IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 1 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 1 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

damuwa ya kayar da shi tofa babu ruwan Safina, ‘yan uwan shi da masoyan shi kawai za a bari da rashinsa, dan haka ya daure ya taimnake su kada ya kassara kanshi, Sulaiman ya san gaskiya aka fada masa dan haka karfi da yaji ya cire Safina daga layin masoyan shi, ya dawo da  farin ciki rayuwarsa, domin ya fuskanci rayuwa ta gaba wato rayuwar karatunsa da kasuwanci su.  Kasuwancin nasu ya kankama, kuma da
alama akwai haske da nasibi a ciki domin da jarinsu mai kauri suka fara harkar.

Alhamdulillah mu hadu a littafi na biyu domin jin makomar Sulaiman da kuma Safina dama irin tataburzar dake tafe cikin ‘yan matancin Safina

.
Inka ki ji… 2

A bin duniya ba ya ɓoyewa, kokarin Safina na boyewa gidansu abinda ta yiwa Sulaiman bai kai gaci ba. Baki dayansu suka faru a fallo Inna banda fada babu abinda suke yiwa Safina bisa rashin adalcin da ta yiwa Sulaiman. Hayaniyarsu ceta janyo hankalin Mallam Yusuf wanda yake gida bai fita ba kasancewar Safiya ce, hakanne ya tilasta masa lekawa falon domin ganin abinda yake faruwa.
Shigowarsa ceta maida kowa a hayyacinsa inda Mallam Yusuf ya tambayi Inna akan abinda yace faruwa. Sai dai kafin Innar takai ga bude baki sai Safina tayi karaf tace “Baba haka kawai wai…””Yi min shiru!” Mallam Yusuf  ya daka mata tsawa “Kena tambaya ko kuma a mahaifiyarki?” Ya maida dubansa ga Inna domin jin abinda zata ce.

Www.bankinhausanovels.com.ng
“Wallahi Mallam Yarinyar nan ceta bata min rai shi yasa nace yayyenta suyi mata fada shi ne take dagawa mutane murya haka tamkar sa’o inta”.
Safina dake kuka tace baba wallah rahma ce tazo tamin munafurci shine suka rufar min da fada ba tare da nayi wani laifi ba
Yaya abbas dake zaune yace rufema mutane baki ko in bubbuge ki waye yake yi miki muna furci?
Malam yusuf ya daga masa hannu karka dajeta abbas kaifa ka fiye zafin zuciya abi komai q sannu idan akace mitum yayi laifi
Ai kamatq yayi a fara bincikawa kafin a tabbatar
Inna tace ai malam da barinsa kayi ya bigeta domin komai akayi mata ita ta jiyo malam yusuf yace to ai ni har yanzu banji musabbabin wannan fadan ba  inna tqce akan yaronnan ne sulaiman dake nemanta malam kasan dai shekaru hudu kenan harda yqn watanni yana neman aurenta kasan dai duk irin dawainiya da wahalqr da yake a kanta a kullm cikin kyautata mata yake dare da rana dubi dai yaddah ya dauki nauyin Www.bankinhausanovels.com.ng karatunta kagin a fada maka har yaje ya biya a yakaice dai duk ya tare karfinsa a kanta kuma ya sakankance shine zai aureta sai yanzu rana tsaka da tafiya tayi nisa take neman yi masa butulci tunda yanzu kanta ya waye, Dama ni tun a watannin baya na lura da take-taken ta, sam ta daina damuwa da lamarinsa kamar da. Tun a watannin baya na lura ya daure kafarsa daga zuwa gidan nan kuma ko maganarshi ba ta yi bare ta nuna damuwarta akan hakan”.
“Da kaina na tambayeta ko akwai abinda yake faruwa amma sai tace min babu komai, bayan ‘yan kwanaki naga abin bai sauya ba sai na titsiyeta ta fada min gaskiya a lokacin sai cewa tayi wai yan uwansa ne da abokansa suka zuga shi wai ya rabu da ita waita fi karfinsa ba zai iya sarrafata a matsayin matarsa ba tunda ta fishi karatu mai zurfi, wai kuma da ma can ba kaunarta suke yi ba, a lokacin ban yi gaggawar karyatata ba amma duk da hakan ban gamsu da maganar tata ba domin sanin yanzu Safina ta koyi karya da yaudara.
Inna ta ci gaba da cewa “Ran nan da Rahama ta zo shi ne na tuntubeta tunda nasan sun fi kusa, babu yanda za ayi ace bata san komai game da batun ba, hakan kuma aka yi ashe itama lamarin na damunta, a labarin da Rahama ta bani ni dai ban ga laifi yaron nan baki dayan laifin na Safina ne domin har buyar masa take yi tace bata nan, ya sha zuwa nemanta har
can gidan Rahaman basau daya ba, basau biyu Www.bankinhausanovels.com.ng
ba”. Cike da takaicin jin abin dake faruwa Malam Yasuf yace “Safina gaskiya ban ji dadin abin nan da kika yi ba, a sanin da na yi miki ke yarinya ce mai hankali da sanin ya kamata, ban yi zaton iya yin watsi da kyakkyawar tarbiyyar da muka baki ba, abinda kika yi sam baki kyauta ba domin ya saba da koyarwar addinin Islam, sanin kanki ne cewar karya, yaudara da cin amana ba abubuwa bane masu kyau, dan haka ki gaggauta yin nadama tare da neman afuwa yaron nan domin kin zalunce shi”.
Mallam Yusuf ya yi kwafa sannan ya ci gaba da cewa “Amma mu ba zamu zuba miki ido ba tunda dai mu muka haifeki ba ke kika haife mu ba”. Ya baiwa Ismail Umarnin ya nemo Sulaiman domin suji ta bakinsa game da lamarin. Www.bankinhausanovels.com.ng
Jin haka sai Safina ta dada rushewa da kuka tana fadin “Dan Allah Baba kayi hakuri kar ka neme shi, wallahi yanzu Sulaiman ya daina sona, idan aka neme shi zai ga kamar neman kai ake yi dani”.
Inna tace “Au, tanan kuma kika bollo? Ai
indai akan mubi son ranki ne sai dai ace ba ma
sonki, idan har kina da gaskiya ki bari a nemoshi

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page