GIDAN AURE CHAPTER 5 ZAHRATEEY

GIDAN AURE CHAPTER 5 ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Gidan Ahmad*

+

Lamarin rayuwa yana tafiya yadda ubangiji ya tsara da dadi da ba dadi, wasu suna hakuri wasu suna butulci ga ubangiji wasu basa duba na kasa dasu kullun sena sama dasu ta yadda ba zasu ta6a godewa Allah ba. Ina ta fama da laulayi me wuyar sha’ani ga shi uban gayyar ya koma bakin aiki, sai da nayi sati uku a Kano saboda jikina ba dadi sannan na dawo Kaduna, har yau na kasa fita aiki dan ba wani karfi bane dani, ko da na fada wa me gadi ina dauke da ciki be damu ba a cewarsa hakanne zai bashi damar mallakata ni kuma a nawa 6angaren hakan be min ba domin ba zan iya auransa ba saboda ba lailai a samu yarda a tsakanin mu ba dole zaa samu zargi.

Gidan su Ahmad sunyi matukar farin ciki da wannan cikin daya bayyana a jikina, shima Ahmad a wannan karon so da kauna ya daurawa cikin jikina a zuciyata nake cewa rashin sani yafi dare duhu domin da ya san ko cikin waye da be daura mishi so da kauna haka ba. Tabbas ya makaro lokacin da naso in samu cikin nashi ya kama ya rinka hadani da maganin hana daukan ciki a yanzu kuma da cikin ya kasance na wani shine ya daura wa kansa son cikin.

Na so in sanar dashi gaskiyar lamarin amma na kasa nafi so koma meye sai na haihu kafin ayi shi, kuma na kudurta a raina na gama zama da Ahmad tunda har ya yi sanadin dana fara muamala da wani namiji da aurena  har ya kai ga samun ciki.

_________________________

*Gidan Salmanu*

Cikin amincin Allah aka yi biki lafiya aka watse lafiya amarya ta tare a 6angaren da ango ya gina mata ta gefen Mama. Burin su Mama dai be cika ba saboda amarya macece me addini, girmama na gaba da sanin yakamata, sun so ace ta shiga gidan da rashin mutunci a Faiza sai kuma adduarsu be kar6u ba, domin zaman lafiya sukeyi da uwar gida wanda hakan ya sawa zuciyar mijinsu natsuwa.

Sati biyu kenan da tarewarta a gidan kuma komai na gidan tana fahimta dai dai gwargwado hatta yadda Mama ke muzgunawa Faiza. Duk wani rashin mutuncin da Mama keyi wa Faiza ta saka wa ranta cewa ba zata ta6a bari ta gwada yi mata ba ma’ana sawa zaman aurenta ido da hanata jin dadin zama da mijinta. Kamar kullun idan Salmanu ya dawo sai dai ya jefa kullin abin da ya kawo ta window to yau ta dauki aniyar lalata wannan doka dolene a kawo abu ta daki kuma babu wanda ya isa yasa musu ido.

Fitowa tayi a dai dai lokacin Mama na alwala ta fashe da kuka, cike da tashin hankali Mama ta nufe ta har zaninta na faduwa “yar arziki irin albarka waya ta6aki a cikin gidan nan da kike da gata gaba da baya?” Sake fashewa tayi da kuka kafin tace “shikenan idan mijina zai shigo min da abu sai dai ya jefa ta taga ba zai shigo ta kofa ya ajiye ba saboda baya son matarsa ta gani ta hana mu zaman lafiya” ta fada tana kara karfin kukanta, cike da rashin gaskiya da damuwa duk Mama ta duburce “kiyi hakuri kinyi yar nan, hakan ba zai sake faruwa ba, ina kake kai Salmanu? To daga yau kar a sake irin haka idan ka shigo mata da abu ka kai mata cikin daki meye na jefawa ta taga saboda tsoron matarka, kar inji kuma kar in sake gani, ya zaka rinka abu kamar 6arawo ko mara gaskiya, ka kiyaye nan gaba” Salmanu daya fito daga daki cike da jindadin maganin Mama da akayi a yau ya amsa da “to ba za’a sake ba”.

Mama na shiga ciki suka tafa da Faiza, shima Salmanu ya sauke ajiyar zuciya cike da farin cikin sauyin da suka samu albarkacin auren Dada, tabbas ta kasance alkairi a cikin rayuwarsu hakan ya kara mishi so da kaunarta domin tana kawo haske a zaman aurensu Faiza ma ta fara samun yancin kai.

_________________________

*Gidan Faruk*

Jiya wa yau lamarin gidan bata chanza zani ba, abin dai kullun sai karuwa yakeyi gidan ya zama kamar gidan haya Faruk ya biyewa amarya Wasila sun koma kamar kishiyoyi, ya fada ta fada harda zagin iyayensa duk ta nayi, lamarin ma ya sake lalacewa domin yaran shi sun dawo hutu gida sun iske abin da yake faruwa suma sun jone yau su shiga wa Anty Wasila gobe su shigawa Faruk abin dai da Nafi tayi gudu shine yake faruwa.

“Wace yar iska ce ta sauke min ruwan dana dora zanyi wanka dashi? Idan banda rashin kirki ba, nida gidana za’a hanani jin dadin rayuwa, to wallahi an fara kaini bango zanyi rashin mutunci fiye da yadda ake tsammani” fitowa Wasila tayi tana tauna chew gum “yar iska tana can gida bi ma’ana tsohuwarka, ko kuka ince yaran daka tara marasa tarbiyya kila dayansu ta dauka, amma ka duba da kyau nafi karfin ka kirani da yar iska tunda baka kamani dumu dumu ina iskancin ba ehe, kuma da kake cewa zakayi rashin mutuncin ai dama ka saba sai dai ka kara kan wanda kakeyi din ko zai kara armashi mtss” taja tsaki ta koma daki, cike da 6acin shi kuma yabi bayanta, Nafi na zaune taji karan tsintsinka mari halamin ko kowa ya ba kowa ko kuma daya cikin su akayi wa, cikin sauri ta kwashi shinkafar da take gyarawa ta koma daki ta rufe kofa.

Yau dai abin nasu har asibiti kowa da bandeji a kai kamar goggoro, abin kunya ya yi yawa yaran har da kukan su domin wai basuyi tsammanin cewa Anty Wasila yar daba bace, sosai furucin su ya 6ata mata rai taji bakin ciki sosai ta kuma kudiri niyyar ci musu mutunci da hanasu kwanciyar hankali, Nafi dai yar “sannu Allah ya sauka ne” daga nan ta tsuke bakinta bata sake cewa komai ba har aka sallame su daga asibiti ita da take fama da cikin jikinta ina zatayi abin da zai jawo mata fitina.

*Gidan Hafiz*+
Tun zuwan kanwarta gidan ta samu saukin lamura domin daga Hafiz har matarsa natsuwa sukayi dan ganin ba sauki a tare da rayuwar Latifa, sosai ta kasa ta tsare ta hana kowa jin dadin rayuwa, Zaliha da danta ne kawai suke sakata su wala suyi duk abin da suke so cikin kwanciyar hankali babu takura, ita da tazo ziyara sai ta buge da zaman vigilantee a cikin gidan.
Sosai Zaliha taji dadin al’amarin har bata son Latifa ta tafi saboda ta fara samun freedom a cikin gidan ta, ladabi da biyayya Hafiz keyiwa Latifa komai tace shi yakeyi babu jayayya, abinci sai abin da Zaliha take ra’ayi ake dafawa a gidan, kayan miya kuwa sayayya me rai da lafiya yakeyi tunda dama yana da abin hannunsa kawai dai a matarsa da yaran sunna yake kashewa inji shi da fada, Zaliha ko oho in dai ba wanda ake dan ajiye mata na sawa a abinci dan ya kara dadi da kamshi ba sai dai ta jiyo kamshin nama a dakinsu amma ko dandano bata kai a bata tayi ba balle tayi zaman ci harta koshi, yanzu kam alhamdulillah har cewa takeyi gwara da Latifa tazo sa6anin farkon zuwanta da take kuka take ikirarin cewa zata kashe mata aure, ashe gyara tazo yi ba lalatawa ba.
Kamar kullun suna zaune a daki ta kwalawa matar Hafiz kira, abincin da za’a dafa ta dibar mata kafin ta fada mata yadda take so a girka, yanzu abin ya yi nisa har umarni Zaliha ke badawa a cikin gidan ba boka ba malam kawai aikin tsagerancin Latifa, matar Hafiz kuwa kamar zata mutu haka takeji kullun dan aikin asirin da tayiwa Hafiz ya fara lalacewa kuma tunda ba aiki take zuwa ba bata da damar fita ko ina kullun tana gida a tsare kamar ragon layya, duk hanyar da tabi dan son zuwa gurin boka ta kasa samu domin Latifa ta kasa ta tsare ta hana ruwa gudu.
Yanzu dan shege ya samu matsayin har yana iya watayawa a cikin gidan ubansa, sai yanzu ma ya fahimci cewa lailai Hafiz ubansa ne kuma yaran gidan suka gane cewa shi din yayansu ne kuma jininsu ne, sosai ya zama dan gatan ubansa aka chanja mishi kayan sawa kala kala aka mai dashi makarantar da yaran gidan suke zuwa, duk abin da aka yiwa yaran wanda shi bai samu ko kwatanshi ba yanzu ya samu har ma fiye da nasu, musanman ya sayowa Zaliha kaya masu kyau da tsada wanda rabonta da ganin haka tun suna saurayi da budurwa, a gidan shi bayan kayan auren ta bai ta6a sinana mata komai a harkar kula da lafiyar jiki da tsaftarsa ba, domin da ita da babu duk dayane a gurin sa.
Akace mahakurci mawadaci, mai hakuri ya kan dafa dutse har ya sha romonsa, yau ta tashi da matsanancin ciwon kai da tashin zuciya, tashin farko aka sanar da ita cikin da take dauke dashi na wata biyu, murna kamar anyi mata albishir din zuwa makka, duk da cewa bata cire rai daga samun rahamar ubangiji ba amma kuma batayi tsammanin samun ciki nan kusa ba, sosai tayi murna tayi godiya ga ubangiji, tun a asibiti ta fara sadaka har suka dawo gida, wannan dalili yasa Latifa ta sake gyara zama tace babu inda zataje kafin ta tafi a kama a kashe mata yar uwa a banza tunda yar uwar nata ta zama lusara.
_________________________
*Gidan Jamilu*
Cikin lokaci kankani ya gama gininsa wanda har zuwa lokacin Jawahir bata farga da abin da ke shirin faruwa ba, kanwar abokinsa yake so a halin yanzu kuma har an saka rana, a takaice dai saura sati biyu auren invitation card ya fara ziyarar gidajen jama’a haka zalika Jawahir a ire iren shegen yawonta ta kyello ido a kan katin gayyatar auren mijinta, sosai ta shiga tashin hankali da ya kai ta ga faduwa, cikin azama aka garzaya da ita asitibi sannan kawarta da suke tare a lokacin ta kira mijinta ta sanar dashi halin da ake ciki.
A lokacin Jamilu yana gurin sake printing wasu I.V tare da abokinshi Isa yayan matar da zai aura, saboda wanda akayi duk sun raba ana bukatar kari a wasu manyan mutane, ko da ta kira ta sanar da shi sosai hankalinshi ya tashi saboda yana son Jawahir sosai, damkawa Isa komai ya yi sannan ya figi sabuwar motar da ya saya ya wuce asibitin Sauki inda aka kwantar da ita. Ko da ya isa Asiya tazo ta shiga dashi kafin ta mishi sallama ta wuce saboda bikin kanwarta akeyi kuma dinner za’a tafi, zama ya yi yana kare mata kallo, riga da skirt ne na lace dinkin ya zauna sosai a jikinta kamar ba zai fita ba saboda yadda ya d’ameta, tasha kwalliya tamkar wata karuwa wai a haka matarsa ce, takaici ne ya kama shi tunawa da cewa maza da yawa sun gama kalle mishi ita, tagumi ya buga yana kissima irin abin da ya dace ya zartar a kan shegen yawon data aza wa kanta.
Kusan awa biyu da zuwansa ta farka dauke da addua a bakin ta, ba laifi akwai riko da addini ta wani fannin amma ta wani guri kuma kamar wata arniya haka rayuwarta take, idonta ne ya sauka a kansa wani kululun bakin ciki ne ya ziyarci zuciyarta, wai ita Jamilu zai yaudara zai yi aure ya kasa sanar da ita sai dai taji a gari, bata damu da karin ruwan da akeyi mata ba kawai ta fizge tayi ficewarta, yana kiran sunanta ma kota kulashi idonta a rufe yake yana ci da ruwan bala’i da masifa, Napep ta tara ya kaita gida, shi kuma ya tsaya biyar bills din asibiti cike da tashin hankali da damuwa ya bi bayanta, yana isa ya yi parking motarsa a waje saboda ba zai iya jiran me gadi ya bude mishi gate ba, cikin sauri ya shiga har yana tuntu6e.
A zaune ya sameta kamar tayi fadowar yan bori, dankwalinta a gefe kayan jikinta kamar an kwato a bakin kura duk tabi ta yayyaga kanta duk a barbaje kamar kan mahaukaciya, kuka takeyi iya karfinta duk ranta a jagule yake, jin shigowarsa yasa ta kara fashewa da wani kukan saboda takaici daya sake turniketa “saboda cin mutunci da nunawa duniya cewa baka sona shiyasa sai a gurin biki zan tsinci katin aurenka, auren ma dan tsaban cin mutunci da kanwar abokinka, dama zuwan Iklima gidan nan duk saboda tana son ka ne? Hakan ma ya yi Allah ya ba da zaman lafiya nagode da mutunci” duk da cewa ita ta jawo har ya sanya wa zuciyarsa shaawar aure amma kuma sai yakejin jikin shi ya yi sanyi yake ganin kamar bai kyauta mata, ina laifin ya nemi wata wacce bata sani ba, sai dai kaddaran aurensa da Iklima tsararre ne tun fil azal dan haka babu tsumi babu dabara, zancen kuma ya nemi aure har an saka rana har an fara rabon kati bada saninta ba akwai laifinta a ciki saboda bata da lokacinsa balle har suyi magana ta fahimtar juna, shi dai yana ganin duk suna da laifi amma zai yi kokarin gyara gidansa babu sanya a wannan ga6ar, rarrashinta ya shiga yi duk da cewa taki daina kuka ta koma wani abin tausayi duk tayi laushi da yawa.
______________________

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page