IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 13 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 13 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

idanuna sosai idan na masa rashin mutunci zagin jama’a kawai ma ya ishe ni.
Nafisa tace “Tsaya jin kunya ki cuci kanki, idan baki koreshi ba, haka zai ci gaba da nace miki yana zuwa gidanku yana raina miki hankali, banda rainin wayo ina ruwan shi da samarin ki? Ke da kike da kamar Kamal me za ki yi da wani Sulaiman”. Da wannan hudubar ta Nafisa ta zuga ta tsaf harta kuduri aniyar yiwa Sulaiman korar kare domin a yanzu kadan take jira su rabu har Allah-Allah take Sulaiman ya yi wani dan yunkuri domin tasamu kafar da zata yi

masa kaskanci sai aka ci sa’a Sulaiman bai zo ba kuma bai bugo wayaba. Ana cikin haka Rahama ta zo gida zata yini nan suka hadu da Safina suna cikin hira suka gangaro zancen Sulaiman, Rahama ta soma yi mata maganar sabida tana son ganin Safina da Sulaiman a tare domin namijin kwarai ne tace.
. “Ina mutumin ki Sulaiman kwanaki ya zo gidana neman ki”. Ta tabe baki. “Rabu da shi kawai daga yanzu koda ya
zo gidanki nemana ki daina sauraronsa domin ba Sulaiman din da kika sani da bane, yanzu duk yabi ya zama kamar mahaukaci baki ga talauci ne ya same shi ba, domin naji ance sun samu matsala da maigidansa ya koreshi daga kasuwa”. Rahama ta rike baki cike da rashin jin dadin yanda Safina tayi maganar, tace “Ayya rayuwa kenan ashe Sulaiman yana cikin jarrabar rayuwa, to yanzu ya maganar aurenku?” Safina tace “Tab” Har da tafå hannaye zancen kike so, ni kuwa ta in azan iya auren Sulaiman?


Rahama cikin razana ta buda idanu “Saboda me? Ba zaki aure shi ba? Alhalin akwai alkawarin aure a tsakanin ku” Safina tace. “Wannan da kika sani amma banda Www.bankinhausanovels.com.ng
yanzu, ni kuwa ta yaya ina ganin kashi da rana zan saka kafa na taka, idan na yarda na auri Sulaiman mai na kasa ya ci bare ya baiwa na sama”. A hasale Rahama tace “Wai me kike son gaya min ne? ko kina son tabbatarwa duniya da ainahin kalar mu ne?, inbanda haka ya za ki fasa auren Sulaiman, ai bai kamata ki juya masa baya ba don bashi da shi, mene ne aibun shi mutum mai mutunci, ko ya talauce ai bashi ya dorawa kansa ba ballema har yanzu yana iyakar kokarinsa akan ki”. Ta dan sassauta murya data fahimci maganar da take yi ba shiga kunnen Safina take ba.
“Haba Safina ina hankalin ki ya tafi Sulaiman da yake matukar sonki shi ne fa ya gina miki rayuwa, yake da burin-ingata miki nan gaba, me yasa za ki juya masa baya, idan kika yi haka sai hakkinsa ya kamaki domin koda zagin jama’a kawai aka barki dashi ya ishe ki, kowa yasan irin dawainiyar daya sha dake…” Tayi saurin daga mata hannu.
“Kinga kada ki cika ni da surutu, ke za ki yi min zaman auren? Ko kinfi son na aure shi komai ya gagare ni sai dai ku rinka taimakamin idan dan ta abinda ya yi min ne sai a biya shi har da riba, domin Kamal ba matsiyaci bane yafi shi komai”. Taje ta kinkimo kayan daya kawo mata ta turawa Rahama wai dan ta burgeta “Duba kiga inda ake harkar arziki, wannan ya dame Sulaiman ta koina”. Rahama ta dubi tulin kayan data kawo mata ba tare data duba ba ta tabe baki tir da wannan sabuwar halayyar taki domin kin bani
mamaki sosai ki rasa wanda za ki yiwa butulci sai mai tsananin sonki so na hakika, wanda kowa ya shaida mai sonki ne, mai kaunarki ne, mai son ci gabanki ne…”. Safina tayi saurin dakatar da ita cike da izgilanci haba Hajiya Rahama mene na tada jijiyar wuya? Sulaiman dinan fa ba dan uwanku bane, ba dan uwan mijinki bane balle kiji haushi. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Amman ko ba dan uwana bane aike ‘yar uwata ce kuma dole idan kika yi ba daidai ba na fada miki gaskiya domin wannan hukuncin da kike shirin yanke wa tsananin butulci ne da yaudara har da zallunci ma, in banda haka tayaya za ki yiwa Sulaiman haka? mutumin daya dade yana jiranki, ya yi wahalhalu da dama akan ki, ya gina rayuwarki da ilimin, kin riga kinyi alakawarin auren shi sannan daga baya kice kin fasa, alhalin a addinance ma baki kyauta masa ba domin addinin mu ya yi hani da karya da kuma yaudara, wannan hanyar fa da kika dauko bamai bulewa wa bace, kamata ya yi ki nutsu kisan abinda kike
yi domin rayuwa bata da tabbas abubuwan da kike hasashe ba lallai su zama gaskiya ba domin Allah baya barin hakkin wani akan wani, ni dai ina baki shawara idan kin dauka zata yi miki amfani, domin ni ‘yar uwarki ce bazanga kina shirin yin abinda zai cutar da kena kyale ba”, Cikin tabbatarwa Safina tace.
“Kwarai nasan ba za ki bani shawarar da zań cutu ba, amman gaskiya ba zan iya dauka shawarar ki ba domin ni ba zan iya yin auren kakani-kayi ba, nafison na yi aure na kece raini inda zan huta wani nawa ma ya huta don yanzu kowa gudun wahala yake yi babu wanda zai so ya yi rayuwa cikin talauci, idan na yarda na auri Sulaiman kamar na siyawa kaina wahala domin ba zai iya daukar dawainiyata ba dan ni bukatatuna yawa gare su, ke kanki a yanzu kinsa nafi karfin auren Sulaiman dube ni ki dubi fatar jikina idan na aure shi mai nakasa yaci bare ya baiwa na sama? Yadda nake son jin dadi da more rayuwa, ai idan na auri Sulaiman gaskiya na ruguza rayuwata, don haka niba zan yi abinda zan kwari kaina ba”. Rahama kuwa sai duban Safina take yi tana duban fatar jikinta luki-luki kamar zaka taba jinni ya fito kamar wacce bata taba shiga rana ba,ta nisa tace mata.
“Amman kinyi babban kuskure da kike tunanin auren Sulaiman shi ne kwarar kai domin Sulaiman shi ne mutum mai zuciyar farantawa wanda yake so, kuma yana da zuciyar neman halak, ko a cikin masu dukiyar sai kin tara kafin ki samu mutum mai sakin hannu kamar Sulaiman, ni a ganina auren shi ba shi ne cutuwa a gareki ba, wannan yaudarar da kike wa samari shi ne cutar kai domin addini ma bai yarda da hakan ba, kamar yanda kika yiwa Sulaiman karya za ki aure shi daga baya kika dawo kike neman yi mai butulci saboda kin samu wanda ya fishi abin duniya”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sulaiman tun ranar da suka rabu da Safina bai sake samun sukuni ba, haka ya yi ta kwanciya a daki yana murkususu har abin yana neman ya zame masa cuta, ko abinci baya iya ci bashi da aiki sai dai ya kwanta ya yi ta juye-juye yana tunani, ya rasa abinda yake masa dadi a duniya, ba abinda ya tsaya mai a zuciya irin mugun butulcin da Safina ta ke neman tayi masa, ya tuna irin tsananin son da yake mata da irin wahalhalun da yasha akanta, duk duniya babu wanda ya wahaltawa kamarta, tafi kowa cin moriyarsa sabida tsananin son da yake mata ya gwamace daukar nauyin karatunta sabida baya son wani ya saka hannu a cikin sha’anin Safina, wani irin
so yakewa Safina da shi kansa bai san iyakarsa ba, amman a yau an wayi gari Safinar da yake so yake kauna ta juya mai baya, nan take yasake jaddada al’amarin kaico lallai duniya ba alkawari domin da duniya da gaskiya da amana ruwa ba zai dafa kifi ba, Iliyas ya katsewa Sulaiman tunanin daya zamo abokinsa a tsawon kwanakin nan, ya yaye labulen yanayin sallama, bai zauna ba sai ya tsaya yana karewa Sulaiman kallo ganin yanda ya koma da kuma yanda ya amsa sallamar, ya je dai ya mikamai hannu suka yi musabaha, dayaga Sulaiman yana ta faman yake hakora wai a zuwan fara’a yake sai ya biye masa ya shiga janshi da hira mutumina kayi wuyar gani kwana biyu harna gaji da cigiyarka, shi ya saka na biyo sawu naga abinda ya boyeka a gida baka fita majalisa? Ya dan kawar da kai.
“Kai dai bari kwana biyu bana dan jin dadin jikina”. Iliyas ya girgiza kai cike da rashin yadda “Bayan rashin lafiya akwai wani dalilin daban” Cikin mamaki Sulaiman yace “Kamar wanne kenan?”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Koma dai mene ne kai kafi ni sani, domin batun yauba na karanci damuwa karara akan fuskarka, tuntuni na fahimci kana da damuwa a cikin zuciyarka amman kana boyewa a tunanina idan har amincin mu dake tsakaninmu gaskiya ne bai kamata ka ɓoyemin komai ba, domin sanin kanka ne ina tare da kai bazan guje maka ba kowanne hali ka shiga ko wuya ko dadi, kamata ya yi a ce duk wani yanayi da kake ciki nine mutum na farko da zaka fara sanarwa don haka ko me ya dameka wannan zurfin cikin ba zai haddasa ma komai ba sai bacin rai”. Sulaiman ya yi shiru yana nazarin zantukan, yasan gaskiya dayace kuma yaga rashin jin dadi a fuska Iliyas ya matsa ya dafa shi.
“Kayi hakuri abokina ka daina zargina ko ina son boyema halin da nake ciki ne kasan kafi karfin komai a wajena, kai shakikan abokina ne bani da sama da kai, tare muka tashi muka yi kuruciya, muka yi wasa tare muka yi duka gwagwarmayar yarinta data neman ilimi, har Allah ya rayamu zuwa yanzu ni da kai a yanzu mun wuce matsayin abokai sai dai mu kira kanmu ‘yan uwa, ta ya mutanen da suka shaku haka har daya zai iya boyewa daya matsala? Kawai dai na jinkirta ne har sai na gano ainahin abinda yake shirin faruwa dani”. Iliyas ya dan yi murmushi saboda abokinsa ya yi kalamai da suka sanyaya masa zuciya, sannan yace.
“Wai wace irin matsala kake fuskanta alhalin nasan kai mutum ne mai sa’a?”.
“Ai ba kullum ake samun sa’a da nasaraba”.
“Amman dai nasan baka da matsala data wuce ta wannan yarinyar”. Sulaiman ya dan sosa keya cike da damuwar abinda zai fada “Wallahi a yanzu ma ita ce babu ja a zancenka” Iliyas ya Harare shi cike da takaici.”Ai baa bin mamaki bane dan ta sanyaka a Www.bankinhausanovels.com.ng
cikin matsalä, tuntuni nake saran a dalilin yarinyar nan zaka iya tsintar kanka cikin matsaloli domin ina tsoron al’amarin ta dan haka nake da niyar idan har na samu ta barmin kai da lafiyarka da hankalinka aina godewa Allah”, Sulaiman sai ya tsinci kanshi da rashin jin dadin abinda abokinsa ya fada. “Ta barni da hankali kamar yaya?”
“Ina nufin idan ta gama karbe abin hannunka kar ta dawo ta karbe hankalinka da lafiyarka ta barka ba nutsuwa”. Sulaiman cikin son abar wannan maganar yace “Kace kana son kaji damuwa ta amma kuma baka barni na fadama ba”.
“Ai ko baka shaida min ba nasan bai wuce kace kana fuskantar wani babban kalubale daga yarinyar ba, shi ne ka dorawa kanka damuwa kake neman ka cutar da kanka, ko ba haka bane?”. Sulaiman ya nisa.a ture maganar wasa wallahı da gaske
wannan karon Safina ta juya min baya, ta fara yimin
kora da hali”. Iliyas ya gyada kai.
“Nasan daman komai dadewa akwai ranar da hakan zata faru, shi ya saka kullum nake gargadinka kabi a sannu, saboda irin wadannan matan basu fiye cika alkawari ba sabodą takamarsu suna da kyau, basu da burin daya wuce su yi ta wanke samari suna cutarsu”. Sulaiman yace.”Nasan akwai mayaudaran mata amman ban taba saka Safina a sahunsu ba, domin nayi zaton kaunar da take yi min ta gaskiya ce, nayi tsamanin zata aure ni shi yasa data juya min baya ta saka ni cikin shakku da juyayi”. Iliyas yace “Lallai har yanzu baka san halin mata ba, to idan Safina bata nuna maka haka ba tayaya zaka gane ainahin halayyarsu ta ‘ya ya mata?”. Sulaiman yace “To yanzu dai mene abin yi?”.
“Mene ne abinyi kuwa daya wuce ka hakura da ita, tunda ba akan ka aka soma shan wahala da dama akan mace daga baya ta dawo tace ta fasa”.
“Gaskiya bai kamata na hakura haka da wuri ba, sabida bata fito tace ta fasa aurena ba, kawai wulakanci take yi min iri-iri shi yasa na shiga cikin damuwa kwarai”. Iliyas yace. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ai ba sai ta fito ta fada maka cewar ba zata aureka ba, wannan abun da take yi maka shi ne alamar bata yi da kai, hannunka mai sanda kawai take yi maka, a maimakon ta fito fili ta fada maka kawai ka nemi wata, ko baka ji ance kora da hali yafi kora da kara ba?”. Sulaima yace “Duk da haka bai kamata nayi gaggawar janyewa ba, so nake idan ka samu lokaci kaje wajen Safina ku tattauna ko a samu wajen da matsalar take?”. Iliyas ya danyi shiru zuciyarsa cike da tausayin halin da abokinsa yake ciki, domin yasan so musifa ne kuma Allah ya riga ya dorawa abokinsa sai dai a taya shi da addu’a Allah ya yaye mishi, idan banda jarabi na ubangiji ta yaya kyakkyawan matashi kamar Sulaiman zai zauna ya lalace akan yarinya guda daya tayi ta wahalar da shi? Sulaiman ya katse shi tare da fadin,
“Abokina kayi shiru ko wannan hanyar ba mafita bace?”. Iliyas yadan tausasa harshe cikin kyakkyawan kalami ya dafa kafadarsa.
“Ba wani abu kada ka damu zan baka duk wani goyon baya da kake bukata, za mu je ga Safina mu lallameta ko za a yi nasara domin a yanzu na daina ganin laifinka, na gano bakai ka dorawa kanka ba, ba yin kanka bane ubangiji ne ya jarrabeka da son Safina, sai mu tayaka da addu’a Allah ya saka ka cinye Www.bankinhausanovels.com.ng jarrabawar” Yace “Yauwa abokina abinda nake son ji daga gareka kenan”. Cikin hira Iliyas ya janye shi daga maganar Safina ya shiga wata maganar har sai dayaga ya ware yana kyalkyala dariya sannan suka yi sallama ya tafi atlest dai ya rage kaso mai yawa daga cikin damuwar da Sulaiman yake ciki, dama amfanin abotar kenan, kasancewa tare da aboki a kowanne hali na kunci ko na damuwa.
Sai da aka samu kusan sati biyu sannan Sulaiman ya tuntubi Iliyas da maganar zuwa gidan su Safina, sabida tunda suka yi maganar kullum da ita yake kwana yake tashi, kawai ya bada lokaci ne dan kada Iliyas yaga kamar ya fiye

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page