dan lokaci mal tsawo sai

ga Maryam, ta ce, “Mama Ink na kira’

Na tashi ina takawa a hankali kamar yadda na

san Aliyu na rudewa idan ya ga ina irin wannan

tafiyar. Na shiga na yi sallama, na sami kujera na zauna, na gai da Baba Suraj ya amsa, sannan ya ce,Mun z0 lallashi ne Asiya

Mama Inki ta ce,A gaskiya ni kam ban san

Aliyu ya yo waya nan gidan ba, sam ba ta fada mini ba. Ko da yake dalilin da yasa na san har akwai rigima a tsakani, ganin ta na yi tana kuka, da na matsa mata da tambaya har sai da na ji dalilin son ta tafi bayan hutu bai kare ba. Abin da ya fi bani dariya a wannan rigima Suraj shine, ita Asiya ta fita da niyyar Aliyu ne ya zo har ta karasa wajen motar da sauri, saboda ta ga jar mota

kalar ta Aliyu, sai da ta je daf da shi sannan ta ga Kabir ne, ita ba ta san bambancin mota ba, idan dai ta ga kala shi kenan”

Sai aka Kyalkyale da dariya gaba daya, na ji

kunya na hada kaina da gwiwa.

Sai Mama Inki ta tashi, shi kuma Suraj ya ce,

“Alhaji na falonsa ne ko yana cikin dakinsa Hajiya?”Ta ce,Yana nan falo shi da yara”

Suraj ya ce,Bari in je in gan shi” Suka fita aka barni da Aliyu, muka yi shiru ba tare da wani yà ce da wani uffan ba. Sai zuwa can

Aliyu ya yi dogon numfashi ya ce,Asiya!”

Sai na ji tsigar jikina ta yi yarrr! Ya ci gaba da

kiran sunana kamar sau uku, sannan na ce,

“Na’am Ya ce,Ba ki huce ba ne har yanzu? Ko so kike in durkusa a bisa kan gwiwata Asiya?”

ya taso yazo ya zauna kusa dani bisa doguwar kujera. Ya ci gaba da cewa,Ki yi hakuri, ki yi mini magana ko na ji sanyi Sai na daga kai a hankali na dube shi, na yi murmushi na ce,

“To Aliyu me zan ce maka ka yi fadanka har ka gaji, kuma ka huce don kanka, to ni ai yar kallo ce”. Sai na juya masa kwayar idona gaba

daya, don daman naga hankalinsa ya yamutsa, jikinsa ya saki na san ya shiga wani hali. Sannan ya ce mini,Asiya,yar kauye, daga

yau kada ki sake hada motata da ta Kabir, shi tasa passat ce, tawa kuma sunny ce, zan mai da kalar tawa mai ruwan ganye don kada ya kara ruda ki, ki fita zuwa gare shi

Na harare shi na ce,Ai wallahi kai ne

bakauyen birni tunda kake, bari aji asirin gidanka, ai ko ka gama kauyanci”

Sai ya yi sauri ya kama mini hannu ya ce,

“‘Asiya yau kin gama dani kwarai, karshe daga yanzu ko mai zai faru ban Kara yin yadda wani zai ji, kuma ma ai laifin ki ne, na yì kokari inyi magana da ke kin ki yarda, saboda haka dole ta sa in bari Suraj ya ji”

Na langabe kaina na kara lumshe idona, na ce,

“Aliyu sakar mini hannu yanzu idan Baba Suraj ya dawo fa, ko wani yaro ya shigo?”Ya ce,

“An ki saki me kika gama cewa yanzu,

ba cewa kika yi na bari an ji asirin gidana ba wanda a zahiri kin nuna mini kin zama iyalina ke nan, kuma in Allah ya yarda haka din ne.

To sai me don Suraj ya ga hannayenmu hade?

Ko kin san idan na rike hannunki wani irin sanyin dadi nake ji yana shiga mini jiki, in rika jin wata ni’ima na shiga cikin jijiyoyina.

Kai Asiya abin da nake ji a raina ba ya misaltuwa, sai dai kawai na san yadda nake ciwon begenki a zuciyata, haka ke ma a taki zuciyar abin yake”

Sai na ji gyaran muryar Suraj, na yi sauri na

fizge hannuna, na kuma matsa gefe guda. Sai Aliyu ya kyalkyale da dariya ya ce,

“Kya karaci gulmarki ki daina

Na ce,Sai dai mu karata tare da kai”

Ya ce,Asiya ashe kina da baki haka?”

A daidai wannan lokacin ne Suraj ya shigo, ya

ce,Yau fa ga wata ga zarah, Aliyu hankali ya kwanta an samo kan Asiya, amma jiya kai da mahaukacin kare daya kuke Ya ce,

“Shegantaka za ka yi mini a gaban yar

taka? Daman ta fara raina ni”Sai muka fita tare da su, ina yi masu rakiya

kamar yadda na saba. A nan ya ce mini,

«Gobe Lahadi zai zo da farfe goma ya kai ni gidan abokin aikinsa

saboda ya riga ya yiwa matarsa alkawarin kawo ni kafin in koma Malumfashi

Na ce, “To, Allah ya kai mu lafiya’

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page