ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 12 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 12 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

saboda ina kallon sa rannan da ya z0 mini hira muna tare da su Mama Inki, bayan sun gaisa lafiya, sai ya yi mani wani irin kallo wanda ya sa duk ilahirin tsigar jikina ta tashi.

Sannan ya ce, Yan hutu babu magana?”

Na ce, Ina yini?” Ya Ce.

“Da ban yini ba kya ganni a nan, har in

roki gaisuwa Sai Mara Inki ta tashi tsam ta bar mana falon. Aliyu ya ce mini,

“Don Allah duba a firij ki ga idan.

akwai fura ki bani, idan babu ki bani nono kindirmo insha” Na tashi na nufi kicin, sai naji Aliyu ya kira sunana cikin murya mai taushi. Na juyo nace Na am Ya ce,

“*Allah yasa baki da miji sai Aliyu, a ran

da na aure ki, sai na goya ki don dadì”

Muka (yalkyale da dariya, na karasa da sauri,

na sami dan karamin kwanon sha na zubo masa fura na doro bisa tire, tare da ludayi da sukari cikin dan kofi, da kofin shan ruwa da ruwan sanyi domin sha Na dauko na taho ina takawa dai-dai, kai idan ka ganni a wannan lokaci ka ce muna tsakiyar sabon

amarci ne. Na aje masa a gabansa. Ya ce,

“Sannu bebina, sai dai kuma ba na shan

fura da sukari Na ce,Ai shine dalilin da ya sa ban zuba a ciki ba, ka ga da na yi laifi”

Ya ce,Haba! Dalin dina ba kya laifi ko kin

kashe dan masu gida’Sannan ya ce,

“Asiya sai muje gobe mu yi hoto ko?”

Na yi ajiyar zuciya na ce,Hoto! Tafdijam! Ba

na iya daukar hoto da namiji”Ya yi farat ya ce,

“Da yake namijin dodo ne ba Ya dinga magiya yana nanatawa. Na ce,A’a

idan dai maganar hoto ce an duke mu jiya a nan gida, idan an kawo na baka”

Ya yi fushi ya tashi zai tafi, na ce,

“Aliyu taliyar ke nan?”Ya ce,

“Allah ya ba mu alheri”, Ina cikin daki sai tunanin gida yazo mini, nace,

“Yaya Aliyu zai dauki zafi dani a kan maganar

hoto kawai? To idan mun dauki hoto da shi idan na je gida na ce musu wane ne? Daga zuwa hutu sai a ganni tare da saurayi na yi hoto, ana iya dauka sheke aya ta nazoyi, gara dai idan a Malumfashi ne idan na

tambayi mahaifina da yardarsa sai mu je mu dauka. Kashe gari da misalin Karfe sha daya na safe, Mama Inki ta leko dakina ta ce, ‘

“Na ji ki shiru ne, lafiya dai ko?”

NaCe,Wani littafi na samu mai dadì nake

Karantawa Ta yi dariya ta fita., Amma wannan ba shi ne dalilin ba. Da sassafe maigadi ya bani takarda ya ce,Aliyu ya kawo ta, amma ya shige wajen aiki”Da na karanta shine tá Bata mini rai saboda yaCe mini shi ya san akwai yadda nake daukarsa a zuciyata, bani daukarsa mutumin kirki. Wanda ni ba

haka bane, ina karewa kaina mutunci ne da na iyayena,

saboda na san abin da mahaifina ba zai so ba kenan, balle mahaifiyata su da halacci da kauna suka samo asali daga wajen su.

A daren wannan rana dai, na yi wanka na shirya ina zaman jiran Aliyu, saboda haka na san zai zo.Amma sai na ji shiru, hankalina ya kara ta shi, ga shi har tara na dare ta kusa amma ban gan shi ba.

Sai na shiga daki da niyyar in fidda kwalliyata

in mai da kayan barci, sai ga Ummi ta shigo ta ce mini,Anti Asiya maigadi ya ce ki je ana kira”

Na yi sauri na rike hannun Ummi muka fita, na

hango jar mota irin ta Aliyu, na Kara da sauri ni a zatona Aliyu ne, amma me zai faru Ashe ba shi bane, wannan saurayin ne Kabir wanda muka je gidan su da Mama Inki.

Nan de na sake shiga cikin wata damuwa,

yanzu abin Aliyu yaz0 tunda ban fidda ran zuwan saba, me zan ce masa?

Na dube shi fuskata murtuke na ce,

“Ina yini?” Ya yi sauri ya fito daga cikin mota, ya koma bisa kan motar ya zauna, yace

“Saurin me kike yi haka daga zuwa ki ce mini ina yini?”Na ce,

“Wallahi ina da aikin yine shine dalili”.

Ya kuma ce mini, “Ai tunda kin yi babban bako

sai ki hakura da aikin yau saboda a gaskiya. ina da albishir da na z0 miki da shi kala-kala”

Na ce,

“Ban tari numfashinka ba, sai dai idan

ka matsa, mini da in tsaya, za ka takura mini”

Sai ya yi dariya ya ce,Eh, kina da gaskiya

Asiya, wallahi banga

laifinki ba saboda akwai maganar kuruciya a jikinki, duk yadda na zo in nuna

miki yanzu da wuya ki fahimce ni, sai dai a hankali idan ina kawo kaina har Allah ya taimaka ki gane manufa ta, har ki gane bukatar da namiji idan ya zo

wajen ‘ya mace wadda ba ta wuce magana ce ta so da kauna ba Na yi sauri na daga kaina na dube shi, duba irin na rashin jin dadì, na ga ya ya Kabir zai z0 mini da wannan magana haka? Kuma ni ga shi kullum fadan

da mahaifiyata take yi mini kada in wulakanta duk wanda ya ce yana sona, saboda idan kai aka wulakanta ba za ka ji dadi ba, kuma ma wanda ya ce yana sonka ai ya fi wanda ya ce bai kaunar ka. To ni yanzu ya ya zan yi kenan? Saboda agaskiya son Aliyu ya yi zurfi a cikin zuciyata. Zuwa can Kabir ya ci gaba da cewa,

“Saboda haka ba zan matsa miki da ina son amsar ki farar daya ba, zan ba ki lokaci isasshe, yin gaggawa a kan duk wani al’amari

na fannin rayuwa ya kan kawo dana sani”

Ya yi murmushi ya ce,Ko ya ya kika gani?”

Na ce,Eh, haka ne abin da ka fada gaskiya

ne”Sannan ya ci gaba da’ ‘yan surutai har Ummi ta fara hamma, nace To Kabir na gode sai da safe”Na dan nuna alamar tafiya, sai ya ce,To Asiya sai yaushe kike so in dawo?”

Na ce,A gaskiya bani da zabi a halin yanzu”.

Sai ya ce,To shi kenan bari in ba ki lamba din

wayar gidana, idan kina da hali sai ki buga mini ki gaya mini lokacin da ya kamata in zo ba tare da na zo na matsa miki ba”

Ya fiddo makudan kudi ya miko mini, na ce,

“Kai a’a, kada mu yi haka da kai, Kabir rike kudinka na gode Na ja hannun Ummi shima yayi sauri ya rike hannunta ya mika mata wanna kudi ya ja mota ya

tafi. Har na taka matakalar shiga gida sai na ji an kira sunana da murya mai rudarwa mai tada hankalin wanda ake kira, na juyo a hankali sai na ga Aliyu.

Gabana ya yanke ya fadi, sai zuciyata ke bugu

irin amon kokara, jikina ya fara kyarma. Na budewa Ummi gida ta shiga, yayin da na bi Aliyu jikin

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page