KASAR WAJE CHAPTER 10 BY MARYAM DATTI

KASAR WAJE CHAPTER 10 BY MARYAM DATTI

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Cikin jin dad’i yace to Bari Salisu ya shigo zai turo Allah ya saka an gode sosai
Tace babu komai a gaida goggon da sauran mutane suka yi salllama
Nan ta Kira Aliy shima tace yazo dama d’akuna uku ne a jere a gidan sai tsakar gida d’aya nata da yara mata d’aya na su Yusuf d’aya na babansu da yana Raye shi take so a gyara a siyowa goggo yalwati katifa da ledar d’aki ayi penti
Aliy ya iso ta masa bayani yace babu damuwa Inna da tun ranar da akayi pentin kika fada da gaba daya akayi ranar ma sabida pentin ya saura
Toh tace suka je d’akin suka gyara ita da aliy da layla
Kafin aliy ya je siyo katifa da carfet jin ance tsohuwa ce shi yanason tsofaffi sannan ta bashi 30k da wayarta tace za a turo accnt ya tura da 30k din.

Tun 7:am Yusuf ya gama shirinsa cikin pencil jeans dark blue da cover shoe da t.shirt na supermarket yana zaune yana cin bread d’in da hayfa ta had’a masa sandwich ta fito da d’an akwatinta a hannu ta zauna gefensa tana kallonsa har ya gama karyawa ta kwashe kayan shi ko kula ma da akwatin baiyi ba ta dawo

d’an kallonsa tayi cike da fargaba ta mik’a masa akwatin dukda ta yage d’an takardar da ke manne da kudin agogon
Kallonta yayi saidai duk ta gama tsurewa sosai ta dake tace gift ne sabida ka rik’a dawowa gareni akan lokaci

Kallonta yake bai gane ba itama ta kasa qara magana…

A hankali ya bud’e ya ga agogon maidawa yayi ya rufe ya mik’e

Rik’oshi tayi tace pls mamana ta bani kuma sai naga yafi kyaw da maza…

Kallonta yayi yace “No” kiyi anfani da abinki…!

d’an rungumoshi tayi cikin salon jan ra’ayinsa tace kenan mamana ba mamarka bace?

Shiru yayi….

Tace shikenna ni mamana tana yawan cemin abin miji na matarsa ne haka nata nasa ne amma tunda b…. Yace is OK

d’an murmushi tayi ta d’auko agogon ta saka masa a hannunsa ya masa bala’en kyaw rungumeta yayi yace “Nagode”!

Itama sosai ta qara rungume shi tace “I love u”..!

Yace “me too much baby”..!

Ya qara mata peck a goshi yace ki kula sosai da kanki in kuka tafi aikin kinji? 
Eh tace tana masa peck a kumatu itama ya wuce domin kuwa ya makara cewa akayi 7:am ta sameshi a gun aiki

Bayan fitarsa ta fara aikin gida da ta dawo aikin Bahrain zata d’auka made tace

Itama 10:am ta gama shiri driver yazo suka wuce.

A kamfani tanata shan harara ta bayan ido a gun Liliana da raudha saidai da sun had’a ido su yi mata murmushi har aka gama launch su da basuda aiki suka wuce gida ita kuma suka fara shirin Wucewa Ontario.

A supermarket an nunawa Yusuf kantar sa ta aiki inda daga customers sun shigo zai mik’e ya d’auka kwandon turawa yaje cashier ya bashi list d’in su yaje ya zab’ar musu kayansu yazo ya zuba ledoji ya raka su dashi har mota ko taxi..

Babban baqin cikin Yusuf shine domin kudinsa yayi auki dole ya haqura da pool yana full tym a supermarket wato 7:am to 9:pm

Inda ya kira Yasir da ke ta jiransa a pool ya masa bayani inda yacewa yasir kada ya bari a d’auki wani ya daure ya had’a duka yana yi sabida kud’insa ya qaru shima

STORY CONTINUES BELOW
Sosai kuwa shawarar Yusuf ta yiwa yasir dad’i domin har ya kusa dama gama nasa yaje yin na Yusuf da tsammanin Yusuf d’in ya makara ne

Koda suka yi sallama yasir ya nufi office d’in ogansu yayi masa bayani ogan ya amince domin dama yasir ya riga Yusuf fara aiki a gurin nan ogan ya lissafa abinda ya saura daga kud’in Yusuf ya bawa yasir yace ya bawa Yusuf.

A Ontario anata shooting inda manyan kamfanonin tallah suka zo ganin shooting harda kamfanin Harpic na wankin abaya nan kuwa hayfa ta qara samun kasuwa domin suma suka yiwa Armando magana

Wajajen 5pm ne Yusuf ya nema layin hayfa kusan sau biyar off yayi tunanin qila hanya ne bari ya mata msg ya mata msg shima duk ya fara laushi inda yake aiki babban supermarket ne mutane ko wani 5mnts suke shigowa
Kusan 11:23pm suka gama shooting d’in Ontario suna hotel a masauki hayfa da duk tayi laushi sabida bata tab’a aikin video ba sau kusan goma anayi a gogeq har dai aka samu yayi yanda ake so inda gobe zasu qarasa a cubec daga cubec zasu bi jet din kamfanin su dawo Toronto

Bayan tayi wanka tana zaune falon hotel d’inta mai girki ta kawo mata abinci tsabar gajiya da kewar mijinta ko kallon abincin ba tayi ba ta fara nemansa domin wayarta na kashe tasan ya neme ta.

Yana gida yana d’umama abincin da tayi masa kafin ta tafi dukda ba wani yunwar Ya keji ba domin shi yasir sauran abincin jiya yaci da hayfa ta musu ya wuce club
Wayarsa yaji tana ringing ya qaraso ganin number ta ya bari kiran ya tsinke kafin ya jefa kiranta

a hankali ta sallama

Shiru yayi….

Itama shirun tayi..

Ajiyar zuciya tayi..!
Yace mai yasa layinki baya shiga..?

d’an ajiyar zuciya tayi tace ” 4give pls na manta shine a masauki”

Ajiyar zuciya yayi yace kina ina yanzu?

Tace masauki…

Ina su Clara?

Qirjinta taji ya buga…

Tace sun fita..!

Yace OK ki kwanta yanzu ki huta sai da safe za muyi magana…

Toh tace… Yace gobe wani tym za ku dawo?

d’an shiru tayi tace da angama taron IA

Yace OK to ki kula da kanki pls 4me kinji?

d’an ajiyar zuciya tayi tace IA… Kaima haka

Zata kashe wayar taji muryarsa ” Miss u over”

cikin sanyayiyar murya tace “me too”..!

shiru suna jin numfashin juna kafin yace “nyt baby kada mu makara aiki mu duka”

ajiyar zuciya tayi tace “nyt my’ne” suka yi sallama cike da shauqi da begen juna..

Shi Yusuf da k’yar yaci abinci kad’an ya kira yasir yana aiki a club suna fira har kusan 20mnts suka yi sallama Yusuf ya kwanta

itama hayfa ga gajiya ga bacci a dole ta d’anci abincin kad’an ta sha coffee ta kira Ammah sunata fira kusan 40mnts kafin suka yi sallama inda ammah ke fad’a mata babansu na fama da hawan jini.

5:11am Yasir ya iso suka yi sallah tare da Yusuf domin ya riga yayi wanka a club da zai dawo suka karya suka fita tare yasir ya nufi pool Yusuf supermarket

Yana tsaye cleaners na aiki ya kira hayfa suka sha fira saida itama driver yazo ta masa sallama.

Haka yana aiki msg ya shigo koda ya duba masallaci ne sun kirashi wai sun bashi apointement yau bayan Ishaa

Sosai Yusuf ya shiga farinciki da fatan Allah yasa sun d’aukeshi ne gaba d’aya da haka yaci gaba da aikinsa

A cubec su hayfa sunsha aiki bayan sun gama wani kamfanin yad’a labarin new African Body a duniyar d’inkunan duniya ya nemi yiwa hayfa interview
Inda suka yi ciniki da Armando $25000 nan ya biya aka gyara hayfa inda ta buqaci saka abaya domin yin interview d’in yane kanta tayi sai tazama kamar balarabiyar Sudan
Haka aka yi aka gama inda suka wuce airport
5:40pm suka dawo Toronto hayfa duk tayi laushi sosai tace wa Armando driver ya ajiyeta gida kawai suka yi sallma

Bayan ta iso wanka tayi ta kwanta bacci ganin bata sallah
Yusuf ya kirata har ya gaji babu ansa ya kira café akace tana gida kallon agogo yayi ya kusa tashi amma daga nan kuma masallaci zai wuce kada yayi latti tun ranar farko a dole yace bari ya hak’ura sai ya ji kiran masallaci kafin ya koma gida

Hayfa sai 9:38pm ta farka saidai babu Yusuf wayarta ta d’auka ta fara nemansa shi kuma yana tare da committee masallaci yana rubuta contract na aiki da zai fara a yau ma ba gobe ba

Bayan ya gama signing contrac aka nuna masa d’akinsa da komai da makullai da zai rik’a bawa cleaners suna zuwa da asuba mace d’aya namiji daya kowa na aikin b’angaren jinsinsa

Yusuf na d’akinsa na gadi yana canza kaya zuwa wanda suka nuna masa na aikinsa yana tunanin yanzu hayfa ta nacan tana jiransa zama yayi kan y’ar kujerar d’akin ya kama kansa bari ya gama yaje gun zamansa na gadi sai ya kirata

Hayfa ta gaji da kiran wayarsa ta zauna shiru kan kujera dama yasir ma da Yusuf ya fad’a masa bazai koma gida ba shima a waje yaci abinci ya wuce club

Bayan ya gama shiri yana zaune ya jefa kiranta
Tana zaune gun taji qarar wayarta a d’aki da sauri ta shiga ta d’auka ganin sunansa taqi d’agawa
Qara jefawa yayi a dole ta ansa taqi magana wai tana fushi
Drewdrop pls 4give me ina gun aiki ne sai gobe zan miki bayani kinji

Kuka ta sakar masa kawai…

d’an rik’e kansa yayi yace pls 4give me baby zan miki bayani gobe IA

Katse wayar tayi ta qara sakin kuka wai su haka za suyita rayuwa aiki aiki kullum

Kallon wayar yayi shima duk zuciyarsa babu dad’i ya so yi mata msg ya fasa domin Idanunsa ne kad’ai zasu sauko masa ita daga fushin da tayi+

Yana gadin ya tuna yau 5dys yana neman Aliy shiru sai kawai ya jefa layin Aliy

Aliy na game shima a TV d’akinsa kiran Yusuf ya shigo ya ansa

Haba Mutumina wai Ina ka shiga na keta nemanka duniya?

Aliy yayi ajiyar zuciya yace Rasuwa a kayi inata wuni gidan makoki…

Cikin muryar damuwa Yusuf yace waye ya rasu?

Aliy yace Alhaji shamsu…!

Mugun bugawa qirjin Yusuf yayi yace tun yaushe? Haba Aliy shine ka kasa nemana ka fad’amin?

Aliy yayi ajiyar zuciya yace kada ka damu nasan fargabarka na yi magana da yaron Alhajin wanda zaici gaba da kula da dukiyar Alhajin zaka ci gaba da biyansa ko wani wata uku

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace da gaske Aliy?

Aliy yace IA

Yusuf sosai yayi farinciki tare da godewa Allah da yake had’ashi da abokan arziki kamar Aliy da Yasir

Godiya yayiwa Aliy sosai Aliy yace zan bud’e wani account gobe da sunanka sai Layla tayi signing can zaka riqa tura kud’in yanzu

Yusuf yace babu damuwa gobe zan turo maka kud’in bud’e account d’in sannan kaima pls sauran babu yawa ka saka mai a mashin d’inka

Aliy yace toh godiya na ke angon khadija wai yaya take?

Yusuf yayi ajiyar zuciya yace tana lafiya…

Aliy yace ka kula da ita da kyaw da alama tana sonka sosai..

Yusuf yace kai yaya ka sani?

da sauri Aliy ya gyara bakinsa yace tun lokacin bikinku mana…

Yusuf yayi murmushi yace nagode, wlh Aliy sosai rasuwar Alhaji ta tab’ani

Aliy yace wlh kuma saida ya warke a y’an kwanakin kafin rasuwarsa

Yusuf yace Allah ya jiqansa ya masa rahama ya saka masa alkairin da yayi a duniya da lahira

Aliy yace amin suka ci gaba da hirarsu ta tsakaninsu kafin daga bisani suka yi sallama…!

Kukan shagwab’arta tasha ta gaji kafin ta mik’e ta d’an had’a abu taci tasha coffee ta kunna data suka fara chart da aminiyarta sai kusan 2:11am suka rabu ta mik’e ma doguwar kujerar ta fara bacci

Yusuf bayan sun idar da asuba a masallaci ya bawa cleaners key da sauri ya kamo hanyar gida bcs 6:13 gashi 7:am supermarket so yake yazo ya lallab’a gimbiya ya shirya zuwa aiki

Yana hanya suna waya da Yasir inda suka had’u hanya suka qaraso gidan saidai Yusuf ya kalli Yasir yace ka jira na duba abu tukuna ka shigo

Dariya ce ta kub’ucewa Yasir Yace “wlh kana cin fuskata amma ba komai ay nima nafara shirin auren nan bari a gama waec a Nageria zaka sha mamaki”

Shi Yusuf dariya ma Yasir ke bashi yanzu wai yana jiran layla

Shiga yayi kuwa tana falo tana baccinta qarasawa yayi a hankali ya d’auketa kamar baby ya wuce da ita d’aki ya kwantar ya fito ya bud’ewa Yasir ya shigo

STORY CONTINUES BELOW

Yasir ya bud’e fridge sunada d’umame dayawa na abinci don haka ya d’auka d’aya ya d’umama musu shi da Yusuf ya had’a musu coffee

Yusuf shi wanka ya shiga dukda a d’akinsa na gadi na masallaci akwai toilet amma tsabar saurin yazo yaga gimbiya baiyi wanka can ba

Yana fitowa wankan tana d’an bud’e idanunta kad’an kafin ta juya fuskarta

da sauri ya qarasa ya d’ago ta yana kallonta taqi kallonsa

Ajiyar zuciya yayi yace pls dewdrop 4give me kinga rayuwarmu muna buqatar dayawan abubuwa ki duba muna buqatar gidanmu in bana aiki ya kike ganin zamu rayu?

hawaye ta fara masa…

d’ago fuskarta yayi da kyaw yace pls baby ki fahimceni ya fara share mata hawayen yana kallonta da yanayin da ke zautata ya birkita mata zuciya

shiru tayi saidai ba tayi magana ba…

Rungumeta yayi yana rad’a mata da IA wata rana zaki rik’a korana na fita kina buk’atar hutu

Duka ta kai masa a qirji ya saki d’an dariya yace yau zaki aiki?

Girgiza kai tayi alamar ah ah

Yace toh da 11:40 ki fito ki sameni gun aiki muyi lauch muna fita brk 12 kawai tazara ce tasa bazan iya dawowa gida ba

Toh tace ya d’auko wandonsa da ya cire ya zaro katin supermarket ya bata da address a jiki yadda zata isa gurin

Tashi yayi ya bud’e wardrobe ya d’auki wani milk jeans yasa dama yasa boxers tun a bayi ya d’auki wani t.shirt d’in na aiki sabida guda biyar aka bashi

Bayan ya gama shiryawa ta saka hijabi har qasa na sallah hannunsu na rik’e suka fito falon 6:43 Yasir ya kallesu ya ce barka da fitowa madam

Barka tace kawai…

Yusuf ya kalleshi yace babu tym na karyawa muje kawai

Yasir yace nidai nayi kuma dole ka jira zan dumama wancan jolof d’in mai zogale zan tafi dashi

hayfa tace Bari kaima na nad’e maka brkfst d’in

Toh kawai yace shi bayason lattin aiki

Haka Yasir ya gama ya d’auki abincnsa inda hayfa ta d’auki na Yusuf suka fito duka su hanunsu na sark’e da juna za ta raka su har taxi

Saida suka samu taxi mijinta ya mata peck a goshi suka wuce ta dawo gida..

gidan Liliana…

Liliana ta kalli Raudha tace amma ke zakir ya tabbatar miki nan ne gidan?

Raudha tayi tsaki tace ay kinji damuwata da ke kina tunanin a sanin halina da Zakir yayi zaimin qarya ne?

Liliana tace haka ne to ko tafiya yayi in ba haka ba tun 12 fa muke zaune qofar gidan har 4am ay da ya dawo tunda duk aikin kwana a nan bai wuce wannan tym mutum ya tashi

Raudha tace tactic zan canza…

Liliana tace kamar yaya…?

Raudha tace zan saka Zakir ya samomin number sa….

Liliana tace no ba Zakir ba…

Raudha ta kalleta tace sai wa?

Liliana tayi murmushi tace nima zan baki gudunmawa akwai wnn blond da ke aiki tare da su naga yana shiri sosai da d’an uwan guy d’in kuma da alama mayen kud’i ne sabida ranar da muka je na bashi $500 nace ya fad’amin sunansu yace “Yasir da Yusuf”

zanje club yau ni kad’ai sai na tsuma shi ko $3000 in bashi na tabbata ko bayada number zai samo mana amma zakir zasu fara zarginsa in yana ci gaba da neman sanin rayuwarsu

STORY CONTINUES BELOW

dariya raudha ta saki tare da dukan liliana tace shegiya kin fara wayo tun bayan rabuwarki da Nadal

d’an b’ata fuska liliana tayi tace why kike tayarmin da tabona kinsan har yanzu inason nadal fa

Raudha tayi tsaki tace ay sai kiyi tayi…

Liliana taci gaba da bata labarin yadda zata yaudari Tiffun ya samo musu number Yusuf da haka hankalin Raudha ya kwanta domin da number Yusuf za ta rik’a kama locations d’in da yake in ta kirashi

Murmushi tayi da tunanin daga ganin Yusuf zai iya Love da uwa uba sex domin shine jigon relationship a gurinsu.

A Nageria bayan Baba Haladu ya gama Karin kumallo ya sallami goggo alje da cewa zaije majalisarsu ta badarawa ganin aminansa malam jibrin da Malam arzuka inda Driver zai ajiyeshi bayan ya sauke yara makaranta

Yana gaban babbar sienna d’in tasu yaran duk suna baya sai khairat a jikinsa a gaba har suka sauke su Essence su kuma suka wuce Badarawa inda a hanya suka fara hira da driver

Driver yake cewa Baba haladu shi d’an sokoto ne

Da sauri Baban yace sokoto?

Eh yace iyayena da kakanni duka

Ajiyar zuciya yayi yace kasan sokoto kenan da kyaw?

Mutmushi yayi yace eh Alhaji mai yasa kuke tanbaya?

Baba yace inason zuwa ne neman wasu surukaina saidai bansan ta ina zan fara ba sabida ni daga Maiduguri sai Kaduna na sani cikin k’asarnan

Driver yace ya sunansu…?

Ajiyar zuciya BABA yayi yace wlh sunayen ne ban riqe ba amma suna rubuce a gida amma fa kusan 63yrs rabon da sanin inda suke

Tab yace baba ay ko iyayena ma ba  lallai an haifa ba lokacin amma dai zamu iya zuwa muyi ta nema qila Allah yasa mu dace

Baban yace yawwa yanzu sai yara sunyi hutu sai mu saka lokaci muje amma kada ka fad’awa uwar d’akinka komai koda y’ar uwarta ko yaran ma kaji ni?

Yace babu komai BABA Allah yasa dai mu dace da abinda zamuje nema

Baba haladu yace amin Allah yayi maka albarka

Amin yace suka ci gaba da y’an hirarraki har suka iso badarawa inda Baba haladu ya bawa Driver 3k kyawta dama Ammah na bashi 10k duk sati wai na kashewa bayan babu abinda basuda komai yi musu akeyi wanki guga girki saidai idan sunyi sha’awar cimarsu ta tsofaffi goggo ta dafa musu sabida tuni Daddy yana can gun course d’insa saura ma 2mths ya gama sai training 6mths

Gidansu Yusuf..!

Inna da layla sosai sun gama gyarawa goggo yalwatu d’akinta kuma sun gama girki domin baffa yahuza yace suna dab da shigowa Kano Aliy zaije tasha ya d’aukosu da motar gidansu sabida ance k’afar goggo yalwatu na kumbure baya son motsi dayawa

Toronto…

11:23am Hayfa ta gama shirinta tsaf cikin wata had’add’iyar abaya da aka bata a cikin wanda tayi tallarsu kwanaki abayar kana ganinta kasan wuta ce ta kama gashinta tsakiya ta yane kanta inda tasa wani lopas cover d’an ubansu shima cikin kayan da Armando ya basu ne gift d’in promotion na kamfani

Sosai tayi kyaw ta saka wani agogo mai qananan bracelets har kala hud’u da zobe biyu kawai ta rataya jakarta Luis vilton na kayan lefenta dama ta dafawa Yusuf jolof na couscous da nama da vegetables da zogale ciki sabida tunda yasan tazo da zogale yace komai zata dafa ta saka masa zogalen

Taxi ta d’auka ta bashi address d’in supermarket d’in

Koda ta iso su Yusuf saura 18mnts su fito brk don haka taga gurin da ake zama akwai tebur d jujeru biyu ko wani tebur ta je can da nisa ta zauna ta d’an kunna data tana kallon msg d’in grp d’insu na Zamani skull dukda ba tab’a magana ta keyi ba

Saidai tashin hankalin da ya fara tinkarota a gurin shine kallonta da taga mutane nayi sosai wanda hakan na nuna wasu sun gane ta kenan as Model wacce kamfanin su Armando suka sakawa suna “Angel Body”

Sunkuyar da kanta tayi tana b’oye fuskarta saidai dole bata tsira ba don ma an fito da kwalin close na supermarket d’in cewa sai kuma 1:pm za a bud’e dama kowa yasan qa’idar

d’an mik’ewa tayi ta bar gurin taje ta can bayan supermarket d’in tana hawaye idan wani ya furta aikinta a gurin nan shikenan tata ta qare…

Yusuf da ya fito yana ta duba gurin baiga hayfa ba  bayan ya ce mata akwai kujeru ta zauna gurin kan su fito wayarsa ya fitar ya jefa layinta

Kuka ma take yi kiran ya shigo a hankali ta ansa..

Yace kina ina?

Tace ta baya..!

Yace ki zo ina gaba a kujera zaki ganni..

Cikin sassanyiyar murya tace “pls my’ne kazo ta nan yafi shiru..

d’an ajiyar zuciya yayi Hayfa batada son mutane ya juya ya bi bayan can ya hangota ta had’a kai da gwiwa da d’an hanzari ya qarasa ya zauna yana d’aga kanta yace” dewdrop mai ya same ki”?

d’an murmushi ta qaqalo tace kawai kaina ke d’an ciwo

Peck ya mata a goshi yace “sorry baby gajiya ne” in kika koma gida ki qara yin bacci kinji?

Toh tace…

Mik’a masa abincinsa tayi tace “kanajin yunwa ko”?

Eh yace amma ba yunwar abinci ba

d’an kallonsa tayi cikin rashin fahimta

Shafa fuskarta ya fara yi yana mata wani irin kallo

Yace “inajin yunwar matata ne”..!

d’an sunkwi da kai tayi cikin kunya ta kasa cewa komai

Yace wai bak’on bai tafi ba har yanzu..?

d’an duka ta kai masa a qirji..

Janyota yayi yace “pls a taimakamin mana”

Tace yaushe za muje gurin da kace za muyi 2dys in na dawo?

Ajiyar zuciya yayi yace yanzu ay babu rana kinga na fara wani aikin kwana jiya kuma albashin yanada kyaw ga lada

Kallonsa tayi cike da mamaki…

Labari ya bata na aikin masallaci yana bata tana hawayen yadda sam baya hutawa sannan mainene makomar aurensu babu wani lokaci isashe da suke da shi na Kansu

Riqe fuskarta yayi yana lallashi tare da nuna mata aikin na lokaci ne nan zuwa wani lokaci zai bari IA sabida inason fara karatu

Badai ta dena hawayen ba ya rungumeta yana rad’a mata in kuma zaki zo can mu kwana tare shikenan inada d’aki a gurin

d’agowa tayi tace “da gaske inzo”?

Shi tsokanarta yake

saidai ya ga ta d’auka da gaske..

Kallonta yayi da mamaki yace “zaki iya zuwa”?

Girgiza masa kai tayi…!

Kallonta yake sosai yana jin wani masifar sonta..!

qara rungume ta yayi yace zan tanbayi ogana na masallacin in ya amince zan biyo gida mu wuce

bata ce komai ba suna dai rungume da juna kafin ya d’an saketa tace toh kaci abincinka saura 15mnts ku koma aiki

“Toh” yace ta bud’e abincin ta fara bashi da kanta har ya qoshi ta rufe sauran tace ka ajiye ko anjuma ko?

Murmushi yayi ya shafa fuskarta yace “Nagode baby”..

Sunyi firarsu kafin Yusuf ya rungumeta ya mata peck a goshi suka yi sallama ya koma aiki ta kamo hanyar gida

Wajajen 5:13pm Yusuf ya d’an samu kiran Hamzad yace masa matarsa na da tsoro bata iya zaman gida ita d’aya za tazo ta tayashi zaman aiki in babu damuwa

Hamzad sosai ya qara yaba hankalin Yusuf d’an yaro dashi yayi aure domin gudun fad’awa fitinar sha’awa

Dariya yayi yace babu komai amma d’akinka zata rik’a zama bawai ta fito waje inda kake zuwa patrol ba

Yusuf cikin farin ciki yace Nagode sosai suka yi sallama

Yayi wa hayfa text ya fad’a mata kuma yace abaya zata saka dukda d’akin nasa na d’an nesa da masallacin can baya ne.7:23 Yusuf duk a gajiye ya iso gida hayfa tuni ta gama shiri kuma tayi wanka tayi girki+

Wanka yayi ya fito ganin hayfa na sallah yasan tayi tsarki don haka ya je falo zai fara cin abinci Yasir ma ya shigo shima duk yayi laushi suka yi sallah tare suka fara ci abinci suka d’an zauna fira duk Yusuf hankalinsa na d’aki ya samu ya kwashi gara kafin su wuce

Yasir ne ya dawo dashi tunaninsa inda yake bashi labarin sun fara waya da Layla ta wayar Innarsu ashe ma laylan na da waya yanzu

Yusuf dai kallonsa yake domin duk a matse yake

Haka dai suke ta hirar sama-sama har kusan 9pm Yasir yace zai tsaya yayi aski da gyaran fuska daga nn ya wuce club suka yi sallama ya wuce

A hankali ya shiga d’akin tana shafa lotion ya qarasa ganin kallon da yake mata tasan kwanan zancen

d’aukarta kawai yayi ya kwantar ya fara romancing baji ba gani kamar maye

A hankali da zazzafar buqata ya fara mata hidima suka farantawa juna rai sosai yana jin kamar ya shigar da ita jikinsa

Suna manne da juna agogon hannun Yusuf ya buga 10:pm a mugun firgice suka mik’e duka suka shiga wanka da sauri suka shirya ta d’auki jakarta suka fito gidan

Allah ya taimakesu Hamzad na tilawar haddarsa suka iso ya kalli Yusuf yace “ka kiyaye latti Oga bayason haka in yaji bazai maka uzuri ba”!..

Yusuf ya ce IA..

Nan ya musu sallama ya shiga motarsa ya wuce su kuma suka wuce d’akin Yusuf ya canza sosai hayfa taga kayan sun masa kyaw farar shirt ce da dark blue wando da bak’in Takalmi

Mik’ewa tayi tai masa peck a kumatu ya rik’o hannunta yace yanzu ki kwanta zanje na fara patrol haka akeyi ko wani 30mnts

Rungumar juna suka yi sosai kafin ya fito ya barta ta kwanta kan doguwar kujerar d’akin

Haka dai ko wani 30mnts ya fita ya dawo tana bacci yana kallonta sa’in shima ya d’anyi baccin na mintuna ya sake fita ya dawo har asuba ya tayar da ita tayi alwala ya wuce masallaci ta bisu bayan Idar da sallah ya bawa cleaners key suka kamo hanyar gida duk yayi laushi

A gida wanka yayi ya d’an kwanta jikin matarsa tana shafa kansa ya samu d’an bacci yace mata 6:45 ta tashe shi

Yasir ya dawo ya shigo dama Yusuf ya masa text cewa in ya iso kawai ya shigo ya karya ya wuce sai sun had’u da yamma haka kuwa yayi ya wuce pool shima

Allah sarki Allah ya taimaki kowa amma haqiqa ko wani qoqari na tare da sakamako na alkairi.

6:45 hayfa tsabar tausayin mijinta na ganin yadda yake bacci kamat jariri yasa taji kamar kada ta tasheshi amma dole ta yi

d’ora hacinta tayi kan nasa tana jan numfashin sa hannunta kuma tana wasa da nipple d’insa a hankali ya saki wani ajiyar zuciya ya bud’e idanunsa sai cikin na ta

Murmushi ya mata ya shafa fuskarya yace “love u baby”

Murmushi ta masa itama

A hankali ya mik’e ya sake shiga bayi yayi wanka ya fito ya shirya kamar tayi kuka domin abincin ma nad’e masa tayi kada yayi lati gurin cin abincin.

Haka rayuwarsu ta kasance kullum cikin aiki ranar da hayfa ta samu sarari tabi Yusuf masallaci itama sunata shirin Gala gashi sosai ta samu qananan aikace-aikace na tallace-tallace sai contract d’inta na foundation d’in magajin saudiya tuni Armando ya karb’a inda ya fad’a mata yawan kud’in a naira tace ya raba ya tura rabi sauran ya bud’e mata account a nan Toronto sabida yace zai karbar mata takardar k’asa saidai tanata tunanin yadda za tayi da Yusuf ganin last mth ya saya musu na 3mths dama yawanci na 3mths yake saya musu kafin ya qare ya sake tara wani kud’in

STORY CONTINUES BELOW

Yusuf yana aiki yana tunanin number da ke yawan yi masa msg na tsiya gashi ko yayi reply ya tanbaya anqi fad’a masa ya kira aqi ansawa dole ya hak’ura tun yana sharewa zuwa yanzu ya fara damuwa da sanin waye wannan

A kwanakin ya fara reply in aka masa saidai shima yanaso ne yasan waye shiasa.

A b’angaren Raudha sosai take cikin nishad’i na ganin alamun Yusuf ya fara shigowa hannunta sai sunyi zurfi zata fara masa magana ta wpp

Koda Yusuf ya ansa albashinsa na farko na masallaci ya sayi waya kalar tasa ta da wato wace ke hannun hayfa saidai itama hayfa Bunil ya bata IPhone11 pro irin ta su Raudha amma dole ta b’oye tana ma tunanin bawa aminiyarya ne Salma idan ta koma hutun azumi Nageria sabida salman wai Wayarya Infinix take anfani dashi har yanzu

A b’angaren Yusuf sosai ya maida hankali wajen ganin ya tara kud’i ya kama musu gidan madam Hayek da ke kusa da na Yasir

Haka hayfa ta fara zuwa aiki wasu garuruwa inda sai ogan café ya kira Yusuf yace masa Contract suka samu na biki ko ceremony ko dai qarya kala-kala tun abin na damun Yusuf na tausayawa hayfa har ya fara hak’uri ganin shima ba zama yake ba

Yanzu ga tafiya zuwa Jidda inda nan ne za a fara taron foundation d’in magajin Saudi gashi duk k’asar da zasu bud’e reshe to wace aka zab’a wakiltar k’asar aikin duba project d’in na wuyanta wannan yasa za’a biyasu da tsada inda sintirin zuwa Nageria ya kama hayfa dukda ma an bata zab’in garin da zaifi dacewa a Nageria

Inda ta cewa Armando Kaduna nan suka duba gurare ta internet inda suka zab’i guri A babban titin Kinshasa road U/rimi

Haka suke aikin ita da Armando online dole take zuwa kamfani sabida tsoron kada Yusuf ya ganta da Laptop yace ina ta samu saidai A yanzu wunin kamfanin ya fara isarta tana son ansar laptop d’in yaso za tace masa kud’in café ta tara ta saya…

Tana tashi kamfanin ganin 3:35pm ta wuce gurin Yusuf

Yana aiki yanzu duk colleagues d’insa sunsan hayfa yayinda a lot sunsanta a dalilin su d’in masu karanta models magazines ne a supermarket d’in kansa akwai magazines d’in da hayfa ke ciki amma Allah bai qaddaro Yusuf ya gani ba izuwa yanzu kuma kunsan bature shi baya shiga sabgar da ba tasa ba

A bayan gurin da suka maida na zamansu a dole

Kallonta yayi yace dewdrop yaya? Kinga ba tym d’in brk ba ne kada mijinki yayi laifi ko..?

d’an b’ata fuska tayi tace “shikenan bari na tafi to”..

Janyota yayi jikinsa yana kallonta yace duk duniya babu wani hidima da yafi naki ina jinki…

Tace dama na tara kud’ine inason sayan system..

d’an shiru yayi kafin yace “ki bari na dawo gida za muyi magana sosai IA..!

Toh kawai tace suka runguma yayi kissing d’inta ya koma aiki ta wuce

Bayan shigarsa gun aiki wani colleague d’insa Sebastian ya tanbaya da kamar nawa za a samu system?

Sebastian yace ay munada su a sama wajen electronic in kanaso kawai kayi applying ka d’auka sai ana cirewa a kud’inka

Sosai Yusuf yaji dad’i inda suka haura shi da Sebastian sabida matar Sebastian na aiki a saman

Nan ta nuna musu wanda zaifi kyaw da mata na zamani saidai da d’an tsada amma Yusuf ya ansa ya cike komai ta saka aka nannad’e masa kamar gift jakar system d’in ma kawai d’aukar hankali take.

Sai bayan ya tashi supermarket ya kira Yasir

Yasir yace ina k’ofar gida ka qaraso muci abinci yau da wuri zan shiga club

STORY CONTINUES BELOW

Yusuf yace “OK” ya kashe wayar ya kamo hanyar gida

A gida hayfa tuwon shinkafa tayi miyar kuka yaji daddawa da nama

Bayan tayi magrib tana d’aki tana karatun qur’ani suka shigo dukda gaskiya yanzu karatun ma ba sosai take yi ba tayi busy sosai wajen neman duniya Allah ya kyawta

Jin qanshinsa ta d’an juyo domin tunda ya fara aiki supermarket ya maida hankali wajen anfani da turare..

Qarasawa yayi bayan ta yana tsaye ta rufe qur’anin ta mik’e ta nad’e daddumar ta juya zuwa gareshi

Wani janyota yayi jikinsa ya rungume sosai suna ajiyar zuciya zuwa yanzu wani irin kusanci ne da shak’uwa suke ji sosai kamar su d’in dama can tare suka tashi kafin suyi aure

d’an d’agowa tayi tana kallonsa tace “kai kad’ai ne”?

peck ya mata a goshi yace “mu duka ne yana dariya”

d’an tureshi tayi tace “shine harda tsokana ko”..?

Sorry baby yace muje ki bamu abinci lokaci na tafiya ko yau za’aimin rakiya?

Tunani tayi tanada aiki sosai da Armando ya bata na lissafin k’auyukan da ke jahar Kaduna da yawan mutanensu da makarantun gomnatin k’auyukan

Shafa fuskarsa tayi tace “my’ne inada wani abu da na keson dubawa internet daren yau 4giv me gobe IA”..!

Kamo bakinta yayi yai kissing yace “Uzurinki ya karb’u” ya rik’ota suka nufo falon sabida bata cire dogon hijabin sallarta ba

A falo Yasir ya kallesu yayi mitmushi mugun birgeshi suke yadda suka gina So da shak’uwa tsakaninsu kamar tare a ka haifesu

Gaisawa suka yi da hayfa ta wuce kanta ta d’umama musu miya ta juye a bull ta kawo musu da ruwan wanke hannu kafin ta koma d’aki

Sosai suka ci tuwon shi kansa oga Yusuf yayi lodi alhalin yawanci fa hayfa saita qara shiga internet take musu gitkin

Bayan sun gama suka yi ishaa tare ta bisu Yasir ne yayi musu jam’i bayan sallah suka d’anyi hira Yusuf da Yasir inda Yasir ke fad’awa Yusuf su shirya fara karatu wannan komawa da za a yi nan da 5mths

Yusuf ya d’anyi shiru kafin yace zan gani dai Allah ya mana jagora

Yasir yace amin suka yi sallama Yasir ya wuce club

Yusuf ya mik’e hayfa na duba wani american buk yace “dewdrop ki rufe idanun ki ina zuwa yanzu sai nace ki bud’e fa zaki bud’e”…!

d’an dariya tayi tace “toh” ta rufe idanun..

Falo ya dawo ya d’auki jakar system d’in ya shiga har gabanta ya zauna sannan ya ajiye mata gabanta yace “ki bud’e”

A hankali ta bud’e wani irin ajiyar zuciya tayi ganin kyakykywan jakar system d’in sannan ta kalleshi bai ce komai ba ta k’ara kallon jakar a hankali ta bud’e taga system d’an ubansu Acer sosai yayi mata kyaw taji yama fi Apple d’in da su Armando kyaw da daraja a idanunta

Wani irin hawaye ne suka zo mata da ta kasa b’oyewa

Oh oh oh yace “meye haka”..?

Kallonsa tayi sam ta kasa magana da duk halin da yake ciki baya tab’a kallon kansa sai ita shi kansa yanada buqatar isasun kayan sawa don ma aikin supermarket wando ake canzawa kawai da Takalmi amma still yanada buqatar kaya to ma ina ya samu kud’in sayan wannan kyakykyawan system d’in

Katse mata tunani yayi… Munada shi a gurin aiki na anso miki… Za tayi magana ya had’a bakinta da nasa yana mata wani had’add’en kiss da numfashinta ma kusan fisgewa yayi

A hankali ya d’ago yana kallonta yace “pls kimin biyayya karki ce komai jst ki yi abinda kike son yi..”

Ajiyar zuciya tayi ta rungume shi tana furta “I love u so much my’ne”…!

Yace “love over baby”

Sun dad’e rungume da juna kafin suka saki juna suka fara d’an hira kafin ya wuce masallaci sun dad’e tana kwance jikinsa yana bata labarin Abokinsa Aliy suna dariya kasancewar Aliy akwai abin dariya alarm d’insa ya duba saura 20mnts da sauri ya mik’e yasa takalmi suka rungume juna akayi kiss na tsiya da romance a tsaye kusan 5mnts kafin ta saka hijabi ta rakoshi har sai da ya shiga taxi ta dawo gida

Kunna system d’in tayi ta d’auko jakarta ta d’auki flash d’in ta da Armando ya bata ta shiga internet ta fara aikinta sosai tayi aiki saidai ko wani 1hr za suyi waya da Yusuf kafin kowa ya koma aikinsa inda itama sai kusan 3:45 am ta tsaida aikin ta kashe system ta kwanta domin Armando yace jibi zai tura da reports d’insu Saudia shiasa babu lokaci kuma tsabar son kud’i irin na Armando haka ya qara tranning hayfa kwata-kwata sunqi saka kowa cikin aikin daga shi sai ita sannan wai qarshen wata zasu Nageria su Zab’i k’auye d’aya da za suyi hotunan da zaayi calender da t.shirt da komai dai na foundation d’in wanda hotunan zai zama hayfa da yaran qauyen ne..

Wannan ma shine babban tashin hankalin hayfa yadda za tayi tafiyar ta yaya zata sanarwa Yusuf dukda Armando yace ta bari yasan abinda zasu shirya shi da ogan café da tuni ta daina aiki gunsa

A screen d’in system d’in hoton Yusuf ne a Supermarket yana tsaye zai d’auka abu ta masa yayi kyaw matuqa kamar wani star ko d’an k’wallo sabida sosai jan t.shirt d’in aikin supermarket ke masa kyaw

Sannan sunansa ne da na ta password d’in system d’in inda tasa “YuHa” a yayinda Armando ya tanbayeta sunan da za tayi anfani da shi a matsayinta na ambassador d’in foundation d’in na reshen Nageria tace “Khadija Yusuf Suleiman”

Kwata-kwata hayfa ji take rayuwarta yana tafiya ne tare da albarkar Yusuf domin tasha zama tana tunanin inda ba suyi aure ba ta yaya za tazo Canada sannan shi ya tilastata aiki a café har ta had’u da Armando lallai to duk wani ci gaba da arzikinta yana qarqashin albarkar auren Yusuf!

kwanaki na wucewa lokaci na tafiya.

Innarsu Yusuf ce a tsakar gida ita da goggo yalwatu inda goggon ke hawaye ganin itama ciwon qafa ya sata gaba ta kalli innar Yusuf tace “lauratu nima haka zan mutu ban qara ganin Inzo haru ba ko zuri’arsa duk haka kowannen mu ya rasu da wannan bak’in cikin nima haka zan tafi da shi ta fashe da kuka…

Lallashinta inna tayi tace kiyi hak’uri goggo addu’a za muyi tayi inda rabo sai kiga an gana haka malam yayi ta neman shima har ya tafi ke kinsan wannan ne dalilinsa na zaman mu kano amma Allah bai cika masa burinsa ba sai addu’a

Goggon tace laifinmu ne kowa yasan inzo da zafin rai wai yace yunwa yake ji guziri ya qare innarmu tace ya bari mu shiga gari shikenan su Hammadi da gambo da danbaji suka fara tsikarinsa wai ya faya ci hakan yasa muna shiga mota ya wuce wai zaije neman abinci shikenan har yau ta qara fashewa da kuka

Inna dai sai lallashi take goggo tace wlh idan Isuhu ya dawo dole mu fita neman inzo

Shiru Inna tayi tab ta ina yaushe Yusuf zai dawo saidai bata furta komai ba sanin halin masifar goggon.

yau saura 16dys madam hayek ta tashi su Yusuf su koma inda saura 39dys Gala sannan saura 8dys zuwan su hayfa Nigeria domin kamfaninsu ma ita da y’an uwanta wai 2wks b4 azumi za suyi innogration na bud’e shi saidai lokacin hayfa ta dawo Canada

Yusuf ma anata shirin abubuwa da akeyi na azumi a masallacin su inda akwai ranar rabon kayan azumi ga mabuqata musulman Toronto da masu kud’i da ministan keyi duk shekara

A gefe sosai Yasir ke nace kiran layla dukda ba wani sakewa take ba tana jiran sai taga result d’inta tukuna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page