Hausa Novels

RAWANIN TSIYA CHAPTER 6 BY FADEELAH

RAWANIN TSIYA CHAPTER 6 BY FADEELAH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

3 days later!!+

BUGAJE INDUSTRIES

KANO- CENTRAL

Zaune yake a ofis dinshi yayinda yake qoqarin kammala project dinshi na online course din da yake yi.

It’s been 3 months kenan da yayi registration na wani advanced course mai suna Strategic Business Analytics a ESSEC Business school na qasar France. Sadiq dai yayi Online business courses dayawa, wannan yana daya daga cikin abinda ya sanya ya zama professional when it comes to business dealings. A yanzu haka wannan particular course din ba kowa ne zai iya yin shi ba domin kuwa sai kana da wasu special qualifications.. Course din yana da bala’in wahala sannan ga tsada. Lokutta da dama Sadiq yakan yi da-na-sanin yin course din saboda yana draining mishi energy da time sossai.. though he has gained alot from it don kuwa it’s an advanced business strategy wanda yake applying in both companies that he is running toh amma dai kawai ya gaji.3

Ranar Saturday da Sunday ne za’a yi presentation na final project through Zoom wanda daga shi an gama sai karbar certificate. Sossai ya qagara a gama ya huta.7

He has spent alot of his time and energy, infact harda sleepless nights in order to get his project done.. Yanzu haka yana finishing touches ne and going through to correct the minor errors he’s made..

Hanifa ce ta shigo office din kai tsaye ba tare da tayi sallama ba balle ta qwanqwasa qofar.. ita dai Suzan tun tana zuwa tana ba Sadiq haquri akan yadda Hanifa take shiga ofis dinshi har ta daina tunda dai ta kula ‘yar mai kamfanin ce kuma da alama bazata taba dainawa ba.

Wasu files ne na gani a hannun ta yayinda ta qaraso wurin shi tana hararar shi ta zauna ta tura mishi su gaban shi a wulaqance ba tare da tace komai ba.

Har yau idan Hanifa ta tuno yadda Sadiq ya barta ta kwana a Cell ji take yi kamar ta shaqe shi.. A yanzu haka sai gabza mishi harara take yi wanda bai ma san tana yi ba!

Sadiq wanda as usual bai dago kai ba balle ya kalleta ne yake mamakin halin banza irin na Hanifa.. and this brought him back to the conversation he had with her Dad 3 days ago.

A ranar dai Sadiq ya lallaba Paapa ne ya ce mishi zai yi tunani akai and he will get back to him.. he couldn’t say no amma kuma its definately a NO.. Babu yadda za’ayi ya dauki yarinyar da ya tsana ya kai ta gidan shi.. dukda kuwa dalilin yin haka is something he’d love to do amma still.. Tsanar da yayi ma Hanifa is just out of this world.4

Addu’a yake yi akan Allah yasa kar Paapa ya qara dauko mishi zancen wanda in less than a month da ya rage mishi ya tattara yayi tafiyar shi..

Hanifa wadda take zaune tayi zooming takardun da suke gaban shi da kuma manyan litattafai na Business.. hakan ya tabbatar mata da lallai karatu yake yi.

Bata ankara bane ta ji wayar shi tayi ringing yayinda ta ga ya duba..

Video call ne from his Mini-Me

Answering yayi tare da saita wayar da kyau a kan phone stand yadda zata dinga ganin fuskar shi.. Ko da na leqa, fuskar wata kyakyawar cute yarinya na gani, tana yanayi da Sadiq amma ta fi shi haske.

“Assalamu alaikum” ta fada cikin zazzaqar muryarta mai masifar dadi.

“wa’alaikis Salam Asma’ul Husna sarauniyar mata” ya fada yana murmushi.

STORY CONTINUES BELOW

“ni fa ba wani dadin bakin da zaka yi mun Big B.. ina ta jiran call dinka na ji shiru and I called you baka yi picking ba.. I am sure kunyi waya da Ya Hanan” ta fada cikin shagwaba

“hey my love yi haquri.. Your Big B has been soo busy with his project, remember I told you cewar gobe da jibi ne presentation din mu? infact mine is tomorrow.. Gani nan ina qoqarin in kammala ne. kiyi haquri I swear I was gonna call you.. kin san Big B cannot survive a day without hearing from his Mini”

Hanifa wadda take sauraron su da farko tayi zaton budurwar shi ce wanda har tana mamaki ya bar conversation din open tana ji amma kuma yadda sukayi addressing juna da ‘Big B’ and ‘Mini’ ne ya sa ta gane qanwar shi ce… Haka kawai sai ta ji sun bata haushi, ko meyasa???

Murmushin Jin dadi na ga tayi sannan tace “I missed you alot Big B.. rabona da ganin ka fa kusan five months.. tunda ka fara zama a Kanon nan baka qara zuwa Switzerland ba unlike before that you come even twice in a month..”

“Sorry my love.. you know abokin Abba needed my help shiyasa amma I am almost done here  plus ke ma ai saura two weeks ki gama Zurich ku dawo gida and we will all be back together insha Allah”

“Yes Big B.. wallahi na qagara in gama mu dawo. Dagaske a Nigeria zan yi Masters dina and please don’t say no”1

Murmushi yayi yace “I wont my love, duk abinda kike so shi za’ayi..”

“Yauwa, thank you so much, you are the best big brother and I love you”

“You are the best little sister and I love you too Mini-Me.. and please kiyi karatu sossai, I just dont want you to pass, I want you to graduate as the best student in Zurich.. please do make me proud”

“Insha Allah Big B, I wont let you down”

Murmushi yayi yace “thats my Mini, Now can I get back to my project work??”

“Yes you can..”

“toh ki gaida mun da Naana, ki ce mata I love her to the moon and back and that I will call her later”

Shiru tayi bata ce komai ba yayinda take kallon shi tana ta turo baki..

Murmushi yayi yace “Okay, Okay.. I love you too my dearest Asmy, more than life itself and I will call you too later”

Murmushi tayi tace “I love you”

“bye???” ya tambaye ta

“No”

“what again Mini??”

“My kiss”

Gani nayi yayi mata blowing kisses yayinda ta cafke tana murmushi tace “thank you Big B, Bye”

“Bye”

Bayan ya kashe wayar ne ya cigaba da project dinshi yayinda Hanifa take zaune…

Wayar shi ce ta qara ringing.. Ko da ya duba sunan productions Manager ya gani – Isma’il

Yana answering ne yace “Mr Isma’il how is it going??”

Shiru yayi yana sauraron abinda Isma’il din yake fadi.

Ji nayi yace “ah okay, I am coming” sannan ya kashe wayar ya miqe tsaye..

Da sauri Hanifa ma ta miqe tace “ban gane ba.. ya za’ayi in shigo ofis dinka in dade a zaune sannan ka dade kana hirar banza a waya ka kasa tambaya na what I’m here for and now you just stand up and leave me here??? like what do you mean??”1

Sadiq wanda ko kadan bai bi ta kanta ba ya nufi mini lounge dinshi ya dauki wani file da yake kan centre table sannan ya wuce zai fita..

“You need to sign these papers now, its urgent” Hanifa ta fada da sauri da ta kula dagaske fita zai yi ba tare da ya saurare ta ba.

STORY CONTINUES BELOW

Har ya bude qofa ne na ga ya juyo ya kalle ta sannan yace “leave them there, idan na dawo zanyi signing. if they were urgent you would have asked for my signature as soon as you came in instead of sa mun idanuwa da kika yi kamar mayya”4

Daga nan ya juya ya fita yayinda ya bar Hanifa tsaye cike da mamakin kalaman shi…

Ranta ne yayi mugun baci.. wato dai Sadiq baya taba missing opportunity na ya wulaqanta ta..

Ni kuwa nace ke kina missing ne???2

tsaki tayi sannan ta wuce ta fita.

********************

Hanifa dai har ta shiga ofis dinta ta zauna sai kawai ta tuno da kalar wulaqancin da Sadiq yayi mata..

Zaraf na ga ta miqe yayinda ta fara kai da komowa a tsakar ofis dinta..

Ji nayi tace “this is enough Hanifa.. dole in nemi abinda zanyi mishi da zai bata mishi rai shima, bai kamata in barshi ya dinga wulaqanta ni ba yadda ya ga dama simply because da kudin shi ake running kamfanin nan..”

Cak na ga ta tsaya yayinda ta saki murmushi tace “I know what to do” Daga nan kuma na ga ta wuce ta fita da sauri.

Ni kuwa nace ina zata je??

Ko da Hanifa ta fito daga ofis dinta gani nayi ta wuce ofis din Sadiq straight.. Tana qoqarin shiga ne Suzan tace “Ma’am he is not back..”

“I know, I just want to pick up something I left” ta fada ba tare da ta jira jin abinda Suzan din zata ce ba ta shige ofis din.

Da sauri na ga ta nufi desk dinshi ta zauna kan kujerar shi ta janyo Macbook dinshi..

Project work dinshi da yake yi ne akan screen din.. briefly na ga tana ta scrolling tana kallon abinda yayi. Dukda she is not familiar with abinda ta gani ta sani cewar it’s an outstanding work wanda babu qarya aikin natsuwa yayi shi.2

1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE