MALIKA MALIK BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 14 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 14 BY JANAFTY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yana Nunata da yatsa cikin Fushi ya Furta”Ashe haka kike Zahra bansani ba,agidan Uban wa na gayamiki zan saki Malika in ta haihu..? Yaushe na taba tattauna wannan mganar dake don Ubanki..? Yafada yana kwalalo mata ido,..

   Daga Zahran har Saleema atare jikinsu ya Fara rawa,Zahra na Dafe da kunci lokaci daya hawaye suka wanke mata Fuska ganin irin Tozarcin da Saleem yayi mata agaban kishiya da yan”uwanta harda zaginta,ganin haka yasa ta jajige Razanarta ta mike ga kanta tana Fadin”Eh mana kazo da borin kunyama Tunda kaga gaban matarkace? in ba kai ka gayamin ba wazai Fadamin ba,ko kasheni zakayi bazan Fasa fadan kai ka gayamin baka Son Malika ba, Baka kaunarta,kai cemin ma kayi baka Kaunar mai kaunar….”Jikake Tim..”!Zahra ta Fadi akasa,wanda Saleem yasa kafanshi ya kwasheta zuwa kasa,kafin ya fara kokarin kwancen belt din wandon Jeans din dake jikinsa cikin Zafin rai da Zuciya yake Fadin.

“Ba malika ne baniso ba,kece bantaba kauna ba Zahra,kuma yau zan tabbatar miki da cewa Na tsaneki…!..”Yafada yana kwanto belt din Malika ce ta mikama Joda Ayda ta isa gareshi tana Riko hannunshi take Fadin”Plz mallam A’a kada kafara ba mutumcinka bane,juz leave her,ka barta da Halinta..”Fizge hannunshi yayi har sai da Malika ta kusa Faduwa ko,sai da tayi da gaske,ta iya tsayuwa bisa kafafunta dakyau.

  Bai Saurari Malika ba,ya shiga Tsulama Zahra belt din ba ji,ba gani yana Fadin”Zaki fadamin waya gayamiki kokuwa haryanzu kina kan bakanki..”Yake Fada yana Shimfidamata belt din ta ko’ina,Itako Tun tana Dauriya Harta Saki baki tana ihu da kuka,Joda ko sai dariya take ranta yayi mata Dadi,Malika ce idanuwanta ya cika da kwallah don ita bata saba ganin Tashin Hankali ba,Wajen goggo Hadiza ta nufa Tana jan hannunta take Fadin”Goggo don Allah ki saka baki,kiba mallam Hakuri don Allah ya bar dukannta..”Goggo Hadiza tace”Ki rabu dashi Yanzu ko nayi mai mgana baji zai yi ba,kema kiyi Shuru da Bakinki..”

Dole Malika tayi Shuru tana Raba ido itako Saleema jikinta ne yakara Daukan mazari saboda tsoro ta Rakube jikin bango tana rawan sanyi da makyaryarta tana Tsoron kada Zahra taji duka tace abakinta taji,ai tasan yau kwananta ya kare,itako Zahra ganin zai mata illah ne yasa ta Rike belt din da hannuwanta duka biyu tana kuka take Fadin”Wlh ba kai ka Fadamin ba,zan Fada…!Zan Fada wlh…”Take Fada tana kuka kamar wacce ake zare Ranta,.

Idanuwanshi Jawur,yace mata”Ki yi hanzari sanar dani wani munafikin algumgumin ne ya sanar dake wannan mganar,har kike jifan Matata uwar ya’ya da ita,ki sanar dani Wanene ko wacece…? Ya Fada cikin Tsawa Zahra na Sosa gefen kunnenta inda Belt ya sameta,😂kallon Saleema take wacce ke girgiza  mata kai alamar karta Fada,ganin haka yasa Saleem ya Ware ido yana kallon Saleema yana Fadin”Au kece Don Ubanki…”?Yafada cikin Tsawa da Tambaya yana nuna ta da belt din dake hannunshi.

Saleema ta fara ja da baya tana mannewa jikin bango take Fadin”A…A

1 2 3 4 5 6 7Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE