ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 11 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 11 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

 

an saka masa talabijin da radiyo da tarho da

madubai da sauran kayan Kawa na alatu barkatai.

Na san lalle idan Allah ya bani Aliyu na aura na

more, saboda duk namijin da ya san zafin uwarsa, toya san mutuncin mace, balle kuma idan ka sami shiga wajen mahaifiyar.

Bayan mun yi sallar azuhur da la’ asar, sai Aliyu ya shigo ya ce,; “Ku fito in sa muku kaset”.Na ceHabana yi zaton gida za mu yanzu?”Ya ce,Eh, haka ne, idan da arziki ai nan ma gidan ne, ko da yake gidan dodo ne, kada ya cinye ku gara ku fito mu kai ku gida”

“. Ya fita abinsa.Sai Hajaru ta ce,

“Gaskiya kin Bata masa rai Anti Asiya, don kin ga yana ciwon son ki shi yasa kike masa yanga”.- Ita kuma Maryam ta ce,Anti Asiya kin more ke mai kyau shi mai kyan, Allah ya baku *ya ya masu kyau” Na yi wata irin dariya nace, Maryam da shirme kike tun kafin a yi maganar aure har kin fara maganar abin da za a haifa

Sai na tashi na dauko man shafawar Aliyu ina

shafawa, sai ga shi ya kara shigowa, ya ce,

Maryam ku fito ku kalli kaset mai kyau na sanya muku Suka yi sauri suka fita, na yi sauri na biyo su,sai Aliyu ya kama bakin kofa ya tare yace,Zoki gani idan ban hada ki da jikina na matse ki ba”Na hada kai da bango na yi shiru. Sannan ya dauko turare ya rika fesa mini, yace, Bari in Karasa miki kwalliyarki,

sai dai kuma bani da hoda da jan baki, kinga kwalliya ta kamalla ke nan”.Na yi sauri na sami kofa na fito na bar shi a daki, na je na zauna kujera daya da Maryam, na ga ashe kaset din da ya kunna nashi ne lokacin yana

America inda suke Kara koyon tukin jirgin sama.Wallahi abin har tsoro yake bani, yadda na gasu Aliyu suna kasa-kasa su yi sama, kana su lankwasa wani gefe ko dama ko hagu. Na ga Aliyu babu abin daya shallai. na ce a raina Lalle ka ci sunan ka,”Gadanga kusar yaki’ Aliyu zakin Allah”Wai duk zaman nan Aliyu babu abin da yake yi sai aikin kallo na yana lumshe ido, ashe kuma Suraj

yana kallon sa, sai Suraj ya ce,Tun da nake ban taba ganin dan banza kamar ka ba, a ce mutum ba shi da kunya, Asiya fa

“yata ce idan da arziki ai na zama

ubanka”,Aliyu ya ce,Amman dai babu arzikin in dai kai ne uban, ashe da na yi uban banza. Har ka manta da abin da kake yi mini a gaban mutuniyar taka Jamila?°Suka fashe da dariya. A daidai wannan lokaci ne sai ga yaron gidan

Aliyu ya shigo mana da gasasshen nama da nonon kwali, daman tun zuwan mu

Aliyu ya aike shi unguwar Sarki ya sawo mana

Muka ci muka yi Kat, muka dauki kwalin nono

kowa yana tsotso. Sai kawai na ji Aliyu ya ce,

Aliyu”Na yi sauri na rufe fuskata don kunya.

Na ji dadi lokacin da Suraj ya ce, “Na ga rashin

kunyar taka ta yi yawa ku tashi mu tafi gida, haka kawai ka hana yarinyar mutane sakewa”

Na zillo na riga kowa tashi, bayan mun fito na

radawa Maryam na ce,Ta ce Aliyu ya bamu aron kaset din da muke kallo

Tana gaya masa dadì ya ishe shi, ya yi sauri ya shiga ya dauko mana. Muka tsaya a wani kantin super market ya saya mana alawa masu dadin gaske da cingam da biskit da dai kayan kwadayi iri-iri.Lokacin da muka isa kofar gida har magariba ta kawo kai, muna fitowa

sai na ga Aliyu ya fiddo

wasikata ya karanta ya girgiza kai, na harare shi na shige gida inda ya kyalkyale da dariya.

‘A wannan rana tunda na yi sallar isha na koma bisa gado na lafe babu abin da nake yi sai tunanin

yadda al’amuran wannan rana suka kasance tsakanina da Aliyu, saina dinga ganin abubuwa suna gilmawa ta

gabana kamar fim.

Sati, biyu da suka wuce idan an ce zan kamu da ciwon so, zan ce ‘a, amma yau ga shi nice ko abincin dare na kasa ci don tunanin kaunar da nake wa Aliyu.

Na yi sauri na je na kunna kaset din bikin

saukar karatun su a America, na koma bisa gado na

kwanta ina ta aikin kallo, ban gama ba sai misalin daya na dare,

na tashi na yi nafila na roki

Ubangiji Allah ya sa nan da shekara guda ina gidan Aliyu

Kusan kullum abin da ke faruwa a hutuna na

Kaduna, idan Aliyu bai zo ba yana aiki, saboda aikinsa canji-canji ne, idan rannan bai z0 ba, to duk jahar da

ya sauke, lalle ne ya bugo mini waya.

Mama Inki kuwa idan za ta unguwa, to nice

‘yar rike jaka, a. dalilinta na shiga manyan gidaje da dama. Ba ni manta wannan ranar da na raka Mama Inki gidan wani kasaitaccen dan kasuwa mai suna Alhaji Muhammad.

Lokacin da muka shiga dakin Hajiya Asabe,

wato kawar Mama Inki, sai muka same ta zaune tare

da wani saurayi mai suna Kabir, bayan na durkusa na

gaishe su, sai Hajiya Asabe ta ce,

“Ina kika sami ya kyakkyawa haka?”

Mama Inki ta yi dariya ta ce,

“Yata ce ta Malumfashi”

Sai Hajiya ta ce,

“Ko ita ce Asiya da kike

magana?” Ta ce, “Kwarai kuwa ita ce”

Hajiya Asabe ta ce,

“Kai ko Kabir ba ka ko

bamu waje kana ganin na yi manyan baki”

Sai ya yi dariya ya ce,

“To bari yau in canji mai

aikin in kawo wa bakin naki ruwan sha’Ta ce,

“To ai ko na gode”

Muka yi dariya. Sai Mama Inki ta ce, *

«Wannan dan wajen Hajiya Babba ne wanda kika ce yana rike

da kamfanin Alhaji na Legos?”

Ta ce,Kabir ba,eh shine jiya yazo  hutu nan

Su Mama Inki suka ci gaba da hirar su, yayin

da na sami wata mujalla mai suna Hotline na koma gefe guda na manta da su Mama, karatu ya dauke mani hankali.

Bayan mun tashi Hajiya Asabe ta kawo wata

‘yar jaka ta yan mata mai kyau ta bani da pantis da under wear da kayan shafawa ta ba ni. Na yi godiya mai yawa.

Na san Aliyu ba zai zo ba a wannan dare, na

sanya kaset dinsa ina kallo, in jin dadi don ina jin muryarsa ga zahirinsa ina kallo, sai na ji dakin ya yi

mini daci, in ji babu abin da nake so illa na ji

hannayensa masu taushi suna rike da nawa.

Idan son samu, ne in ga na dora kaina bisa

kirjinsa, wai ya ya zan yi a wannan rana? A gaskiya Aliyu namiji ne cikakke mai kyan Kira, kallon sa ma kawai zai haddasa sha’awa a zuciyar mai bege, ga muryar Aliyu mai zurfafa jin sanyi a zuciyar mai saurare.

Ko da yake na lura da Aliyu idan zai yi mini

magana har canza salo yake yi, ko a gaban wane ne,

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page