RAWANIN TSIYA CHAPTER 9 BY FADEELAH
RAWANIN TSIYA CHAPTER 9 BY FADEELAH
Kamar yadda aka tsara, Abbu (Hanan’s Father) ya zo Nigeria sun hadu da su Big Daddy (Yazeed’s father) da Dad (Faisal’s Father) da Barrister mijin Hafsat, Yazeed da Faisal sun je Kano neman auren Sadiq.. Paapa da abokanen shi sun karbi baqin nasu cikin karramawa. Dayake dai harka ce ta girma komai anyi shi cikin tsari.. A nan suka nemi a sanya ranar biki Sati biyu kacal…2
Paapa ya dan yi mamakin jin sun buqaci ayi bikin so soon amma kuma daga baya sai yayi tunanin qila shi Sadiq din wants to just quickly fulfill his wish ne and send her back kamar yadda ya umurce shi..1
Sun jaddada ma Paapa cewar basu buqatar komai na daga kayan daki da sauran su tunda dama ba addini ya tsara lallai sai anyi haka ba.. All necessary formalities were done and it became official- Auren Sadiq da Hanifa nan da sati biyu!
Hankalin Hanifa ya tashi jin cewar an sa ranar bikinta in 2 weeks- bikinta da maqiyin ta SADIQ. Sossai abun ya dame ta.. gaba daya ma ta zama confused.. Tabbas tana da plan din da zata yi executing a gidan Sadiq amma kuma dukda haka jikin ta yayi sanyi… Ko me yasa???1
Hanifa dai ta gaya ma su Paapa cewar Sadiq ya bata blank cheque na lefen ta da hidimar biki amma kuma ta gaya musu cewar bata son lefen don haka bazatayi amfani da kudin shi ba..
Shi kam Paapa babu abinda ya dame shi da wannan dukda kuwa yayi mamakin ace yadda Hanifa take da son kashe kudi sannan an bata blank cheque amma ta qi amfani da shi? Unbelievable!!
Could it be a sign na cewar Sadiq ya fara gyara ta kenan tunda a dalilin shi for the first time she has uncountable money at her disposal amma kuma she refuse to spend???3
Well, a wurin Paapa dai whatever the case may be, tayi daidai tunda dama auren ba lasting zaiyi ba don haka gwara kar ta kashe mishi kudi a banza (even though deep down within him yana so auren yayi lasting coz he knows Hanifa will never get a good husband kamar Sadiq din)4
Mamy kuwa ta lallabe ta ko da kadan ne ayi lefen amma sam ta qi.. Gyaran jikin ma da za’a yi mata cewa tayi bata so, a cewarta wa zata gyara ma jiki bayan ko hannunta bazata taba bari ya taba ba balle….
toh fa!
Kai gaba daya komai na shirye shiryen bikin Hanifa ta qi tayi participating. Mamy da dangin mahaifiyarta su suke ta kidan su suna rawar su..
A bangaren Sadiq ma babu wani abinda yake yi na shirin bikin.. He was so occupied with work da kwata-kwata ya manta cewar zai yi aure.. kai har tafiya yayi a tsakanin wannan lokacin..
Shima dai kamar yadda ya fadi ma Naana baya son wani event don haka kawai da zarar an daura auren shikenan..
Tuni IV na daurin aure ya fita.. ya bi ko ina a qasar Nigeria. Dukda abin low-key ne sai da aka samu ‘yan nacin da suka zaqulo hotunan Sadiq da Hanifa suka baza a social media.. tuni suka zama talk of the town..
Kowa yana murnar bikin Sadiq a cikin dangi amma banda Asma’u. Gaba daya ko maganar bikin bata so ta ji balle sunan Hanifa… Ita kuwa Hanan ta zama indifferent about it, a part of her is happy for him and a part is not!! Ta sani cewar tunda ba auren shi zata yi ba bai kamata tayi mishi baqin ciki ba dukda shi din ba son auren yake yi ba..2
Ana saura sati daya bikin ne su Jameela da Nana Fatima suka iso Nigeria.
Sossai suka dinga qorafi jin an ce babu event din da za’a yi har a bangaren amarya.. Har kiran Sadiq suka yi suka sanya shi a gaba suna ta masifa amma kuma ya dinga basu haquri..
STORY CONTINUES BELOW
Su kansu Faisal da Yazeed sunyi qorafi har suka gaji.. Babu shiri suka haqura suka qyale shi.. a cewar su tunda dai zai yi auren ai shikenan!
Su Hanan ma tun ana saura sati daya suka iso.. tunda suka iso kuwa tana nan maqale da Sadiq.. hatta ofis tare suke zuwa.. Har yawon shopping suke zuwa tare da Asma’u kamar ba wanda ya rage sauran kwanaki ba bikin shi..
this is to show how very much unimportant he takes the wedding!!!
hmmmmmm!!!!!!
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
*
*
*
*
ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA
A yau Juma’a, Yau ne ranar daurin auren Hanifa da Sadiq wanda za’a yi bayan sallan juma’a a Central Mosque.
Garin Kano ta cika da manyan baqi a wannan safiya domin dai it’s the Union between the Children of two Rich, powerful and sophisticated families.
Amarya Hanifa dai tun jiya da dare da ta shiga dakinta bata qara fitowa ba gashi a yanzu har qarfe Goma sha daya na safe..
Tun kwana biyar da suka wuce gidan ya cika da baqi ‘yan uwa da abokan arziki.. Dangin mahaifiyarta har wadanda suke qasar Morroco duk sun zo..
Tun da safe kowa tambayar whereabouts din amarya yake yi amma babu ita..
Abin mamaki shine duk wanda aka aika ya je ya kira ta sai su dawo su ce tace tana zuwa.. hatta Mamy da ta kira ta a waya cewa tayi tana zuwa amma kuma bata fito din ba. Da Mamy ta kula da take-taken ta ne ta kira Paapa a waya ta sanar da shi.. Shi dai Paapa jin an ce tana responding sai yace a qyale ta, idan ya dawo he will handle her.1
Dangin su Hanifa dai basu yi mamakin wannan al’amari ba tunda sun ji labarin cewar arranged Marriage ne.. su kam sun sani sarai girman kai irin na Hanifa bazai taba bari tayi soyayya da namiji har ta kai su ga yin aure ba don kuwa tun tana qarama babu wanda bai san halinta ba.
Mai karatu, ni kam da na kula kamar babu yadda za’ayi in ga Hanifa sai wata dabara ta fado mun.. ladder na hau na shiga ta window don in gano muku abinda yake wakana a cikin dakin..
Kwance take a kan resting chair na dakinta yayinda idanuwan ta suke a rufe.. Karatun Al-qur’ani na ji yana tashi in a very low volume yadda idan ba kana daf da ita ba bazaka taba ji ba..
Hanifa dai ba wani zurfi tayi a karatun Al-qur’ani ba domin kuwa bata yi sauka ba amma kuma karatun addini is the one thing da Paapa yayi mata tsaye akai tun tana qarama- babu laifi kuma ta samu dukda ba wani mai zurfin gaske ba…
A dalilin ta iya hada baqi shiyasa ko wuraren da ba’a koya mata ba ta iya karantawa.. Hadda ne dai bata iya ba sai ‘yan surorin qasa wadanda basu da tsawo..
A yanzu haka Suratul Maryam take sauraro.. she has been listening to the recitation of the Holy Qur’an tun Safe da ta tashi daga bacci…
A jiya ta kwana cikin wani yanayi- Yanayin da ita kanta bata iya fasalta shi.. she was feeling all sorts of emotions.. Jikinta ne yake qara sanyi wanda bata san dalili ba.. even after ta riga ta shirya karta ma Sadiq rashin mutuncin da ko kwana uku bazata yi ba a gidan shi zata dawo, a part of her is telling her cewar ba abinda zai faru ba kenan.. but why???5
Gaba daya ta farka feeling very weak, she slept on an empty stomach and yanzu haka bata ci komai ba.. tana da fridge danqare da Chocolates dinta da sauran kayan ciye-ciye a dakinta amma hatta su ta kasa ci.. tayi losing appetite completely.